Author : LEEMA Category : KDP NOVELS
make up sai kamshi take zuba wa ta wuce su sai nuna ta ake cikin gidan ana gulma...
Safiyya tace yanzu haka wurin ɗan iskan nan Bobby zata ko..?,baby tace Ni ban san wani Bobby ba..!,oh na manta ai wani saurayin shukura ne tunda suka dawo gidan nan idan mijin ta ya tafi duty na dare Bobby yazo su kwana tare ko taje dakin shi...
Baby ta katse ta shi Bobby wane ne..?,wani ɗan makaranta ne ya kama haya nan kusa damu shine suke soyayya da kuma taufeeq ya sani amma baya magana,zan faɗa maki amanatul amana wata rana da dare dani da Ibro muka leka ta window shukura muka ganta tsirara da Bobby ya hau saman jikinta yana mata wani abu tana ihu tana jin daɗi wai shine Ibro yace ai cinta yake yi(🙆🏼😳🙈)
Jikin baby yayi sanyi,Safiyya tace ni dai amana na baki idan kika faɗa ma taufeeq wuta bal bal Kuma sai kin biya Ni tuwon da kika ci yau...!, ƙaramin tsaki baby taja ta Koma ciki shiru tana tunanin rayuwa shike nan ita kuma haka rayuwar ta zai ci gaba da tafiya babu wani ci gaba..?,daga wanan bala'i sai wanan!!
Yaran gidan ko su Amina da fati suna kofar gida wurin hira da samarin su,Ibro da Safiyya kuma suna ta window maman Daniel suna leken wani romantic nollywood Film da take kallo mai cike da Shashanci har ta hango su ta rufe window ta,suka koma kofar gida suka leken yankin su dake makure jikin gini maza na lagudan jikin su cikin duhu sai zuwa karshe goma sha ɗaya suka shigo gida lokacin su Safiyya suka dawo ciki da gudu ko wane ya shige d'akin nan da shukura tace baby ta Koma ashe nan yaran ke kwana saboda ya abu tayi wani aure bazawarin ta na zuwa mata kwana,,fati ta kunna wayar ta lenovo kirar China ta gada fitina nan taga baby kwance inda take kwanciya dundu ta dirka wa baby" a zabure ta mike waya kawo ki d'akin nan..?,Safiyya tace ai ya abu(maman su)tace ta dawo nan da kwana,oh ta matsa can gefen Ibro akwai wuri mana amma ta kwanta wurina,Safiyya tace Baby Koma gefen can akwai wuri nan katifa muke sawa Ibro yana fitsarin kwance shine yake kwanci ya saman tabarma ta shek'e da dariya;,baby ta mirgina gefe dama ba jin daɗin baccin take ba saboda bashi da banbanci da kwanciya saman tsakuwa..
Suka shinfida yaleluwar katifan da kodaden zuwa gadon suka kwanta su fati da Amina na ci gaba da hira da samarin su a waya,Safiyya sarkin bacci har tayi bacci abunta,gefe kuma baby ta sa kanta wurin kafafun ibro tana ta tunani bacci yaƙi zuwa can taji Ibro ya daura mata ƙafafuwan shi a kanta sai ta ƙara matsawa gefe can taji shaaaaaa"ya zuba fitsari wurin fuskarta haushi ne ya kamata ta koma gefe ta zauna tana sharar kwalla har asuba bata samu bacci ba...
Cikin su babu wanda ya tashi yayi sallah ta fito bucket ta gani da guga a gefe na ya abu ta dauka ta nufi rijiya cikin Sa'a babu taro da yawa ta dibo bucket ɗaya ta shiga wanka ta daura alwala tayi sallah tana zaune gefe har ta fara jin hayaniyar mutane alamar kowa ya tashi yana harkokin gaban shi haka Safiyya ce ta bata ruwan koko tasha!
