CUTARWA COMPLT BY AYSHERCOOL

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 74

9K to 12K   out of 219.4K words

masa Wawainiya, kuma kin ga shi Wan boko ne, iya ta ce sai na bi su Rabiu kudu neman kuWi, bana son yin nesa da ku, amma na fuskanci idan na cigaba da zama a haka, wahala zamu cigaba da sha""."

"Mariya ta nisa ta ce ""To, ni dai dan ta ni, wallahi baban ummi zan cigaba da ha™uri, komai lokaci ne, amma duk abun"

"da ya shafi umarnin iya, babu ruwana a ciki, Allah ya taimaka ya bayar da sa'a, ummi kam za ta yi gwagwarmaya wadda sai dai mu bata gudunmawa ba zamu iya tare mata ba."

"""In sha Allah komai zai zo da sau™i, kuma zai wuce umminmu zata rayu cikin farinciki"""

"""Allah ya sa"""

"Ya amsa mata da ""Amin"""

"Abu kamar wasa, Iya ta din ga yi wa balarabe kwarmato, a kan lallai ta yi magana da Rabi'u ma™wabcin su, lallai ya"

"nemo kuWi, ya bi shi lagos, ya Wora shi a kan hanyar neman arziki."

"Bashir ba shi da kuWin da aka ce ya tanada, dan kuwa rabi'u cewa yayi ya tanadi dubu Wari, harkar fawa yake a lagos,"

ya je ya koya masa.

"Ya ce wa iya ba shi da halin kuWin nan ta ce ""Ai dama ba zaka yi su ba, Allazi babu wanda ya karSo jakadancin talauci zuwa duniya, ka je ka tambayi ilyasu, ko sagir, ga saminu, ko Yahaya, tun da su masu zuciyar nema ne, kuma ba a"

"rasa nono a riga, su baka aro."

"Bashir baya son dalilin da zai sanya ya keta billensa ya nemi alfarmar ´an uwansa, saboda yadda ba sa yi da shi."

"Amma bisa ga umarnin iya, ya tambayi sagir aron kuWi, amma ya kada baki ya ce ""In ara maka kuWi, ka biyani da me?"

"Gaskiya ba zan iya ba, kuWin nan masu wahalar samuwa, na baka in yi sadakar dole da ba niyya, kayi ha™uri kawai"". Ya ji ciwon abun da yayi masa, amma ya dake ya gayawa maman ummi."

"Ita kanta mariya abun yayi mata ciwo, abun da iya take musu ya sanya ta tsane ta, duk da ita ta haifi mijinta, tattara"

"samirun ta, har da zobenta da aka saya mata lokacin aure ta sayar, sai ganinta yayi da kuWi, dan ita kanta wula™ancin da ake yi masa yana bata haushi."

Ya din ga yi mata faWa a kan sayar da kayanta da tayi.

"Ta ce ""Idan har tafiyarka zai sanya iya farinciki, a daina wula™anta mu, ka tafi kawai Allah ya tsare"""

"Ya ri™e hannunta ya ce ""Na gode mariya, Ubangiji Allah ya saka miki da alkahirin sa, ya ™ara miki ha™uri, kada Allah"

"ya sa na ci amanarki, ko a yanzu ko a gaba, Ubangiji Allah ya kula mini da ku"" haka ya din ga zuba mata addu'a kamar ta yaye masa gaba Waya matsalolin sa."

"Saura kwana Waya ya tafi, da ya shiga ya fita, sai yayi musu addu'a, ya sanya musu albarka da ita ummi."

"Da daddare mariya ta shirya masa kayansa a wata jaka, tana ta yi masa addu'a. Ya zura mata ido yana kallon ta."

"""Wai wannan kallon fa?"""

"""Da za ace in nuna matar aljanna a duniya, zan nuna maman ummi"""

"Tayi murmushi ta ce ""Zaka fara ko?"""

"""Allah ba wasa nake ba amaryata"" ta kwashe da dariya ta ce ""Ko ba amarya ba, da wannan ´ar tamu nake amaryar,"

"in zo in fara tara kayan Wakin auren ummi, wai wa ya ganni maman amarya ranar auren ummi ba zama""."

