Chapter 23 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   23 / 35

66K to 69K   out of 103.7K words

shike Nan na kafurta na Koma mara imani.!,wanan suna ye ddashi suka dace domin shine ya mutu kafiri mara imani ta hanyar sab'on Allah!

Umma sai data rumtse idanun ta jin wanan zafafan kalamai akan ɗan data haifa,ammie ko ji tayi kamar ta shak'e baby har lahira,ya hydar da baya cikin hayacin shi bai san wani irin waina suke toyawa ba.

Cikin daga murya aunty sadeeyah tace Allah ya Isa tsakani na dake baby,irin tarbiyyar dana baki kenan?,kina son janyo mun zagi da tuzarci a idon duniya.?,wallahi ban yafe maki ba....

Nurse be ta iso wai likita na son ganin su, Alaji habu ya riko hanun Sadiq suka nufi office d'in...,yace dama akan maganar gawan ne sun gama duk wani necessary arrangement suyi signing Kawai su ɗauke shi!

General Sadiq yace mai zai hana gawan ya kwana a hospital tunda bashi da muhalli a Barrack d'in idan suka ce zasu tafi dashi kano wahalar zai masu yawa,tunda akwai makabarta cikin Hospital d'in gobe zasu zo ayi jana'iza a nan.

Duba da irin mutunci dake tsakanin General Sadiq da doctor Adebayo yace shike nan ba Matsala,shima Alaji habu yaji daɗin shawarar.

Haka suka nufi gida jiki ba kwari cikin mota sai koke koke suke,shi dai ya hydar kamar mara hankali har yanzu ko komai bai ce ba.


Duk wanda ya kamata su san da arasuwar yan uwa da abokan arziki an sanar dasu gobe da ƙarfe 9:30am za'a yi jana'iza a teaching hospital.

Matan abokan aikin su sai shigowa suke suna masu umma gaisuwa...,lokacin da labari ya isa wurin mr and Mrs Emanuel hada taka rawar farin ciki burin su ya cika,nan take tace zasu shirya zuwa garin su domin gabatar da bukin mutuwar Justina.

Baby hankalin ta kwance tana d'aki tayi bacci ta har gari ya waye bayan sallar asuba aunty sadeeyah ta raba masu Alkur'ani domin a karanta bude wa kawai baby tayi amma cikin zuciyarta tana addu'a kada Allah ya sada shi da rahamar shi,azabar kabari,quncin kabari Allah ya tabbatar dasu a gare shi, Allah yasa wutar jahannama ta zama makoma a gare shi.


Ƙarfe 9:30am aka gama shirya gawan shi a hospital suka sallace shi aka nufi makabarta dashi ana saka shi a rami lokacin ya hydar ya saki wani irin ihu wanda ya razana sauran Mutane,yana sambatu don Allah a cire dan uwan shi a cikin wannan rami bai mutu ba da ranshi,kada su azabtar dashi da ɗan uwa da ranshi..., General sadiq sake sharan hawaye ya riko hanun shi suka nufi wurin mota mutane sai tausaya masu ake har aka rufe shi aka shafa addu'a sanan suka koma gida.

Su umma na ganin dawo War su nan wani sabon kuka ya barke babu mai rarashin wani.

Bayan kwana biyu General Sadiq ya fito da duk wani kaya da yaya Mallam ya Mallaka ya damk'a wa umma,ya sanar da su akwai kuɗaɗe MILLION huɗu cikin account nashi zai basu ATM d'in a tafi dashi.

Umma tace babu abinda take so cikin kayan ,shima ya hydar yace baya so aka sadaka dasu.

Kuɗi kuma aka yanke shawarar za'a siya wuri a nan kauyen su a gina Masallaci ana sallah ciki ta zame mashi sadakatul jariya.

Sanan General Sadiq yace yana so daga yau riƙon baby ya koma hannun Ammie domin itace mahaifiyarta tafi cancanta ta riƙe ta.

Daga cikin d'aki baby ta kurma wani uban ihu tana faɗin NOOOOOOOO!!!


_Halimatu Sadiya Muhammad_

*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..

