Author : LEEMA Category : KDP NOVELS
mai cotonou take Karatu.
Shirin komawa take yi sisi domin bata tunani zata sake dawo wa hutu sai ta gama tunda semester biyu ya rage masu.
Kafun ta koma sai data je kumbotso ta ƙara kwana biyu sanan ta dawo ranar da zata tafi har da kuma a airport saboda auren sarah da za'a yi bata nan.
Ta koma schl lafiya da yake basu fara lecture ba sai anyi placing results Wanda yayi passing dashi za'a yi proceding zuwa final level,yanzu kawai daga bacci sai ibada da chat cikin Hikima da wayau sai da sadat yasan sunan schl ɗin nasu domin yana da niyar zuwa ayi ta ta kare idan bata sonshi kawai ya hakura Allah ya bashi wata.
Kwana biyu da dawowar su aka fitar da result nasu wanda baby Bata da matsala ko ɗaya duka courses ɗin nasu tun daga first semester har second Bata da kyara.
Kawai ta fara process na registration da sauran abubuwa cikin kwana biyu ta gama ta amshi course outline the time table nata.
RANAR Sunday aka kawo mata fresh student a matsayin room mate nata wata yarinya wace ba zata wuce 18yrs ba daga agadaz sunanta khaleesi bata ko jin Hausa daga turanci sai Yaren su.
Lafiya lau suke zama tana putting nata through Har aka fara leactures ita dai bata sake ganin rahama ba ashe ta samu spell over.
Sati biyu da komawar ta makaranta sai kiran sadat ya shigo wayarta wai tana ina.?
Tace tana class Wai ta fito yana cafteria.
Ta ɗauka wasa ne bata damu ba ta ci gaba da karatun ta can ya sake kira shine fa ta fito ta ganshi zaune ya sanya yadi mai kyau da shek'i wanda ya amshi jikinshi har ana ganin farin vest dake ciki.
Kujera ta ja ta zauna nesa dashi tare da gaishe shi,ya amsa idanun shi kyam a kanta Domin wata ɗaya kenan cur da haɗu wani su bai sake ganinta ba sai yau.
Ya karatu"yace da ita a sanyaye?
Alhamdulillah ya aiki?
Da sauki gani nazo ganin matata.
Uhm tace kawai,babe don Allah ki bani dama mana na azabtu akan son ki,kin san bani na daura wa kai na ba amma kina wahalar da zuciyata.
Sadat Ni ban wahalar da kai ba shi yasa tun a farko naso ka fahimce ni amma ka kasa.
Ok kina nufin inyi hakuri kenan?
Eh tace a takaice.
Zan yi hakuri amma sai kin faɗa mun dalilin da yasa bakya sona.
Hawaye suka wanke mata fuska sadat ba wai bana son ka bane,idan na faɗa maka labari na walahi sai ka tsane Ni tsana mai tsanani wanda zai dakushe son nan a cikin zuciyar ka.
Kin gane feel free and tell me everything INSHA Allah zan fahimta kuma ba zai saka in tsane ki ba.
Ta ɗauki lokaci mai tsayi tana kallon shi cikin ido ta rumtse ido ta buɗe wasu hawaye Masu zafi suka sake zubo mata nan take tayi ƙarfin hali ta fara bashi labarin tun daga tasowa ta a gidan karuwai har wahalhalun da tasha na rayuwa zuwa zamanta Lagos har ta gane Gaskiya,mutuwar yaya Mallam har zuwa dawowa ta kano cikin da tayi,mutuwar ammie haihuwarta da auren ta daya watse sanadiyar mutuwar yaya ɗan Gusau!
Zaro ido yayi yana share hawaye domin wani irin tausayin ta yake ji yana shigar shi,yana imagining yadda ɗan adam zuwa sha wahalar rayuwa har haka ga kadarori iri iri.
Share mata hawaye tayi da hanun shi har ta samu natsuwa ya riko hanunta duka biyu ya saita kanshi.