"Yayi dariya ya ce ""Kema Win yaushe aka yi naki auren ki ke hango auren ummina, in sha Allah sai ta yi karatu mai"

"zurfi, Allah ya sa kan na tafi Win nan akwai rabo a cikin nan, ummi ta samu Wan uwa"""

"""Amin ya Allah, ni kaina ina son jariri wallahi"""

"""To Allah ya bamu mai amfani, ya bani kuWi na halal na wadata ku, mu rayu cikin farinciki"""

"""Amin, amma yanzun ma Alhamdilillah, ai kuWi ba su ne farinciki ba"" sosai suka din ga hira, tana ce masa ban da"

"kallon matan yarabawa idan ya tafi lagos, ya din ga yi mata dariya."

"Har ta yi barci, amma shi ya kasa bacci, ya tashi daga kan gadon, ya koma shimfiWar ummi, da ta yi nisa a baccinta"

sosai.

"Ya kunna fitila yana kallonta, sam bai ga munin ´ar sa ba da mutane suke faWa suna zuzutawa."

"Ya din ga shafa gashin ummi, yana kallonta."

"Mariya ta yi juyi ta hango shi, ta ce ""Baban ummi, ko saka maka ita zan yi a jakar ka ku tafi, wannan ™auna haka?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Ko yara nawa zan haifa ummi ta daban ce a zuciyata, ina ™aunar yarinyar nan"""

"Mariya ta ce ""To kar dai ummi ta mamaye ko ina a zuciyar, a rage mini wuri"""

Yayi murmushi yana cigaba da kallonta.

"Juyi ummi ta yi taga hasken fitila, Wan razana ta yi, saboda haryanzu ba ta manta yadda aka yi mata fyaWe ba, dan"

"daren da aka yi mata fyaWe ta tuna, da ™arfe ta ce ""Baba"""

"Ya ce ""Na'am ummina"""

"""Kai ne"" tayi maganar tana shafa fuskarsa."

"""Eh Ummina"""

"Ta ce ""To"" ta cigaba da lumshe ido zata koma bacci."

"""Ina ™aunar ki ummina, Allah ga ´a ta da mata ta, Allah ka kula mini da su, ´ar kyakywar Wiya ta"" yayi maganar yana"

jan kumatunta. Ummi ta Wora hannunta a kan nasa tana murmushi ta cigaba da bacci.

"Washegari da zai tafi har soro suka raka shi, ji yake tamkar kar ya tafi, amma yana fatan idan har tafiyar ta sa zata"

zama silar walwalar iyalin sa gara ya tafi.

"Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana neman yi musu tijara, sannan suka rabu ya"

tafi.

"Kwanaki uku da tafiyar baban ummi, kewa duk ta ishi ummi da mariya, sai dai tafiyar ta sa bata sanya sun samu"

"sassaucin jaraba da masifar iya ba da gore-gore, gashi a lokacin waya bata yawaita ba, dan haka ba wanda ya san halin da wani yake ciki."

"Bai fi sati biyu ba da tafiyar sa, abun da ya bar musu duk ya ™are, gashi abu kamar wasa, muraran yara ke cigaba da"

"cin zalin ummi, ga farmaki da Idris yake cigaba da kai mata, loka-lokaci da wasu daga samarin gidan, dan ma yanzu ta yi wayo sosai da sosai, da ta gansu sai gudu."

"Cin zali a wurin ´an samarin yaran nan maza, tamkar sun samu sa'ar su, saboda tana mace, abu kaWan sai a kai mata"

"duka, ko ayi mata wata izayar ko a gida ko a makaranta, saboda ana ganin ummin tamkar sokuwa, kuma babu mai tare mata, da mariya tayi magana iya tayi kanta da tijara."

"Šan abun da ya rage a hannunta, ta fara fanken sayarwa, saboda ta samu abun juyawa, amma sai da iya ta cinye"

"jarin da cin bashi, tare da tula mata ayyukan da zasu hanata sana'ar."

"Abubuwa fa suka fara yi wa mariya da ummi yawa, duka ko ta ko ina, wani ta iya karewa, wani ta kasa sai dai tayi"

kuka ta gaya wa Allah.

"Tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta samu da ™yar ta ji™awa ummi garrin kwaki, bayan ta dawo daga makaranta"

"tana sha, ta ji hayaniya ta yi yawa a waje. Bata damu ba ta cigaba da aikinta."

"Da gudu Alhassan ya shigo ya ce ""Babar ummi Albishirinki?"""

"Ta kalleshi ta ce ""Albishirina kuma? Menene?"""

"""Wai baban ummi ´an fashi suka kashe a hanya, zasu taho gida daga ikko!!!"""

