Chapter 4 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   4 / 35

9K to 12K   out of 103.7K words

da kyau a matsayina gidan k'aunar mace,maganar hydar kuma ta fuskanci shi mutum ne mai tsattsauran ra'ayi baya ɗaukar raini ko kaɗan shi yasa basa jituwa kuma Quruciya ce ke damun su da zaran sun mallaki hankalin kansu zasu yi zumunci sosai Musamman idan suka san dukan su ciki ɗaya suka fito;"shima Mallam haka yake nuna ma umma Quruciya ce idan suka mallaki hankalin kansu zai zaunar dasu ya faɗa musu itace uwa su duka ba kamar yadda hydar ke guranta ma yaya Mallam a kullum riƙon shi akeyi zai bata tarbiyyar ammie,shima yaya Mallam yana gani ai mama ladi ta haifi hydar,umma ta haifi ammie,ya tabbatar ma umma ko bayan ransu yaya Mallam zai rungumi yan uwan shi kuma ya kyautata masu:,,,Cikin ikon Allah nayi saukar al-Qur'ani mai girma lokacin bukin walima ba ƙaramin kuɗi yaya Mallam ya kashe ba saboda kayan da nayi amfani dasu daga Kano yazo dasu da Mallam yayi faɗa sai Mallam saminu ya Sanar dashi ai yaya Mallam naɗa ƙoƙarin neman na kanshi...!,a kwana a tashi na kamala primary lokacin inada shekaru goma sha biyu dai dai yaya Mallam ya kamalla secondary shima...,abun mamaki babu komi a kirjina amma lokacin ne fara al'ada (menstruation) nayi fama da ciwon mara kusan kwana uku ban san wanda ke kaina ba sai da aka fitar dani ƙaramin asibiti(primary health care) dake ƙauyen mu akayi mun ƙarin ruwa tare da allurai sanan jinin ya fara zuwa umma sarakan kunya dakin mama ladi na dawo ta koya mun komi yadda zan tsaftace jikina,ta sanar dani hukunci ya yau kaina yadda ko wane babba ke ɗaukar zunubi haka kuma za'a rubuta mun idan na Sab'a wa Allah,sallah nasan baki da matsala da wannan yayan ki ya tsaya sosai ganin kinyi sabo dashi alhamdulillah,haka kyautata ma iyaye da sauran na gaba dake kin san al'adan ƙauyen nan da yarinya ta fara jini na farko a gidan su zata fitar da miji da tayi na biyu a saka lokacin aure bayan jini na uku ne za'a d'aura mata auren yanzu idan akwai wanda kike so sai ki sanar da ya'yan ki...!,raina ya ɓaci sosai domin inada burin yin karatun boko mai zurfi nasan kuma yaya mallam kawai Zai tsaya mun in samu cikan burina ai kuwa ina barin d'akin mama ladi na nufi Majalisar su yaya Mallam(inda yake zama hira) da kuka na zayane mashi komi gaban abokan shi,su kam sai dariya suke mana ya ce in share hawaye babu wani aure da za amun da zarar sakamakon mu ya fito makaranta kwana na yan mata zai kai Ni a Kano,farin ciki fal rai na;da yake ya kamala karatu shima sakamako yake jira sai bai koma kano ba kullum cikin lalab'an mallam da abarni na samu ilimi mai zurfi domin yana da muhimmanci a wurina fafur yaƙi amincewa sai da ya haɗa da Mallam saminu sanan mallam ya amince ba'a son ranshi ba haka mama ladi da umma na bata so haka ba amma ya suka iya da yaya mallam,shi kam ya hydar cewa yayi duk na tafi makaranta ya zame hanun shi a kai na sai dai na nemi wani ɗan uwan bashi ba..!,ko a jiki na dama na matsu na huta da azabar shi,,,lokacin da common entrance d'in mu ya fito yaya Mallam da kanshi ya shiga ya fita ya nema mun Government Girls Secondary School shekara (GGSS shekara) da taimakon mallam saminu aka kammala komi ranar da zan tafi sai murna nake zan koma kano kusa da yaya na hadda cewa ba zan sake zuwa kumbotso ba sai dai su Mallam su zo gani na!!!

