Chapter 10 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   10 / 35

27K to 30K   out of 103.7K words

pant idan ina Bacci kema zai fara saka maki idan kika zo dakin mu da dare ko idan ya kama ki a lungu,Allah na sonki ibro bai saka maku katon yatsan shi ba da sai kin kuka Wallahi...!,shiru baby tayi tana sauraren ikon Allah ashe dama saboda haka Ibro ke yawan shishige mata musamman da dare idan an aikita yataa binta a baya!!

Washe gari tunda safe shukura da kanta tayi wa baby wanka ta haɗa masu tea suka yi breakfast ta k'ara gyara mata kayanta zuwa 9:40am tayi sallama da mutanen gidan domin yaya Mallam ya bugo ma taufeeq akan ya kawo ta airport Yana jiran su....

Shukura hadda kukan munafu nci suka shiga adaidaita har airport yaya Mallam na sanye cikin uniform d'in su na sojoji a gaba an rubuta A.mallam suka gaisa da taufeeq cikin girmamawa baby na gaishe shi amma ko kallo bata ishe shi ba yace da taufeeq su jira Bara yazo...

Suna zaune a wurin taufeeq na mamakin ikon Allah domin dai oga aminu yace mai baby yarinyar shine sun rabu da matar shi amma menene hujar shi na nuna mata tsana haka..?

Sai da aka fara announcing passenger idan suna kusa su matso jirgin su zai tashi sanan ya dauko rafar yan dubu dubu ya miƙa ma taufeeq yana ƙara mai godiya..., taufeeq ma godiya yayi mashi yana daga ma baby hannu hadda hawaye saboda ya shaku da ita tunda yake bai taba ganin yarinya mai hakuri da ibada irin baby ba duk da bata wuce 11yrs ba amma akwai kau da kai ga natsuwa.

Cikin jirgin baby na zaune kusa da yaya Mallam ya daura belt ya daura mata bai sake kallonta ba hankalin shi na kan wayan shi da yake kashewa.

Baby ta fara tunanin ya rayuwarta zata kasance tare da wanan mutumin da ko gaisuwa ta bai taɓa amsawa ba,shike nan ta rabu da ammie har a bada ba tare da ta amsa mata dumbin tambayoyin da take son mata ba!!

Yaya Mallam sai lokacin ya kare wa baby kallo kama take da shi sak haɗa baƙin fatan,idanu,hanci da baki nashi ne,yanayin jiki ne kawai na ammie baban tashin hankali yanzu idan ya isa mai zai fada wa abokan aikin shi,wacece baby a wuri shi bayan kowa yasan bai taba aure ba!!!


~kuyi hakuri da wanan bana jin daɗin jiki ne~


_Halimatu Sadiya muhammed_

*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..


*SUCCESS IS NEVER ACHIEVED BY THE SIZE OF OUR BRAIN BUT IT IS ALWAYS ACHIEVED BY THE QUALITY OF OUR THOUGHTS*


~🅿23-24~



11:30AM jirgin su yayi landing a Murtala Muhammad international airport a ikeja,Lagos State passenger suka fara sauko wa a hankali ciki harda yaya Mallam wanda yake rike da hanun baby hannu ɗaya kuma bag nata ne har suka sauko wani crut ya iso har inda suke ya sara mashi tare da amsar bag ɗin yana sauri ya buɗe masu back sit na wani hadadden landcruser suka shiga ya rufe sanan ya dawo mazaunin driver yaja motar tafiya mai tsayi ya kai su "Battalion Nigerian army barrack dake odogunyan ikorodu nan cikin Lagos ɗin,tun daga gate na farko ake sara mai har suka isa army staff Quarters yayi kwana shiga wani gate da aka rubuta"CAPTAIN'S BLOCK" jerin wasu gidaje madaidaita zagaye da furanni yayi parking a hanzarce ya fito ya bude motar yana Sara ma yaya mallam fuskar nan a murtuk'e ya fito baby na biye dashi rik'e da bag nata ya murda wooden door din wani kamshi da sanyi ya masu sallama ya shige abunshi,baby da taga tsayuwar ba zai mata ba ta shiga amma wayam bata Ganshi ba....

