Chapter 15 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   15 / 35

42K to 45K   out of 103.7K words

tana sauraran shi har suka isa gida motar yaya Mallam na bayan nasu ta shiga ta haɗa komi nata ya rako ta cikin gidan.


Bata yi aikin komi ba domin Peter na nan iyakan ta kallon film idan ta gaji ta koma dakin ta kwanta har zuwa dare da yake ranar Friday ne babu islamiyya,su Captain suna wurin aiki.


Bayan sallar isha'i gidan yaya Mallam suka haɗu su biyar da abokan su nan suka ci dinner suna ta hira har zuwa 10pm kowa yace zai shige BLOCK nashi lokacin Captain sadiq yace wai ina daughter be.?

Yace inaga tayi bacci,ok ka faɗa mata da safe aunty'n ta sun sauka lafiya tana gaishe ta..yace ok mu kwana lafia gwauro.


Sai da ya rufe ko ina ya nufi d'akin baby fuskan Nan tashi a murtuk'e yayi banging door d'in,"kwance take saman bed tana bacci hankalin ta kwance..,ya riko kafafun ta duka biyu ya jawota feyt ya zubar da ita saman tyles ɗin.!

Baƙin ta ɗauke da sallati ta buɗe idanu,yaya Mallam ta gane tsaye kamar a mafarki..,don uwarki daina kallo na,shegiya kawai,babu yadda banyi ba kada kizo duniya amma sai da ta haife ki,kika zame mun ibilishiya,kin hana Ni jin daɗin rayuwa kullum da baƙin Cikin ki nake kwana nake tashi,ban taɓa son ki ko son ganin ki ba cikin duniya kina numfashi,wallahi tun da aka samu cikin ki duke wani farin ciki da walwala nawa ya kau,na zama abinda na zama ne(army) kawai don na wulakanta rayuwar ki idan kina raye,idan kin mutu in wulakanta rayuwar uwarki...,sai gashi Allah ya kawo ki cikin sauki ƙarƙashin kulawa na!

Now listen and listen Good,zan baki wasu task guda Uku idan har kika aiwatar da su yadda na umurta shine zai wanke mun zuciya yasa na yanta ki,ki zama Y'A KAMAR KOWA!!

Ita dai binshi take da idanu bata gane inda maganganun shi suka do saba,ashe dama yasan makircin da ya ke kulawa shine dalilin sake wani shi da ita?

_TASK NO-1:-za kiyi tarayya(having sex) da Captain sadiq kafun ya wuce Canada kuma ki tabbatar cikin shi ya shiga jikin ki!!_

Idanu ta ci gaba da zare wa tana girgiza kai alamar ba zata iya ba hawaye na zuba a idanun ta...

_TASK NO-2:-zaki shaidawa duniya Cikin shine ta hanyar shigar da ƙara kuma ki nuna so kike ki haifa masa cikin shi!!_

_TASK NO-3:-zaki zauna a duk inda yake da cikin nan har ki haihu duniya ta sani ki damk'a mashi abinda kika haifa shike nan ki dawo wurina!!_

_kuka ta shiga yi mai sauti tana faɗin"papa bani da kaman su a duniya sun yi mun abinda iyaye na da suka haife Ni basu mun ba,wallahi ba zan iya cin amanar aunty sadeeyah da UNCLE Sadiq ba!!_


Baby!,Baby!!,Baby!!!.., either u do as I said ko ki nemi wani uban bani ba,dama na gaji da ganin ki a duniya,wallahi i never wish for your success,I always pray for your downfall cuz u are a disgrace to me and entire family bastard kawai, na baki nan da gobe ki fara aiwatar da wanan aiki ko ina kashe ki na rantse da Allah Yadda na haifi shegiya kema sai kin haifi shege kin goya,d'akinya fice a d'akin...