Kuka ta fashe dashi Alaji habu Allah ya tsinewa wa kauyan ci,halinci,Quruciya da kuma Don zuciya wanan tafiya nawa zuwa Kano shine babban ƙaddara wanda akewa lakabi da DaNa sani K'eya ce,wallahi dana san ƙaddara da rabon baby zai kai Ni garin Kano dana bijirewa yaya Mallam na bi umurnin iyayena,na tsaya an aurar dani kamar ko wace yarinya a kauyen mu!!!!

Jiki a sanyaye ya buɗe ƙaramin fredge dake gefe ya dauko guran Chi exotic Mai sanyi ya tsiyaya mata tare da kai wa dai dai bakin ta,dole ta buɗe baki ta kurb'a kaɗan tare da sauke sassayan ajiyar zuciya ya ake cup d'in Yana tapping bayanta har natsuwar ta ya dawo sanan ta ci gaba..


Gidan Mallam saminu muka fara sauka matar shi gwaggo larai kamar yadda naji yaya Mallam ya kirata mace mai fara'a da mutumci ta amshi mu hannu biyu haka yaranta duka yan maza biyu ɗaya warin yaya mallam, ɗaya wari na,bayan nayi wanka naci abinci da Sallah aka nuna mun wurin kwanciya ba'a jima ba nayi bacci da safe bayan mun gama karyawa nayi wanka su yaya mallam suka rakani har makarantar mu koda muka iya an gama assembly Ana nuna mun ajina jss1A aka bani green house wani mallami ya kira head girl ya damka mata amana ta,sai da aka gama komi su yaya Mallam duka tafi jiki a sanyaye nikam masha kuka yamun alƙawarin zai rinƙa zuwa duba Ni Lokaci zuwa lokaci;tun ban saki jiki ba ina tunanin gida yau yaya Mallam zai zo duba Ni,gobe ne shiru har na saki rai na ina karatu sosai kuma ina ganewa duk da ba kamar kauyen mu bane amma bani da matsala tunda na iya karatu da rubutu turanci da lissafi (maths and a English) ke wahalar dani headgirl na taimaka min sosai har lokacin ziyaran ɗalibai yayi ranar yaya Mallam da gwaggo larai suka zo mun da kayan cielye ciye kala kala banda miya da aka mun na stew da yaji naman kaji da farar shinkafa,da muka kebe nake tambayar shi jarabawar su yace nashi waec bai kyau ba credit uku ya samu saura pass Babu maths da English,shi dai kabiru ya dace babban ɗan Mallam saminu yanzu haka ya samu gurbin karatu a College of Islamic and legal studies;ban ji daɗi ba gaskiya nayi ADU'A Allah yasa ya samu Neco yace Amin yana faɗa mun ai yaje gida ma kwana kin baya su umma na gaishe Ni kajin da akayi miya ma Mallam ya bayar,nayi godia da zasu tafi na kira head girl suka gaisa,ya bani dubu biyu na damka mata ta aje mun nasha kuka kamar kullum!,,haka rayuwa taci gaba da tafiya ina karatu sosai duk wata idan zan yi al'ada kamar zan mutu sai an mun ƙarin ruwa da allurai har muka samu watani uku a makaranta sanan muka yi hutun zangon farko lokacin nayi kwana biyu gidan Mallam saminu muka nufi kumbotso da yaya Mallam yana mun tsiya wai na ƙara kiba da girma hankalina kwance bana kewar