_Every moment of life is a step towards death.Our sincere condolence goes to the family of Captain Abdullah(yaya Mallam),pls accept our most heartfelt sympatheties for your loss.May jannatul FIRDAUSI be his permanent home in the hereafter Amin_👏🏻👏🏻



~🅿53-54~




Daga cikin d'aki baby ta kurma wani ihu tana faɗin"NOOOOOOOO!

Hankalin kowa ya koma gareta amma banda General Sadiq da aunty sadeeyah,sai da ya gama karantar su tsaf sanan yayi gyaran murna;kada ku wani damu da duk abinda zata aikata,tafiya dai ya zama dole a gare ta idan har ta ɗauke Ni da Uba lalai ne tabi umurni na FINAL.

Umma tace sadiq a wannan lokaci irin ku sun yi ƙaranci,mutane masu amana,gaskiya da sadaukar wa,tabbas kai aboki ne na hakika ka zame wa marigayi uwa da uba kuma ɗan uwa haka baby kun bata tarbiya,Ku nuna mata so da kauna Allah kadai zai iya biyan ku ladan wanan hidima da ku kayi ina fata zumunci ya daure a tsakanin mu na har abada, Allah ya sanya maku albarka, Allah ya kare ka da kariyar sa a duk inda kake a faɗin duniya, Allah ya raba ku da sharrin mahassada,shaidan,mutum da aljan Amin.

Ya hydar yace,umma ta gama faɗin komi nima ina ƙara gode ma ku tare da fatan alheri a duk inda kuka kasance....,aunty sadeeyah ta rik'o hanun ammie,"Ina ƙara jajanta maku akan rashi da muka yi na ɗan uwan mu fatan Allah ya sada shi da rahamar sa amin,don Allah kuyi hakuri da baby wallahi ba haka take ba zaman ta Sokoto duk ta canja wanda ban san dalilin ba,na tabbatar maku za ku ji daɗin zama da ita.

Murmushi ammie tayi,uhmm na fahimci haka dama yaro idan ya kai wani certain age(adolescent stage) idan ba ANYI da gaske ba tankwasa shi zai wahala ku taya mu da addu'a na yi maku alkawari zan kula da baby fiye da tunanin ku,zan daura daga inda kuka tsaya wurin bata tarbiyya,INSHA ALLAH zata samu ingantaccen rayuwa wace ta rasa a baya...,duka suka amsa da Allah ya bada ikon Amin.

Alaji habu yace maganar karatun ta yanzu a wani mataki take.?,ss2 dai take kuma son nuna tana da kokari sosai,"cewar General Sadiq.

Shike nan dama zamu koma sokoto ganin likita zan je har can gidan gwaggo a dauko kayanta sai a amsa mata transfer letter taci gaba da karatu wurin mu.....,hakan ma yayi zan yi kokarin yin waya da gwaggo kafin ku tafi.

Suka ci gaba da tattaunawa dai domin ranar za subi jirgin 3:pm zuwa Kano,su General Sadiq kuwa washe gari zasu nufi Yola.

Zuwa karfe biyu kowa yayi Sallah sun ci abinci, General Sadiq ya shiga d'akin babu wace ke zaune saman bed da alama taci kuka har ta gaji.


Ya jima tsaye yana nazarin ta daga bisani yace BABY!,shiru ba amsa..., ɗago idanun ki ki kalle ni., still Bata ce komi ba kuma bata kalle shi ba"I SAID LOOK INTO MY EYES,ya FAƊI cikin ɗaga murya!

A hankali ta ɗago suka haɗa ido,nan da nan ta sauke nata idon domin nashi kamar garwashin wuta ya koma saboda kad'uwa.


Kin ga alamar wasa a idanu na.?, girgiza kai tayi,ya sake daka mata tsawa"OPEN YOUR MOUTH AND TALK,tace a'a....

