Chapter 3 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   3 / 35

6K to 9K   out of 103.7K words

rabani da kauye na!!

BABY itace kaddarar data ruguza duk wani buri nawa a rayuwa!!!

BABY itace kaddarar data sani cikin wanan kazamtaciyar rayuwa alaji!!!

A razane ya mike tsaye yana nuna ta da ɗan yatsa tare da girgiza kai kada kice mun baby diyar cikin ki ce..?

kada kice mun wanan yarinyar dana gani mai yanayi dake itace baby..?

Kin taba aure ne ammie..?


Idanunta da suka canja launi saboda tsabar kuka ta dago tana kallon alaji habu dasu!!!



~K'ak'a k'ara k'ak'a masu Karatu kunji wanan chakwakiya kuwa nikam nace wani labari ne wanan ammie ke boye wa shekara da shekaru wanda bata son kowa ya sani,,shin zata sanar da alaji habu gaskiyar labarinta???,,,ku dai ku kasan ce tare da LEEMA domin jin yadda wanan chakwakiya zata kasance~


_Halimatus sadiya Muhammad_

*LEEMA*

*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..





~🅿7-8~


Idanun ta da suka canja launi saboda tsabar kuka ta ɗago tana kallon alaji Habu dasu na wasu dak'ik'ai tabbas baby d'iya tace nice na haife ta da ciki na ITAMA 'YA CE kamar kowa!!!


Mani irin kishi ya murtuk'e shi numfashin shi na sama yana ƙasa yana ƙara zaro idanun shi ammie inason sanin komi a yanzu kada ki boye ko kalma daya Daga cikin labarin ki wallahi idan kika faɗa mun k'arya za kiyo nadama...!,kayyah alaji bana son tuna komi na babin rayuwata shine dalilin da yasa na zaɓi zama gidan kazo nazo domin yin rayuwa mai y'an ci dana koma gaban iyayena,bani da burin aure Alaji habu mu hakura kawai da wanan magana na maka alkawarin zan zauna dakai kamar yadda macen aure ki zama da mijinta,zan baka dukan wani hakkin da macen aure ki baiwa mijinta har ma fiye da haka amma bata hanyar aure ba!

Bazan amshi tayin ki ba domin rayuwa mai tsafta nake so muyi,Ni dake mu tsira daga azabar Allah ya zama dole ki daure ki sanar dani labarin ki ammie!

Shike nan alaji tunda ka matsa zan sanar da kai gaskiya koni wacece.


*LABARIN AMMIE*

Iyayena yan asalin karamar hukumar kumbotso ne dake jahar kano,mahaifina Mallam Aminu ya kasance wanzami ne wanda gado yayi tun iyaye da kakanni bashi da wata sana'a data wuce wanzan ci yana fa matan aure uku;inna lami itace babba wacce auren saurayi da budurwa suka yi Allah bai bata haihuwa ba bayan wasu shekaru mahaifina ya auri mama ladi suna zaune lafiya itama shiru kusan shekaru biyar ko batan wata bata taɓa yi ba sai aka ba mahaifina shawara ya kara aure inda ya haifi umma ta mai suna jummai watanni goma cif ta ta haifi ɗa namiji murna wurin Mallam da sauran matan gidan ba'a magana duk da ba wani ƙarfi ne dashi ba amma iya gwargwado anyi shagali ranar suna yaci sunan mallam(Aminu) ana kiran shi da mallam,rainon shi ya koma hannun inna lami iyaka shan nono ke kawo shi wurin umma bayan wattani shida sai ga wani ciki a jikin umma,murna wurin Mallam ba'a magana ga cikin yazo da laulayi matuka 'hankalin kowa ya tashi da irin laulayi da take yi,inna lami ta bada shawara a cire shi a nono zata haɗa mai abincin yara na gargajiya zai murmure,haka kuwa akayi inna lami na kula da Mallam Karami,mama ladi na kula da umma har ciki ya shiga watanni bakwai lokacin ta murmure suka ci gaba da harkokin su gwanin sha'awa lokacin haihuwa ta sake samun namiji yaci sunan mahaifinta Aliyu (ana kiran shi hydar) mama ladi tace itama ta samu nata hydar ya koma d'akin ta komi ita ke mashi, lokaci na tafiya mai gari ya naɗa Mallam sauratan baraden kumbotso saboda yana ɗaya daga cikin dattijawan kauyen aka bashi kyautar gona madaidaici ya fara noma a hankali har Allah ya sanya mashi albarka ciki ana samun amfanin gona sosai har ya fara gwada noman rani cikin ikon Allah Aka samu amfanin gona,rayuwar gidan mu gwanin sha'awa saboda idan ba sani kayi bazaka taba cewa kishiyoyi bane,ga Mallam Karami da hydar sun taso kaman yan biyu kamar yadda na samu labari wurin umma sai da suka shekara goma a duniya ta samu ciki na lokacin kuma inna lami tayi fama ciwon daji na mak'oshi(throat cancer),ciwo sai gaba yake kullum har ya kai bata iya magana,aka shigo da ita cikin garin Kano babban asibiti likita ya tabbatar wa Mallam idan ba aiki akayi mata ba bazai warke haka nan ba kuma kudin aiki kusan million ɗaya da rabi ne,Mallam ya dawo yayi buga buga duk inda zai samu rancen kudi ya haɗa amma babu a karshe ya sayar da gona kin shi manya guda biyu akan dubu ɗari biyu(lokacin kuɗi nada daraja),wasu kiwo na mama ladi da umma na duka sun bayar anata buga buga da kyar aka haɗa dubu ɗari biyar za'a kai a fara aiki kafin a samu saura cikin ikon Allah koda Mallam ya isa rai yayi halin sa nan Mallam ya fadi ƙasa sumamme shima sai da yasa ƙarin ruwa jin shiru yayi yawa mai gari ya tadda mutane biyu abi bayan shi lokacin da suka isa mumunar labari ya riske su babu bata lokaci suka samu hyan akori kura aka dauko gawan inna lami zuwa gida,liman ya bada umurni ayi saurin mata sutura a kaushe ta,bayanin tashin hankali dasu mama ladi suka shiga ba'a magana musamman Mallam karami da take uwa a gare shi domin a wanan lokaci bashi da masaniyar mama ta haife shi,haka aka shirya inna lami Mallam na zubda hawaye aka kaita gidan ta na gaskia sanan aka ci gaba da amsar gaisuwa har kwana uku sanan jama'a suka dauke ƙafa aka bar Mallam da