kowa shi kam duk ya rame kullum da tunani na yake kwana yake tashi har muka iso gida murna wurin su umma ba'a magana ganin na ƙara girma da hankali bana irin Quruciya nan da wauta har muka ɗan fara shiri da ya hydar wanan zuwa domin tun da asuba zan tashi inyi sallah,gyaran gida wanke wanke in daura girki,idan kowa ya tashi in gaishe su da yake muna da rigiya kusa da gida nan zan shiga jidan ruwa sai na cika komi namu yaya mallam kam baya jin daɗin hakan wai wahalar tamin yawa nikam ko ajiki na don na saba a makaranta...!"bayan kwana biyu Mallam ke sanar damu za'a naɗa ya hydar Sarkin noman kumbotso duk da shekarun shi ashirin da uku amma wanan shekara yafi kowa samun amfanin gona fanin hatsi,murna sosai na taya shi haka yaya Mallam,ranar nadi muka sha kwalliya akayi girke girke iri iri na zamana sai rumfar mai gari ga makida na gargajiya suna kadawa aka naɗa ya hydar kusan su shida kowa da nashi sarautar Hakimi ya bashi kyautar yar shi Asiya sadaki kawai ake buƙata a saka lokacin aure murna wurin mallam ba'a magana haka taro ya watse..!,da dare ɗan mai anguwa ya aiko yana kirana Kofar gida ai kuwa yaya Mallam ya fita yana kumar baki kamar zai dake shi wai karatu zan yi ba aure ba kada ya sake zuwa idan ba haka ba zai daure shi...!,washe gari magana ya karade ƙauye abunka da ƙaramin gari magana har gaban mai gari Mallam ya bada hakuri akan yaya Mallam bai kyauta ba kuma zai tsawata mashi,da Mallam ya dawo da maganar gida yaya Mallam ya hasala ya shiga haɗa kayan mu wai kano zamu koma ba zan sake zuwa hutu ba sai na kammala karatu(Quruciya dangin hauka)na biye mashi muka nufi kano gidan Mallam saminu na karkare hutuna koda je su yaya mallam ya fito ta neco ya lashe komi hadda "B"guda biyu yake sanar dani yanzu jamb take son rubutawa ya tafi jami'a nima in mashi alkawari zanyi Karatu sosai bazan saurari samari ba insha Allah zan ga tubar karatun baya son in gama wahalar karatun in Koma aure ƙauye yadda mata ke wahala da yara,""nan take nayi mashi alkawari zan yi karatu sosai koda baya nan ai kuwa tun daga lokacin ban ƙara zuwa hutu kumbotso ba har akayi auren ya hydar banda labari yaya Mallam yazo mun da kayan buki ranar ziyaran ɗalibai da sak'on gaisuwa daga su mallam,nayi farin ciki sosai yaya mallam yace wai wani irin abinci ake baku a makarantar nan naga kin ƙara girma sosai "sai lokacin ta lura da nonowa da suka fito a kirjin ta wanda yafi komi girma a jikinta ko daga nesa ka hangota su kake fara gani itama abun haushi yake bata shi yasa take biyu ta kwana da hijab a hostel gashi bata da rigar mama ko ɗaya,yace shikenan yana so idan anyi hutu zasu tafi kumbotso suyi kwana biyu ta cinye sauran hutun a Kano tare dashi