Listen and listen Good,yanzu ba tare da bata lokaci ba za kibi ammie'n ki da yan uwanta zuwa kano,wacce ta fi kowa iko da kusan ci dake, Allah yasan na riƙe ki bisa gaskiya da amana,i did all my possible best to make u happy and who you are today!zama na dake ban taɓa daukan ki a matsayin bare ba sai d'iya wacce na haifa,haka mata ta kin su kulawa, soyayya,kauna da yarda a wurin ta,dispite all that,we ask for nothing in return,lokaci yayi da zan baki umurni kibi ko kina so ko bakya so ya zama dole ki koma hannun Ammie,ki zama mai biyayya a gare ta da duk wani na gaba dake wanda rashin yin haka a gare su zai janyo rashin jituwa a tsakanin mu,na rantse da Allah idan kika sab'a mata BAN YAFE MAKI BA,Allah ya kai ku Lafiya"ya juya ya fita.

Tashi tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa dama bata zo da wani kaya ba sai tsarabarta na wurin aunty sadeeyah babban jaka ciki ta saka abaya ta fito lokacin duk suna palour ita ake jira,ko kallon ta aunty sadeeyah Bata yi ba suka fito domin masu rakiya airport....,koda suka Isa passenger basu gama taruwa ba saboda sun fita da wuri.

General Sadiq gefe tare dasu ya hydar suna ƙara tattaunawa akan matsalar baby...,gefe ɗaya kuwa aunty sadeeyah CE ke ƙara kwantar masu da hankali har aka fara kiran passenger faruk na hanun baby ta zo har wurin da su General ke tsaye ai nan take ta fashe da kuka tare da rungumo aunty sadeeyah tana faɗin"aunty kiyi hakuri don Allah ba zan sake ba...., rungumo ta tayi tana tapping bayan ta cikin tsigar rarashi,it ok baby,idan kun tafi ki zauna da kowa lafiya kin ji, always be a good girl Allah ya maki albarka Amin.

General Sadiq da jikin shi yayi sanyi yace ku tafi suna jiran ki sai mun yi waya ko.?,tayi nodding suka tafi.


Suna tsaye har jirgin su ya tashi sanan suka nufi gida cike da kewar su.....,basu tsaya bata lokaci ba suka shiga haɗa kayan su(gado da kujeru dama nan suka same su),komi nasu wanda suke so suka haɗa aka zuba cikin motar shi dana sadeeyah wanda driver zasu ja tun da asuba zuwa yola domin su General Sadiq jirgin safe zasu bi.....,tun a daren suka fara sallama da yan uwa da abokan arziki.

Da misalin ƙarfe 9am suka kama hanyar Yola by air..


Around 4:10pm jirgin su ammie ya sauka a kano,gidan ammie suka nufa direct inda su Hadiza da saratu suka shirya masu abinci aka yi serving kowa Banda baby wace tace ba zata ci ba,ammie tace da Hadiza ta kai kayan baby d'akin da take kwana nan zata zauna,da yake gidan ba bakon baby bane ta gane d'akin da ba'baa mairo ta zauna ne amma an gyara shi sosai da babban gado ga plasma tv manne a bango....,wanka ta shiga tayi sallah.

Su umma ma sallah suka yi domin ranar zasu koma gida,da suka kebe ta ƙara yiwa ammie nasiha sosai akan rayuwa kuma ta riƙe baby akan amana da gaskiya.

Driver alaji habu ya basu ya kai su gida cike da arziki haka suka rabo da ammie jiki a sanyaye.

Da yake ranar ba gidan ammie ya kamata ya kwana ba sallama ya masu ya nufi gidan hajia mariya tare da saratu.

Tunda baby tayi sallah tana zaune bakin gado ta haɗa kai da guiwa maganar duniya Hadiza tayi amma bata amsa ta ba dole taje ta faɗa ma ammie,da kanta ta shigo Dakin tare da zama kusa da baby ta dafa ta,"meke damun ki baby.?,shiru babu amsa,ko zama dani ne ba kya so.?,ta amsa da eh...,Ni kuma ina son ki a na son zama dake har ga Allah domin nice na haife ki duk duniya baki da tamkar Ni...

Oh yanzu kika san _NIMA 'YACE_.?,ko ada can ke y'ata ce baby Quruciya da rashin yadda da ƙaddara yasa na wulakanta ki sanan abinda ya faru a baya ya wuce ki daina tuna shi ina jin ciwon hakan.!

