Author : LEEMA Category : KDP NOVELS
Binta tayi adu'a ma iyayenta kamar yadda ta Saba sanan taci amala kadan tasha magani nan ya buge ta sai bacci kamar saboda tsoro ko tsakar gida shukura bata fita hira ba bare wurin Bobby.
Tun daga ranar shukura ta saukaka ma baby kulawa na musamman take bata,abinci akai akai,itace ke mata wanka,ta wanke kayan baby duka ta goge ta mata kitson rubber Mai kyau komi ta samu baby ce har mijinta ya dawo daga Katsina lokacin hanun bai gama cikewa ba amma suna zuwa dressing a wani Chemist kusa dasu"tambayar duniya shukura taki sanar dashi abinda ya samu baby,itama baby daya tambaya tace babu komi gajia yayi ya kyale su cike da zumudi ya faɗa ma baby papan ta zai zo karshen sati su tafi tare",ai kuwa ta shiga murna sosai tana farin ciki zata rabu da wahala.
Yanzu alhamdulillah babu abinda baby ta rasa gidan taufeeq sai ilimi domin babu boko babu islamiyya,data gama kama ma shukura aiki taci gaba da zaman banza saboda bata da abokiyar hira sai Safiyya wace rabin labarin ta gulman yan gidan ne!
"""Yaya Mallam ba shirin zuwa Kano ne wani aiki ya taso musu na gaggawa kuma yana ɗaya daga cikin wa'yanda aka zaba zuwa dajin nan wanda zasu shafe watanni a ciki,waya ya Daga ya kira taufeeq yana ƙara bashi hakuri akan ya kara rike mashi baby har ya dawo zai Turo mashi wasu kuɗaɗe ya ƙara wurin hidimar baby,,,godia sosai yayi ma Yaya Mallam irin kulawar da yake dasu akan baby,fatan alheri yayi ma yaya Mallam da adu'a samun nasara akan abokan gaba suka kashe wayan"abinda keba taufeeq mamaki tunda oga aminu ke kira bai taɓa tambayar lafiya baby ba ko yace a bata waya suyi magana!
shukura kam tun tana ɗari ɗari kada hajia Balki ta dawo gidan mijinta yasan zalunci da tayi ma baby har aka kwashe wata ɗaya bata dawo ba ta saki ranta idan muguntan ya tashi mata tasa babu aikin abinci da diban ruwa wani lokaci hadda wankin under Wears nata, boxer da singlet na taufeeq.
"""Alahi habu ya samu kawu shi da maganar ammie bai boye mashi komi ba akan rayuwar ta sanan ya sanar dashi kuɗi rin auren ta da yake dashi,"kawu idrisu yaji daɗin wanan kudirin na alaji habu ko babu komi zai ceto rayuwar ta daga halaka ta hanyar raya Sunnah,ya nuna mashi ya kamata suje ga iyayenta kamar yadda ta fadi tunda umman ta nada rai a daura aure can,alaji yace yafi so kawu idrisu ya zama waliyin ammie a daura auren daga baya zasu tafi ga iyayenta,yace Allah mana jagora...,tun daga lokacin aka fara shirye shiryen auren ba wani shagali dai za ayi ba amma alaji ya saki kudi saboda saura wata ɗaya ta kamala istibra'i a d'aura aure,tare da uwar masu gida suka haɗa lefe daidai yada take so,ga gyaran jiki tana shan shi hadda na hauka komi saya ake ana durama ciki,ana cusa ma gaba saboda alaji habu.
Lokacin da alaji habu yaje ma matar shi hajia mariya da maganar aure ko a jikin ta domin tasan babu abinda ta rasa a gidan mijinta kuma ba wuri ɗaya zasu zauna ba menene matsalar ta,fatan alheri kawai tayi mashi.