kafin ya fara karatu;cikin nasara suka fara zana jarabawar lokacin su headgirl na shirin rubuta waec har suka kamala aka rabu cikin kuka saboda koda zasu dawo su headgirl sun gama haka suka ɗauki hanyar kumbotso su umma nataurna bayan watanni shiga rabon su da Ita washe gari gidan ya hydar ta yini da matar shi mai kirki tsaran ta yan sha Uku har tabar gidan ya hydar bai dawo cin kasuwa ba,washe gari suka juyo zuwa Kano,ya hydar yayi takaicin hakan domin yana son Neman gafarar yaya Mallam domin Mallam ya sanar dashi komi akan shine mahaifin su kuma umma ta haife su duba rikon su kawai inna lami da mama ladi su kayi ranar yayi kuka saboda abubuwan da ya rinƙa yiwa babban wannan shi yaya Mallam yana goranta mashi iyayen shi sun rasu...!, ai kuwa kamar jiki ake su iso kano ciwon marar ammie ya tashi bai zame da ita ko ina ba Sai asibiti inda aka duba ta likita yace bai kamata ko wane lokaci ana mata ƙarin ruwa da allurai ba gwara a bari tayi endouring pain din nan,yaya Mallam yace yanzu ba wani abu da za'a mata yanar irin matan..?,yace ai yawan ci mace mai kananun shekaru haka take fama wasu har sai sunyi aure an fara shigar su(sex)yake ragewa with time Kuma da ta samu ciki shike nan ya wuce,yace ya gode pain killer Kawai ya basu suka dawo gida tayi ta fama gwaggo larai na tausaya mata har tayi kwana bakwai da take yi ta gama,shi kam yaya Mallam bashi da tunani sai abinda likita ya sanar dashi idan ba shigar (sex)ammie akayi ba ciwon bazai ragu ba Allah yasan tunda aka haifi ammie ya kamu da ciwon sonta bashi da buri da ya wuce ya mallake ta amatsayin matar shi uwar ya'yan shi shine hikimar da yasa ya hanata sauraran kowa har sai ta kamala Secondary schl dai dai har service yayi lokacin takai shekaru sha takwai sai suyi auren su,yanzu haka zai zuba idanu tayi ta shan wahala gaskiya gwara ya shigewa ko sau ɗaya ne ta rage jin azaba ai babu mai ganewa tunda shine zai aureta...!(RASHIN SANI YAFI DARE DUHU),,,,haka kuwa akayi ranar da dare Mallam saminu na wurin bada karatu,gwaggo larai kamar tayi bacci domin da tayi sallar isha'i take bacci yaran ta kuwa duk suna makaranta yaya mallam ya kira Ni zuwa d'akin su cikin natsuwar ya sanar dani abinda likita yace da kuma kudirin shi...!,cikin jimami nace yanzu yaya mallam kana ganin babu wanda zai gane...?,yace a'a saboda yana matukar sona yayi alƙawarin babu wanda zai san wanan magana kuma yasan idan mallam ya samu labari muna don juna zai farin ciki da hakan,babu wani bata lokaci na biye wa daɗin baki irin na da namiji,son zuciya da rudin shaidan RANAR ASABAR ASHIRIN GA WATAR MARIS SHEKARA ...,MISALIN KARFE TARA NA DARE YAYA MALLAM YA SAMU NASARAR KAWAR DA BUDURCINA ALAJI HABU!!!!