Abu ɗaya zaki mun a duniya wanda zan yadda kina sona kuma ba zan sake tuna abinda ya faru a baya ba...,fadi ko menene idan bai saɓa wa Shari'a ba zan maki shi.

Ok daga yanzu kada ki sake shiga tsabgata,kada ki sake kira na diyar ki koda wani ya tambaya ban haɗa komi dake ba,idan kika mun haka kin gama mun komi a duniya ba zan sake tuna baya ba zamu zauna lafiya!

Idanun ammie sharaf da hawaye tayi nodding kai,shike nan idan har hakan zai faranta ranki consider it done,ta tashi ta fita jiki a sanyaye tana iya duk nata tayi banging door din ta faɗa saman gado tare da fashe wa da wani irin kuka mai cin rai,"Ya Allah why am I suffering for someone's mistake.?,why me.?,Allah ka agaza mun yaya Mallam ya tafi ya bar i da baƙin ciki a duniya Yau gashi sanadin Abunda ya aikata nice KE wahala..., Hadiza da tunda suka fara magana da baby tana tsaye tana ji har suka gama ammie ta koma d'aki gashi shiru bata fito ba, shine dalilin da yasa ta bita d'akin nan ta same ta tana kuka tana sambatu....,itama kuka ta shiga yi domin tasan komi mamanta ta sanar da ita duk abinda ya faru tsakanin ammie da yaya Mallam har haihuwar baby.

Rarashin ammie ta shiga yi tana kwantar mata da hankali domin su ba Baby LOKACI su gani ko zata saki jiki dasu,da kyar ammie tayi shiru domin bata so Hadiza ta sani ba sai gashi anyi komi a kan idanun ta.


Haka gidan ya kasance shiru ammie na d'aki bata fito ba,baby na d'aki hadiza ne kawai a palour tana kallo itama gajiya tayi ta nufi d'aki dauke da plate na abinci da bottle na ruwa ta kai wa baby wacce har ta fara bacci Hadiza ta tashe ta,da kyar da magoya ta ci abincin kaɗan sanan suka kwanta.


Da safe tare da Hadiza suka gyara gidan suka haɗa breakfast,domin baby ta lura tana da hakuri da sauƙin kai...,ammie da zazzaɓi ta tashi saboda kuka da damuwa da ta saka wa kanta,Hadiza ta taimaka mata tayi wanka ta ɗan sha tea kaɗan sanan tasha magani taci gaba da bacci....,koda Hadiza ta faɗa wa baby ta shiga ta duba ammie banza tayi da ita domin ba damuwar ta bane.

Kallo suke a palour amma hankalin Hadiza na kan ammie,jim kaɗan sai ta shiga ta duba ta shiru bata tashi ba,waya ta daga ta kira Daddy (alaji habu) yace gashi nan zuwa.

Baby kuwa ta kira aunty sadeeyah suka sha hira domin ta shaida mata sun isa Yola lafiya faruk na can yana ta wasa da yan uwan shi....,murmushi tayi,ina gaida uncle nasan fushi yake dani aunty ki bashi hakuri Allah mun shirya da ammie.!,iba fushi yake dake ba abunda ki yine Bai ji daɗin shi ba kuma INSHA ALLAH idan na tafi Kaduna zan biyo Kano in gan ku.

Yauwa aunty na sai kin zo suka yi sallama....,koda alaji habu ya iso baby ta gaida shi kamar yadda taga hadiza tayi har ƙasa,ya amsa masu ya haura saman.

Babu laifi ta tashi kuma taji dama, rungumo ta yayi a jikin shi yana shafa jikinta a hankali tare da kwantar mata da hankali...,tayi luf ajikin shi ganin haka yasan abinda take so domin rabon shi da ita kwana hudu kenan,bai bata lokaci ba ya haɗe bakin shi da nata Yana kissing cikin kwarewa tare da shafa dukan sassan jikin ta...,nan take ta rashin lafiya ya tafi ta biya mashi suka faranta wa juna rai.

