Chapter 17 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   17 / 35

48K to 51K   out of 103.7K words

zai tashi zuwa Canada.

A ƙasa ta zauna tare da tataru dukan natuswan ta tana kallon yanayin fuskan shi wanda ya rikide don ɓacin rai.

Deeyah zan sanar dake wani sirri wanda baki sani ba game da baby,ki gafarce Ni na boye maki komi lokacin da zan tafi da ita Sokoto nace dake gwaggo ta nemi da a kawo mata yarinya da zasu zauna tare tana ɗebe mata kewa wanda na zaɓi baby saboda natsuwa ta...,maganar gaskiya Captain Aminu ya tashi kashe baby shi yasa na ɗauke ta daga wurin shi(nan take ya sanar da ita asalin labarin baby kamar yadda yaji a bakin yaya Mallam har zuwan baby Sokoto ).

Kafin yakai karshen labari sadeeyah kuka take na fitan hankali har tana shesheki saboda tashin hankali,mamaki da kuma rudewa,tunda Allah ya halicce ta ko a Film bata taɓa ganin irin wanan kwaba ba ,wai yaya yayiwa kan wanshi ciki har ta haihu abinda aka haifa ta rayu a tsakanin su..!,tarin tambayoyi ya cika mata zuciya wanda tasan babu mai amsa mata shi a yanzu sai shi Captain Aminu!

Hannu ya miko mata,jiki a sanyaye ta miko nata ya matse cikin nashi, hannu ɗaya yana share mata hawaye"kiyi shiru haka nan ƙaddara ce da tsautsayi wanda ɗan adam ba zai iya wuce ƙaddara shi ba kin san bana son kuka fa kada ciwon ki ya tashi,shiru tayi ba tare da ta ce komi ba.

Nanauyar ajiyar zuciya yayi,kin san menene matsalar yanzu.?

Ta girgiza kai!,baby ta canza completely,da zu gwaggo ta kira Ni tana faɗa lalai sai inzo in tafi da Baby ba zata iya da mugun halin ta ba,bata magana da kowa,bata hira da kowa,abinci sau ta ga daman ci, schol bata amsa sunan da aka saka mata abubuwa iri iri,kin san gwaggo tsohuwa ce bata da isasshen lafiya,bana so baby tayi abinda zai tayar da ciwon gwaggo idan yaran ta suka sabo labari baby ba zata kwashe lafiya dasu ba....

Katse shi tayi,yanzu me kace da gwaggo.?

Ce mata nayi tayi hakuri yau ake taron suna zan biya can gobe kafin in Koma Lagos!

Abban faruk nifa ban ga laifin baby ba wallahi ko ɗaya,kafi kowa sanin halin baby ba haka take ba yanayi ne ya canja ta,wallahi koda nice baby ba zan saki jiki da kowa ba wanan ai ba ƙaramin abu bane ace iyayen ka ciki ɗaya suka fito babban matsalar ma sun nuna kiyayya a gare ta ba dole tayi taka tsantsan da mutane ba,ta zauna a matsayin ta kada ta jawa kanta gori da cin fuska a cikin mutane,,kwata kwata baby guda nawa take da za'a damu da canjawan halin ta.?,yarinya karama wace kwata kwata bata wuce 12years old ba,Dame zata ji.?,halin da iyayenta suka saka ta ciki ko yawon bin gidajen mutane zaman rik'o.?

Gaskiya abban faruk ban amince ta tafi Sokoto saboda abinda baby ta aikata ba,kawai ka kira gwaggo a waya ka bata hakuri idan ba zata iya zama da baby ba a dawo da ita wurina koda a daki ɗaya zamu iya zama tare,ita kuwa baby Ni da kaina zan kiranta in rarrashe ta.

Tunda ta Fara magana kallon ta kawai yake yi domin akwai alamar gaskia a tattare da maganganun ta...,na fahimce ki aunty baby sai dai bai kamata a dauke ta daga wurin gwaggo ba zata ga kamar rashin kunya akayi mata yanzu zan bata hakuri sai kiyi magana da baby akan haka.

Koda ya duba agogo karfe 8:30pm,nasan gwaggo bata yi bacci ba Bara in kirata yayi dialing number.....

Har ya kusa katsewa ta dauka da sallama wake magana.?,kai gwaggo duk tsufan ne yau kuma murya na ne ba'a gane ba.!

Sadiqu bana son sakarci ba kakan ka nake ba haihuwar ka nayi"cikin zuciyar shi yace na jawa kai na masifa da daren nan.