Kuka mai ƙarfi ta fashe dashi tana buga kanta da karfen gado,shima cikin hawaye jikin shi ya matukar sanyin yake ƙoƙarin rike ta amma ya kasa...

Sai da ya bari tayi mai isarta yaci gaba da sallati yana istigfari wanan kwaba da mai yayi kama....?,muryan ta yaji tana faɗin nasan tabbas duk namijin da yaji wanan labari nawa ba zai taɓa aure Na ba shine dalilin da yasa a duniya ban taɓa kawo ma kaina zanyi aure ba har in koma ga mahaliccin na!!!

Shiiii ammie wanan dalili ba shi zai hana Ni auren ki ba domin labarin ki ya zama iznah a gare Ni da sauran al'umma baƙi ɗaya ki daure ki karkare wanan labari INSHA ALLAH wahalar ki ta yanke a duniya.

Cike da kwarin gwuiwa taci gaba....,nasha kuka a daren na azaba shima harda hawaye da kyar ya lalab'ani a cewar shi mallam saminu ya kusa shigowa a rufe gida in tashi in tsaftace jikina insha paracetamol in kwanta,,,haka kuwa akayi da kyar na samu bacci da safe na tashi da zazzabi(ashe tun a daren nan na samu ciki bamu sani ba tunda kwana ɗaya kenan da gama al'ada ta),hankalin ya Mallam ya tashi sosai aka mun allurai a chemist duk da tafiyata ta canja gwaggo larai ta barshi a rashin karfin jiki ne sanadiyar zazzaɓi dana tashi dashi tun daga ranar yaya Mallam ya koma wani irin jarababbe kullum da dare sai ya shige Ni kafin yayi wanka ya tafi masallaci wurin ɗaukar karatu,idan Mallam saminu yayi magana me yasa yake zuwa latti yace sai ya gama karatun jamb yake fitowa har aka samu tsawon sati ɗaya muna Abu ɗaya tun ina jin zafi bana sakin jiki har na fara jin daɗin abun na fishi zak'e wa har hutu ya ƙare gidan babu wanda ya fahimci komi duk da anga mun ƙara shak'uwa sosai tare muke yin komi aka barshi akan shakuwa ce na jini,ranar da zan koma makaranta haka muka rabu da alkawaruruka masu dama akan wanan abu zai kasance sirrin mu babu wanda zamu sanar wa duk runtsi da wuya muna tare har mutuwa...!, Mun shiga jss2 lokacin su headgirl sun tafi na fara shan wahala kamar yadda sauran ɗalibai ke sha saboda haushi na kawai jira ake headgirl ta wuce a Fara cuɗani lokacin nayi baƙi na rame wahala har wata ya ƙara aka shiga sabon wata bangaren al'ada ba"nisa keyi tsakiyar wata"...,shiru har wani wata lokacin kuwa na fara laulayi komi naci sai amai ga kasalance sai faman bacci bana tabuka komi a aji aka kira wayar mallam saminu ai kuwa ya tadda yaya Mallam yazo a duba Ni aka bani permission zuwa gida har na samu sauƙin koda muka nufi asibiti gwajin farko ya nuna ina ɗauke da juna biyu na wattani biyu...!,duk da shekaru na sha uku a lokacin nasan ciki ba abun wasa bane kuma ba ƙaramin abun kunya na aikata ba ɗaukar ciki ba tare da aure ba,idan aka samu labari a ƙauyen mu nasan na gama yawo domin sai mun sha surutai ana iya faɗin saboda haka ne yaya Mallam ya hana Ni aure da sauraren kowa don yamun ciki...!,maganar yaya Mallam ya dawo dani daga dogon tunanin da nake yi,yanzu dai kibar kuka mu tafi gida tunda na samu makarantar horar da sojoji dake Kaduna zan wuce kafin nan zan sanar da Mallam a ɗauka mana aure da mun dawo Kano zan nemi aminta cen likita a zubar da ciki sai a akara daura mana aure kici gaba da karatu domin wanan Magana sirri ne a tsakanin mu minti alkawari duk runtsi babu mai sani!!!!



~THIS IS JUST THE BEGINNING~


_Halimatus Sadiya muhammed_

*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..



~🅿11-12~




🅱an kawo komi a zuciyata ba muka sallami gwaggo larai zamu kumbotso lokacin Mallam saminu na kasuwa tayi mana Allah kiyaye hanya, tafiyar ya kasan ce wani irin domin har muka isa kowa da abubuwan da zuciyar shi ke sak'a mashi a nawa bangare roƙon Allah nake kada iyayena su fahimci halin da nake ciki while yaya Mallam yana tunanin wani likita zai gani a cire cikin dake jiki na...!,Da sallama na fara shiga gidan na tsinkayi muryan mama larai tana maraba da yan makaranta ammie'n babanta"murmushi na saki a kasalance na rungume ta sai kuka wiwi ,tace jumma fito kiga ja'irar yarinya....,umma ce ta fito daga rumfar Mallam da alama abinci ta kai masa tace ai kun fi kusa in banda shagwaba daga shigowa sai kuka ina mai sunan mallam din..?,muryan shi suka tsanko yana faɗin umma a bita asannu rashin lafiya tayi shine aka bata hutun kwana biyu har ta warware,mama larai ta ƙara ɗago ni daga jikin ta ai ko ta faɗa sosai tayi baƙi yanzu debi ruwa kiyi wanka kizo ga hura can wanda umman ki dama wa Mallam ki diba za kifi jin daɗin shi,sum sum ta

4 / 35