Bayan komi ya lafa suka yi wanka tare ya shirya ya fito har wurin mota ta raka shi ya nufi wurin aiki.koda tadawo ciki suna kitchen ta dan leka su tare da faɗin sanun ku da aiki.?,Hadiza tace ah aunty har kin fito ya jikin.?..,ta amsa na warware me kuke dafa mana ne baby.?,"idon matambayi,shike amsar da ta bata.!,murmushi tayi ta koma palour kawai domin ranta ya ɓaci da maganar baby,iqrah chennal ta saka inda karatun Alqur'ani ke tashi..., relax tayi saman three seater karatun na ratsa ta har aka kira Sallah ta haura sama.

Kamala aikin suka yi aka zuma a foodflask ko wace tayi wanka suka yi sallah baby tabi lafiyar gado abunta .

Wuraren la'asar tace su shirya zasu fita wanda baby bata so ba amma Hadiza ta matsala suka shirya suka fita cikin motar ammie sai Nasarawa G.R.A tayi parking mota gefe suka shiga da sallama,"madaidaicin gida ne mai ɗauke da dakuna manya uku gefe sai babban palour shima da daki ɗaya ciki da toilet ,muryan wata mata suka jiyo daga kitchen Wanda ko a mafarki baby ba zata manta muryan ba"ba'baa mairo shine abinda babu ta furta tare da shiga kitchen din a guje ta rumgume ta tana faɗin ba'baa mairo ashe kina nan.?,wacece wanan haka zata k'arasa ni.?

Tana dagowa suka haɗa ido da ammie gefenta Hadiza ne sai wace ke rungume da ita,"nice baby ba'baa mairo baki gane Ni bane.?...,baby dama kina raye Shekara da shekaru babu labarin ki muna ta cigiya da Ammie shiru!

Ina nan ba'baa yanayin rayuwa ne,ya bayan rabo.?,sai alheri baby mu shiga daga ciki mana...,suka isa palour'n aka gaisa tace Hadiza dauko maku zobo a fridge Nan take tayi wa ammie gaisuwa rasuwan yaya Mallam,sai da ta bari hankalin su baby ya dauku wurin kallon film taja hanun ammie zuwa kitchen Dama DAMBUN shinkafa take yi.

Kallon ammie tayi,ashe an samo baby kuma.?,,kuka ta fashe mata dashi dama abinda ya kawo Ni wurin ki kenan ba'baa mairo ki taimaka baby na Nan saka mun ciwon zuciya.!

Cikin sanyin jiki tace saboda mene?.,ammie ta kwace komi ta sanar da ita tun haɗuwar su a Sokoto har dawo wannan su.!, ba'baa mairo ta jinjina maganar sosai duk da tasan ba'a kyauta wa baby ba Amma bai kamata tayiwa iyayenta haka ba",tau ammie kin san yaran yanzu ka haife sune baka haifi halin su ba Musamman ya'ya mata idan ba'a tsawata masu da wuri ba ,zai zame masu matsala a rayuwar su na gaba,zan so kiyi duba da rayuwar ki a baya yadda kika taso da irin soyayya da yaya Mallam ya baki tare da hana kowa tsawata maki, menene hakan ya haifar a gaba.?, BABBAN abun kunya,rugujewar farin cikin ki, ɓacin suna,lalacewar tarbiyya ga tsarabar haihuwa.

Tun wuri ki tsawata wa baby wallahi,bilahil azim idan har kika mayar da kanki uwar banza wai kina daukan wani banzan alkawarin yarinya ƙarama sai kin yi kuka a gaba,ba baki nayi maki ba,kada ki yadda soyayyar d'iya ya rufe maki idanu ki ƙasa ganin gaskiya,kada ki sake Tarihi ya maimaita kanshi Ni dai na baki shawara a matsayi na ta uwa a gare ku baki daya daga ke har mijin ki shawara ce.

INSHA ALLAH ba'baa mairo zan kula Nagode,,yauwa taci gaba da bata shawarwari Yadda za ta zauna lafiya da baby har suka kamala aikin ba'baa ta kira baby ta kwashe kayan zuwa palour cikin plate ɗaya ta haɗa masu suka ci sai magrib suka biya gidan hajia mariya dake lamid'o crescent har zuwa isha'i suka nufi gida.



Haka rayuwa ya kasance

23 / 35
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted