Chapter 30 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   30 / 35

87K to 90K   out of 103.7K words

yasa kika boye mun alakar ki da uncle Christ.?

Ki gafarce Ni wallahi sharrin shaidan da son zuciya kuma soyayya ya rufe mun ido shi yasa.

Shike nan na fahimta dama can haka Allah ya rubutu zai faru bamu isa mu kauce wa wanan ƙaddara ba sai mu ci gaba da addu'a Allah ƙara kare wa ya rufa asiri Amin.

Yanzu shi uncle Christ ya San kina da ciki.?

A'a tunda muka je yola basu yi waya ba kuma da muka dawo ana cikin tashin hankali shi yasa.

Amma zan so ki kira shi muji ta bakin shi..,kuka taci gaba da yi Hadiza bana son bata maki Rai kuma amma naso rufe babin tarihin shi a rayuwata .

Na sani baby Kawai Kira muji...number ta saka tare da yin dialing

Can ya ɗaga da kakkausar murya yana faɗin baby.

Tace na'am idan ba zaka damu ba zan so muyi magana..,no ba sai kin bata bakin ki ba nasan kice na wuce ban sanar dake ba,maganar auren mu da sauran su,barin faɗa maki Babu sh yadda nasa Kafa nabar kano haka na saka ƙafa na shure soyayyar ki domin Ni ban taɓa son ki ba jikin ki nake so kuma na samu final.

Murmushi mai ciwo tayi,gashi yanzu ina dauke da cikin ka na wata ɗaya da sati ɗaya.

Cikin wa.?,God forbid ki nemi wanda ya maki CIKI ba dai Ni ba domin ban sanki ba kuma babu wanda yasan nayi soyayya dake,beside ma ina zaki sake gani na.?

Oh haka kace shike nan wallahi yadda kayi sanadin bakin ciki a zuciyarta da mom Dita har ta rasa ranta kai ma sai ka dandano baƙin ciki i promise ta kashe wayar.

Faduwa tayi jikin Hadiza tana kuka mai cin zuciya...,baby kinga illah soyayya da kafiri kenan ya yaudare ki yaci amanar ki domin ba auren ki zai yi ba,how stupid u are to think that he'll definitely married u or come back for u baby.?

Baban abunda ya rage maki a yanzu shine dukufa da ibada, istigfari da nan zaɓin Allah, INSHA ALLAH General Sadiq zai bi maki hakkin ki kamar yadda yace zai binciko shi kuma ya gurfanar dashi a gaban kotu.

Tun daga ranar suka mayar da hankali wurin revision domin exams NASU dake zuwa suna haɗawa da adu'oi,zaman su gidan hajia mariya sai godiyar Allah domin babu abinda suka nema suka rasa, duk da tasan Baby nada ciki bai saka hajia ta kyamace ta ba illah janta a jiki da tayi sosai tana kyautata mata tare da kwantar mata da hankali.
Mallami aka samo har cikin gida yake shigowa masu karatu da yamma,suna zuwa hospital a kai akai duba sister'n su.

Sati ɗaya da haihuwa aka yi zanen suna a masallaci yarinya taci suna NAZIYA kamar yadda ammie ta buƙata.


Sun Fara zana jarabawar NECO ranar Wednesday Wanda driver yake kai su before su fito yana waje yana jiran su ya dawo dasu gida.

Hadiza suna ci gaba da soyayya da Mallam munir wanda ke so ta bashi dama ya turo iyayen shi a masu baiko amma tana jin tsoro.



Komawar General Sadiq imo State ya saka wani abokin aikin shi dake aiki a river state ya binciko mai Christ Wanda Dama iyaye da kakanni shi ba boyayyu bane cikin Sa'a aka yi nasarar cafke shi yana dawo wa daga club da dare, General Sadiq ya bada dama a tsare mai shi a cikin Barrack na port hacourt tare da bashi horo mai tsanani har sai ya zo.

Ai kuwa yasha ɗan banzar duka har an sauya mai kamani sai kuka yake yana tuba domin yaji jiki.

Kwana biyu a kulle ana azabtar dashi sanan General Sadiq ya iso wurin shida yasa a hira shi sai da yaji tausayin shi.

Ya dube shi kasan dalilin da yasa aka dauko ka.?

Ya girgiza kai a wahalce,amma kasan baby a kano.?

Yace eh,ok me ya haɗa ku.?

Ba kunya ya bayyana komi kuma yana neman gafara.

General yace tunda aka nemi gafara yanzu zamu gaban iyayen ka sai ka fadi abinda kayi and ya zama dole kaje kano ka bata hakuri da alƙawarin zaka kula da ita da abunda zata haifa,hakan ba yana nufin idan ta haihu za'a baka abunda ta haifa ba.!,ko ɗaya ita keda iko dashi domin ba zamu ba kafiri ya bata ma jinin mu tarbiyyar ba.

Cikin sauri ya amince da duka sharudan General aka saka shi a mota jina jina sai gidan su.

Inda hankalin iyayen shi a tashe yake kwana biyu basu ga shi ba an saka cikiya babu labari..,ganin shi haka da jami'an tsaro hankalin su ya tashi sosai aka fara koke koke sai me jin abunda ya aikata yafi komi bata ma uban shi rai wanda ita uwarshi tasan ya saba ɓacin ranta kawowa da ya koma kan musulma duk yan matan su na kudu ya rasa wace zai wa ciki sai musulma.

Grandfather nashi doka shak'e sarki ne ya goyi bayan jikan shi yana neman kawo Maganar banza, General yace a bayar da christ Barrack aci gaba da hora shi har sai sun shirya amsan laifin ɗan su.

Uwar ta shiga kuka tana magiya har dai aka sasanta ya basu sati ɗaya su tafi kano idan ba haka ba zai saka a rufe mai christ har ta haihu.


Bayan ya koma imo state ne ya kira alaji habu ya sanar dashi yadda akayi da christ,yace kawai ya kyale shi ba sai sun zo ya tayar ma baby da hankali ba domin yanzu ta manta da komi karatu take yi,in dai maganar kula da ita da abunda zata haifa ne insha Allah ba zai basu kunya ba,suka yi sallama.

Bayan wattani biyu sun kammala Neco aka shirya masu walima haɗe dana saukar al-Qur'ani mai girma a cikin gida aka yi,su umma duka sun zo duk da tana fama da ciwo cikin zuciyarta taki magana ne kada hankalin kowa ya sake tashi,duniya babu abinda ta nema ta rasa yanzu,ta riga ta manyanta ƙarfi ya ƙare sai fatan gamawa da Duniya lafiya.

Walima ya samu halartar yan uwa da abokan arziki inda aka ci aka sha akayi adu'oi na musamman ga marigayi ya Hajiya Hadiza (Ammie).

Alaji habu ya basu kyautar waya kirar Ta android ko wace a cikin kwaliyin ta da layi(dana burin ammie kenan sai sun gama jarabawa ta basu kyautar waya babba)
An dauko naziya daga Hospital yanzu madara aka rubuta mata shi take sha tayi kyau abun ta kamar ba haihuwar watani bakwai ba,fuskarta sak ammie sai shiga rai kowa na sonta da tausayinta.


Cikin baby nada wattani uku yanzu suka shirya zuwa kumbotso hutu har sakamako ya fito,driver aka saka ya kai su wacce baby ta kwashe komi nata domin umma tace nan zata ci gaba da zama har ta haihu.

Haka suka bar gidan cike da kewar baby naziya.

Yaya ɗan Gusau ya sake yiwa General Sadiq tuni akan maganar auren baby da take son yi.

Yace ya bashi nan da watani shida(dai dai ta haihu) INSHA ALLAH zai sanar dashi halin da ake ciki.

Ranshi ya ɓaci yadda ake mai yawo da hankali kawai ya shirya zuwa kano domin magana da alaji habu!

_Halimatus Sadiya Muhammad_
*L££MA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..