Kuka mai cin rai ta fashe dashi tare da buga kanta da bangon d'akin"wayyo Allah na,Ni baby laifin me na aikata wa Allah da yasa na zo duniya ta wanan hanya..? kaifin me nayi Wa iyayena da basa sona..?,kowa gudu na yake babu wanda ke so na rab'e shi sai wayan'nan bayin Allah da suka mayar dani Y'A ,suka nuna wa duniya"NIMA Y'A CE kamar kowa,,,wayyo ammie na kin cuce Ni da kika dawo dani wurin papa mugu ne azzalumi baya tsoron Allah,,ammie kin cuce Ni da baki mayar dani wurin mahaifiyata ba"YA ALLAH KA ƊAUKI RAYUWA TA A WANAN DARE KO ZAN HUTA DA WANAN BAK'AR UKU'BA(subhanallah)!!


~ku gafarce Ni kuka ba zai bari naci gaba da typing da,ku sani Yan uwa musulmai wanan labari ya faru ne a gaske sai canje canje da aka samu na wasu part da umurni da aka bi na mai labari wacce ta hana aru ita "TRUE LIFE STORY" a saman littafi~😭
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..




*Masoya littafin"NIMA 'YA CE"ina yi maku fatan alheri a duk inda kuke,ina nishadan tuwa da comments sai kun yi hakuri da wasu abubuwa dake faruwa cikin wanna littafi wanda alal hakika ya faru ne a gaskiya ba zan so canza alakar labarin ba,ku sani ɗan Adam baya wuce ƙaddara shi ko ina yake a faɗin duniya, Allah bamu ikon kiyaye wa amin_*💞💞





~🅿35-36~


____""A daren ranar bata runtsa ba tayi kuka,kuka na fitan hankali,tayi adu'ointa na neman kariya Daga sharrin papan nata,ta saka wanan ta kwance wan can har aka kira Sallah asuba tana jin lokacin daya fita zuwa masjid kamar mutumin kwarai"tace cikin zuciyar ta",sallah ta gabatar itama ta jima cikin sujjada tana neman zaɓin Allah akan wanan masifa da yake son kunno Kai a tsakanin ta da mutanen da suka riƙe ta da gaskiya,ga Bacci tana aji amma ina bata da kwanciyar hankali.

Zuwa 9:40am ta fito bayan ta watsa ruwa babu kowa a palour'n da alama har kitchen da alama yaya Mallam ya fita wurin aiki,break fast ta gani saman dianing table"shima Peter ya gama aikin shi ya fita",ruwan tea Kawai tasha ta rasa mafita wa zata faɗa ma damuwar ta ya fahimce ta.?

Saboda Allah yanzu da taga gaban mahaifiyar ta akwai wanda ya isa ya tunkaro ta da wanan mumunan aiki.?,wai uban daya haife ka shine ke da wanan irin buri akan ka,saboda shi ƙaddara ta afka mai ya aikata zina shike nan ita ma yake so ta aikata,zinah ma da aminin shi wanda ya rike ta da amana,kai gaskiya ba zata iya ba sai dai ya kashe ta wallahi.

Zuwa yamma ya dawo daga wurin aiki har d'aki ya same ta,tana zaune idan banda aikin tunani babu abinda take yi"wani irin tsawa ya daga mata.!,babu alamar tsoro a idanun ta itama tayi mashi kuri domin tabar jin tsoron shi a yanzu...

Wane shawara kika yanke akan assignment Dana baki.?,ko dar babu cikin zuciyar ta tace"ba zan iya aikata wa ba!!

Bindiga ya zaro yayi pointing nata dashi kashe ki ba abu bane mai wahala a wurin na kuma na kashe banza babu abinda zai faru....,hawaye na zirya a idanun ta tace"papa KA kashe Ni domin nafi bukatar mutuwa da rayuwa a wanan lokaci rayuwata bata da wani amfani wanda suka haife Ni basu dauke Ni a bakin komi ba menene amfanin rayuwar tawa.?,na taso cikin wahala da ɓacin rai,ban taɓa sanin daɗin uwa ba domin ba tare da ita na tashi ba ammie itace ma cen da ta raine Ni da daɗi babu daɗi kuna tare har Allah ya haɗa Ni daki,,wallahi kwara ita sau dubu da kai...

Tsawa da daka mata"yi mun shiru makira,kalaman ki ba zasu taɓa tasiri a zuciyata ba wallahi ko kukan jini za kiyi yau sai na kashe ki,sanan ita ammie tace maki ba itace mahaifiyar ki ba.?