Sai zuwa karfe goma shukura ta dawo ta bude daki ta kwalo ma baby Kira,da sauri ta isa d'akin ta gaishe da shukura,,a wulakan ce ta amsa tace tayi saurin haɗa wuta a murhun gawayi ta girka ma Bobby abinci zai zo amsa idan ya dawo schl ,ta amsa da tau cike da kasala ta haɗa wutan ta shiga gyara kayan abinci gashi Babu isashe ruwa a gidan haka ta rinka wahala har ta kamala ta zuba a foodflask masu kyau wanda ko taufeeq bata taɓa ganin an bashi abinci a ciki ba,wani ikon Allah don tsabar zalunci irin na shukura ko dandano bata bari baby tayi ba tace da baby ta dauki babban kula ta bi Safiyya wani gidan ruwa kusa ta dauko leda biyu masu sanyi ta bisu talla...!,a razane baby ta kalle ta mama me,ban taba zuwa talla ba tunda aka haife Ni don Allah kiyo hakuri ki bani ko wane irin aiki ne banda talla..!,wani mahaukacin mari ta wanke baby dashi tana huci baby b'ata lokaci da ɗauki kulan ta fice da gudu tana kuka sai da fitsari ya zubo mata a wando...
Safiyya ta kalle ta menene kuma..?,cikin kuka ta faɗa mata sai data gama kwasar dariyar ta tace nasan wacce ta bada wanan shawara wallahi ya abu ce hegiya maman mu,amma baby zaki iya kuwa..?,wurin da muke zuwa talla akwai nisa fa Kuma masu ruwa sun yi yawa wani lokaci Ni kam ɗakunan samari(Male hostel) nake kai taka su samun hannun a wando(vaginal) a biyani kuɗin ruwan,saboda wanda bai sayar ba uhmmn ranar ya abu sai ta kusan kashe ka da duka ga rashin abinci, shine ko su fati ai suna kai gyada d'akin maza ayi sadaka a biya kuɗin..!,shiru ya biyo baya Safiyya tace jira in SAKA riga mu fita tare.
Gidan ruwa suka fara zuwa suka ɗauki ruwan leda biyu aka zuba ma baby a kula amma kamar an daura mata buhun shinkafa saboda bata saba daukan abu mai nauyi ba sai wurin shukura tafiya mai nisa ya kai su Bayero University baby sai nishi take sama sama saboda wahala Safiyya sai dariya take shek'e wa dashi domin ita sun saba ai kuwa direct male hostel ta nufa ,baby kam dama tace a sauke ta wurin gate ta aje kulan ta zauna tana hutawa,zuwa minti ashirin Safiyya ta fito da kula Empty Babu ruwa tana ya mutsa fuska Baby tace menene kuma ina ruwan..?
Ke dai wani gabjejen kato ya saye ruwan ya shigar sani d'akin su sai zungurawa mun abun fitsarin shi yake a gabana ina jin ciwo amma bai bari ba shege sai da yaga dama ya bani kuɗin"lokacin babu ta tuno da abinda head Master ya taba mata akan kuɗin exams Nan take ta fara hawaye gudu suka ji daga bayan su security ya biyo wasu almajirai da suka hauro ta katanga suka shigo suna wa ɗalibai sata shine aka biyo su wani ya faɗa kan kular ruwan baby ki make tas tas ya tatake su shima security daya biyo almajirin ya ƙara take sauran ruwan ji kake tamm ya zame kasa ai kuwa a guje Safiyya taja hanun baby suka bar makarantar domin tasan idan har ya kama su kashin su ya bushe sai da suka yi nisa baby tace gaskiya Ni komawa sanyi in ɗauko kulan mutane gashi an faɗa ruwan ko ɗaya ban sayar ba me zan ce da shukura na shiga Uku ta fara kuka...