Rana bata karya sai dai ita d'iya taji kunya ranar juma'a bayan sallar juma'a aka daura auren HADIZA AMINU(AMMIE) DA ALHAJI ABUBAKAR MAGA(ALAJI HABU)akan sadaki Naira dubu hamsin,bayan daurin Aure aka gabatar da walima na cin abinci a gidan gonan shi...,can gidan kuwa yan daudu da yan bariki sun cika ana ta shagali sai kida ke tashi ana cashewa ita kam ba'baa mairo sai mamaki take ina ammie ta samo wanan zugan tsiyar,amarya tasha kwala na kece raini ta zuba gwala gwalai sai sheki take ana ta shagali har dare lokacin daga amarya sai ba'baa mairo wacce ta ƙara gyara gidan,Alaji babu ya shigo da sallama hanun shi riƙe da leda, ba'baa mairo na kitchen tana wanke plates da suka b'ata suka gaisa ya haura sama amarya na zaune saman gado cikin wani boyl less Mai ɗaukan ido tasha kwaliyya sosai da sallama ya shiga d'akin sai fashe wa tayi da kuka sosai kamar wace aka aiko ma sakon mutuwa...!!!
_Halimatus Sadiya Muhammed_
*LEEMA
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
~sensational Heart touching story~
*BY*
*LEEMA*
_DEDICATED TO KANO STATE_
*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..
~🅿21-22~
A hankali yake takawa har zuwa inda take ya zauna saman bed leda dake hanun shi ya aje saman chest of drawer sanan ya rungumo ta yana tapping bayan ta har tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya"yau rana ce na farin ciki ba kuka ba yanzu ki tashi muyi alwala mu gabatar da nafila raka'a biyu domin miƙa godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya nuna mana wanan rana....,jiki a sanyaye ta yaye mayafin dake saman kanta ya rik'o hanunta har toilet sai daya fara alwala sanan ya bata wuri tayi koda ta fito har ya shimfida babban darduma yana jiran ta,hijab ta ciro cikin wardrobe tabi bayan shi ya tadda sallah a sujjada na karshe sun kai kusan mintuna goma kowa karon Allah bukatun shi kafin daga bisani ya sallame ya haɗa hanayen shi biyu ya shiga kwararo adu'oi tana amsa wa da Amin har suka shafa ya fuskance ta tare da mata tambayoyi akan addini..?,Alhamdulillah abinda ya shafi shika shikan musulunci,tsarki,alwala da sallah ta bashi amsa dai dai sai ɗan abinda ba'a rasa ba,mikewa yayi ya nufi kofa ya fito har palour ya rufe kofar ya shiga kitchen ya dauko plate da cups ya dawo Da sallama hannu ya mika ya dauko leda da ya shigo da ita gasasun kaji guda biyu ne sai hollandia youghurt ya kalleta amarya bismillah..,"cike da jin nauyin shi tace na koshi kaci kawai,ya kwaikwayi yadda tayi magana shima ya koshi da taga da gaske ba ci zai ba ta saka hannu yana bata a baki tana bashi har suka yi rabin ɗaya ta nuna da gaske a koshe take ya kwashe kayan ya nufi fredge dasu,toilet suka koma a tare suka yi wanka da brush suka fito ko wane daure da towel ta haye can karshen gadon ta kwanta tana karantu adu'a kwanciya bacci,shi kuma yana tsaye yana fesa turaruka har ya kamala ya hawo gadon tare da jawo ta jikin shi yana shafa bayanta a hankali cikin kwarewa tun tana noke wa har ta saki jiki komi ya wakana...
Sun kai wani lokaci kafin su samu natsuwa sanan yayi kissing forehead nata bacci yayi gaba da su sai da asuba suka farka,a gurguje yayi wanka ya nufi masallaci ya bata wuri tayi wanka ta fara gabatar da nafila kafin farilla ta jima sosai cikin sujjada tana adu'oi Allah ya basu zama lafiya da zuri'a dayiba,Allah ya jikan mahaifinta ya bata ikon ganawa da umman ta kafin ta koma ga mahaliccin ta....,koda ya shigo tana karatun Alkur'ani mai girma wuri ya samu ya kwanta har ta kamala ta aje komi cikin girmamawa ta gaishe shi,rik'o ta yayi zuwa jikin shi"amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida..,fari tayi da idanu wace ni fatana Allah ya albarkaci auren mu alaji na,ya amsa da Amin ta ƙara shigewa jikin shi ba'a ɗauki lokaci ba bacci ya kwashe su.
Kiraye kirayen wayan Alaji da ake ta yi akai akai ya tashe su daga bacci tsaki yaja ya mika hannu ya dauko wayan yadda yake amsa wayan zai nuna maka wanda ake wayar da ita tana da matukar muhimmanci,jiki a sanyaye ammie ta shige toilet tayi wanka koda ta fito yabar gidan..., jiki ba kwari ya shirya cikin super wax babban duk da ba make up tayi ba amma taya kyau sosai ta sauko lokacin ba'baa mairo tana kitchen suka gaisa ta kama mata har suka kamala breakfast suka shirya a table ta dawo palour shiru alaji bai dawo ba sai zuwa 11:30am taji tsayuwar motar shi da hanzari ta fito har wurin mota ta tarbe shi ya fito tare da ware mata hanayen shi ta shige jikin shi ya rungume ta tsam yana shaƙar kamshin jikin ta"honey pot u luk stoney,thank U tace suka nufi ciki yana kame kame wai uwar gida ce ta kira shi yara sun damu basu Ganshi a gidan ba shine yaje ya gansu.
Murmushi tayi kawai duk da ranta ya ɓaci,muje break fast na jiran ka...,aush sowie da baki jiraani ba nayi breakfast tare dasu shine ma dalilin da yasa ban dawo da wuri ba"har ga Allah bata ji dad'i ba amma ya ta iya haka zata hakura tunda mijin wata ta aura,ruwan tea kawai ta iya sha ya kwala mata kira ta haɗa mai ruwan wanka babu musu ta taya shi har ya shirya cikin yadi navy blue Mai laushi yace zai tafi can gidan kawu idrisu baƙin da suka zo daga ƙauye yau zasu juya zai sallame su.
Har wurin mota ta raka shi ta bude ya shiga ta zauna saman laps dinshi ta sagala hanayen ta duka biyu a wuyan shi sanan ta haɗe bakin su wuri ɗaya tana kissing dinshi sai da tayi mai isanta tace a dawo lafiya Allah tsare hanya plz don't stay long,jikin shi a mace yace insha Allah I will be back soon yaja motar tana tsaye har ya fita ta sauke nanauyar ajiyar zuciya ta dawo ciki zuwa d'akin ba'baa mairo da sallama ta shiga...,"Barka da rana hajia..?,Barka dai ba'baa y gajiyan aiki..?,babu gajiya hajia kome za'a girka na rana..?,ki huta kawai ba'baa anjima zan girka sai idan kina bukatar wani abu ki girka..,hira suke yi suka ji sallama alamar sun yi baƙi.
Fitowa suka yi ba'baa mairo ta buɗe kofa sai ga mata kusan shida da yara ƙanana daga gani yan ƙauye ne,bayan sun gama shigowa ne driver ya gaishe ta Yana mata bayani alaji ne yace a kawo su suga wuri kafin su koma,tace ok shi alajin yana ina..?,ya wuce gidan hajia(uwar gidan shi),ciki ta dawo suka gaisa da baƙin suna mata bayani yan uwan ne su, murmushi tayi ai driver ya min bayani bismillah ku zauna mana, ba'baa mairo ta dauko masu drinks da snacks,ammie ta dauko foodflask cikin kayan breakfast din su na peepe soup din kifi danye ta aje masu yaran sai wasa suke a Parlor'n wasu har san Centre tables bata ce dasu komi ba ba'baa mairo taba umurni ta daura shinkafa shiga kicaniyar haɗa miya har aka kira sallah alaji bai dawo ba lokacin ta kamala miya ta nuna ma baƙin dakin da baby tayi zama su shiga suyi sallah,ta koma dakin ta tayi wanka ta gabatar da sallah,a gagauce ta shirya cikin geznah skyblue ta zuba gwala gwalai ta fito suka gabatar da baƙi da abinci da drinks sai yaba mata suke tana ki suna faɗin tafi hajia mariya mutunci da kulawa har suka ga driver yace su fito alaji yace motar da zai mayar dasu ya iso...,ta basu kyautar sabulai da turaruka masu sauƙin kuɗi ta raka su har wurin mota suka tafi.