Zan sanar dake abinda baki sani ba a yau Hadiza(ammie) itace mahaifiyar ki uwar mu ɗaya uban mu ɗaya da ita,Ni aminu Mallam nine elder brother na ammie Kuma Ni ne nan nayi mata ciki taurin kanta yasa ta haife ki ,wallahi kashe ki zai fi komi faranta rayuwata a duniya....

Duke wa ƙasa tayi tana sallati duk wani addu'a daya zo bakin ta shi take yi"wanan wane irin kwamachala ne.?,yaya yayi wa kan wansa ciki???

Ai ko a garin arna ba'a wanan ɗan yen aiki,,papa don Allah kace ba gaskiya bane abinda kunnuwa na suke ji,wayyo naga rayuwa,wane irin jahilci ne haka,wane irin dabban ci ne wanan,iyayen ku suna ina kuka aikata hakan?

Suna gidan uban ki muka aikata yar iska ban yi niyyar sanar da kowa wanan sirri ba tunda har kika saka na fade abinda na sheka goma sha biyu ina boye wa wallahi kashe ki zan yi!

Ai kwara na mutu da wanan baƙin fenti da kuka shafa mun,gaske dai bana samun kulawa a wurin ammie ashe itama haushi na take ji,shi yasa bata so nayi mata maganan MAHAIFIYATA ashe itace ta haife Ni!wallahi tur da hali iri naku, Allah wadai da wannan kazamin rayuwa....,mari ya dalla mata,har kin isa ina fadi kina fadi!!!

Na isa har na wuce Captain Aminu ka kashe Ni nace ta riko hanuwan shi duka biyu tana ƙara tura bindigan a cikin ta....

Crut Peter dake labe a kofar d'akin tun da suka fara hayaniyar wanda haka ya nuna yaji komi da suka fadi,a guje ya fita zuwa block ɗin Captain sadiq dai dai zai fita cikin gari suka yi karo da Peter...!

Yana hakki yace oga Sadiq kazo babu lafiya ,oga aminu zai kashe yarinyar nan dake gidan ka.!!!

A guje ya bankade peter ya Isa gidan Captain Aminu,yana shiga ya jiwo hayaniyar su a d'akin baby, bankade kofar yayi a guje ya shiga tsakanin su sai da Captain Aminu ya faɗa saman bed,ITA kuma ta haɗa kai da bango,,,hanunta ya jawo ta tura ta waje yana faɗin"run for ur life baby,tsayawa tayi kamar gunkie ko gezau bata yi ba..,tsawa ya kara daka mata" i Said get out!!!

Fita tayi zuwa gidan Captain sadiq tana hawaye domin zuciyar ta a bushe yake,da wanan mugun labari da taji wallahi gwara mutuwar ta!!

Kallon kallo suka shiga yiwa juna na Tsawon lokaci..,Captain sadiq yace yaushe ka fara shaye shaye ban sani ba.?,laifin menene ta aikata da har za kayi barazanar ɗauka rayuwar ta saboda Allah yarinya ƙarama kamar baby zaka nuna wa bindiga!!!!


Waya faɗa maka barazana nake mata sadiq..,kafi kowa sanin halina bana barazana da bindiga koda ga abokan gaba idan na nuna sai na harba,kafi kowa sanin idan na har ba sai rai ya fita...

Yanzu kana nufin kashe ta kake da niyyar yi.?,sosai ma kuwa and babu wanda ya isa ya hana Ni aikata hakan domin ba uban wani ne ya haifa mun ita ba!

Kada ka manta da hanun ka,ka danka amanar baby a hanuna na wanda da bakin ka lokacin ka mallaka mun baby halak malak baka da wani sauran iko a kanta,idan ma wani laifi ta aikata ka sanar dani mana.

Sadiq laifin da baby ta aikata ɗaya ne"shine zuwan ta duniya a matsayin 'ya ta wanda idan ba kashe ta nayi ba hankali na ba zai taɓa kwanta wa,zuciyata ba zai taɓa samun farin cikin da nake nema ba,sadiq a dalilin haihuwar yarinyar nan na tafka Babban abun kunya wanda zai rinƙa bibiyata har karshen rayuwata,adalilin haihuwar ta na rabu da iyaye da kowa nawa,adalilin haihuwarta na kasa yin aure wanda inada bukatar haka...