Wallahi idan kika koma babu ruwana kulle ki zai a dakin masu gadi sai gobe ki dawo gida gwara kiyo hakuri muje ana shukura hakuri kawai,,shiru tayi na wani ɗan lokaci suka ci gaba da tafiya har gida tana kuka suna isa Safiyya tace "asiri mato nike in ka gane da kai nike guntu ya sauka",dama matan gidan da sun ji haka sun gane me ake nufi wani gulma mai zafi aka samo kowa ya halara ana sauraron Safiyya,ta kali shukura wallahi sai kin biya zan sauke wanan guntun idan ba haka ba shike nan kuma guntun ya shaafi kowa cikin gidan nan..!,sanin halin Safiyya ba zata taɓa fadi ba sai an biya yasa shukura ta bata naira hamsin,tace saura maman daniel,aunty grace da ya abu domin ba'a kyauta zan sauke wanan guntun ba...!,tsaki suka ja kowa na don jin gulma kuma basu son bada kuɗi dole suka biya hadda uwarta nan take ta zayane masu abinda ya faru da baby a makaranta...
Bata ida ba shukura ta kurma ihu a dole tayi asarar kula da ɗari biyu na ruwa ta kamo baby dake rak'ube a zaure ta shiga kwallo da ita har kofar d'akin su tana duka gamu da kafa tana zage zage ruban barkono ta bude ta kamo hanun baby ta daga pillow sai ga sabon razor baby na shure shure tana ihu shukura ta tsatsaga mata yatsun hannu ta zuba dake barko nu tana ƙara kallo da ita a a gigice ta balle dakatar dakin tana ihun kiran ammie ammie ammie zan mutu kizo ki tafi dani wallahi ba zan iya zama a nan ba zata kashe Ni na tuba Bata san inda take saka kafarta ba har tabar cikin gidan aguje tana ratsa lunguna...
"""Hankalin ammie ya kwanta yanzu bata da wata Matsala sai taci ta kwanta sai sallah suna zama lafiya da ba'baa mairo itace ke daɓe mata kewar baby idan ka ga yadda ta koma ta ƙara kiba da haske alamar biyu ya nuna a jikin ta,uwar masu gida na kawo mata ziyara akai akai ta koma da alheri sosai..,shima alaji habu ba'a barshi a baya ba yana kula da dukkan wasu bukatun ammie baya yawan zuwa gidan saboda zuciyar shi na raya mashi abubuwa da dama baya iya ɗauke idanun shi a kanta idan har ya biyewa son zuciya zai iya afka mata a koma gidan juya shi yasa bai damu da zuwa gidan ba sai waya.
""A Lagos kuwa yaya Mallam ya gama haɗa dukan wani plan akan baby so yake aiki ya rage mashi ya aiwatar da abinda yayi niyya akan baby,da zaran ya samu Lokaci cikin satin nan zai shiga kano"waya ya daga ya kira taufeeq bayan sun gaisa yake shaida mashi idan ya samu dama zai shigo kano,yace shima yana wurin wani aiki sai karshen sati zai koma kano suka yi sallama.
~OH JAMA'A KO MENENE KUDIRIN YAYA MALLAM AKAN BABY???~
_Halimatu Sadiya muhammed_
*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
~sensational Heart touching story~
*BY*
*LEEMA*
_DEDICATED TO KANO STATE_
*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..
~Fans Ina matukar jin daɗin comments naku yana ƙara mun kwarin guiwa sosai na typing musamman LEEMA NOVEL FANS GROUP~👍🏻👍🏻💞💖💖
~🅿19-20~
Gudu sosai baby keyi bata san inda take jefa ƙafafuwan ta ba sai saman titi ji kake k'eeeeeeee an take burki...!,wata mace ta fito tana faɗin subhanallah ta nufi baby a hanzarce yarinya daga ina haka,baki ji ciwo ba ko...?,a razane baby KE juye juye nan ta gane baby ba cikin natsuwa take ba ga hanunta da aka kama aka tsatsaga da razor sai zugi yake mata ta koma kamar sabuwar kamun hauka rungume ta matar tayi tana shafa bayanta a hankali tana tofa mata adu'oi har ta natsu,mutane sai kallon su ake ta rik'o ɗaya'n hanun mai lAFIA ta shiga da ita mota suke nufi nearby private clinic ta tambayi health recorder Ina doctor..?,yace sai sun saya card 500 naira kafin suga nurse on duty, Babu musu ta cire 1k ta bayar aka tambayi baby sunan ta..?,tace Baby kawai,matan ta ce rubuta haka nan ta bada shekaru da address wanda taga ya dace aka nuna masu wani office wata nurse ce zaune tana aiki suka gaisa ta nuna mata hanun baby tana mata bayanin tsautsayi ya ritsa da ita tazo giftawa Allah yasa dai bata ji rauni ba sai wanda ke hanunta wanda bata san yadda ta same shi ba...!