Alaji habu bai dawo gidan ba sai bayan sallah isha'i yace ta shirya zasu fita..,babu musu ta saka Arabian gown marron Wanda yasha stones tayi Rolling veil nashi basu tsaya ko ina ba sai bakin gate din wani babban gida a unguwar lamid'o crescent yayi horn Mai gadi ya buɗe masu girma da faɗin gidan ya ninka nata sau uku riko hanunta yayi har babban palour na gidan yace ta zauna yana zuwa ya haura sama....,"furnitures set biyu ke palour'n saboda girman shi wall paper ne zagaye da bangon palour'n ga set na kayan kallo masu kyau da tsada,sai sanyin Ac da kamshi ke tashi daga gefe tafka tafkan window size hotunan hajia mariya ne rungume da yaranta,wani tare da alaji,wasu kuma ita ɗaya nan ta fahimci gidan uwar gidan shi suka zo nan take gaban ta ya yanke ya fadi ganin irin kyau da tsari na hajia mariya har kusan mintuna talatin basu fito ba har ta fara kosawa da zaman can taji alamar saukowa da hayaniyar mutane koda ta duba,alaji habu ne rungume da yaran shi,hajia mariya na take masu baya cikin shiga na alfarma less din dake jikin ta yakai dubu hamsin banda gwala gwalai tun daga kunen,wuya har hannu zasu kai dubu ɗari biyu sai sheki take nan take ammie ta daburce domin hajia mariya tayi mata zarrah sosai wurin kyau,tsari da kuma wayewa har suka karaso kallon su take suka zauna saman three seater yaran su na rungume a jikin su.
Jiki a sanyaye ta gaishe da hajia..,lafiya kawai tace ta ci gaba da hira da mijinta cikin harshen turanci yaran ma babu wanda yabi ta kanta sai usaman Karami yace da ita "Hello,ta amsa da hey suka ci gaba da zuba ma daddy'n su shagwaba ammie ko yar kallo ta koma har zuwa 9:30pm ta mike tare da faɗin sai da safen ku....
Babu wace ta kalle ta bare su amsa mata,alaji ya kalli hajia me yasa kika yi haka bayan tun a sama munyi dake zaku gaisa...?,tsaki taja saboda me zan gaisa da ita bayan ta aure mun miji tana neman nisanta ka da yaran ka wallahi ba zan taɓa sonta ba ta zauna can gidanta nima ina gida na period...,haba hajia why do u hate her dat much..?,bcuz she's a prostitute pretending to be innocent!!
Yaran ya kala yaga sun zuba mashi idanu yace dasu zai tafi sai gobe nan take usman ya saka mai kuka zai bishi...,faiza da yake itace babba tace U Are not going anywhere shut up,Sarah tace Mummy I hate day bitch and I don't want to see her near us again...Yan hanun yaranta taji suka haye sama alaji na tsaye yana kallon ikon Allah kamar ba itace hajia mariya dakata nuna bata da matsala da auren shi ba lokaci ɗaya duk ta birkita mashi lisaffi duk yadda akayi zugata akayi,jiki ba kwari ya fito.
Ammie na duke ƙasa ta haɗa kai da guiwa tana kuka riko hanunta yayi ta kwace da ƙarfi kada ka sake tabani mugu azzalumi kawai,adalci kenan tunda muka tashi bacci baka zauna ba kana hanyar gidan nan bai isheka ba sai daka dauko Ni aka ci mutumci na hankalin ka ya kwanta,wallahi da nasan haka kake da ban aure ka ba....