iyalan shi cikin jimami gidan ya koma shiru kamar babu kowa saboda rashin walwala,mama ladi ta yanke shawarar Mallam karami ya dawo d'akin ta saboda cikin umma yayi nauyi,Mallam kam yana cikin wani hali saboda duk cikin matan shi yafi son Inna lami bashi da tamkar ta matar rufi asiri tun bashi samun ko sisi suke tare har Allah ya buda mai bata taɓa nuna ɓacin ranta ba shekarun su ashirin da aure Allah ya amshi ranta tana da shekaru talatin da shida a duniya,sauran kuɗin daya rage a hanun shi ya biya bashin mutane yayi wa matan shi alkawarin biyan su kiwon su da ya sayar ko wacce tace ta yafe har lahira,sauran ƙaramin gona daya rage mallam ya amshi takin gwamnati bashi ya fara noma kullum tare da yaran shi yake zuwa suna taimaka mashi;Bayan watanni biyu Allah ya sauki umma lafiya ta samu d'iya mace ranar ansha kuka a gidan domin tunawa da inna lami wace ta taɓa cewa jumma gaskia idan kika sauka lafiya sunan surukar mu za'a saka duk da bata raye ayi mata takwara kinga mu Allah bai bamu haihuwa ba amma zuwan ki ko wacce ta samu d'a wanda zata yi alfahari dashi,idan Allah ya saukeki lafiya ammie ta zama taki...!,ranar suna kuwa akayi mun huɗu ba da sunan mahaifiyar mallam "Hadiza"ana kirana da ammie,na taso cikin so da kauna,kulawa da tsantsan kyautatawa daga wurin iyayena da yan uwana musamman ya'ya Mallam yana matukar ji dani,shine goyona da an gama mun wanka wani lokaci ko ina kuka da kyar mama ke amsana a wurin yaya Mallam, ya hydar haushi abin yake bashi yana faɗin zaka shagwaba yar mutane domin kai ba ɗan gidan nan bane riƙon ka mama ladi keyi ranshi ya ɓaci sosai da jin maganar hydar ranar kuwa ya samu umma yana tambayan ta da gaske ne shi ba dan shidan bane riƙon shi ake yi...?,abunka da ɗan fari tana matukar jin kunyar shi tace eh haka ne Allah yayiwa mahaifiyar ka inna lami rasuwa yanzu baka da kamar Mallam da mama ladi jiki a sanyaye ya samu mallam a hanyar shi ta dawo wa daga rumfar mai gari ya tambaye shi da gaske bashi bane mahaifin shi..?,yace waya faɗa mashi wanan magana..!,yace umma ce"yace duk abinda ta faɗa maka gaskia ne bamu muka haife ka ba Allah ya amshi mahaifiyarka (Mallam ya dan ganta maganar umma da kunyar ɗan fari ne),ranar ya kebi a dakin su(wanda d'akin inna lami aka kyara musu nan suke zama),yana cikin kuka ya hydar ya shigo yana tambayar shi musababbin kukan nashi..?,yace ai akan maganar daya faɗa mashi dazu ne umma da Mallam sun tabbatar mashi iyayen shi basu da rai riƙon shi ake yi a gidan,ya hydar yace ai na faɗa maka saboda sam bakayi kama da yan gidan nan ba kowa ya Fika kyau da hasken fata yanzu dai kayi hakuri muci gaba da masu addu'a kawai;tun daga lokacin yaya Mallam ya dauki kanshi amatsayin maraya abinda ke damun shi daya nuna kulawa sosai akan ammie sai hydar yata gwale shi ko a gaban wanene yana nuna zan shagwaba mashi yar uwa,wata rana da ranshi ya ɓaci yakai kara wurin mama ladi dariya kawai tayi saboda a ganinta yaranta ke cin su ta bashi hakuri;inada shekaru uku umma ta sake samun wani cikin mai matukar laulayi fiye da cikin ya hydar sai kulawar mu duka ta koma wurin mama ladi tunda asuba take tashi tayi aikin gida da bin kari su Mallam su tafi gona lokacin tare dani yaya Mallam ke zuwa ya goyani suna aiki,idan sun dawo tare muke zaga gari yawo da