Author : LEEMA Category : KDP NOVELS
ya dosa kenan wannan shine papan ta wanda ya haife ta...?,gashi ammie tace ba itace maman ta ba,kenan wacece maman ta..?
Adaidaita suka shiga taji yace Mallam nan kurna zaka kai mu,adaidaita yaja suka kama hanya jugum har suka isa lungu lungu ne sai kwata har bakin wani gida ya biya suka fito waya ya shiru daga aljihun wandon shi yayi dianing wani number "yes Ina kofar gida sai ya kashe....,wani mutum siriri fari tasa mai ƙaramin jiki ya fito har ƙasa ya kai yana gaida yaya Mallam da harshen turanci yace ya tashi mana ya bashi hannu suka gaisa"ya koma harshen yar banci suka ci gaba da magana yana nuna baby da alama akanta suke magana(Ni dai ban gane komi ba don baji nake ba Lol),sai gyda kai mutumin da aka kira da taufeeq yake yi naga yaya Mallam ya ciro bandir na ɗari biyar biyar ya bashi suka yi sallama ko kallon baby Yaya Mallam bai yiba ya juya fuskan nan a murtuk'e ya wuce...!,mutumin ya amshi jakar baby tare da rik'o hanunta suka shiga ciki.
Gida ne wanda da gani na haya ne d'akuna sun kai biyar ciki a jere tsakar gidan duk ya fafashe babu haske a tsakar gida kowa na sha'anin gaban shi Da alama mazauna gidan ba yan gari bane aiki ya kawo su ,tafiya suka yi har kifar wani daki madaidaici ya shiga da sallama wata mace mai kimanin shekaru ashirin da biyar k'atuwa ta amsa da fara'a amma ganin shi riƙe da yarinya yasa ta canza fuska,babu komi cikin dakin sai katifa madaidaici da akwatuna uku na kayan su"ya zaunar da baby a gefen katifan kayanta na gefe,matan ta mike tsaye tana masifa da harshen yar banci,naji mijin ya kirata da shukura cikin natsuwa yana mata bayani da yar banci tare da zaro kuɗin da yaya Mallam ya bashi yana nuna mata,ai kuwa ta warce kuɗin tana yashan haƙora a dole taga kuɗi...!,kallon baby tayi omoge yaya sunan ka...?,ta amsa da baby,ah Baby yaro mai chau papan ka tace zaka zauna damu for a while kafun tazo hutu dama Ni bata haifu ba ina so yaro sosai from now on call me mama me,shey u understand English..?tace yes mama me,,Gud girl"mijin da ya fita jin Hausa yace baby ki kwantar da hankalin ki papan ki zai koma wurin aiki gobe zaki zauna damu ki ɗauke mu kaman iyayen ki nida matata shukura Yoruba wan osun ne tare da papan ki muka yi training a Kaduna da yake Ni police ne kuma kurtu aka ajeni Ni nan Kano ina gadin gidan senata night duty Nike yi yanzu zan wuce aiki idan kina son WANI abu ki fada ma shukura...,,tace tau kawai !
Shirya wa yayi a hanzarce ya musu sallama ya tafi,shukura ko an samu duniya sai rawa take tana raira waka da Yoruba nci tana kirga kuɗin wanda dubu hamsin ne chif"kallon baby tayi u wan take ur bath ne..?
tace no,kayi beshi yanzu zan dawo tana daura zani saman skin tight trouser dake jikin ta da wani bingileliyar riga kai yasha kitson attach ta fita da kudin....,kallon d'akin baby ta k'ara Yi wayam daga ledar ƙasa sai katifa da fankan sama tayi imani ko d'akin su na tukuntawa yafi wanan sosai gefen katifan ta kwanta tare da rumtse idanu tana tunanin rayuwar ta shike nan haka zata ƙare daga wanan gidan zuwa wan can gidan..?,menene tayi wa iyayenta da basa son ta shin wacece ammie a wurin ta...?,shi kuma papan ta menene dalilin shi na daure mata fuska hada kawo ajiyar ta kada dai shima banzatar da ita zai yi kamar yadda uwarta ta batta hanun ammie...?