Kin gane ko babe wanan ba matsala b'ace domin kema 'yace kamar kowa,abubuwan da suka faru is part of your destiny babu wanda ya isa ya canza haka,ki gode wa Allah da ya baki ikon cinye wanan jarabawa har kika fara samun sauyin rayuwa which I believe zai daure har abada INSHA Allah ina tare dake bazan taɓa juya maki baya ba cuz KE nike so and nothing can change that.
Calming nata yaci gaba da yi har ta sake ranta suka taɓa hira yace ta shiga masjid tayi sallah anjima zai dawo su tafi gidan grandparents nashi ta gaisa dasu.
Godiya ta mashi ta wuce hostel Yana ta kallonta har ta shige sai tausayinta yake yi koma bai ga laifinta ba da ta ki amincewa dashi a farko.
Wanka ta fara yi tana jin wani natsuwa da nishadi tayi sallah ta jima tana adu'oi kafin ta kamala taci abinci ta kwanta sai 4:30pm ta farka a gurguje ta watsa ruwa tayi sallah saboda leacture da suke dashi.
Tana Isa venue d'in lecturer ya hana ta shiga dole ta window ta tsaya har ya gaba ta dawo hostel.
Around 8pm tayi ta wanka chikin riga da skirt na atamfa Mai kyau ta saka hijab madaidaici ta ɗauko phone nata saboda sadat ya iso,koda ta isa wurin motar yana sanye da ƙananan kaya ya ƙara kyau sosai ta shiga siyasa yaba kwaliyya yake yana zolayarta wai amarya suka isa gidan.
Irin gidajen gargajiya nan ne na sarauta amma komi na ciki na zamani ne,suka zauna a wani sitting room Mai kyau da tsari har grandma nashi ta fito wacce ta manyanta sosai suka gaisa tana ta sanya ma baby albarka da fatan alheri.
Daga bisani uncle's da auntie's nashi suna ta shigowa ganin baby ana gaisawa har suka gama shigowa sanan suka nufi part d'in grampa nashi wanda yana riƙe da wani traditional tittle bayan sun gaisa.
Yace sadat ya masu bayanin komi game da baby Wanda wanan ba matsala bane ta ɓangaren su amma basu san gefen Dad nashi ba tunda Bahaushe ne ko zai amince,sun yi assuring nata komi zai zo da sauki idan har tana son sadat Kuma ta amince dashi zasu tsaya masu har ayi komi lafiya.
Godiya tayi masu da zasu tafi aka haɗa mata sha tara na arziki ya ajeta makaranta.
Bata yi baccin kirki ba tana tunanin maganganun grandparents nashi domin ta ga alamar akwai Matsala maybe sun fara magana da Dad d'in ne oho.
Tashi tayi ta gabatar da sallatul istikhara sanan ta samu bacci mai cike da muna nan mafarki masu ban tsoro!
_Halimatus Sadiya Muhammad_
*L££MA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
~sensational Heart touching story~
*BY*
*LEEMA*
_DEDICATED TO KANO STATE_
*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..
*_Every moment of life is a step towards death.my sincere condolences goes to the family of Alhaji Ibrahim Bello ribah [my family] for the loss of our beloved wife and sister"Maryam bello gwandu",uncle Ibrahim (prince)pls accept our most heartfelt sympatheties for your loss.Allah ya raya abinda ta bari ya sanya mata albarka amin_*
~🅿75~
*LAST PAG£*
Da safe ya dawo cikin schl ɗin sun jima tare yana kwantar mata da hankali da bata tabbacin komi zai zo da sauki su dage da adu'oi haka suka rabo tana matuƙar jin kewar shi.
Cikin kankanin lokaci soyayya mai ƙarfi ya shiga tsakanin su wanda bata iya runtsa waba tare da taji shi a waya ba,sune vedio call,chat da waya akai akai.
