Author : LEEMA Category : KDP NOVELS
karatun akwai banbanci sosai amma a hankali take fahimta da ta dawo schl taci abinci tayi sallah sadeeyah ke mata lesson a gida zuwa 4pm ta shiga islamiyya idan ta dawo da dare Captain sadiq ke biya masu ita da sadeeyah.
Hankalin baby kwance bata da matsalar komi tana samun kulawa sosai wurin sadeeyah da Captain sadiq wanda ko wane lokaci daya dawo office Yana gida idan ba masjid ya fita ba sai in wani aiki ya kai shi cikin gari ko wani gari shine suke zaka su biyu abun su, sadeeyah bata da irin munafuncin nan na matan barrack Babu ruwan ta da shiga block ɗin kowa tana gidan ta bare azo a turke ta tayi gulma ko munafunci wanda aikin yawan cin matan barikin kenan da an tura mazajen su wani gari wurin aiki Sai a kafa chamber na gulma da munafunci akan turke turke har ayi faɗa.
Yaya mallam kuwa bai sake bi takan Captain sadiq ba bare baby Koda kuwa sun haɗu a office sallama kawai ke shiga tsakanin su tun Captain sadiq na damuwa har abun ya fice mai akai.
Yanzu baby ta zama fes da ita,taɓa mayar da hankali a karatu sosai aikin gida ma ba'a barta a baya ba tare suke yi da da sadeeyah har ta saba da mutane da dama cikin barrack din saboda tana da natsuwa.
Sadiq duk weekend zai tura baby gidan yaya Mallam ta gaishe shi amma da kuka take dawo wa saboda zagi da cin mutumci sai abinda ya manta!
"""Alaji habu bai zame ko ina ba sai gida ya tambayi ba'baa mairo tun wani lokaci ammie ta fita .?,tace ba'a jima ba ci gaba yayi da Safa da marwa shiru shiru bata dawo ba har dare.
Can wurin Uwar masu guba da kuwa bayan ta gama sauraren korafin ammie shawara ta bata da ta daddaka kwalban turare karami har ya zama gari kullum tana Barbada ma alaji habu cikin abinci ki abun sha har ya ƙare"slow poison ne a hankali zai rinka cacakan hanjin shi har su katse ya mutu cikin ruwan sanyi babu wanda zai tuhume ta tunda abun zai dauki lokaci kafin ya rasa ranshi...,cike da farin ciki suka dake kwalban ta dawo dashi gida dama yanzu ta iya driving da kanta take zuwa ko ina.
Tana sallama taji muryan alaji habu yana faɗin"ki koma gidan uwan da kika fito.."dama tasan za'a yi haka tunda ta shigo taga motar shi cikin gidan saboda lokuta da dama idan ya riga ta dawo wa gidan zargi iri iri babu wanda ba ya mata!
Ranta a b'ace ta bashi amsa babu inda zan tafi domin bani wani gida da ya wuce na aure na. ,Aure!,ashe ke ɗin fa matar aure ce kike yawo kwararo kwararo gidan karuwai neman mazan banza kin raina ma mijin ki....
Dakata Alaji habu na gaji da wanan cin fuska naka,har tsawon wani lokaci zan zauna a gidan ka kana kunsa mun baƙin ciki kala kala,na safe dabam na dare dabam,shike nan kuma bani da halin fita sai zargi.???
Ba'baa mairo ce ta fito domin abun nasu ya koma bata haushi tun yana bata mamaki su kenan kullum cikin faɗa kamar ba auren soyayya suka yada ba!!!
Kallon ba'baa mairo yayi"ki faɗa mun tsakanin ki da Allah wace macen arziki zata rinƙa zuwa gidan karuwai da auren ta.?
Shiru tayi domin bata gane inda maganar ya dosa ba...,ammie tace na tafi sai kayi yadda kaga dama dani aure ba dole bane wallahi wanda kadararen auren naka na rashin yan ci!!!
Ni kike faɗa wa haka.?,an fadi idan ka cika haihuwar uwa.....