Katse ta yayi"enough ammie Dame zanji..?,wani irin cin mutunci kike magana dukan ki akayi ko zagi.. .?,shike nan tunda na auri sarauniyar mata bazan je ga iyalai na ba,for ur information bani da kamar su duk faɗin duniya U can go to hell ,Dama matsalar auren karuwa kenan wacce bata tashi gaban iyayenta ba ilimin addini da tarbiyya bai wa dace ta ba babu abinda ta sani sai kwana da maza,wallahi nayi mugun taimaka maki despite abubuwa masu muni da kika aikata a rayuwar ki na amince da auren ki tun ba'a kai ko ina ba zaki fara tayar mun da hankali,meke jikin ki Banda panko Babu komi ragowar kazamai yaja tsaki!!!
Ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba da jin kalaman alaji habu akanta cike da karfin hali tace" dama nasan rana makamancin wanan zata zo koba dade koba jima sai ka goranta mun,amma ka sani bani ce nace ka aure Ni ba ra'ayin kanka ne haka NIMA Y'ACE kamar kowa kaddarar data ce kawai ta rabo Ni da iyayena badan bana sonsu ko basa sona ba na Barka lafiya alaji habu cikin zafin nama ta nufi hanyar gate Yana Kiran sunanta ko waiwayi bata yiba bare ta amsa har ta fita daga gidan....
"""'''shukura na zaune kofar maman Daniel suna gulman aunty grace kamar yadda suka saba taga shigowar mijinta yana amsa waya har ya shige d'akin tana zaune wurin gulma na cin ta...,baby na zaune kofar su Safiyya tana bata labarin makarantar boko su da zalunci da prefect keyi suka ji muryan taufeeq yana kiran baby...
Da sallama ta shiga d'akin yace ta kira shukura su zo tare....,tare suka shiga ya warware leda daya shigo dashi kaya ne na matasa dai dai jikin baby da takalma biyu.
Ya kalli shukura da baby yace yanzu na gama waya da papan ki yana cikin garin nan tun juya ashe har sun kamala aikin ya dawo lafiya yanzu hutu yake yi,yace a haɗa kayan ki gobe za kubi jirgin karfe goma na safe zuwa Lagos,yanzu zan dauki photon ki a waya na a cire ayi passport dashi...
Murna sosai shukura ta shiga yi domin tasan yaya Mallam yaba mijinta wasu kuɗaɗe kuma zata samu rabonta a ciki...,baby ta rasa farin ciki take yi ko baƙin ciki Ace watannin ta uku a gidan papanta bai taɓa waya da ita ba ko bada sakon gaisuwa a gare ta ba,haka ammie tunda suka damka ta hanun shi basu sake waiwayeb ta ba yau rana tsaka ace zata bishi har wani gari Lagos ko yaya zaman su zata kasance oho...!, taufeeq ya katse shirun nata yana faɗin shukura zata gyara mata kai ta tattara shirya kayanta shi zai fita.
Kuka ta fashe dashi tana fadin uncle Ni ba zan bi papa na ba wurin ka zan zaun...,ya katse ta zaki ji daɗin zama da papan ki domin mutum ne mai natsuwa da kulawa ki share hawaye shukyra zata taimaka maki ki gyara komi naki kinji...?,ta gyada kai ya share mata hawaye sanan ya dauke ta pics har uku da wayan shi ya fita.
Shukura haushi baby taji tana farin ciki Allah ya raba ta da wahala baby nason bijirewa,wurin wata mata kusa da gidan suka bada kayan baby ta wanke na kuɗi shukura ta tsefe mata kai ta mata wani kitson suna ta shirye shirye kafin kace me,shukura ta yaɗa labari cikin gida gobe baby zata wuce ta huta da wahala sai tayata murna ake,Safiyya tace ma baby nikam na tayaki murna zaki bar gidan nan saboda Ibro ya taɓa fada mun wai yadda yake samun yatsa cikin