_palour madaidai mai dauke da set ɗaya round leda sofa furnitures, electronics sai babban elargement nashi kamar zai magana sanye cikin uniform a ƙasa hoton an rubuta"CAPTAIN A.MALLAM", ƙasa ta zauna tana zaran idanu shiru sai kusan minti talatin ya fito sanyi da jalabiya brown Yana amsa waya cikin harshen turanci har ya zauna yana kan wayar wanda ya dauke shi kusan mintuna goma a karshe naki yana faɗin ina gaida sadiya sai ka shigo yayi ending call d'in.

Wurin plasma ya nufa yana kunna plug hanun shi riƙe da remote hankalin shi na kan tv yaci karo da ƙafan baby sai lokacin ya tuna da ita a wurin...,ke ga d'akin alert hand side naki ki shiga ki aje kayanki kada ki kuskura ki leko palour'n Nan until I tell u to do so, nodding tayi ta nufi d'akin babba ne mai dauke da gado madaidaici sai wardrobe da toilet ciki wanka ta fara yi ta canja kaya ta zauna kasa cike da zullumi irin rayuwar da zata yi a barikin sojoji har bacci ya fara satan ta ta haye saman gadon abunka da sanyin AC na bugawa tayi dai dai saman bed sai bacci....

Kurtu(crut) dake wa yaya Mallam aiki ne ya kamala girki ya shirya komi a dianing ya ɗauki nashi ya fita....,yaya Mallam da yunwa ya ishe shi ya buɗe foodflask ɗin"pounded yam ne da water leaf soup(Mrs jibril ur husband's favorite😋😂),murmushi ya saki Bai san dalili ba amma yana mugun son girkin peter a natse yayi serving kanshi yana ci yana santi har ya kamala ya wanke hannu a sink d'in kitchen ya koma rum nashi wanda ke right hand side faɗin tsaruwar shi ma bata baki ne wanka ya sake yi ya shirya cikin blue jeans trouser da white shirt ya fito lokacin ya tuna da wata baby tsaki yaja ya nufi d'akin da take wani irin baƙin ciki ya taso mashi daya ganta kwance saman gadon shi don iskanci da raunin wayau wani irin rankwashi ya dauka mata saman kai a razane ta tashi tana zaran idanu...!,irin tarbiyyar data baki neman ko..?,kuka ta fara yi tana bashi hakuri...

Kada inji pim daga bakin ki idan ba haka ba wallahi sai kin wanke bedsheet din Nan yanzu,ya riƙe kunen ta duka biyu ya murde that should be ur first and last time of sleeping in my bed,Yana nuna mata saman tyles nan shine bed naki a gidan nan understand..?,da ƙarfi tace Yes sir!

Wuce KICI abinci idan kin gama ki wanke kwanonin kafin in dawo saboda ba zama na dauko ki yiba a bariki ya fice abun shi...


Tunda Allah ya halicce ta bata taɓa cin sakwara ba sai ranar ta ɗan tsakura ta shanye miya tas baiwar Allah ta wanke kwano nin a madaidaicin kitchen din nashi ta dawo palour ta zauna saman carpet tana kallon Film abunka da tsautsayi ta manta da warning din daya bata "banda zama a palour"!!!

Shiru shiru bai dawo ba har aka yi Sallah ta gabatar da azuhur ta hanyar duba agogo ba don taji kiran sallah ba can taji ana norking kamar ba zata buɗe ba ta fita"wani gajeren mutum ta gani ba za'a kira shi fari ba kuma ba za'a kira shi baƙi ba yana da kyau sosai kamar bahilace,,gaishe shi tayi yana murmushi ya amsa fuskar shi dauke da mamaki ina kuma AA ya samu yarinya mai kama dashi sak...?,tunda suke bai taɓa sanar dasu yana da sister ba haka basu san yayi aure ba bare wuce diyar shi ce.

