Chapter 28 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   28 / 35

81K to 84K   out of 103.7K words

kira magrib ya fita daga d'akin zuwa masjid.

Hadiza da jikinta yayi sanyi sosai sai addu'a take Allah yasa da sauki dai gashi bata fito da waya ba bare ta kira ammie,toilet ta shiga ta dauro alwala nan gefe ta shimfida dankwalin atamfan ta sanan ta gabatar da Sallah.

Yana idar da Sallah ya nufi wurin doctor yace dashi suna son wuce wa gida.!
Shekeke ya kalle shi irin U are mad din nan,luk general yarinyar nan is weak tana bukatar 1000ml na normal saline ta samu ƙarfin jiki kwata kwata yaushe aka da drip din da zaka ce zaku tafi.?


I don't care Kawai a cire mata gida zamu tafi.

Ranshi ya ɓaci ganin yadda General ke yi mashi shishigi a aikin shi,General u have tó behave yourself cuz we are in the hospital not a battel field.

Gani yayi zai bata mai lokaci kawai ya fita cikin Sa'a ya haɗu da wata nurse tana fitowa daga d'akin...,mallama don Allah drip d'in Nan nake so ki cire nata zata shiga toilet ne.

Da mamaki ta kalle shi,yanzu daga d'akin nake,tana bacci na tayar da ita na mata allurai na saka cin abinci dana tsayar da amai .amma bata ce zata shiga toilet ba.!

Na faɗa maki daga wurin doctor nake yace a cire mata zuwa anjima za'a mayar.

Jin an ambaci doctor ya sa ta koma ta cire mata drip d'in, buɗe ido tayi da kyau ta gane hospital take ga drip din da aka saka mata ko 500ml bata sha ba.

Wani haushi da tsanar baby yake ji na taso mashi,"Hadiza ku same Ni wurin mota gida zamu" ya wuce aBun shi.

Taimaka wa baby tayi ta sauko daga saman bed d'in saboda har lokacin jikinta babu ƙarfi sai ɗan banzan yunwa da take ji,rike hanun ta Hadiza tayi suna tafiya a hankali har wurin motar wanda ya ji ma da isa yana jiran su.


A haukace yake driving har gida,yana parking ya fita ya bar su.

Babban abun haushi gidan cike da mutane ana aiki saboda gobe ne bukin suna,matar shi na jin tsayuwar mota ta mika wa sister ta babyn ta fito domin hankalin ta ya tashi da taga sun dad'e.


Gani tayi ya nufi hanyar bedroom nashi tana son bin shi taji sallamar Hadiza riƙe da baby wurin su ta nufi tana yiwa baby sannu suna ratsa mutane har dakin da sister ta ke zama dama ba mutane ciki sai faruk da yayi bacci,saman matras baby ta kwanta a hankali take furta aunty yunwa,ina jin amai,zuciyata na tashi, kai na ciwo....,hawaye na bin fuskarta.

Zama tayi tana shafa jikin ta wanda yayi zafi rau,me zaki ci babyna?

Jim tayi a hankali ta furta tea ba sugar zan sha,ok barin haɗa maki ta fita zuwa d'akin ta amma hankalinta ya rabu gida uku"mijinta ya shigo rai a b'ace,ga jariri can yana mata kukua, nan kuma ga baby.

Da sauri ta zuba enough milk and milo ta buɗe flask ta zuba ruwan zafi ta kawo ma baby.

Hadiza taimaka mata ta samu tana ina zuwa.

Talafo ta Hadiza tayi tare da jingene ta jikin pillow ta Mika mata cup d'in,duk da zafin da yake dashi amma haka take sha sauri sauri kamar za'a kwace tana lumshe ido.

Hadiza dai na Binta da kallo har ta kammala,"I need more,shine abunda tace zufa na keto mata ko ta ina duk da AC dake aiki.

Yanzu dai ki tashi ki watsa ruwa kinga ana kiran sallar isha'i gashi ko magrib baki yi ba.

Kamar za tayi kuka ta tashi jiki ba kwari domin wani irin mugun kwadayin tea ba sugar ya taso mata da daren nan.


Aunty sadeeyah na fitowa daga d'akin da Baby take ta nufi hanyar d'akin mijinta da sallama ta tura d'akin sai dai abun mamaki sallah yake yi wanda zata ce tunda ta aure shi idan ba matsananciyar rashin lafiya ba jam'i bata wuce shi.

D'akin ta kawai ta nufa domin ba Aminu Junior nono har ya kamala sallah.

Baby na fitowa wanka ta saka doguwar riga mara nauyi wanda ya amshi jikinta boobs Bata suka fito da kyau sai hijab har ƙasa ta kabarta sallah wanda da kyar ta kai raka'a ɗaya a tsaye sauran a zaune tayi. Tana idar wa bacci ya kwashe ta a wurin.

Hadiza dai sai mamakin ikon Allah take abubuwan baby kamar na masu ciki,da sauri ta kawar da wanan tunani tare da yin istigfari.


A d'akin mai jego kuwa hira ne ya kaure tsakanin ta da yan uwa da abokan arziki can taji wayarta na ƙara koda ta duba text ne daga mijinta kamar haka:-
*_Ki amso wayoyin baby da hadiza ki zo daki na dasu yanzu_*

Gaban ta ne ya fadi,zuciyarta na nasa mata abubuwa da dama ta daure ta fita.

Koda ta shiga Hadiza na zaune saman bed suna taɓa hira da sister nata amirah,Baby na kwance saman sallaya tana kwasan bacci duk tayi zuba..,ammm hadiza ku bani Aron phone naku na ɗan lokaci.!

Tau aunty Dama yanzu nake shirin kiran momi ko kin sanar da ita rashin lafiyar baby ne.?

Yanzu dai zan sanar da ita saboda haka ba sai kin kira ba...,dariyar amirah ya katse aunty sadeeyah, KE kuma lafiyar ki.?

Kai aunty wallahi naji kunya ace yan mata kaman su ƙarama waya suke riƙe wa shine muke hira ashe ko ɗan chat ɗin nan da ake yayi basa yi.

Itama aunty sadeeyah tayi mamaki ganin tun wayar da mijinta ya ba baby shekaru hudu kenan har yanzu dashi take amfani.

Hadiza kun ci abinci ko.?,eh naci tare da amirah Baby CE dai taki tashi tana bacci tunda ta idar da sallah..,ok ki tashe ta tahau gado mana ta fita abunta.

Da sallama ta shiga d'akin sai dai waya yake amsa wa taji yana faɗin,evening flight nake so zuwa Kano;around what time Kenan a goben.?,ok 5pm..,yes 3passengers thank u so much air vice Marshal Eric.

Wurgi da wayar yayi saman bed ya mayar da kanshi saman guiwar shi kamar yadda yake a zaune tunda ya idar da sallah.

Zama taya a ƙasa kusa dashi tare da talafo kanshi ta d'aura saman chest nata tana shafawa a hankali kanshi zuwa wuyar shi har fuskar shi.

Lumshe ido yayi yana shaƙar kamshin ta wani irin natsuwa na shigar shi,he believed a duniya ba zai samu mace wacce tasan damuwar shi da kuma maganin damuwar shi irin sadeeyah ba.

Can ƙasar mak'oshinta take magana,dukan tsanani yana tare da sauki haka komi yayi tsanani maganin shi Allah kamar yadda mai hakuri yana tare da Allah,ka sanar dani damuwar ka insha Allah ina tare da kai komin runtsi komin wuya da daɗi babu daɗi.

Shiru tanna kusan minti biyu, ya ɗago kanshi tare da tsura mata ido na ɗan lokaci,"lemme have their phone, Mika mashi tayi duka biyu nan take ya gano na baby Wanda ya bata.

Contact ya fara shiga yaga basu wuce shida ba"best uncle(number shi),best aunty(na sadeeyah),sweet sis (na hadiza),Daddy (na alaji habu),ammie(na momi),lastly sarah dear (2nd daughter na alaji habu). Text massage ya shiga babu ko ɗaya,dial call ma empty, received call Empty,miss call Empty.

Tunani ya fara yi domin dai babu number wani saurayi a cikin wayar,"ba dai alaji habu ya yiwa Baby cikin ba.?
Astagfirullah ya furta a bayane,ya shiga duba na Hadiza wace itama kusan haka ne babu number wani saurayi cikin wayar.

Kallon matar shi yayi sosai yana nazarin ta kamar yadda itama take nazarin shi,wani zuciya na bashi ya sanar da ita wani zuciya na kwaban shi domin yasan halin ta bata iya shiga damuwa ba.

Mikewa yayi batare da bode chest of drawer ya ciro pen da memo ya fara rubutu wanda bai jima ba ya gama.

Inaso kiyi dialing number ammie duk abinda na rubuta a cikin paper Nan shi zaki tambaye ta.

Amsa tayi ganin rubutun kamar zuciyarta ya fashe don tsoro...., ringing wayar ya fara yi wanda ta saka a handsfree zuwa can ammie ta amsa da sallama,aunty sadeeyah ta kafe paper da ido.

Ya kewar yan matan ki.?

Daga ɗaya bangaren ta amsa da akwai kewa kam musamman da dare haka muke zama a palour muna kallo,baby cema Bata damu da kallon ba tana d'aki.

Lallai kam domin har tayi Bacci ma,naga yan mata sun girma da an gama Neco sai batun aure ko.?

Matso wa yayi sosai domin yaji amsar da ammie zata bayar...,dariya mai sauti tayi auntyn su kenan a can Yola suka samu mijin.?

Yola kuma yaran da suka zo jiya jiya.!,,a tau nan dai basu da kowa domin daga schl sai islamiyya basu fita ko ina musamman baby Koda na shirya muje shopping bata zuwa ita dai kullum zaune d'aki kinga ko ba maganar aure.

Ikon Allah ai banga laifin ta ba domin ko da take Lagos daga schol sai islamiyya amma dai gwara su samo musha buki zaman mace haka bai yi musamman a wanan lokaci da maza basu da tabbas.

Allah dai yasa mu dace bara na barki ki kwanta nasan oga na gida,dariya ta saka suka kashe.

Baby Bata fita zuwa ko ina daga schl sai islamiyya a ina ta samu cikin?

Tabbas idan ba cikin gidan nan aka mata ciki ba either a schol ko islamiyya akwai wanda ya rude ta.kaddara Kenan Wanda ya riga fata.

Kallon matar shi yayi da kyau,sadeeyah.!

Ta amsa da na'am.

Muna da shika shikan musulunci guda biyar wanda akwai akwai yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau ciki,a duniya ko wane bawa yana da irin tashi jarabawar ta tsiga dabam dabam domin Allah ya gwada imanin mu.

Jikinta yayi sanyi matuƙa ta kagu taji musababbin wanan dogon huduba.

Sadeeyah rashin lafiya da baby KE yi mun tafi hospital d'azu likita ya tabbatar mana tana ɗauke da juna biyu...

Dafe kirjin ta tayi da hanuwan ta biyu Tare Da zaro idanu bakin ta ɗauke da sallati.!

Juna biyu da abban faruk.?

Kwarai kuwa baby na ɗauke da ciki wanda yanzu nake so mu haɗa Karfi da ƙarfe mu gano wanda ya mata cikin nan.

Babban magana Ni sadeeyah garin yaya Baby ta samu ciki tunda ba fita take ya ba.?

Shine abunda na ke so mu gano a yanzu don haka wani boye boye,kuka ko canza mata fuska ba shi zai solving MATSALAR ba,ina so ki jata a jiki daga daren nan zuwa gobe ta sanar da ke komi idan Allah ya kai mu gobe kano zani tare da su ayi komi ta ƙare.

Shike nan zanyi iyakacin kokari na abban faruk daga goben saboda yanzu tayi bacci.

Shiru suka yi duka kowa da abunda yake tunani cikin zuciyar shi har wani lokaci suka yi sallama ta koma Dakin ta.

Bayan sun idar da sallar asuba General Sadiq ya bar gidan zuwa gidan iyayen shi domin a nan za'a yi zanen suna da karfe 8am.

Dajin da su baby suka kwana ta shiga dama Hadiza da amirah sun fito har sun gaisa da ita suka nufi cikin gida wurin aiki,baby CE ke sharar Bacci...,bubugata aunty sadeeyah tayi ta buɗe ido,"tashi haka nan rana ta fito.

Kai aunty wallahi bacci nake yi..,ke bana son Shashanci ki tashi magana za mu yi.Zaube ta tashi bakin ta sauke da sallati sai a lokacin ta lura da canjawan baby sosai irin na masu shigar ciki.