Lokacin da grandparents nasu suka gabatar da maganar wa iyayen shi mum hada taka rawa samu da farin ciki ga tausayin Baby dake Ratsa ta matuƙa.
shi kam Dad ya nuna rashin amincewar shi gani yake za'a gauraye masu zuri'a da mugun iri yayinda brother nashi da sister suka mara mai baya domin basu ga dalilin auren shegiya wace ta haifi shege ba cikin ma sadat ya boye masu bai sanar dasu brother mamanta ya ma sister nashi ciki ba da abun ya fi haka zama worse.
Wasa wasa Dad yaƙi amincewa a tafi neman auren baby Kano gashi har an sanar dasu alaji habu za'a zo shiru har aka kwana biyu basu zo ba.
Baby na school Bata San wainar da ake toyawa ba domin alaji habu ya hana a sanar da ita kada ta tashi hankalin ta komi nufin Allah ne.
Abun ya zama faɗa tsakanin iyayen shi har mum ta nemi ya bata takardan saki idan ba zai amince da Baby a matsayin matar ɗan shi ba!
Shi kam yace bai sakin ta kuma ba zai amince ba sai dai tayi abinda taga dama babban baƙin ciki yaran shi sun goyi bayan shi da yan uwan shi.
Kullum idan sunyi waya sai tambayi sadat meke damun? ,sai dai yace mata stress ne ya mai yawa domin ba zai iya tayar mata da hankali ba.
Kota wani bangare adu'oi ake yi domin neman zaɓin Allah,ita kam tana schl suna exams Wanda daga shi sai final exams shi yasa bata da lokacin komi sai karatu bata damu da chat ba sai waya suke yi sama sama.
Bayan wata ɗaya da faruwar haka lokacin har su baby sun gama exams hutu suke wanda excursion (case finding) zasu tafi Egypt domin akan shi zasu rubuta project,Dad da kanshi ya shirya mutane yace da sadat ya shirya su tafi kano hada shi neman aure domin baya so a ɗauki lokaci.
Nafila yayi raka'a biyu domin nuna godiya ga Allah da ya nuna mai wanan rana,bai bata lokaci ba ya sanar da friend's nashi kuma ya buga ya sanar da alaji habu suna nan tafe.
Alaji habu ya yanke shawara a tafi kumbotso gaba ɗaya ayi nan aure da yanke lokaci.
Sai dai ya hydar ya sanar dashi yana da tafiya da ya taso mai kawai a yi komi nan Kano tunda shi ɗaya ne namiji a kumbotso.
Ranar da zasu zo manya uku da Dad na hudu,sai sadat da babban aminin shi Khalid suka iso kano,motoci biyu alaji habu ya tura airport aka dauko su zuwa gida koda suka iso an shirya masu abinci a babban sitting room na gidan.
Alaji abu da aminan shi biyu suka tarbe su aka gaisa daga nan aka basu dama suka cika cikin su da delicious kala kala.
Bayan komi ya lafa suka gabatar da abinda ya kawo su(neman aure),nan take aka amince suka bada kuɗin gaisuwa Naira dubu hamsin da kwandon goro biyu,uncle d'in Sadat ya nemi da a yanke sadaki a saka lokaci domin basa so a bata lokaci.
Alaji yace su bashi lokaci idan yayi shawara da sauran yan uwa za'a neme su!
Dad ya yaba da irin tarban da aka masu,haka suma gefen baby sun yaba da natsuwar sadat basu wani ɗauki lokaci ba suka tafi.
Tunda suka dawo yake lafe jikin mum Yana zuba mata shagwaba a dole ya kusa zama ango sai pleading yake tayi ma Dad magana kada auren ya wuce one month....,tayi assuring nashi yadda yake so za'a yi wanda hakan ya mashi daɗi.
Wayar baby yayita nema bai samu ba sai lokacin ya tuna da tana Egypt contact nata na Nigeria bai shiga tunda ba layin can ya saka ba dole yayi hakuri har ta dawo.
Zama suka yi da ya hydar aka yi shawara akan a aje auren sai nan da wata uku dai dai ta kammala exams saboda kada hankalin ta ya rabu gida biyu,sadaki kuma duk abunda ya yanke dai dai ne ya yanke amma ba za'a amsa ba sai ranar daurin aure.