dare muka mu tafi makarantar dare na allo tare tun ya hydar na masifa da faɗa har ya hakura ganin Allah ya haɗa jini na da yaya Mallam sosai shi kuwa Bama shan inuwa guda ko kaɗan komi nashi faɗa da zafin rai kuma baya dariya kullum fuskar nan tashi a haɗe kamar an dauro hadari;haka muke rayuwa cikin rufi asiri umma na fama da laulayi ko ruwa tasha sai amai har ciki yakai watani bakwai aka yanke shawarar zuwa asibiti babba cikin gari,bayan anyi mata hoto(scanning)aka gane cikin yan biyu ne amma basu kwanta dai dai ba(breech presentation) ɗaya da ƙafa, ɗaya da hannu likita ya bada magunguna da za'ayi amfani dasu da shawarar wari akan da taji nakuda a kawo ta asibiti ta haihu; suka dawo gida taci gaba da jinya har lokacin haihuwa yazo aka koma hospital tun safe take nakuda har yamma haihuwa bai zina aka yanke shawarar aiki za'ayi mata,Mallam ya saka hannu aka shigar da ita da taimakon Allah aka ciro yara biyu namiji da mace duka babu rai gashi ta zubar da jini sosai dole akayi mata ƙarin jini likita yaba Mallam shawara akan umma tayi amfani da dubarun tazarar haihuwa(family planning) har na wani lokaci mahaifan ta ya huta kafin ta dauki wani cikin yana ba Mallam bayani akan irin dubarun da ka dasu(methods),babu bata lokaci Mallam ya zaɓi rubbe domin ta samu isasshen hutu,Mallam ya dawo da yaran gida aka kau dasu ya dauki mama ladi damu duka muka tafi ganin umma da jiki wanda sai da tayi sati daya Ka sallame ta taci gaba da jinya a gida tunda lokacin haihuwa ya tsaya bata sake samun wani cikin ba;lokaci na tafiya ranaku,watanni da shekaru na shude wa shak'uwa mai ƙarfi na kara shiga tsakani na da yaya Mallam,inada shekaru shida yaba Mallam shawara a saka Ni a makarantar boko tunda ina zuwa na allo na yamma kuma muna zuwa na dare tare dasu,da kyar da sud'in goshi Mallam ya amince domin bashi da buri da ya wuce ina samu wadataciyar ilimin addini ya aurar dani ga miji na gari,murna wurina da yaya ba'a magana shi da kanshi ya kai Ni model primary school Nan cikin ƙauyen mu aka bani aji ɗaya"da yake yaya Mallam yana zuwa yaƙi da jahilci(adult education) asabar da Lahadi wanda akeyi anan makaranta,ya hydar kam yafi son noma da kasuwanci duk da shekarun su sha shida amma yana zuwa cin kasuwar wasu ƙauyuka nan makwabta;na fara karatuna a Sa'a ina mayar da hankali sosai bani da aboki sai yaya Mallam idan na dawo shike mun bitar karatu na har na allo akwana a tashi na samu nasarar shiga aji biyu lokacin yaya mallam na zangon karshe a nasu karatun wanda dama shekaru uku daka kamala zaka samu damar zuwa makarantar gaba da primary na cikin garin kano Allah yasa yaya Mallam na ɗaya daga cikin wa'yanda suka ci common entrance exams d'in da ayi masu Government day secondary School kano ,lokacin mallam ya fara shirye shiryen tafiyar yaya mallam makaranta ya haɗa shi da aminin shi dan kasuwa dake zaune a sheka cikin Kano yana kasuwancin a yan kaba na kayan miya idan su Mallam sun cire amfanin gona ya sari kayan lambu ya kai kasuwa har ALLAH ya sanya mashi albarka a ciki ya gina gidan kanshi sheka ya koma da iyalin shi;ranar da yaya Mallam zai tafi da kuka muka rabu tun daga lokacin na koma shiru shiru bani da abokin hira sai mama ladi da umma sai in Mallam na gida domin ba ƙaramin wahala ya hydar yake bani ba!!!