Yana murmushi yace amma ke bak'uwa ce ko..?,ta gyada kai...

Muryan yaya Mallam suka ji yana huci kamar wani zaki"uban wa ya baki umurnin fito wa har wani ya ganki...?,cikin inda inda tace dama an...ina zaune ne a nan shine naji ana buga kofa...

Riko hanunta duka biyu yayi da hannu ɗaya ya wanka mata mari ya kara wanka mata wani yana kalle kalle har ya gano wayan charger ya shiga tsulaa mata ba kakautawa....

Mutumin dake tsaye yana kallon ikon Allah yace menene haka Captain AA kamar wata mate naka sai jibgan yarinya ƙarama kake yi akan abinda bai kai ya kawo ba..?,stay out of his captain sadiq Bana son shishigi ok...!,,yaci gaba da dukan baby tana kuka tana kiran ammie,shi kuma sunan ammie nan da take kira yake ƙara tun zura shi yana jibgan ta kamar ya samu namiji dan uwan shi!!!

Captain sadiq yace"enough of dis wanan ai ya zama child abuse idan ba zaka kyale ta ba kaga tafiya ta...,sake baby yayi yana faɗin, start frog jump,ta rikice ta daburce ta rasa ina zata dosa saboda azaba ga bayanta ya fashe sai radadi bata san me ake kira da "frog jump ba"hanyan waje ta nufa a guje ta boye bayan Captain sadiq tana faɗin"wayyo ammie ki cece Ni zai kashe Ni,don Allah kizo ki tafi dani ba zan zauna anan ba na mutu na lalace bayana jini ciwo...

Duk da Captain sadiq soja ne mai da dakakkiyarr zuciya amma sosai maganganun baby suka taɓa zuciyar shi,ya rik'o hanunta yana daura ɗan yatsa a lips nata Yana fadin shiiiii ya isa ba zan bari ya sake dukan ki ba,with me u Are safe!
Ranshi a bace ya juya zai fita...,yaya Mallam yace ina zaka tafi da ita...?,sadiq babu ruwan ka cikin wanan abun ya dawo da ita kana son ja min raini a wurin yarinya in sata punishment ka tafi da ita,kada ka ja mata bala'i da masifa a wanan barikin wallahi domin kare martaba da mutunci na ina iya aikata komi ciki hadda "KISA" idan kana ɗauka wasa ne ka tafi da ita...

Captain Aminu Mallam Aminu do ur worse,Ina ji da GANI ba zan yadda ka kashe ta ba"ITA MA Y'ACE kamar kowa duk da ban san alakar ka da ita ba zan tafi da ita gida na har sai ka huce zan dawo da ita!!!

Idanun shi kamar zasu fado ƙasa yana huci kada ka soma abinda zai kawo gaba a tsakanin mu na har abada sadiq,baka san wacece ita ba,ina na samo ta,menene alakata da ita ba don haka kindly hand her to me!!!

Tsaki yaja idan zaka iya ka kashe Ni sai an jima ya ja hanun baby suka fita...




"""'''Alaji habu ya shiga motan shi a gurguje aka buɗe gate Koda ya fita har tayi nisa da tafiya a ƙasa kasancewa Area din akwai ƙarancin abun hawa ya Parker a gaban ta"na haɗa ki da girman Allah ki shigo Mu tafi gida nasan ban kyauta maki ba insha Allah haka ba zata sake faruwa ba...!,banza tayi dashi tana kokarin canja hanya da yaga zata bata mai lokaci ya fito ya cicibeta ya saka sakin mota yayi locking yaja tana ta bugun kofa sai gudu yake da motar har suka isa gida lokacin 10:20pm a guje ta shige tun nata ta rufe...