Alaji habu ya kira UNCLE d'in Sadat aka sanar dasu an yanke sadaki Naira dubu hamsin lokacin aure kuwa nan da wattani uku masu zuwa,godiya yayi masu ya kashe.
Sadat da kukan shi shabe shabe wai lokacin da aka saka yayi nisa da yawa mum tayi ma Dad magana a rage lokaci mana,rudewa tayi ta shiga aikin rarashi har ya hakura ya koma bakin aiki domin mum ta faɗa mai ya bar komi a hanunta ita zata shirya darling babyn ta.
GENERAL SADIQ ma bai so a saka lokaci mai nisa ba domin bashi da wani buri da ya wuce yaga sun aurar da baby ko hankalin su zai kwanta,aunty sadeeyah ta kwantar mai da hankali suci gaba da addu'a Allah tabbatar da mafi alheri.
Shirye shirye aka fara ta ko wane bangare,amarya na schl tana fama da karatu wanda ango ya kasa hakuri sai da ya kai mata ziyara har cotonou suka sha soyayya ya dawo,tun daga lokacin ya kan je lokaci zuwa lokaci har ta kammala exams tare suka dawo kano.
Su sarah amarya sai tsiya suke ma baby Wai zata shiga sawun su taji Yadda ake ji,ita ko Hadiza dake dauke da ƙaramin ciki laulayi ya sata gaba shi yasa bata wani sakewa cikin jama'a ga karatu yanzu 200level suke going to 300level.
Umma yar kallo ta koma ganin yadda ake ma baby gata ta ko ina kayan gidan ta ma order akayi daga waje wanda za'a wuce dasu kebbi direct.gyara jiki ciki da waje kowa har kuka tasha saboda yadda ake murzan jikinta ga dure duren magunguna har ciwo cikinta keyi.
Su Hadiza sai tsiya suke mata idan ta fara kuka,satin buki na zagayo wa Aunty sadeeyah ta iso kano aka shiga hidima babu kama hannun yaro domin duk abinda ake buƙata sun haɗa shi kuma sun tsara komi walima kawai za'a yi domin neman albarkan aure.
Ranar Wednesday da safe baby ta shige lalle kuma a ranar su aunty samirah suka iso da kayan lefe wanda ya haɗu ba ƙarya,sun gaisa da baby sai yaba tsarin ta suke.
Ranar friday da safe aka gabatar da walima a harabar gidan nasu wanda ya samu halartar yan uwa da abokan arziki na nesa da kusa ciki hadda su aunty ladies da aysha mu'azu wace ke aiki a Federal court of Justice Abuja Allah bai kawo mata miji ba har yanzu, addu'a Baby ta mata Allah ya kawo na gari.
Da yamma ango ya iso da tawagar sa wanda aka kama masu hotel ɗaya shi da iyayen shi nan zasu kwana har gobe a d'aura aure su wuce da amarya.
Yaso kwarai ya kebe da amaryar shi amma babu dama su aunty sadeeyah sun Bata tsaro na musamman.
Washe gari da karfe goma na safe dumbin al'umma suka shaida daurin aure"SADAT ABDULMUMIN DA AISHA MUSTAPHA (BABY),ango sai washe baki yake saboda farin ciki,cikin gida suka shiga aka gagaisawa da mutane.
Zaunar da baby akayi cikin palour aka tasa ta gaba, General Sadiq,alaji habu,ya hydar.
Nasiha mai ratsa zuciya suka mata akan zaman aure sai aikin kuka take yi domin tasan zata yi kewar su sosai.
Nan cikin daki kuwa da kyara aka raba ta dasu naziya,ga little Sadiq dake ta kuka domin yayi wayau sosai,su Hadiza ma kuka suke saboda sabo haka Aunty sadeeyah da Aunty nafisa suka saka ta a mota da zuwa airport domin tare dasu za'a kai ta.