Alamar buɗe kofa taji da muryan shukura mai kama da gangan tsafi;,,baby u don sleep..?,shiru taji ba amsa ta kuna wutan d'akin tare da bajewa a ƙasa ta bude ledan kazan ta da babban kwalin hollandia youghurt apple flavour ta shiga yaga tana korawa da hollandia tana wake waken ta har ta cinye tas ta shiga latsar waya"baby dai na kallon ta da gefen ido har bata san lokacin da bacci yayi awon gaba da ita sai da taji bugun kofa da asuba ashe taufeeq mijin shukura ne ya dawo daga duty da kyar shukura ta buɗe tana masifa yake tambaya tayi sallah kuwa...?,tsaki taja ta koma bacci bubuga baby yayi ta tashi tayi sallah,babu musu ta tashi ya bata buta tana tambaya ina toilet tayi tsarki yace tayi a poo kawai (ashe gidan babu toilet kowaa leda ko poo take bayan gida,sai bathroom guda ɗaya wanda aka zagaye da kwano tun da asuba ake layin wanka a gidan),tana gama alwala ta dawo ciki hijab din ta sabo ta fitar cikin kayan da ammie ta saya mata ya shinfida mata sallaya ta gabatar da sallah,bayan ta gama ne ta jima tana adu'oi kamar yadda ta saba har ta kammala tayi zugum wurin..., taufeeq ne yake ta dawo ta kwanta mana..!,tace bata jin Bacci,gashi yana son kwanciya da matar shi babu hali daure wa yayi ya koma Masallaci dake wajen gidan ya kwanta nan da nan Bacci ya kwashe shi...
Baby na zaune har shukura ta tashi bacci tace da baby ta duba kofar d'akin akwai kwanoni da tukunya ta ɗauki bucket rijiya na kofar gida ta debo ruwa ta wanke mata zata haɗa breakfast,Babu musu baby ta tashi da babban bucket na karfe sai a lokacin ta ƙara ganin gidan da kyau akwai ma yara ashe,kowa nata zirga zirgan shi wata yarinya da ba zata wuce sa'ar taba daga ita sai pant Babu takalmi ko ɗan kwali a kanta dana tsufa ko tsagar kitso baka iya gani sai wasa da kasa take;baby tace don Allah ina ake diban ruwa..?,ta kalli baby sama da ƙasa tana murguda baki,ke kuma daga ina..?,tace jiya papa na ya kawo Ni wurin su aunty shukura zan zauna har ya samu hutu....,katse baby tayi chaf duk faɗin garin nan ya rasa wurin wanda zai kawo ki sai muguwan matar nan shukura...?,lalai na tausaya maki yarinya muje dai ba don halinta ba,shiru baby tayi yarinya nata zuba tana faɗa mata halayen shukura wacce har dambe tana yi da mijinta salihi wanda babu ruwan shi da shiga tsabgar kowa,gata da gulma,karya kwadayi da son abun duniya...!,har suka isa rigiyar kwakwara safiya bata bar zuba ba ashe kowa da guga yake zuwa basu zo dashi ba da yake yan aunguwar sun san rashin kunyar safiya aka ki ara masu guga sai da baby ta ruki wani mutum ya bata da sauri ta cika aka daura ta suka kama hanya tana ci gaba da bata labarin yan gidan nan ta fahimci ƙabila uku ke gidan(baban su safiya ba kane ne kuma shine mai gidan rasuwa yayi,matar shi abu banufa ce yaranta hudu yan mata biyu sai namiji da safiya sune masu gidan,aunty grace wace yar makarnta ce tana zaman kanta,maman Daniel itama zaman kanta take da yaronta ɗaya sai su taufeeq), har suka iso gidan ta samu maman daniel,aunty shukura da yaya abu (maman su safiya) zaune tsakar gidan suna gulman aunty grace,tsaki Safiyya taja tana faɗin daga gani guntu ya sauka..!,baby tace menene guntu kuma..?,gulma mana ai da kin ga sun taru kofar abu(maman su) guntu ya sauka munafukai kawai"abu tace ke Safiya ina kika tafi tunda safe dan uwanki ya wuce makaranta ..?,baby na raka rijiya,tace oho (dama shukura ta basu labarin baby),zaman da akayi wurin zugata ake kada ta samar ma baby fuska taci ubanta ita bada haihuwa ba akawo mata raino waya sani ko shegiya ce...