Ba'baa mairo ta rufe mata baki"a kul na hane ki da Daga harshe akan na mijin ki bare cin mutunci da tuzarci,me kike nufi da cikin iyayen shi.?,so kike ka hawa kanki tsinuwa da fushin Ubangiji.?
Kyale ta ba'baa mairo nima na gaji da zama da karuwa,mara asali da tarbiyya sallaman ta zan yi....
Idan kana yiwa darajar iyayen ka alaji kada ka yanke hukunci cikin fushi ayi hakuri,idan rai ya ɓaci kada hankali ya gushe,kai ne babba a kanta don darajar annabir rahama(S.A.W) ka tafi har zuciyar ka tafi sanyi"tana magana tana nuna mai hanyar waje!
Ammie ta tare kofa ba'baa mairo idan kinga ya bar gidan nan da takardar saki na,dole yau ka sawake mun wanan kadararen aure nashi....,kina jinta ki ba'baa mairo.?
Alaji idan har na isa da kai ka fice a gidan nan,jiki a sanyaye ya fita daga palour'n ya shiga motar shi tare da kifa kai da starin motar!
Ba'baa mairo ta fuskanci ammie da kyau"yau zan sanar dake wani sirri da baki taɓa sani ba wanda ya zama dole ki sani domin naga kina kokarin wuce gona da iri!!!
Cike da mamaki ammie ta ɗago idanu tana kallon ba'baa mairo wai yau ba'baa mairo mai aikin wanke wanke,shara da girki ke gaya mata bak'ar magana!
_Halimatus Sadiya Muhammed_
*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
~sensational Heart touching story~
*BY*
*LEEMA*
_DEDICATED TO KANO STATE_
*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..
_Sweety smasher Ina taya ki murna fara sabon littafin ki mai suna"WANI AL'AMARIN..!,Allah yasa an fara a Sa'a ya bada ladan fadakar wa amin_
~🅿29-30~
Ni maryma uwace ga Abubakar idan baki sani ba ki sani yau uwar shi tasha nono ta saki na kama uwar mu ɗaya uban mu ɗaya da mahaifiyar shi Marigayi ya hajia saratu!
Mamaki,tsoro da fargaba suka cika zuciyar ammie,idan har maganan da ba'baa mairo take faɗi gaskiya ne menene hikimar ta na zuwa gidan a matsayin yar aiki.???
Dafa kafadan ammie tayi,nasan abinda kike tunani sarai nazo gidan ki amatsayin yar aiki yanzu kuma nace Ni gwaggon mijin ki ce...,abinda ya faru lokacin da abubakar yazo wurina da maganar auren ki babue abinda aya boye mun akan rayuwar ki wanda na tausaya maki matuka domin kadarar ki babba ce dole sai akwai babba a tare da ku domin ɗauka ki akan hanya,shine dalilin da yasa na kaskantar da kaina a matsayin yar aikin ki amma yanzu na lura kina neman watsa mun ƙasa a idanu...
Kuka ta fashe dashi tana faɗin na tuba ba'baa mairo na bi Allah WALLAHI ba zan sake ba dama son zuciya ne da rudin shaidan amma ai shima yana da laifi ba'baa ba kya ganin yadda yake abubuwa cikin gidan nan idan ya fita sai ta mai daɗi yake dawo wa...,,kwantar da hankalin ki duk ina sane kuma makircin hajia mariya ne dama idanu na zuba inga iya gudun ruwan shi amma yanzu ya zama dole in tsawata mashi Kuma mu tashi tsaye da adu'a da neman taimako",Nagode Nagode Nagode ba'baa mairo Allah ya ƙara girma ya biya ki
A gaskiya kin tafka babban kuskure a rayuwar ki da har kika biyewa son zuciya tun lokacin da abun nan ya faru da gida kika koma ki haihu gaban iyayen ki,amma Quruciya da wauta ya saka kin shigo bariki kin HAIHU kin kasa kula da ita wallahi HADIZA idan kina son ganin dai dai a rayuwar auren ki gagauta neman gafarar iyayen ki,duk inda baby take ki sanar da ita gaskiya ko ke wace ce a wurin ta sanan ki bata hakuri!...,tana kai wa nan ta shige d'akin ta.