Dafa shi yayi"Aminu ka yadda da ƙaddara ba'a kanka aka fara aikata zina ba kuma ba'a kanka aka fara haihuwa ba tare da aure ba,ka rungumi ƙaddara ka riƙe yarinyar nan ka bata kulawa da take da buƙata wanda bata samu a baya ba,ka nemi sulhu da yan uwanka Finally kayi aure kaci gaba da istigfari.


Sadiq cikin baby ba irin cikin shegen da aka saba yi bane a duniya"NI AMINU NAYI WA YAR UWATA HADIZA CIKI TA HAIFI BABY,YAR UWATA WACCE MUKE UWA ƊAYA UBA ƊAYA ka fahimce Ni Sadiq"ya Fadi cikin Daga murya yana kuka....

Wa'iyazubillah,allahuma ajirni fii musibatii,auzubillahi minash shaidanin rajin,"zame wa ƙasa yayi ya zauna,, Are U kidding me aminu?,what come over u,how comes????


Shima zama yayi kusa da sadiq,wallahi sadiq abinda ya faru kenan banda masaniya ciki ɗaya muka fito dai da komi ya faru,ka faɗa mun wani irin zuciya nike dashi da zan amince da baby.?,da wani idanu zan kalli iyaye na.?,me duniya zata ce game da wanan kwaba....

Shiru na ɗan lokaci Captain Sadiq na nazari...koma menene Aminu ka yadda da ƙaddara kayi accepting baby a matsayin 'ya kamar kowa sanan ka tafi ga iyayen ka nasan hankalin su a tashe yake har sai lokacin da suka ganka.

Sadiq babban abun baƙin ciki wai kamar ammie yar UWATA zata haɗa kai da wani a dawo da baby wuri na saboda tana son tona mun asiri a duniya, recently ya Kira Ni Wai sunyi aure yana so muje kumbotso tare shine dalilin da yasa na canja layi.

Amma kayi kuskure koma ina ga baka fahimce ta ba,ita mace ce dole gidan wani zata ba lallai ne ya aure ta baby na hanun shi ba,babu inda ya fi dace wa da baby kamar gidan ka tunda kai namiji ne matar ka zata iya kula da baby ko don farin cikin ka,,yanzu nasan iyayen ku sun san komi kawai ka hakura ka tafi gida.

Sadiq ba zan tafi ba domin wanan ba ƙaramin abu bane,ita kuma ammie bata da hujjar dawo da baby wurina tun a farko na umurce ta da a zubar da cikin baby Bata aminta ba,yanzu menene nawa,,don Allah sadiq ja cire kanka cikin wanan rikicin ka bani baby Kawai in kashe ta kowa ya huta.

Yanzu kayi wanka ka huta za muyi magana anjima..,da kyar ya lalaba shi ya shiga wanka ya fito daga gidan nan ya haɗu da Peter,tambayar shi yayi abinda ya faru...,ya faɗa mai duk abinda ya sani.

Yace ya shiga ya kwaso mai kayan baby ba tare da sanin Captain Aminu ba yana jiran shi.

Koda ya shiga gida baby na aikin kuka,itama wanka yace ta shiga magrib ya gabato,,babu musu ta shige toilet kuka ya hana ta aikata komi har aka kira Sallah.

Koda Peter ya kawo kayan a parlour ya aje ya rufe gidan ta waje ya wuce masjid.

Daya fito cikin gari ya nufa inda manyan bus suke tsayawa na tafiya zuwa garuruwa masu tashi cikin dare da kyar ya samu ticket guda biyu ya biya zuwa 10pm motocin zasu tashi.

Sai bayan isha'i ya dawo gida koda ya buɗe tana zaune saman sallaya dama ya masu take away na abinci ya aje mata ya wuce d'akin shi ya kai minti talatin yana waya kafin daga bisani ya shiga wanka ya shirya cikin shirt da wando,ya haɗa brief case din shi .