Kallon baby tayi da kyau ta duba hanun tace wanan wane irin zalunci ne yanzu haka ba wurin iyayen ta take ba ko yarinya..?,gyada kai tayi tana faɗin papaw na ya kai Ni gidan aunty shukura ya wuce Lagos shine dana fasa mata ruwa da kula tamun haka,nurse ɗin ta kalli matar" hajia kinji ko na sani wanda yasan zafin haihuwa bazai taɓa wulakanta dan wani ba yanzu bari ayi dressing wound din ya kamata mu nemi iyayenta gaskiya tana haɗa kayan aiki suna tattaunawa da hajia Balki baby dai na faman kukan ta sai da aka kira wata nurse ta rike ta aka fara mata lidocaine injection sanan aka fara wanke wounds d'in duk da alurar da aka yi mata na kashe zafi sai data sha kukanta aka wanke tas sanan aka naɗa hanun da bandage,sai pain killer a aka bata hajia ta biya komi,nurse tace Baby kina zuwa schl..?,tace eh da nike wurin ammie amma yanzu gidan aunty shukura Bana zuwa..
Yanzu kina da number ammie ko zaki gane gidan ta a mayar dake can..?,tace banda number nata,gidan mu na farko na sani ba zan gane wanda ta koma yanzu ba gidan aunty shukura kawai zan iya gane wa,tace shike nan hajia ki kai ta can amma ya kamata ki tsorata matar nan fa kada ta kashe yarinyar mutane "ah haba kada ki damu aiki na ne ai(hajia Balki barrister ce),motar suka shiga baby na mata kwatance har gidan lokacin da suka shiga matan gidan anyi chirko chirko ana gulman shukura zata kashe yarinyar mutane hadda adu'a suke Allah yasa iyayen yarinya su kuleta sai ganin Baby suka yi tare da wata hamshakiyar hajia sun shigo"cikin sakin fuska hajia Balki tayi sallama tana gaishe su ko wace gulma na cinta suka amsa ,a tunanin su itace mahaifiyar baby da Yan sanda tazo kama shukura,,,baby na nuna mata hanya har dakin shukura dake kwasar bacci hankali kwance yamma tayi bata ga diyar mutane ba ko a jikin ta.