Kuka sosai ammie tayi domin tasan gaskiya ba'baa mairo ta faɗa mata tabbatas ya zama dole tafi ganin iyayenta bayan shekaru goma shq ɗaya da faruwar wannan lamari!..., d'akin ba'baa mairo ta shiga ta duka har ƙasa ba'baa ki yafe mun na dauki shawarar ki don Allah ki mashi magana mu tafi tare hadda ke gaba ɗaya domin samun sassauci a wurin MAHAIFIYATA duk da Allah ya dauki ran MALLAM,zan so muje tare da baby idan har tana cikin garin nan,,shike nan ki tafi ki watsa ruwa ki kwanta yanzu zan kira shi a waya da safe za muyi magana"gyada kai tayi.
Alaji HABU na barin gidan ya nufi wurin Uwar gida can ya kwana dama abinda take so kenan.
Da safe da zazzaɓi ammie ta tashi saboda kuka data sha duk da haka tunda asuba ta shiga kitchen ta haɗa breakfast Koda ba'baa mairo ta fito ammie ta kamala komi...,hajia me yasa baki bari nayi aiki na ba..?,murmushi tayi cikin jin kunya ba'baa matsayin uwa kike a wurin mu bai kyautu ki shiga kitchen Ina zaune ba ko a baya da haka ya faru rashin sani ne....,itama murmushi tayi ta nemi wuri ta zauna a palour cikin babban tray ammie ta haɗa mata breakfast nata"nan za kici ko akai daki.?,kawo nan muci tare d'iya ta...,cikin jin kunya ammie ta zauna suka yi breakfast tare da ba'baa mairo tana ƙara kwantar mata da hankali.
Zuwa 10am alaji habu ya shigo gidan da sallama d'akin ba'baa mairo ya fara shiga suka gaisa,ta gabatar mashi da shawara da suka yanke da ammie na zuwa kumbotso wurin iyayenta",yace ai dama tun kafin aure ya so su tafi bata amince ba,zai shiga yaji ta bakin ta ya haura sama lokacin ammie na gyaran kaya cikin wardrob ya rungume ta yana shaƙar kamshin jikin ta"kiyi hakuri dani ban kyauta ba sharrin shaidan ne in Sha Allah haka ba zata sake faruwa ba..,sai daɗin baki yake mata har ta hakuri suka sha soyayyar su tun da safe(Lol).
Bayan komi ya lafa ya ƙara tuntubar ta da maganar zuwa gida ta nuna amincewar ta a sonta a tafi da baby,yace zai kira Kabir (babban ɗan Mallam saminu),yaji idan baby na cikin garin Kano.
Koda suka yada yawa Kabir ya sanar dashi duk yadda suka yi da yaya Mallam a ranar yanzu haka bashi da masaniyar inda ya kai yarinyar ,,yace ya tura mai number Yaya Mallam zai waya dashi suka yi sallama!
Bai sanar da ita ba domin yafi son sai ya gama dukan binciken shi sanan ta sani.
Ba'a ɗauki lokaci ba number Yaya Mallam ya shigo wayar alaji habu yayi saving a lokacin ya kira shi har ta tsinke bai Daga ba....,ya sake kira bugu biyu ya ɗauka..alaji HABU bakin shi dauke da sallama yace ina magana da Captain Aminu ne..?,ya amsa da eh!
Nasan baka san mai magana ba,zan su ka bani Aron hankalin ka muyi magana ta fahimta idan zaka tuna watani biyar da suka wuce a Kano ranar juma'a da dare wani mutum yayi sallama da kai ya kawo maka yarinya"BABY",wace jinin ka ce.?
Huci yaya Mallam ya fara yi yana faɗin,ok na fahimta wulakanci da kamun a Kano bai ishe ka ba har sai ka ƙara kirana a waya don ka tozarta ni...!,wai ma menene haɗin ka da yarinyar da har zaka shiga maganar da baka san mafarin shi ba.?
Duk da ban san mafarin zancen ba,babu abinda ban sani ba tsakanin ka da ammie domin itace matar da mike aure yanzu !!!!,,..katse shi yayi kana nufin ammie tayi aure kuma tana cikin Kano.?