Ayi hakuri gwaggo dama na kira ne akan maganar baby....,katse shi tayi bana son jin komi Allah sadiqu kazo gobe ka tattara ta ku tafi ba zan iya ba yarinya ƙarama da mugun hali sai baƙin rai,gida nawa ne ba nata ba amma sai shan kamshi da dagin kai.!

Ayi hakuri dai gwaggo yarinya ce ƙarama a hankali zata sake rashin sabo ne kwata kwata kwana nawa tayi tare dake.?,wallahi ba halin ta bane canjin yanayi ne nayi alkawari zan mata faɗa kuma za kiga canji.

Rufe mun baki makirin banza ita wanan ce karamar yarinya,wace tasan ta tako ƙasa daga makaranta zuwa gidan nan mai nisa,wacce tasan ta dauke kai bata gaisawa da kowa sai taga dama take cin abinci,bazan iya ba aga kamar kuntata mata nake yi nan kuwa ita ke azabtar dani.

Allah huci zuciyar ki hajia gwaggo uwar gida kuma amarya a gidan marigayi alhaji abu na mama.

Murmushi tayi kamar yana ganin ta,sadiqu ba kakan ka nake ba zan saɓa maka,yanzu dai na hakuri Allah ya bamu hakurin zama.

Yauwa hajiyata kin ga tafiyar da zan yi karo ilimi Canada ya tabbata INSHA ALLAH nan da kwana biyu zan tafi bazan samu daman zuwa maki sallama ba a gafarce mu a saka mu a addu'a Allah ya bamu nasara.

Shike nan sadiqu a riƙe ibada da addu'a shine takobin Mumini nan gida zamu taya ku Allah ya kai lafiya ya bada Sa'a da nasara akan abinda aka sa a gaba na alheri, Allah ya kare ku daga sharrin mutum da aljan Amin.

Amin ya ALLAH gwaggo ayita hakuri don Allah da baby marainiya CE bata san daɗin uwa ba bare na uba kome tayi a Daura ta akan hanya,shike nan sadiqu domin farin cikin ka zan yi komi"suka yi sallama.

Dama hands free ya saka sadeeyah taji duk yadda suka yi da gwaggo,,yanzu ki kira baby mu ji ko.?

Dialing number nata tayi..,lokacin Baby na kwance saman bed nata tana duba littafan ta taji wayan na ƙara wanda tunda aka bata babu wanda ya taɓa kiranta kuma babu wanda ta kira duk da akwai credit a ciki.

Ganin number aunty sadeeyah yasa ta ɗauka da sauri tare da fashe wa da kuka(itama handsfree ta saka),kallon juna suka yi da Captain wanda ranshi ya ɓaci....,baby.!

Na'am,menene na kuka ko baki so na kira bane?,, a'a aunty nayi MISSING naki ne sosai..,common stop crying idan ba so kike kanin ki faruk ya maki dariya ba,,,,dariya ta saka ashe anyi suna aunty.?,eh Umar faruk aka saka,ya ku ke?

Lafiya lau aunty,,Karatu ba wata matsala kina gane wa ko.?,eh aunty Babu Ina Jin daɗin zama amma ba kamar gidan ki ba...,ayita hakuri zaki saba ne a hankali ki saki jiki gwaggo matsayin grandmother naki take KU zauna lafiya komi kike so ki faɗa mata kuma ki rinƙa jin magana bana son rashin ji.

INSHA ALLAH aunty zan kiyaye ina Umar faruk.?,gashi nan yana jin ki yayi missing naki plenty...,dariya mai sauti ta sake itama "haushi ya cika Captain sadiq shida yace ta kira yarinya tayi mata faɗa shine suke shiririta da shirmen su na mata",tsaki da ya jane ya dawo da hankalin ta gare shi,baby me yasa baki kiran mu a waya.?uhm dama ban san da kudi a ciki ba kuma ina zuwa school a gida nake barin wayar ban wani iya amfani dashi ba"ta shirya ƙarya".

Ok kiyi kokari kina kira ana gaisawa muna jin lafiyar ki and gobe idan kin dawo schl ki kira uncle ɗin ki,ki mashi fatan alheri zai wuce Canada..,shike nan zan kira a gaushe shi Nagode "suka aje wayar.

Amma dai sadeeyah baki da hankali abinda nace ki kira kiyi kenan.?,dama duk kece kika sagarta yarinya haka ake faɗa babu wani abu da kuma faɗa mata dangane da iskancin da take ma gwaggo naba..!

Kayi hakuri idan na bata maka rai shi yaro sai da rarashi, faɗa ko duka ba shi zai saka yaro ya gyara mistake nashi ba,a hankali zaka bi yaro cikin Hikima da jan shi a jiki...