~🅿67-68~



Zaman su a kumbotso ba ƙaramin natsuwa da kwanciyar hankali Baby KE samu wurin umma ba,a koda yaushe tana kan yi mata nasiha da bata shawarawari saboda halin rayuwa.

Idan yamma tayi bayan sun Kamala aikin abinci su kan ɗan zaga cikin garin ita da Hadiza tana nuna mata wurare,bayan sallar isha'i kuma suna leka makarantar islamiyya a biya masu karatu su dawo gida.

A yanzu hankalin baby ya kwanta saboda tana cikin yan uwanta na jini suna zama lafiya babu wani fargaba,gori ko tashin hankali ta ƙara sanin daraja da muhimmanci zumunci a kullum burin ta bai wuce Allah ya raba ta da cikin nan lafiya ba domin ta cika burin ammie na ƙarshe a kanta"samun ingantaccen ilimi.

Alkawari ta ɗauka duk abinda ta haifa zata bashi kulawa kamar yadda ko wane ɗa zai samu,zata bashi gata da tarbiyya kuma zata nisanta shi da uban shi sai idan shi har sai ya mallaki hankalin kanshi zata bashi labarin komi idan ya nemi zuwa inda uban shi yake zata sada su domin sauke nauyin da Allah ya d'aura mata,idan kuma bata kai wanan lokaci ba zata bar wasiyya.


Yaya ɗan Gusau zaune a babban palour'n gidan alaji habu ya xayane mashi buƙatar shi na son auren baby,ganin general Sadiq na mashi YAWO da hankali yasa yazo da kanshi.

Shiru ya biyu baya na ɗan lokaci Alaji habu ya nisa,Alhamdulillah mun gode wa Allah da ya kawo mu wanan lokaci da muka dad'e muna jira,dama burin marigayi biyu ne akan baby Wanda Allah bai bata ikon cika wa ba,sune:samun ingantaccen ilimi da muka miji na gari wanda zai riƙe mata Baby akan gaskiya da amana,sai gashi Allah ya kawo mijin wanda ya san Baby yasaan wacece ita kuma ya amince da ita a haka.

Sai dai wani hanzarin ba gudu ba,gwaggo ta san da wanan magana.?

Sosai ma kuma itace ma ta bani kwarin gwiwa akan maganar domin a farko dana samu labari Baby jikina yayi sanyi matuƙa sai na ga ai ƙaddara ce kowa da irin tasa.

Akwai abu ɗaya da yasa General Bai shigo da maganar ka wurin magabatan baby ba GASKIYA wanda nima ban ga laifin shi ba,magana ta Gaskiya baby na ɗauke da cikin watanni uku a yanzu haka wanda wani ɗan bautar ƙasa ya yaudare ta har Allah ya kawo rabo a tsakanin su.

Wani irin zufa ke keto mashi ta ko ina domin yaji maganar unexpected ne wani mugun kishi ya taso mai saboda gaskiya yana son Baby ba zai so wani abu makamancin zargi ya shiga tsakanin shi da ita ba.

Na fahimta babu Matsala zan iya auren ta a haka.

Masha Allah yanzu inaga muyi hakuri har ta haihu sai ka gabatar da kanka a wurin ta,idan kun daidaita ba za'a ɗauki lokaci ba ,zan samu lokaci in tafi can muyi magana da shi hydar.

Godiya ya mashi suka rabu ya koma masauki shi.


Waya Alaji habu ya fara buga wa General akan maganar domin yanzu sun zama family duka ba'a boye wa juna komi tare ake Shawara.

Sun tattauna sosai a kan maganar wanda General ya bashi assurance akan yaya ɗan Gusau zai iya riƙe masu Baby domin ɗan uwan shi ne kuma ya yaba da halayen shi.


Ranar asabar suka shirya da Hajiya mariya zuwa kumbotso domin ta kai na umma naziya ta gani.

Murna wurin su baby baa magana suka shirya abinci kala kala na tarban su hajiya.


Da wuri suka iso gidan saboda suna son komawa cikin lokaci, Baby ta amshi naziya ta rumgume tana mata wasa,Hadiza ta ɗauka,wanan ya dauka wanan ya ɗauka umma dai ta amshe yar jikan ta wace ke kama da mahaifiyar ta sak gata fara fol da ita.