Oya taso mu je,tana biye da ita har d'akin General Sadiq suka shiga ta zauna baby na zaune ƙasa amma bacci bai sake ta ba.

Shiga toilet ki wanke fuskar ki Yanzu...,babu musu ta shiga ta fito riƙe da ciki aunty wallahi yunwa nake ji sosai kuma tea ba sugar nake son sha.

To hell with you and your tea,sit down my friend.

Ganin yada aunty sadeeyah ta buga mata tsawa ya saka ta zauna a razane.

Buɗe idon ki da kyau da kunuwan ki magana zan yi dake na fahimta na rantse da Allah i baki sanar dani gaskiya ba sai na shak'e ki a d'akin nan.

Baby kina ɗauke da ciki na wata ɗaya, wanene ya maki CIKI?

Zaro idanu tayi waje,ciki kuma Aunty wallahi bani da komi.!
Ok shi doctor ne yayi ƙarya ko mijina ne makaryaci.?

Zan so ki kwantar da hankalin ki baby ki faɗa mun gaskiya tun lokaci bai kure ba.

Shiru tayi domin a lokacin ta dawo hayacin ta komi ya dawo mata dala dala tun daga ranar da suka fara magana da uncle Christ har wayarta su ta ƙarshe.

Cikin kuka ta Fara faɗin Papa ka cuce ni, Allah ya isa tsaka nina da kai azallumin mugu Kawai,shike nan bakin ka ya kama ni dama kayi alkawari sai nayi cikin shege,sai na haifi shege na raine shi..,nima na maka alƙawarin zan raini cikin nan har na haife shi domin cikon burin ka.

Keee na kawo ki nan ne don yafi sirri!
Ta faɗa cikin tsawa ba abunda na tambaye ki kenan ba.
WANENE Ya Maki CIKI BABY.?
UNCLE CHRIST ta FAƊI cikin ihu.

Mun shiga uku wanne kuma UNCLE Christ.?

Cikin kuka ta kwashe komi ta sanar da Aunty sadeeyah,rungume ta tayi tana rarashin ta.!

Kayya baby kin yi wauta sosai wallahi namiji ba abun yadda bane baby kazantar tayi yawa Christian mushrikai wanda ya haɗa Allah da wani,kayyah mai afkuwa ta afku ki daina ganin laifin marigayi Aminu duk da an san bakin iyaye kamar dafi take Amma kuma haɗe da ƙaddara.

Kwantar mata da hankali sadeeyah taci gaba da yi har ta koma bacci a jikinta, gyara mata kwanciya tayi cike da matukar tausayin ta sanan ta bar d'akin.

A ranar ko Hadiza bata samu ganin baby ba domin bacci ta yini yi sai da aka kira sallah lokacin gida ya cika da yan suna aunty sadeeyah ta tashe ta wanka ta fara yi ta sha tea Wanda ya zame mata ruwan sha a yanzu wanda idan ba shi tasha ba komi taci sai amai.

Bayan koma ya lafa yan suna sun fara rage wa around 4pm Aunty sadeeyah ta keme da mijinta nan take ta sanar dashi komi wanda ranshi ya ɓaci matuƙa amma ya suka iya da ƙaddara ga bakin yaya Mallam.

Yace ta sanar dasu su shirya 5pm zasu isa airport.

Ciki ta koma ta haɗa masu kayan buki ta miƙa wa Hadiza tare da sanar da ita sak'on General...,hadiza bata ji dad'i ba amma ta dangana hakan da rashin lafiyar baby,gashi ba'a basu wayar su ba bare ta kira ammie.

4:30pm suka yi sallama da kowa suka bar gidan zuwa airport wanda Baby KE faman kuka rarashin Duniya Aunty sadeeyah tayi amma bata yi shiru ba.


Already tun a jiyan yayi waya da alaji habu akan yana so su hadu yadda ya hydar a gidan nan kano yana nan tafe.


5:40pm a palour'n gidan alhaji Abubakar ya masu,alaji habu,ya hydar da General Sadiq suna zaune saman three seater,ammie na gefe sanye da hijab,baby na zaune ƙasa taci kuka har ta gaji.