Ango ke jan motar ya shiga kwantar mata da hankali domin ya tsani ganin hawayen ta,su aunty sadeeyah kunya ne ya cika so ganin yadda yake nuna mata soyayya a gaban su.
Suna isa birnin Kebbi geren motoci ne suke kiran isowar su domin zuwa gida wanda har lokacin amarya kuka take yi.
Ana isa gidan mum dake tsaye da tawagar ta ta nufi mota tare da rungumo Baby tana mata Barka da shigowa family nasu,tana riƙe da ita har bedroom nata inda tayi mata masauki,su aunty sadeeyah kuwa part d'in baby aka nufa dasu tare da biyo su da kayanta.
Gaskiya ba laifi an gyara part din SOSAI duk da ba nan zasu zauna ba Abuja zasu wuce komi yaji sai godiyar Allah.
Mum da kanta tayi feeding baby Shima ya shigo yana ta zuba shagwaba har aka kira sallah na tayi sallah.
Da yamma aka shirya zuwa dinner a royal event center dake cikin garin birnin kebbi, faɗin tsaruwar hall d'in Bata baki ne.
Amarya da ango suka sha anko cikin royal blue shadda sai shek'i suke,ga iyaye da yan uwa cikin anko.
Uwargidan Gwamnan Kebbi ta gabatar da nasiha zuwa ga amarya da ango,daga nan aka fara ciye ciye ga cool music na tshi,ango na lake da amaryar shi ya hana ta sakat sai tsiya abokan shi suke mai.
Zuwa 10pm aka tashi ai kuwa ya ɗauki amarya shi da kanshi sai Safar guest inn,tsoro ne ya kamata yadda ya ke ta murmushi ƙasa kasa ai kuwa ta noke bata shiga ciki,juyin duniya taki amincewa da yaga zata bata mai lokaci ya sungume ta tun daga harabar hotel ɗin har room din da ya kama sai wuntsil wuntsil take yi tana magiya amma ko a jikin shi sai saman bed ya dire ta sanan ya fita ya koma ya rufe motar shi ya dawo ciki tana dunkule saman bed d'in ya fara rage kayan jikin shi ya shiga wanka har ya fito tana zaune wurin da ya barta.
Rik'o hanunta yayi,babe zo muje in maki wanka muyi bacci,kuka ta fashe dashi cikin shagwaba"bana so ka kyale Ni kuma ba zan kwana anan ba gida zamu.
Ni kuma ba zani gida ba saboda nasan mum ba zata amince ki kwana wuri na ba mutane sun yi yawa and Ina bukatar ki kusa dani tonight.
Shiru tayi kawai tana sharan hawaye,kin gane babe ba komi zan maki ba ina son jina a jikin ki ne yau,haka yayita mata daɗin bakin har ta amince ta rage kayan jikinta ta shiga wanka tana fitowa yayi dai dai saman bed Yana Shan farm pride youghurt abun shi daga shi sai boxer, rab'e rab'e ta Kama Yi saboda towel be a jikinta hannu ya miƙa mata ta iso wurin shi a hankali ta zauna tsakanin laps nashi ya rungume ta sosai tare da sauke nanauyar ajiyar zuciya domin shi kaɗai yasan yadda yake ji.
Itama haka kawai ta sake jikinta tare da ƙara nutsewa cikin shi tana lumshe ido har zuwa wani lokaci ya juyo ta suna facing juna haka kawai taji wani nauyi da kunyar shi ya kamata ta done kai cikin chest nashi.
Ɗago ta yayi da niyar haɗa bakin shi da nata wayar shi ta shiga ringing Wanda ya manta Bai kashe ba.
Ganin SWEET mum a rubuce ya saki wani malalacin murmushi tare da sawa a handsfree"hy sweet me...
Shut up baby doll,Ina babyna.?
Relax she's with me mum.
But Why?
Haba mum nida matata kuma sai an tambayi dalili idan na fita da ita!
It ok,Amma kasan ba haka akeyi ba atlest ka yi hakuri har yan uwanta su wuce mana sun shigo nan hankalin su tashe