Sun zauna da ya hydar an yi maganar yaya ɗan Gusau wanda shima yaji daɗin haka domin bai ga amfanin dogon karatun 'ya mace ba a ganin shi a dalilin karatun boko ammie ta samu ciki,yaya Mallam ya guje wa gida,ga baby da ciki suka a dalilin boko.

Lokacin da zasu koma baby taso a bar mata naziya,Hajiya ta basu hakuri da alƙawarin zata rinka kawo ta a kai akai suna ganinta.


Haka dai rayuwa taci gaba su kan je Kano suyi kwana biyu,ana kawo naziya wurin su.

Wayoyin da aka basu ko wace tana chat da nata da yake baby tafi yin face book Nan ta hadu da mutane da dama wa yanda ta sani irin su: sherrif class mate nata a sokoto,aysha na Sokoto har suka yi exchanging contact ta Bata shawara ta fara WhatsApp.

LOKACIN da ta buɗe WhatsApp ne taga aunty sadeeyah, general Sadiq, Meenah,aunty faiza,saratu,Yaya ɗan Gusau wanda aysha ta bashi sabon number baby.

Ta Nan ya fara cusa kanshi wurin Baby wace tun tana share wa har ta saki jiki suna chat sosai kuma yakan kirata a waya wasu lokuta.



*Bayan watanni shida*
Result ɗin WAEC ya fito Alhamdulillah sun yi making babu wa ta matsala wanda haka ya yiwa General Sadiq DAƊI sosai burin shi baby ta samu ilimi.

Tun bayan da baby tayi sallah asuba take fama da ciwon baya kafafunta sun riƙe ga nauyin ciki duk ya sauko mata ƙasa ko daga ƙafa bata iya yi sai daure wa take bata faɗa ma kowa ba tana zaune saman sallaya tana adu'oi har gari yayi haske tana wurin,umma ce ta fara lura da halin da take ciki ta aika yara aka taso ya hydar su tafi PRIMARY HEALTH Care dake cikin garin(dama shi ke amfani da motar ammie).

Umma da Hadiza suka riƙe ta zuwa mota domin ta galabaita,koda suna isa ma aikata basu fito ba saboda 7am lokacin,mai gadi ya kira metron ɗin a waya suka fito domin Nan cikin clinic d'in suke da gida.

Ɗaya nurse d'in ta tambayi Hadiza file ɗin Baby na awo fa?,tace ai bata taɓa zuwa awo ba.

Faɗa suka shiga masu wai yan ƙauye haka suke yi suna kashe kansu ta yaya mace zata dauke ciki daga wata ɗaya zuwa atara ace bata can me take ɗauke dashi ba bare lafiyar ta da abunda ke cikin ta.

Haushi abun ya ba Hadiza tece,mu fi ba yan ƙauye ba ne domin yadda kike takama kina da ilimi haka muke dashi condition ne yayi warranting namu zuwa wannan wuri.

Metron ɗin ta dakatar da hayaniyar ta hanyar shigar da baby labour rum Nan suka ɗauki vital signs nata,aka duba fundal height, presentation anda position na abunda ke cikin ta ana they are within normal range,Nan aka fara bata taimakon gaggawa domin koda suka zo tana 4cm.

Nurse d'in Yar bala'i ya fito tare da kallon Hadiza shekeke,amshi wanan list ɗin a sayo yanzu dasu zamu yi amfani.

Bata bita kanta ba ta amsa ta nufi wurin mota inda babanta yake ta bashi.

Umma tace ta bishi gida su hado kayan haihuwa tunda an ce da sauran Lokaci.


Gida suka fara zuwa har nafisa ta zuba masu ruwan zafi a babban Flask,gefe kuma ta d'aura tukunyar wanka.hadiza tace sannu da aiki mama!

Yauwa ya mai jikin dai?

Da sauki sun ce da sauran lokaci zan ɗauki kaya ne baba na waje.