Tabbas ko ranar da na kawo baby tare muke da ita cikin mota shawara ɗaya zan baka yanzu duk abinda kake yi ka shi rya mu haɗu kumbotso gobe kuma kazo da baby!
Wait wait are u ordering me?,,who am I to order u,shawara ce idan ka dauka ruwan ka,a word is enough for the wise,the word of the elders is the word of wisdom...,kit ya katse kiran!
Da mamaki yaya Mallam ke bin wayan da kallo yanzu kamar shi"CAPTAIN" wani banza ke gaya mun magana hada kashe mun waya.?,yanzu da gaske ammie yar uwan shi tayi aure tana cikin Kano all that while Allah bai taɓa haɗa su ba...,gida babu wanda ya kira shi tace an ga ammie bare ya samu labarin auren ta,,haka na nufin tunda tabar Chemist din nan bata koma goda ba kusan shekaru goma sha daya.!!,wurin wa ta zauna tsawon shekarun nan???,,wurin wanan alajin kawai zai samu amsoshin nan...,amma idan sun haɗu mai zai faɗa mata bayan ya bata mata rayuwa,,yanzu idan ya biso kumbotso ai asirin shi ya gama tonuwa cikin duniya(niko nace yaya Mallam da kunyar lahira ai kwara na duniya),,da wani fuska zai kalli Captain sadiq yace yana son amsan baby ya kai ta gida!
Kai gaskiya babu inda zai tafi alkawari ya dauka ba zai bari wanan magana ya fito ba yanzu wanna ɗan iskan alajin nason tona masa asiri...,sake sake yake cikin ranshi har ya yanke shawara ɗaya ya canja layin waya kuma ba zai tafi kumbotso ba!
Da dare bayan Alaji habu ya dawo daga wurin harkokin shi ya sanar dasu yadda yayi da yaya Mallam, ba'baa mairo tace mai zai hana su bashi kwana biyu su gani ko zai kira idan har bai kira ba sai su shirya su tafi kawai"duka suka yi na'am da wanan shawara...
Shiru shiru yaya Mallam bai kira ba,alaji HABU ya kira wayar tashi a kashe haka ya hakura ya kyale shi da yake gidan hajia mariya yake da kwana shi yasa bai kira ammie ba har ya gama mata kwanan ta biyu ya dawo gidan ammie,, ba'baa mairo ta tambaye shi koya samu yaya Mallam.?,,ya sanar da ita yadda suka yi ..,tace a kyale shi kawai gobe su shirya su tafi.
Da kanta ta kira ammie ta faɗa mata gobe zasu tafi idan akwai abinda take son saya na tsaraba ta amshi kuɗi wurin mijinta ta shiga kasuwa yau.....,bata da wani kuzari tana zullumi haɗuwar ta da umma da ya hydar shi yasa koda ya bata kuɗi komi bata saya ba ta saka cikin handbag,,hakanta kwana jiki ba kwari duk da alaji habu yayi noticing yanayin ta sai bai ce da ita komi ba!
Da safe suka shirya tsaf ba'baa mairo tace ammie ta dibi kaya domin can zasu barta ko kwana biyu ne tayi da yan uwanta su gana...,jiki ba kwari ta diba piya biyu na dogayen riguna da hijab daya suka shiga mota"alaji habu yaja mota tana gefen shi, ba'baa mairo na gidan baya suka ɗauki hanyar kumbotso...