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724

Arewabooks ayshercool7724

YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

P4

"Wani irin jifa mariya tayi da kwanon hannunta, ta mi™e a gigice jikinta na wata irin tsuma, zuciyarta na bugawa da"

saurin gaske amma ta kasa magana.

"Mi™ewa ummi ta yi ita ma, tana bin su da kallo."

"Iya ta fito a gigice ta ™undumawa Alhassan ashariya ya ce ""Uban wa ye ya gaya maka haka? In ji wani Wan iskan""."

"Ilyas da saminu ne suka shigo, fuskokin su babu walwala."

"""Ku gyara wurin da za a shigo da balarabe, Allah ya yi masa rasuwa, tun safe muka tafi Waukko gawarsa"""

"A gigice iya ta ce ""˜arya ne ban yarda ba, ya za ayi ace ya mutu? Balaraben ne ya rasu? Waye ya kashe shi, ya aka yi"

"aka kashe shi?"""

"Sagir yayi sallama tare da idris, ya ce ""A ina za a kwantar da shi idan an shigo ne? Ana jira fa"""

"Mariya ji take abun kamar mafarki, addu'a take Ubangiji Allah ya sanya mafarki ne, Allah ya sa ba mijinta ne ya mutu"

"ba, Allah ya sa ba baban umminta ne ya mutu ba""."

"Magaji ya shigo da tabarma, ya shimfiWa, aka yi sallama tare da ´an sanda, da rabi'u da suka tafi tare, aka shigo da"

"gawar bashir, tana ta Wigar da jini."

"Nan da nan gida ya cika da jama'a, Iya sai ihu take tana kururuwa tana kuka, kai da gani ka san jahilci ya samu gidin"

"zama a wurin iya, saboda yadda take ihun ta shiga uku ta lalace."

"Jiki na rawa mariya ta saka hannu ta buWe mayafin da aka rufe gawar bashir, fuskar nan fayau kamar yana bacci, kamar wanda yayi wanka ya fito haka gawar take, ga ™irjinsa in da aka harbe shi, jini yana ta zuba."

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" shi ne abun da mariya ke ta nanatawa, tare da fatan Allah ya saukar mata da"

nutsuwa da dangana.

"Ummi ta shafa fuskar sa tana faWin ""Baba ka tashi, baba ka tashi daga bacci mama tana kuka"" cikin haWe rai sagir ya"

yi wa ummi tsawa ya ce ta tashi.

"Sa'adatu ta ce ""Haba baban auwwalu, ka tausaya musu mana""."

"Mutane suka cika gidan dan™am, saboda mutane sun san bashir sosai, mutum ne na mutane mai matu™ar ha™uri da girmama mutane."

"Sai ajiyar zuciya kawai mariya take yi, tana rungume da ummi, aka shiga da shi Wakin Iya, aka yi masa sutura, sannan"

aka ce su je su yi sallama da shi.

"Har a lokacin mariya ta gaza zubar da hawaye, sai wata irin ™una da zuciyarta ke yi mata, abu kamar wasa bashir"

"shikenan an yi an gama, rayuwar ta ™are."

"Duk da yarinta ta ummi, amma ta san idan an mutu ba a dawowa, tayi kuka idonta duk ya kumbura, ta dinga taSa"

"shi tana ""Baba ka tashi, ka ce zaka sai mini ´ar tsana in yi addu'a ka samu kuWi, kullum ina yi maka addu'a"""

"Mariya kam zubawa gawar ido kawai tayi, tana kallon ikon Allah, wai bashir ya mutu."

"Sa'adatu ta ce ""Mariya ki ri™e yarinyar nan, za a shigo a Wauki gawar"""

"Mariya kamar sokuwa, dan kamar ma ba ta iya gane me ake cewa."

"Aka zo aka Wauki gawar bashir, ana ta iface-iface, ummi ta ri™e ™afar Saminu wan mahaifinta, da suka Waga gawar, tana wani irin kuka, amma babu tausayi ko imani, ya angije ta ™asa suka yi waje."

"Allah sarki, ba ta karaya ba ta sake bin su, tana faWin ""Ku dawo da baban, zai tashi fa, bacci yake yi"""

"Surayya, wadda take ´ar autar su bashir, ta ri™o hannun ummi tana kuka, ta rungume ta, tana ta rarrashinta."

"Gida ya cika da jama'a ana gaisuwa, mariya kuwa ta samu gindin bishiyar da ke tsakar gidan ta rakuSe, tayi shiru ba"

"ta cewa komai, ita kaWai ta san azabar da zuciyarta take yi mata."