General Sadiq ya fara da sallama sanan yaci gaba,dukan ku nan iyaye ne a wurin baby Wanda Koda ran mahaifinta ko babu i believe zaku riƙe ta to the best of your ability,ba sai na mayar da hanun agogo baya ba cikin ku babu wanda bai san ta hanyar da Baby tazo duniya ba Wanda Yana ɗaya daga cikin ƙaddara na iyayen ta.Bazan boye maku ba zaman baby da Yaya Mallam babu sauki ko kaɗan abubuwa da dama sun faru sai dai yanzu babu wani fa'idar dawo da abinda ya wuce tunda ya rasu fatan Allah ya jikan shi Amin.


Ammie zan fara dake misali an baki amanar mutum ya zauna ƙarƙashin ki,cin shi da shan shi haka kuma da tarbiyar shi kina matukar kokarin ki sai wani ƙaddara na rayuwa ta afka mashi ya za kiji.?

Ba zan ji dad'i ba domin amana ne aka bani zan ga kamar na ci amana ko ban kula da amanar kamar yadda ya kamata ba.

Alhaji Abubakar gare ka,na saka yarinya ta a makaranta wace ba musulma b'ace rana tsaka a matsayin ka na mallakin makaranta musulmi ka mata wayau ka lalata mata tarbiya ba tare da saba'in iyayen ta ba shin kayi mata adalci kenan.?

Wa'iyazubillah mai zai haɗa musulmi soyayya da Christian kuma har ya kai ga wani alaƙa.!, Allah sawake.
Nagode sosai da fahimtar ku.
Baban abunda ya tara mu a nan shine ƙaddara rayuwa dai ta afka wa baby dukan wanan tambaya da na maku a kanta ya faru Allah ya haɗa ta da wani ɗan suka Christian ya yaudare ta yanzu haka tana ɗauke da ciki (watau tarihi ne ta maimaita kanta).

Kalmar nan na karshe ya fara yawo cikin kwakwalwar ammie"yanzu haka tana ɗauke da ciki (tarihi ya maimaita kanshi).

Wani irin ihu ta kurma tare da shako wuyar baby da ƙarfin gaske"baby baki mun adalci ba tarbiyyar dana baki kenan.?,menene kika nema kika rasa a wuri na ashe daman lesson d'in ƙarya da kike tsayawa kenan.!

Alaji habu da ya hydar suman zaune suka yi suna juya maganar cikin ranau domin wanan abu yayi muni da yawa.

General Sadiq ya mike Yana faɗin don girman Allah hajia Hadiza kiyi hakuri wani zagi,cin mutunci da tonon aisir bashi zai kawo mafita ba a yanzu.

Tari ne yaci ƙarfin ta hanunta na riƙe da wuyar baby Nan ta FAƊI ƙasa sumamiya.

Hadiza dake labe tana jin komi ta fado palour'n da gudu tana kuka tare da rufe baby da duka tana faɗin yar iska ashe daman abinda kika kula kenan tare da uncle Christ shi yasa kike zuwa staff room wurin shi bakya so kowa ya sani.?,lesson d'in ƙarya da kike tsayawa kenan.?,na rantse da Allah idan wani abu ya faru da momi ba zan kyale ki ba.

Wanke ta da mari ya hydar yayi,uban wa ya saka bakin ki a maganar manya.?,wallahi zaman ki ya ƙare a kano kema bokon banza da wofi mu gidan mu babu abunda bako ya haifar mana sai abun kunya da nadama.

Alaji habu ya zuba wa AMMIE ruwa taja wani wahaltacen nunfashi wanda ke fita da kyar ai nan take ya sungume ta zuwa hospital tare da su ya hydar baby Kawai aka bari a palour'n tana kuka da shure Shure kamar wacce farfadiya ta kama.

Suka isa aka shigar da ita emergency unit ana ƙoƙarin ceto rayuwar ta amma ina sun kasa dole aka kira doctor on call, Allah ya saka shine doctor nasu wanda ake kula dasu.

Examine nata ya fara yi sosai da sosai amma ina ba haske ya rasa gane komi saboda jinita ya hau sosai ,ga bleeding tana Yi SOSAI ba gagautawa, numfashi ya ki daidaita haka bugun zuciyarta shawara ya yanke after magrib za'a mata aiki saboda ceto rayuwar ta domin bai saka ran babyn da take ɗauke

28 / 35