Koda suka isa an samu canje canje da kyar ta gane hanyar gidan nasu wanda ya koma ginin block yanzu an shafe da siminti amma ba'a yi penti ba,hawaye ya fara tarara a idanun ta saboda tunawa da mahaifin ta, ba'baa mairo ta riko hanunta"ki kwantar da hankalin kin domin abinda ya faru ba laifin ki bane ƙaddara ce..,share hawaye ta yi suka shiga da sallama,aka bar alaji habu cikin mota....,tsakar gidan yan mata biyu ne da wani yaro wanda ba zai wuce shekaru takwas ba suna cin abinci tare can daga cikin wani rumfar kuma wasu mata ne su uku saman tabarma suna hira ....,dayan ta amsa sallamar nasu tare da mikewa tsaye tana faɗin"maraba da baƙi sanun ku da zuwa ki iso nan yafi inuwa ke Hadiza dauko tabarta cikin dakin baban ku...,sai da gaban ammie ya bada dammmm,domin ba kowa b'ace take wanan magana ila nafisa matar ya hydar,yarinyar da aka kira da Hadiza sak ya hydar....,kan ammie a ƙasa suka karasa wurin da aka nuna masu ai nan take sauran matar suka mike a razane dayan tana faɗin"wa nake gani kamar ammie'n Mallam ƙarami.?,,sai lokacin ta daga ido ta gane mai maganar mama ladi ce, ɗaya dake kusa da ita kuma umman su ce "kuma mai ƙarfi ya kwashe ma ammie sai yi take babu kakautawa..m,yarinya ta dawo da tabarma ta shimfida ba'baa mairo ta riko hanun ammie suka zauna tace"ina yinin ku,mun sake ku lafiya.?
Nafisa ta amsa da lafiya lau sanun ku,sai ga yarinya ta dawo dauke da kwanon sha cike da ruwan randa Mai sanyi ta aje masu ta koma wurin cin abincin ta.
Mama ladi da umma dai suna tsaye ko wane da abinda yake sakawa cikin zuciyar shi..., ba'baa mairo tace da alama baku yi farin cikin dawo wanta ba..?,mama ladi tace mun fi kowa farin ciki domin shekaru da dama sun shude mu dade muna rokon Allah ya bayanar da ita cikin koshin lafiya Duk inda take har Allah ya ɗauki ran mahaifin su nayi wani auren yanzu haka ma nazo duba su ne Allah yasa da rabon zan ganta..,"ta nuna umma kin ga umman su tunda aka rasa wanan yarinya bata sake samun kwanciyar hankali ba yau ciwo gobe lafiya abinda ma ya kara tayar mata da hankali shine yadda baban wan su mai sunan mallam ba rabu da gida kwata kwata kusan shekaru takwas kenan rabon shi da ƙauyen nan yana can kudu wurin aikin soja,idan anyi magana yace aiki ya hana shi zuwa,sai godiyar Allah tunda dan uwan shi hydar na kula da ita sosai da matar shi nafisa...
Ba'baa mairo tace Allah ya jikan Mallam da rahama ya kyauta MAKWANCIN shi, Allah ya sanya wa hydar albarka ya shirya mashi zuri'a ku kuma Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana shi kam wanan yaya Mallam Allah ya la'ance shi ya tozarta shi duniya da lahira Amin ammie ta amsa!!!
Umma da tunda suka shigo bata ce komi ba ta daga idanu ta kalli ammie da ba'baa mairo"saboda me za kiyi wa dana wanan mugun addu'ar.?,,saboda shine silar duk abinda ya faru da kowa kuma yake kan faruwar a yanzu"cewar ba'baa mairo...,zan so ku bani dama ayuwa mijin wanan yarinya iso ciki ku gaisa,sanan kuji komi a baƙin shi!
Mama ladi tace ammie dama kin yi aure ne ?..,ta gyada kai tana kallon umma wace fuskantar ke dauke da mamaki!!!
Cikin yaran dake cin abinci mama ladi tace "saidu sheka waje akwai bak'o ka shigo dashi ciki,,ke kuma nafisa kira mijin ki a waya domin shine namiji uba kuma babba yazo ayi komi a gaban shi yana shago...
Da sallama alaji habu ya shigo kanshi a ƙasa ya duka suka gaisa da mama ladi domin nafisa ta shiga daki ta kira mijinta,umma kam ko kallo basu isheta ba,,,,aka bashi kujera ya zauna.
Nafisa ta fito suka gaisa tace yace gashi nan tafe!,,,shiru wurin ya ɗauka kowa da abinda zuciyar shi ke kitsa mai,ammie dai kuka take sharba sosai.....,sallamar ya hydar ne ya saka kowa juya wa banda ammie,hannu ya mikawa alaji HABU suka gaisa,ya gaishe da ba'baa