"Bata san hawa ba, ba ta san sauka ba, ta ji muryar iya na bala'i a cikin mutane ""Dama ya za ayi mutuwar ta dame ta,"

"ai dama ba dan Allah take zaune da shi ba, kalleta a ™e™ashe ko kuka ba ta yi ba, alhalin ita ta takura lallai ya tafi neman abun duniya, ya zo ya wahalta mata, wallahi ban yafe miki ba"""

"Daram! Gaban mariya ya faWi, jin abun da iya ta faWa na ™arshe."

"Mutane suka shiga salallami, surayya ta ce ""Haba iya, haba iya, baki san kukan zuci yafi kowanne ™una ba, gara ke"

"kin yi kukan, ita kaWai ta san me take ji a zuciyarta, da can ba ta ce ya tafi neman kuWi ba, sai yanzu, dama Allah ya yi ajalinsa a can za same shi""."

"Ai nan ta mayar da faWan kan surayya, wanda hakan ya tilasta mata yin shiru, wasu suka goyi bayan iya saboda"

"makira ce, wasu kuma suka goyi bayan mariya, kowa ya san kusan halinta Waya da mijinta, ba sawa ba fitarwa, akwai ha™uri da juriya, mussman a zamanta da iya."

"Yadda ta ga rana haka taga dare, abu goma da ashirin, ga raWaWin mutuwar mijinta, ga sharrin da iya ta ™ulla mata,"

"wai ita ce silar mutuwar sa, ita ta hura masa wuta ya tafi neman kuWi."

"Ta rasa me ta tsarewa iya, take yi mata wannan azababbiyar ™iyayyar, saboda kawai tana auren Wan ta, abun da ba"

"haka take yi wa sauran sirikanta ba, kuma dukkansu babu wanda yake yi mata biyayyar da take yi mata, kawai ta camfata cewar ita ce mai farar ™afar da ta toshe masa hanyar arzikin sa, ya kasa gaba ya kasa baya, gashi ya Wauki son duniya ya Worawa mariya, yana matu™ar son ta da ™aunarta."

"Ko fuskanta Iya tayi sun yi mu'amalar aure, ta ga sun yi wanka, to wunin ranar, haka zata wuni cikin Sacin rai da tashin hankali, a wurin iya ta din ga ™ir™irar mata laifi kenan tana ci mata mutunci, ta rasa wannan masifar, ga uwa"

"uba ummi sunan kishiyar ta ne da ita, wanda hakan ya sa ta ™ara tsanar ummi, ga ´a´anta sun ri™e ta uwa, abun da ta dama suke sha, amma tana masifar kishi da uwar su."

"Washegari da azahar, dangin mariya suka dira a jigawa, suka zo gaisuwa, haka zalika Yahaya, yayan bashir da yake"

"birni, shi ma ya zo ta'aziyya, ya ji mutuwar bashir ba kaWan ba, abun ya girgiza shi, dan kaf cikin ´an uwansa, ko wanda suke ciki Waya, basa shirin da suke yi da bashir, saboda biyayyar sa, yana matu™ar girmama shi."

"Yana son ummi, kasancewar sunan mahaifiyarsu ne shi ma da ita, marigayiyya uwar gidan malam hashimu."

"Ya tarar ana ta fama da ummi, ba ta ci abinci ba, sa'adatu da ba wani shiri suke yi da mariya ba, amma mutuwar"

"bashir, da abubuwan da iya ke ta yi, ya sanya wani irin tausayin su ya kamata."

"Yahaya ya ga yadda ake fama da ummi, tana kwance a jikin mariya, ba wanda ya iya cin abinci a cikinsu."

"Duk da tana tsoron maza sosai da sosai, kuma shi baya yawan zuwa gidan, amma ta gane shi, dan yana kama da"

"babanta sosai, kuma yana bata tsaraba idan ya zo."

"Ya ™arasa ya Wauketa, ya saka hannunsa a nata, ya ce ""Mamana, ki din ga yi wa babanki addu'a, kuma ki din ga cin abinci, kuka ba zai yi magani ba"""

"""Baba ba zai dawo ba ko, ya mutu wai?"" Tayi maganar hawaye na zubo mata, kamar an kunna famfo."