Rufa mun baki don Allah,U ruined everything...,I Said I'm sorry honey...,ok nayi saboda faruk"ya fadi cikin sakin fuska",zan bar ATM dina na currently account saboda buƙatar ki na yau da kullum tunda Yaya Zahra ta ce sai kin yi watani biyu a kaduna kin ga idan akwai abinda kike buƙata ki cire kuɗi kiyi,akwai wani gida da Mallam bello na nuna mun na sayarwa nan bayan su hajja,kafin ku dawa zan turo kuɗin gidan agyara komi ki dawo ciki har inga yanayin zamana a can kinga da faruk yayi six months sai a barshi wurin hajja ki same Ni a canada..., dariya take yi sosai,amma abban faruk baka da dama na tabbata baka kai Ni son faruk ba,Wallahi ban manta da wahala dana sha wurin haihuwa ba ƙafa na ƙafan faruk koda birnin sin zaka tafi shi ɗan wata shida za'a cire a nono!

Wasa nake yi,gobe zaku je ki duba gidan idan ya maki sai in bada half payment and mota na dake Lagos zan saka sergent sagir ya kawo maki saboda hidma .,, Allah Kara budi ya sanya albarka honey.

Amin Amma ba anan ya kamata kiyi GODIA ba sai mun haɗu a Canada...,dariya ta saka tare da ƙara rungumo shi cikin Hikima suka samu natsuwa ba tayi da sun yi sex ba.




*SOKOTO STATE*


_____Baby na tashi Bacci da asuba tayi wanka tare da alwala ta gabatar da Sallah dama ta zo da Alkur'ani izo goma nata dashi take karatu bayan sallamar asuba,tana ganin 6:30am tayi ta shafa adu'oi ta sanan ta saka uniform abunda Bata tsaya jiran kowa ba ta ɗauki schol bag nata ta Kama hanya zata fita,mai gadi na kallon ta tana kallon shi ta buɗe gate ta fita a hankali take tafiya a bunta domin tayi alkawarin ba zata sake shiga motar kowa ba Allah ya halicce ta ne a matsayin kaddarar wasu,ta taso cikin wahala da baƙin ciki yanzu tasan gaskiya ba zata taɓa yadda kyale kyalin duniya ya rude ta ba wanda komin dad'e wa idan har aka san ko ita wacece ba zata ƙara samun wanan gatan ba,gwara tun yanzu ta saba da wahala wanda dama ciki ta taso...,koda 7:30am yayi ta isa schol ta shige class din su ta zauna"dama bata ma kowa magana har corper da ke masu integrated science ta shigo.

A gida gwaggo najin kwaramniya baby har ta fita domin itama data tashi sallar asuba bata komawa bacci, ɗaukar ma kanta alkawarin tayi ba zata sake shiga lamarin baby ba duk abunda taga dama tayi har Lokacin da zata gane gaskia.


Koda gari yayi haske sosai mutanen gwaggo suka fara taruwa kamar yadda suka saba kawo mata gaisuwa a taya ta hira har Lokacin fitan su aiki yayi ta tara su akan kowa ya saka ma baby idanu tayi abunda take so.

A schol sun gama First amsa second period Wanda kusan dukan abinda aka koya masu baby ta sani kuma tana bada amsa idan akayi tambaya har aka tashi break, ɗan sit nata Sherif Ya fita ya sayo egg roll guda biyu da soya milk ya mika mata ɗaya"dama yunwa take ji sosai,babu musu ta amsa taci suna hira cikin harshen turanci yake tambayanta wane schol tayi.?

Ta faɗa mashi COMMAND schol tayi a Lagos,,yace shi yasa kike da brain saboda ku na da kuɗi sosai ,ni government schol nayi domin iyayen na ba hali ne dasu ba ko yanzu wani uncle dina ya saka ni a wanan schl ɗin,,cikin zuciyarta tace gwara da kai kana tare da iyayen ka Cikin jin daɗi,idan da zaka ji labari na kila ko magana baba zaka sake mun .,suka ci gaba da hira har aka dawo break sauran yan class d'in nata gulmar sheriff Wai ya lake ma baby don yaga suna da hali...