Gyara parking yayi ya shigo tare da rufe palour ya haura sama babu irin magiyar da bai mata ba amma taki bude kofar gudun ya tara ma kanshi jama'a tunda ba su ɗaya bane a gidan yasa ya shiga dayan d'akin ya kwanta....,daren ranar cikin su kowa da abinda yake tunani a zuciyar shi har asuba ya tafi masallaci koda ya dawo bata buɗe ba haka ya dawo palour ya zauna.

Ba'baa mairo ce ta fito zata gyara wuri suka ci karo ta gaishe shi ta shige kitchen ta fara aikace aikacen ta sai zuwa 7:30am ammie ta fito cikin doguwar riga na material ya mata kyau sosai ta kashe daurin dankwali fuskan nan babu walwala ta sauko ko kallon inda yake bata yi ba ta nufi kitchen suka gaisa da ba'baa mairo.

Yana son magana da ita amma yana jin kunya kada ta dizga shi a gaban ba'baa mairo can wata dibara ya fado mai"ammie...!,ammie...!!,ammie...

Hajia naji kamar alaji ke yake kira!
Yatsina fuska tayi banji bane kyale shi kawai ba'baa...!,yar nan ba'a haka fa baki san damuwar mijin ki ba don girman Allah kije gare shi!

Ba'baa mairo ta gama kashe mata jiki sun sum ta kama hanya zuwa palour ai kowa ya mike ya dauke ta cak sai master bedroom ya kashe ta da daɗin baki da salon soyayya mai tsayawa a rai,tsakanin mata da miji sai Allah rufo masu kofa nayi....



_Halimatus sadiya Muhammad_

*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..


~MEELAT MUSA~
~ASMEENART ZEEYAN~
~QUEEN ACID~
~AMEERA YOLA~
~FALHAT~
~SARATU MUSA~
~UMMERHERNY~
~MARYAM MUHAMMAD HASSAN~
~Da sauran da ban ambata ba Nagode Nagode Nagode sosai da kulawa Allah yabar zumunci na samu sauki sosai~


_Alhamdulillahi lathii bi'ni'imatihii tatimus- salihin_



~🅿25-26~




🅱a wani tafiya mai tsayi suka yi ba zuwa gidan Captain Sadiq Wanda yake ajerin gidan yaya mallam sanan ginin iri ɗaya ne sai ban banci tsarin cikin gida da yake na Captain Sadiq akwai matan aure ciki sai gidan yafi na yaya Mallam tsari.

Da sallama ya shigo palour'n daga kitchen naji wata zazakar murya tana faɗin"honey har ka dawo da wuri haka?.

Zaunar da baby yayi saman ɗaya daga cikin royal chair dake palour'n ya nufi hanyar kitchen,Yana shiga ya sagala hanayen shi a waist nata tare da kwantar da kanshi a bayan ta yayi lamo idanun shi a rumtse...,da taga haka tasan ranshi a b'ace yake ta dakatar da aikin da take yi tare da yuwo ha tayi facing nashi itama ta sagala hanayen ta a kafadan shi ta rungume shi tsam tana shafa bayan shi a hankali cikin tsigar rarashi,gogan nata sai ajiyar zuciya yake....

Zuwa wani lokaci ta haɗe bakin shi da nata cikin kwarewa tana bashi hot kisses kafin ta jaye,suna haɗa ido ta sakar mashi murmushi mai kashe jiki"honey life is not a waste as long as there is at least one person in the world who cares for u.so when things go wrong and u feel like giving up remember you've get me.

Murmushi ya sakar mata shima,baby each time I look at your gorgeous face,I feel my heart melt in ur love Baby girl...,lokacin ta hango mutum zaune ta sake hanun mijinta ta nufi inda baby take fuskarta dauke da murmushi,dafe kanshi yayi da hannu biyu saboda shaf ya manta da baby.