"""Ba zai dawo ba ummi, amma zai ji daWi idan kina yi masa addu'a"""

"Cikin kuka ta ce ""Na fi son ya dawo"" ya din ga share mata hawaye, cike da tausayawa."

"Sai dai yayi mamakin yadda iya ke ta hantarar mariya, tana cikin alhinin mutuwar mijinta, ga ´an uwanta a gida,"

amma iya na ta masifa da nanata ta kashe mata Wa.

"Ya dubi Iya ya ce ""Haba iya, haba iya da wanne za ta ji? Ya za ayi ta yi sanadiyyar mutuwar mijinta, mijin da suka yi"

"auren soyayya, shekara bakwai tare, ko sulhu ba a taSa yi musu ba, ki ce ita ta kashe shi, ga ´an uwanta a gida ai babu daWi"""

"""Yahaya, ni fa nake zaune da yarinyar nan, ni na san abubuwan da take aikatawa, azabar son zuciyarta ya sanya ta"

"hura masa wuta ya tafi neman kuWi, gashi nan ya mutu a banza, yaron nan ha™urin zama yake yi da ita"""

"Yahaya ya ce ""A'a iya, idan na zo fa muna hira da bashir, a bar kaza cikin gashinta kawai banda tone-tone, amma"

"batun ace mariya ce ta kashe mijinta bai taso ba, dan Allah ki bari ta ji da alhinin da take ciki"""

"Kasancewar yana da abun duniya, domin kuwa lecturer ne shi a kano, kuma albashinsa da tsoka, dan haka yana yi"

"wa iya sha tara ta arziki, a dole ta ja bakinta ta yi shiru."

"Wasa² magana har waje wurin maza, iya ta tubure tana cin mutuncin sirikarta, wai ita ta kashe mata Wa."

"Yayan mariya har cikin gidan ya shiga, ya yi wa mariya wankin babban bargo."

"""Irin tarbiyyar da aka baki kenan dama mariya? Irin zaman da ki ka yi da mijinki kenan, ki kasa zama da shi a yadda yake, ki hura masa wuta ya tafi ajali ya riske shi, kuma gashi an Wora miki, an ce ke ce sila. Mariya kin Sata wayonki, wannan ba tarbiyyar gidanmu ba ce ba, kuma ahalinsa ba zasu taSa mantawa da abun da ki ka yi ba"". Kasancewar yana cikin manyan yayyenta, kuma tana bala'in tsoronsa, dan haka ba ta iya kare kanta ba sai kuka, ga shi a gaban mutane ya din ga yi mata faWa, mariya ta rasa da wanne za ta ji."

Iya kuwa ta samu damar cigaba da ™ullawa mariya sharri a wurin yayanta.

"Yahaya ya tsawatar, saboda shi Wan boko ne, ya ce ba zai yiwu a saka mariya a gaba ace ita take aikata duk wannan"

"laifukan ba. Idan ma haka ne tana matsa masa kan ya rasu yanzu yana ina? Kuma ai mijinta ne, tana da right na ya yi mata abun da take so."

"Šakinta ta shiga ta zauna, tayi kuka, tayi kuka, har zuciyarta ta fara raya mata ko kashe kanta zata yi ta huta da"

wannan azabar.

"Ummi ta zo tana kuka ita ma, dan tun ana yi mata faWan nan ummi take tayata kukan, ta din ga share mata hawayen tana cewa ""Mama ki yi ha™uri, ki daina kuka"" ita kanta yayar mariya, ta san mariya ba za ta aikata haka ba, yadda iya"

"ke yi wa mariya a gaban su, ba ™aramin ™ular da ita yayi ba. Sai dai su al'adar gidan su, muddin ak kawo ™ararka daga waje, ba a taSa goya maka baya, balle kuma a gidan aure, idan miji gutsurar namanki yake yana ci, sai ace ki je ki cigaba da ha™uri, wataran sai labari, kowa ha™uri yake yi."

"Maryam ta tambayeta ina samirunya, ta ga duk babu? Mariya ta™i gaya mata, ta shashantar da zancen."

"Bayan kwanaki uku da share zaman makoki, ´an nesa suka watse, sai masu shigowa jefi-jefi gaisuwa, yayar ta ta"

"zauna da ita, ta Wan din ga Webe mata kewa, zuwa kwana arba'in, aga meye abun yi."

"Gaba Waya mariya ta gama fita daga hayyacinta, kai daka ganta ka san tana cikin alhini, ko abincin kirki ba ta iya ci. Salla kawai take iya

4 / 74