Tare da safiyya suka yi wanke wanke tana zuba mata surutai suka gama ta share dakin ta gyara sai ga taufeeq ya shigo ta gaishe shi,ya tambaya taci abinci kuwa..?,tace a'a..
Shukura ya kwala wa kira Wacce ke zaune rashe rashe suna gulma,tsaki taja tana murguda baki har ta iso tayi tsaye a kan shi,da turanci ya tambaye ta ina abun kari..?,tace bata yi ba!
Bai damu da kuɗaɗen dake wurinta ba ya dauki jug ya nufi wurin mai shayi ya sayo da bread suka yi breakfast lokacin 9:30am yace baby ta shiga tayi wanka,babu musu ta ɗauki bucket ta koma rijiyar ta debo ruwa ta zo tayi wanka (dama da komi nata tazo),ta shirya cikin wani dogon riga yar kanti...
Yace da baby primary nawa kika tsaya..?,tace 4 zata shiga,yace ok yanzu yasan ba za'a dauke ta ba sai da transfer daga schl din data fara ko wani evidence da zai nuna ta taɓa karatu a wani wurin amma zai waya da oga aminu (yaya Mallam),yaji yana dadana waya can ya amsa cike da girmamawa yana mashi bayani da turanci,sai cewa yaya Mallam yayi ai ba makaranta yace su saka ta ba don haka babu ruwan su da karatun ta ya kashe wayan!
shukura da tunda yake wayan take kallon shi daɗi ya cika ta domin ta samu helper ,jiki a sanyaye ya kashe wayan amma yasan tabbats something so wrong some where...
Fita yayi zuwa yan buga buga shi,yana fita shukura ta saka baby dahuwar shinkafa da murhun gawayi (charcoal),duk da bata taɓa girki ba amma zaman ta da ba'baa mairo tana kallon yadda take abubuwa yasa ta gane komi cikin natsuwa da taimakon Allah ta dafa white rice Dama shukura nada stew aka diga mata ɗan kaɗan a plate ta lashe,zuwa karfe biyu taufeeq ya dawo yaci abinci ya kwanta..
Bayan baby tayi sallah ta nufi wurin Safiyya dake shirin fita tallan Pure water lokaci duk yaran gidan sun dawo daga makaranta (babban budurwan mai shekaru sha shida sunan ta amina jss 3 take,sai fati mai shekaru sha uku jss1A,Ibro mai shekaru sha biyu primary 6,sai Safiyya mai shekaru goma wace ke primary 3 amma sai taga dama take zuwa),ganin tayi duka sun shirya Amina da fati sun dauki tallan dafafan gyada,Ibro da Safiyya kuma Pure water zasu fita,tace Safiyya ina zaku..?,ahhh baby cikin babban makaranta talla(BAYERO UNIVERSITY KANO),yanzu sai yaushe zaku dawo..?,sai yamma suka fita abun su....
Zama tayi gefe shiru tana tunanin ammie domin tayi matukar kewar ta .
Tunda ammie ta dawo gida take fama da zazzabi na kewar baby (bahaushe yace sabo turkin wawa),ita kam bata yadda kewar baby ya saka ta zazzaɓi ba illah tunawa da rasuwar mahaifinta ta kusan sati ɗaya tana fama da zazzabi hada ƙarin ruwa ba'baa mairo ke kula da ita yan gidan can nasu duk sun zo duba ta Musamman uwar masu gida nan take yini har ta warware alaji habu ya saki bakin aljihun shi sosai.