Already ya hydar ya saya kaya unisex da setting baf na jarirai,cikin wani jakka ta ɗauki kala biyu kaya na mace da namiji,sau zanuwa uku da riga suka wuce.


Azaban duniya baby ta Sha shi kasancewa haihuwar fari ce gabanta a matse yake duk da ba scanning akayi ba sun ji alama babyn nada girma wanda dole sai an ƙara ta idan kuma ta kasa za su tura su babban Hospital ayi mata aiki.

Kuka, addu'a da nan gafara babu wanda Baby Bata Yi ba a ganinta mutuwa za tayi ta saka aka kira mata umma da Hadiza ta shiga rokon gafara tana barin wasiyya idan mace ce sunan aunty sadeeyah,idan namiji ne UNCLE sadiq.

Kwantar mata da hankali umma ta shiga yi tana bata adu'oi da zata riƙe,Hadiza dai kuka take yi ganin yadda yar uwarta ke wahala.

Ta dauki tsayin awanni shida Da kyar da wahala kan jariri ya fara fitowa wanda sai da aka mata ƙari sanan ya fito duka,ta samo Baby boy fari fol mai kyau da shi.

Bayan an gyara ta an mata dunki inda suka ƙara suka canza mata zani,nurse tace a kawo kunu mai zafi ko tea.

Umma ta haɗa tea mai zafi wanda yaji sugar aka ba nurse ta kai mata domin zai taimaka sauran jinin daya daskare a cikinta zai fito.

Tana zaune saman wani bed na dabam tana shan tea a hankali gefe kuma nurse na gyara jariri ita dai kallon su take tana tuno da abubuwa da dama,can ta saki murmushi tunawa da yadda ta rinƙa haukar shan tea ba sugar lokacin da take da ciki gashi yau Allah ya raba su lafiya,ummm yau ita baby ce ta haifi ɗa nata na kanta bata hanyar aure ba.!

Wa'iyazubillah,ba zata butulce ba tana Godiya ga Allah da ya bata wanan babban kyauta wanda wasu na nema da kuɗi basu samo ba.alhamdulillah iyayenta basu ga wanan abun kunya ba da ambata san halin da zasu shiga ba.


Ana gama gyara baby ya hydar ya biya kuɗaɗen da aka bukata suka shigo ganinta kowa sai murna yake ana mata barka,basu jima ba aka sallame su suka koma gida.

Umma da kanta tayi wa baby wanka saboda jariri sai da yamma za'a mai,wurin bada nono aka sha fama da ita domin babu kai(nipple),Shima ko an saka mai a baki baya kama wa ga nonuwa sun ciwo sosai lokacin da ya fara kamawa sai data kwala ihu saboda azaba gashi ruwan yaƙi zuwa nurse tace a barshi yayita tostso ruwan zai zo a hankali.
Duk da bata samu wanan gata ba a lokacin da ka haife ta amma ta jinjina wa iyaye mata yadda suke wahala da ciki,haihuwa har zuwa shayarwan.

Waya ya hydar ya bugawa su Alaji habu da su General sadiq ya sanar dasu haihuwa.

Washe gari sai ga hajia mariya,aunty faiza,saratu da usman sun zo da abun arziki iri iri,sai bin naziya baby keyi da ido saboda tayi wayau sosai tana rarafe ko ina har tana kama kujera ta tashi.

Duk wani gata da ake yiwa mace idan ta haihu Baby ta samu ta ko ina kayan sawa jariri,nata abinci da sauran su duka an kawo.

General ya bata hakuri ba zai samu zuwa ba saboda aiki da ya mashi yasa sai dai matar shi zata zo ta kwana biyu.


Su Alaji habu sun zo da abun arziki sosai yadda rago babba koda yayi magana da baby tace sunan UNCLE sadiq take so a saka,yayi wa yaro huduba da sunan


Ana gobe zanen suna Aunty sadeeyah taso da irin nata abun arzikin wanda sai da ya saka baby kukan farin ciki da kukan rashin ammie'n ta.

Washe gari

30 / 35