Sallama hajia Balki ke kwada wa cike da masifa shukura ta tashi sai tayi tuzali da hajia Balki ai nan jiki na rawa ta fito tana gada wurin zama har ƙasa ta kai tana kwasar gaisuwa...,hajia Balki tace ina mijin ki...?,tana kame kame tace tayi tafiya ne",ok zauna aunty shukura ita kuma tana riko hanun baby"shukura shawara zan baki a matsayina mace yar uwanki kuma lauya mai aiki da qungiyar kare hakkin mata da kana nan yara(women right),hasashe na ya zama gaskiya ba kece mahaifiyar baby ba,Allah ne ya haɗa ku zan so kiji tsoron Allah ki rike ta da amana ɗa na kowa ne ba lallai ɗan daka haifa shine zai duba ka ba,Allah kaɗai yasan abinda zata Zama nan gaba,wanan abinda da kika mata ayau ya zama child abuse Wanda za'a hukunta ki a akai amma me..?,ina baki shawara da ki kiyaye gaba saboda abun duniya Pure water na ɗari biyu kula da bai wuce 2k ba zaki ɗauki makami(razor) ki tsaga yatsun yarinya ɗaya, ɗaya har biyar for goodness sake,Babu zuciya ne a kirjin ki...?,ko babu imani ne a tatare dake bayan duka data sha bai isa ba hadda amfani da makami..!,,that is beyond reasonable doubt gaskiya,is too much for her at her age wanan ya zama domestic violance zan baki Shawara guda ɗaya mai muhimmanci idan har kin san ba zaki iya riƙe ta ba KINDLY take her back to her parents ,idan lallai sai kin zauna da ita dole kada ki sake koda wasa ki sake daura mata talla...!,kada ki sake dukanta domin ITAMA Y'ACE kamar kowa kasancewa ba kece kika haife ta ba that will not be an excuse for u to maltreat her madam shukura yanzu irin firgice wa da tayi ba don Allah ya kiyaye ba wa yasan idan zata shige..?,ta haye saman titi da wani mara imanin ya kad'e ta taji rauni kota rasa ranta ya gudu sai ya kenan...?,Na hada ki da girman Allah ki mayar da ita wurin iyayen ta kawai cuz zan sake dawo wa gidan nan wurin mijin ki idan na samu labarin sun yi mata wani abu zan sa adaure mun ku wallahi,Ta mike tsaye ga ledan magungunan ta nan yanzu a bata abinci taxi sai ta sha magani ta kwanta tana bukatar hutu kada a tashe ta sai ta tashi da kanta...!
Ok hajia ba za sake ba wanan ma ba plan nawa bane ya Abu yace ayi mata shi,i promise such mistake will never happen again I swear madam,hajia Balki na rike da hanun baby tace atau yanzu dai is left for u ,shekaru na goma da aure ko miscarriage ban taba samu ba kin samu fine girl from no where kina maltreating nata,zan dawo da mijina idan bakwa sonta ku bani..,tana magana tana tafiya rike da hanun baby,shukura na bin su a baya har wurin mota tana godia ""shafa kan baby tayi kiyi hakuri kinji baby Allah na tare da mai hakuri insha Allah za kiga riban hakuri sai na sake zuwa insha ALLAH,baby na sharan hawaye tace Nagode jiki a sanyaye hajia Balki taja motar ta kamar kada ta rabu da baby Allah ya daura mata son baby...
Suna dawo wa cikin gidan aka shek'e da dariya ana nuna shukyra,masu Allah ƙara nayi,masu dama tafiya akayi da ita suka fadi..,ita dai bata tanka ba domin akwai mugun tsoro tayi daki"BA GONI SAI ALLAH SPECIAL BREAD ta dauko ta zuba stew da ice fish a plate ta aje ma baby a gabanta bata ce kala ba ta fice,baby kam ta shiga ci saboda tun ruwan koko da Safiyya ta bata da safe bata sake cin komi ba gashi yanzu pass 5:0pm,sai da taci kusan rabin bread ɗin sanan ta kira da ruwa tasha magani ta kwanta ai kuwa sai bacci....
Shukura na zaune kofar d'aki abun duniya ya isheta har magrib baby Bata TASHI ba ,fita tayi ta sayo masu amala da miyar yauki lokacin baby ta tashi da tsamin jiki sai hawaye take saboda zugin da hanun ta ke mata,shukura ta shigo"sorry baby oya come lemme bath u ,baby ta girgiza kai domin a tsorace take da shukura ok come and brush yr teeth before u eat again,a hankali ta bude baki"i want to pray,cike da mamaki take kallon baby ga hannu nade da plasta,jiki a kukuje tana kiran sallah za tayi,ai kuwa bata hana ta ba a hankali ta tashi shukura na zuba mata ruwa tana alwala da hannu ɗaya har ta gama ,aka shinfida mata sallaya ta zauna ta gabatar da salolin da ake