Yaya Mallam tunda ya koma hankalin shi ya kasa kwanciya babu abinda yake tunani sai cin mutunci da tonon asiri da ammie ta jawo mashi,ya rasa gane menene alakar ta da babban mutum kamar alaji habu har yake bugun gaba da zai kare mata hakkin ta idan har yana raye,yana barazanar ruguza farin cikin shi ta hanyar dawo da abinda ammie ta haifa hanun shi"ashe labarin da mai chemist ya Sanar dashi lokacin daya dawo sayo magani gaskiya ne wai ammie ta zazzage shi yayi kokarin dakatar da ita ta kwada mai karfe ta gudu,ashe da gangan tayi don ta Saɓa alkawarin da suka ɗauka a farko...???
Ya dau alwashin sai ya mayar da rayuwar baby abun tausayi a duniya sai ammie ta gwamaci zubar da cin nan tayi da haihuwar baby!!!
_HALIMATUS SADIYA MUHAMMED_
*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
~sensational Heart touching story~
*BY*
*LEEMA*
_DEDICATED TO KANO STATE_
*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..
_Jamila Musa(meelat) ina taya ki murnan dawo wa daga honemoony tawan Allah ya albarkaci zuri'a ya raya mana su amin,muna jiran K'WARATA_
_hajia Maman mamy Yar India Aci gaba da sabarbado mana ILU A JAMI'A mu sha nishadi_
_ummerherny wanan shekara @360 kika dawo domin DAN ADAM BUTULU na kawo light fiye da tunani mai karatu,na hango mema na korafin kina neman shale mata wurin posting a kullum_
_fatee teerje gaskiya kina mana ruwan page a rinka mana koda read more 20 ne a rana ƘADDARA TA(labarin rayuwa na) na fadakarwa yana sani shiga wani yanayi na sanyin jiki da kariyar zuciya Allah ya kare duka nin musulmai a duk inda suke amin_
_Asmeenart naki salon na dabam ne rubutun naki haka yake zuwa da sabon salo a ko wane lokaci wurin zakulo mana matsalolin rayuwa na yau da kullum haka yace a cikin littafin BAD'ALA_
_saleehart beauty,oum Ahmad, jidda,Yar Beji ,khaleesi da sauran marubutan mu na brilliant writer's Ina maku fatan alheri kuna koka wurin fadakarwa,ilmantar wa,nishadan tarwa tare da wa'azantar wa Allah saka da alheri_👏🏻👏🏻👏🏻
~🅿17-18~
🅱aby zaune kusa da taufeeq tana sharar kwala,shukura na gefe tana latsan waya kamar yadda ta saba"taufeeq yace baby Ni zan tafi da motar office zamu suna jira na idan akwai abinda kike so kima shukura magana sati ɗaya kawai zanyi ki bar kuka...!
Share hawaye tayi tana gyada kai,ya kalli shukura cikin harshen turanci "zan tafi",,ok kawai tace ya dauki brief case nashi ya fita(kalubale gare mu mata wai ace mijin ki zai tafiya babu wani magana mai daɗi ko Addu'a da zaki raka shi da shi irin hakan yasa wasu matan ke dauke hankalin su a waje da kalamai masu daɗi),yana fita ta wuce kofar ya Abu...
Kina ciki ashe..?,tsaki taja delu tabargaza(wata dilaliya ce mai kawo masu kaya) ta dame Ni da zirya kin san bugun gyada na dauka bashi ko Naira ban biya ba har yanzu ga yaran nan har yanzu shiru basu dawo talla ba...!,cikin burkutacen Hausa ta tace taufeeq taje wani aiki a Katsina za tayi mako ɗaya zata dawo ina son spending night with Bobby shege yaron na baby will be my only obstacle yanzu"ta ƙara jan tsaki...!
Ya abu ba wai karatun boko tayi ba amma zama bariki yasa ta na jin turanci kuma tana iya juya harshe,kema shukura kina da matsala me akayi akayi wata baby da har zata hana ki jin daɗi rayuwar ki ko taufeeq dake auren ki bai zama matsala ba bare wata baby"kawo kunne kiji wani plan da nake dashi akan baby,kuskus suka yi,shukura ta shek'e da dariya tana faɗin "oshe wo abu..!,oshe wo abu..!! ,Suka tafa ta hade girar sama da ƙasa tare da faɗin"1,2,3 Acton Baby........