Kallon matar shi yayi deeyah zan kai ta clinic nan cikin Barack idan na dawo zan maki bayani,rudewa tayi sosai ganin halin da baby KE ciki nan take ta fara hawaye...,ya dafe kanshi,ya Allah kin fara ko.?
Bana son kukan Nan Kinga Allah ya tsare bata wani ji ciwo sosai ba ki kwantar da hankalin ki!

Hanun baby ya rik'e suka nufi clinic,ITA kuma sadeeyah nan ta zauna tana sharban kukanta"Allah ya yita mace mai rauni sosai abu kadan ke tayar mata da hankali.


*WANENE CAPTAIN SADIQ MANGAL*???


Captain Sadiq mangal haifaffen garin Adamawa state ,yola ne iyayen shi fulanin asali ne tun daga kan kakani,ya taso cikin so da kauna da kuma kulawa na iyaye da yan kowa saboda shine last born Yana da yane maza biyu da mata biyu ko wane na zaune tare da iyalan shi,cikin Yola ya fara tun daga nursury, primary har secondary daya kamala ya tafi NDA KADUNA Wanda a Nan suka hadu da yaya mallam abota mai karfi ya shiga tsakanin su har suka kamala cikin Sa'a,lokacin posting aka raba su yaya Mallam na Lagos aka tura Sadiq ibadan sai bayan yayi aure ne aka dawo dashi Lagos kwata kwata watannin su shida kenan da aure.

Sadeeyah Mamman turaki haifafiyar garin Kaduna ne ta taso cikin rufin asiri kasancewa mahaifin su bashi da wani karfi kuma suna da yawa agidan su yasa tunda ta kamala Secondary School Bata samu daman zuwa gaba ba har Allah ya haɗa ta da sadiq ranar passing out nasu ta raka aminiyar ta saboda elder brother Bata yana cikin wanda suka kamala training ɗin, ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba aka tsayar da lokacin aure akayi da farko ta fara zama a Yola lokacin yana aiki a ibadan da aka mayar dashi Lagos suka tafi tare.


""Wurin da yayi jini aka wanke sanan aka shafa mata magani,nan take akayi mata allurai aka basu kwayoyin magunguna suka nufo gida,lokacin sadeeyah ta kamala girki da take yi har tayi wanka tana zaune cikin English Wears tana jiran dawowar mijinta.

Tana jin sallamar su ta mike tsaye tare da tarbo su ta kama hanun baby"sannu kin ji yaya jikin,akwai wani ciwo da kike ji yanzu..?

Deeyah allow her to rest mana wanan irin tambayoyi kamar yar jarida!..,cikin wasa yake mata magana still Bata saki hanun baby ba yanzu muje kici abinci sai ki kwanta zan konaa maki fan Yana iska na hura wurin zaki samu sassauci....

Baby da tunda tasan ciwon kanta bata taɓa samun kulawa irin na yau ba ta shiga mamaki wanan bayin Allah da Allah ya haɗa ta dasu wanda basu san ko ita wacece ba amma suna nan nan da ita....,iska sadeeyah ta hura mata a fuska"ki daina dogon tunani cuz is not gud for ur health,baby taki nodding kanta tana zama saman carpet,sadeeyah ta nufi kitchen ta zubo ma baby jelof na SHINKAFA da waya data gama sai ruwan sha ta aje mata,cikin kulawa tace idan baki koshi ba ki ƙara.

Hanun mijinta ta riko suka nufi bedroom nasu,honey kayi wanka zan shirya abinci.

Murmushi yayi ya shige toilet ta fito palour ta shirya komi saman dianing table tana kallon yada baby ke saka loma kamar wacce ta kwana da yunwa,cike da tausaya wa ta kada kai ta koma d'akin dai dai ya fito har ya saka riga mai ƙaramin hannu mara nauyi na shan iska da three quater hanun shi riƙe da gwangwanin body spray Yana fesawa....,amshe gwangwanin tayi tana faɗin ya

10 / 35