~manage plz~


_Halimatus sadiya muhammed_
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..


_Believe that when it comes to friends,Quality is much better than Quantity#HAWWA M.U SMASHER {c'weety smasher}_





~🅿9-10~



🅱ayan tafiyar yaya Mallam nayi jinya na kusan sati ɗaya bana zuwa makaranta sai da ya hydar ya tsawata sanan na cire komi a rai na rungumi karatuna da yake lokacin primary2 nake makaranta allo kuma nayi nisa domin ina son karatu sosai da sosai...'mama ladi da umma kuma sun haɗa kansu tamkar ciki ɗaya suka fito idan an cire amfanin gona Mallam na kawo masu kayan miya gida ana zuwa saya su samu kuɗin kashi,ya hydar yanzu da kanshi yake fita da kayan zuwa kasuwanin ƙauyuka yana sarar wa ya dawo da riba mai tarin yawa domin Allah ya bashi baiwar sanin dubarun kasuwan ci;can Kano kuwa yaya Mallam ma yayi jinya sosai na rabuwa da ammie kafin daga baya ya mayar da hankali a karatu idan sun tashi sai yabi Mallam saminu kasuwa yana taya shi zama a rumfar shi har yamma su dawo gida da dare kuma yana zuwa karatun Alkur'ani wanda ake yi cikin masallaci,gashi a lokacin ba kowa keda wayar hannu ba musamman kauyen mu bare yaya Mallam ya kira gida kullum da tunanin ammie yake kwana yake tashi har akayi hutun zango na farko(1term),ya matsa wa Mallam saminu yana son zuwa gida hutu,goma na arziki ya haɗa mashi har tasha ya kai shi tare da saka shi motar zuwa kumbotso koda ya iso Mallam na rumfar mai anguwa,ya hydar ya tafi cin kasuwan Dala ammie kuma na makarantar allo na yamma bayan sun gaisa dasu umma ya kasa jira har makarantar allon ya bita ai kuwa a guje ta faɗa jikin shi cike da farin ciki tana bashi labarin irin cin zalin ta da ya hydar yake yi ai kuwa nan ranshi ya matukar ɓaci ya rik'o hanunta har rumfar mai gari wurin mallam,bayan ya gama gaisawa da kowa suka nufi hanyar gida,zabbi Mallam ya yanke mashi ya bada umurni ayi soye mashi yaci daɗi,da ya hydar ya dawo ya yau shi da faɗa kamar zai buge shi akan me zai rinka takura wa ammie ko dan yaga baya gari...?,dariya ma abun yaba hydar yace ikon Allah Ni da Yar uwanta bazan tsawata mata ba..!,mace ce aure zata yi nan gaba don me zan sakar mata tana Shashanci..?,wanan ba matsalar ka bace nidai na faɗa maka idan na sake samun labarin ka bugeta wallahi sai na rama mata..!,ba shakka yaya Mallam ka nuna mun ka tafi murni saboda ammie zaka dake Ni..?,Mallam ne ya tsawata masu ko wanne na huci kamar zasu buga haka dai yaya Mallam yayi hutun nashi na sati hudu baya shiga tsabgar ya hydar kullum shi ke kai Ni makaranta idan an tashi ya dauko Ni mu yita yawo har yamma ya kaini makarantar allo idan lokacin tashi yayi mu dawo tare ranar da zai koma sai da Mallam ya nuna ɓacin ranshi sanan ya tafi da yamma kamar jira ya hydar yake yabar ƙauyen ai kuwa ya zage mun jiki ciki da waje da kyar mama ladi ta amshe Ni a hanun shi umma kam ko kallo ban isheta ba domin itama abun ya yaya Mallam ya fara bata haushi saboda ɗan fari ne shine dalilin da yasa bata iya dogon magana dashi;haka rayuwa taci gaba da tafiya duk hutu sai yaya Mallam yazo mun da tsaraba kala kala daga birni duk ƙauyen mu babu yarinyar da ta kai Ni gata a lokacin nan ta fannin kayan sawa,kayan wasa Saduƙu wasu abu da mace ke ado dashi idan yaya Mallam ya gani sai ya sayo mun,umma idan suna hira da mama ladi ta rinƙa nuna ɓacin ranta akan hakan a ganinta abun ya wuce wuri gaskiyar ya hydar ne,yaya Mallam na shagwaba Ni da yawa duba da Ni mace ce gidan wani zani,babban damuwar ta yadda kullum kwanar duniya kiyayya ke k'aruwa tsakanin yaya Mallam da ya hydar ko kaɗan basu shan inuwa ɗaya kuma duka saboda ammie ne..!,mama ladi takan nuna mata ai ba komi bane alama ce ta tsantsar soyayya wanda ko bayan ransu zai rike Ni

3 / 35