Daga d'aki ta amsa Yes mama me..,ta iso a guje;,,me kake a daki shiru..?,,na kwanta ne, kunnen baby ta kamo daga yau ba zaki sake kwana cikin dakin nan ba tunda bana uban ka bane, kuɗin da uban ka ya kawo sun kare oya go back inside and pack ur bag I will show u ur new room,sum sum ta Koma ciki tana hawaye ta dauko yakar kayanta wanda sunyi dirty saboda rashin wanki ta nufo inda suke,wani daki kusa dasu shukura ta nuna mata koda ta shiga ko plasta ba'a shafa a bango da Kasan d'akin ba,zinc ne a sama, window da kofa hangan gan ba'a Saka komi ba buhu ne malale a Kasan d'akin idan ka taka tsinin Duwatsu na soke maka ƙafa, gefe ɗaya ta aje jakar ta shiga kuka sosai domin ta tuna da rayuwar ta na baya duk da bata samun fuska a wurin ammie amma bata taɓa kwana da yunwa ba idan har tana gari, bata taɓa kwana a kaskantacen muhali ba "kuka taci gaba dayi tana faɗin ammie nayi kewar ki don Allah ki dawo ki tafi dani bana jin daɗin nan din,ammie wayyo ammie da papa ka zo mu tafi na gaji da zama a nan...!
Shukura ta leka d'akin common ka fita kazo ka debo ruwa a rijiya yanzu..!,,jiki a sabule ta fito tare da ɗaukan bucket na karfe ta nufi rijiya tana sharar kwala haka taje mutane sun yi yawa wurin saboda lokacin rani ne sauran rijiyoyi na kusa sun kafe dole sai an jira ruwan ya taru a rijiyar kowa ya saka guga ya diba gashi bata da guga,gefe ta zauna tayi tagumi tana kallon kowa yayi ready suna kira asaka kowa ya diba...
Har yamma baby Bata samu diba ba karshe ta hakuri tayi ta koma gida lokacin yaran sun dawo daga wurin talla jiki a sanyaye ta shigo gidan tana rabe rabe shukura ta hango ta ai kuwa ta kwala mata kira ...!,jiki na rawa ta karaso wurin,ai kuwa shukura ta riƙe wuyana ta tura cikin bucket din tana dirka mata dundu tana zagi wai gidan uban wa ta shiga sai yanzu ta dawo babu ruwa wallahi yau bata da abinci a gidan nan ta saka ƙafa ta shure ta daga ita har bucket din suka gangara gefe duk ta kukuje ta mike tsaye tana kuka ga yunwa na cinta tun ƙarin safe,,Safiyya ce ta zo kusa da ita tana kwasan dariya idan dai wanan azaluman shukura ce wata rana sai ta kashe ki yarinya babu mai hana ta a gidan nan kowa ɗan gaban kanshi ne gwara ki gudu wurin iyayen ki...!,kallon ta tayi menene kuma ɗan gaba..?,ahhh na manta baki gane hausan tamu na gidan nan ina nufin kowa mugun kanshi ne kawia ki basar idan an bani abinci na zamu ci tare,gyda kai tayi kawai har duhu ya fara bata samu yin Sallah ba Safiyya ta kawo tuwon masara da miyar kuka suka ci,tace don Allah Safiyya samo mun ruwa zan yi Sallah ne..!,dariya ta sake yi sannu Malama ta dauko mata buta da ruwa tayi alwala cikin dakin nan tayi magrib da isha'i tana zaune cikin duhu d'akin ko wuta babu Safiyya ta shigo da gudu baby,baby fito kiga guntu ya sauka...
A sabule ta fito Safiyya ta rike hanunta tana nuna mata shukura da ta fito cikin kwaliyya tana rufe daki haka ta wuce su cikin jeans trouser da hookie shirt rike da purse kai babu dankwali fuskan ta yasha