Koda ya shiga d'akin tana wurin zaune bata ci abinci ba...!,baby ya Kira sunan ta.
Kallon shi tayi ba tare data amsa ba.

Inaso ki ɗauki abinda ya faru yau a matsayin kaddarar ki,ki sani ko wane bawa yana da nashi jarabawar na rayuwa,ke musulma ce wace ta yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau,ki yadda dani Wallahi ban taɓa sanin abinda Aminu ya aikata kenan ba wanda ya raba shi da kowa nashi sai a yau,tabbas zuciyar shi cike yake da kiyayar ki zalla babu soyayya"baby zaman ki ba zai yiwo a cikin Barrack d'in Nan ko garin nan ba,, Allah yasan nida sadeeyah muna son ki duk da bamu san komi a kanki ba yanzu ma sanin wanan sirri ba zai canja komi daga son da muke maki ba,,Kinga yanzu saura kwana biyu bukin suna,naso mu tafi Yola tare amma hakan ba zai samu ba saboda ba kowa zai fahimce Ni ba akanki zan so kiyi hakuri zuwa karfe goma zamu bi luxurious bus mu bar Lagos...

A razane ta kalle shi,wallahi bazan koma wurin ammie ba kwara in zauna ya kashe ni gwara shi ya nuna mun soyayya duk da na karya ne,amma ita ban taɓa samun kwatan kwacin haka ba ta tsane ni,tsana mai girma tunda har ta iya boye dangan taka dake tsakani na da ita.!!

Wait baby,ba wurin ammie zan mayar dake ba,wurin da zan kai ki idan ba kece zaki nemi ammie ba har ki bar gidan ba zata taɓa ganin ki a ba, kinga lokaci ya kusa ga waya nan karama (baby Nokia) akwai layi a cikin number na Dana sadeeyah duka na saka maki dashi zaki tafi idan kina da bukatar wani abu ko akwai abinda ya shige maki dubu ki neme Ni cuz bana son kowa ya san inda zaki koma,karatu zaki ci gaba a can tashi mu tafi kayan ki na palour.

Tashi tayi jiki a sanyaye ta fito yana rike da jakan ta da brief case nashi sai daya tabbatar babu mutane a BLOCK ɗin nasu yace ta shige mota da sauri a buɗe yake.

Da sauri ta faɗa mota, shima ya shiga tare da bata wuta suka bar Barrack din idanun baby na zubar da hawaye tana yiwa wurin kallon bankwana.




"""__Tunda ammie suka dawo wani sabon babin soyayya suka buɗe ita da alaji habu duk ranar girkin ta yana manne da ita aiki da Sallah kawai ke fitar dashi,shawarwari da umma ta bata tayi amfani dasu wanda ta fara da kiran hajia mariya a waya kullum safe su gaisa tun tana shan kamshi har ta sake fuska,,ko wane weekend sai ta kai mata ziyara da tsaraba niki niki kafin ka sani ta saye zuciyar ta suka zama damkar ciki ɗaya suka fito,yaran ma sun sake da ita har suna zuwa mata weekend basu da abokiyar shawara sai ammie.

Ta fannin ba'baa mairo ko wane ranar juma'a ammie na kai mata ziyara ta wuni har dare da girki mai kyau da alheri kala kala.

Hadiza karama kuwa ta samu admission a lupaloy secondary School kano inda ta fara jss1.

Ammie yanzu bata da wani buri da ya wuce ta kyautata ma umman su da ya hydar duk abinda ta samu su take tura wa ana mata kiyo,idan Kudi ne ya hydar ke juya mata har ta saya ma umma furnitures ta gyara mata palour da kayan kallo,ga chest freezer data saya mata har paint ta saka anyi wa gidan nasu,ita kuma nafisa engine na nika ta saya mata ta rinka sana'a...,yanzu ta gane uwar masu gida baƙin ciki take mata sam bata sonta da arziki shi yasa ma ta janye jiki da ita ko waya bata kiran ta,idan itace ta kira sai tace mata bata gari!

Tana ƙara gode wa Allah da ya bata gwarzon miji irin Alaji habu wanda ke sonta saboda Allah,ya

15 / 35