Haka suka ci gaba da ɗaukan darasi har zuwa 1:30pm da aka tashi,tare suka jera da Sherif zuwa gida a ƙasa yana ta mamakin Yadda yar gidan masu kuɗi zata yi tafiyar ƙasa mai nisa haka,ana kai wa titin gidan su baby sherrif yabi hanyar shi ta tsallaka ta shige gida lokacin mutane sun rage yawa sallama kawai tayi har zata shige d'akin ta,sai ta tuna da maganar aunty sadeeyah ta dawo baya ta gaisa da mutanen dake palour'n,ta shiga kitchen ta gaushe dasu halima da aiki,ta wuce d'akin gwaggo ta gaishe ta,ba yabo ba falasa ta amsa mata,baby ta dan jima zaune ta tashi ta shige d'akin ta...,wanka ta fara yi tare da gabatar da Sallah sanan ta fito zuwa inda ake jera abinci ta diba a plate ta koma d'akin taci abunta,bayan ta gama Bacci ya kwashe ta sai la'asar ta tashi tayi sallah ta fito palour (dama abinci rana gaba ɗaya ake yi zuwa dare), Lokacin su halima sun wuce gwaggo ce zaune da wasu mata suna hira,gaishe su tayi ta zauna gefe hankalin ta na kan program da ake yi a TV...

Can dai ta tuna bata kira uncle Sadiq ba kamar yadda aunty sadeeyah ta umurce ta..., d'aki ta Koma tayi dialing number nashi har ya gama ringing bai Daga ba,ta sake kira shiru.

Lokacin data kira yana can suna rigima da yaya Mallam akan ba zai daga ko nan da can ba sai ya fito mashi da yar shi domin ba shine ya haifa mashi ita ba,,yace bashi da iko a kanta don haka bai isa ya tsare shi sai ya fitar da baby ba...,ranar ran maza ya ɓaci kamar zasu buga sai da aka raba su yaya Mallam yana kumfar baki wai Captain sadiq ya saka baby ta Raina shi Wallahi abun kunyar nan da suke gudu sai ta aikata shi a duniya,yadda ya ma wata ciki ta haife baby,itama baby haka za'a mata ciki ta haihu wanan alkawari ya ɗauka masu tunda suka ɗauke ta aka hana ta bin umurnin shi...,,ran Captain sadiq a b'ace ya haɗa dukan abinda zai buƙata ya saka driver ya kai shi hotel ya kwana domin saboda ɓacin rai ba zai iya kwana cikin Barrack d'in ba...,cema sergeant sagir yayi ya dawo da safe ya kai shi airport daga nan ya wuce yola da motar sai ya dawo a motar kasuwa.


Yaya Mallam baƙin ciki da hasada ke cin shi domin dai Captain sadiq ya fishi komi a duniya kuɗi,ilimi,daukaka da kuma kwanciyar hankali...,wanan yasa ya dauki alwashin sai ya wulakanta rayuwar Captain sadiq a duniya wanda dole sai baby na kusa dashi ya zama dole ya nemo baby ko don cikar burin shi!.


*KANO STATE*

ammie an zama babban mace domin ta samu soyayya da kwanciyar hankali a gidan mijinta,suna zaman lafiya sosai da uwar gida hajia mariya,ko wace na ganin mutuncin yar uwanta,yaran suna girmama ammie kamar itace ta haife su basu da abokiyar shawara sai ita musamman faiza da take babba lokacin da za'a zo nan auren ta gidan ammie akayi komi.

Alaji habu ga gama masu shirye shiryen zuwa aikin hajji wanda ammie,umma da faiza zasu tafi tare lokaci ɗaya domin akwai tafiya a gaban shi yaso kwarai su tafi da ammie sai dai ba zai samu ba saboda bata jin daɗin jikanta.

Bayan tafiyar shi rashin lafiya ya tsananta hajia mariya ta wuce da ita Hospital akayi dukan gwaje gwaje da ya kamata sakamako ya nuna tana dauke da juna biyu,,,murna wurin hajia mariya da yara ba'a magana,ita kam ammie ba haka taso ba domin wani dalili nata na daban!!!.


_Halimatu Sadiya Muhammad_
*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..



~🅿41-42~




____Cikin na ammie yazo da laulayi matuƙa wanda hakan yasa da alaji habu ya dawo daga tafiyar shi ya rarrashe ta akan tayi hakuri da tafiya aikin Hajji har wani shekara lokacin ta haihu.

Kuka ta saka masa ita dole sai ta tafi idan kuma ya hana ta wallahi zubar da cikin za tayi...,ranshi ya ɓaci sosai har ya furta duk abinda ya faru da cikin nan a bakin auren ta.!,kuka ta fashe mashi dashi wanda ya ƙara tunzura shi ya fita ya bar mata gidan,tun daga ranar bata sake gane kanshi ba da abun ya ishe ta,takai ƙara nshi wurin ba'baa mairo wacce ta kira su duka ta masu nasiha sosai,ta bashi umurni akan idan da yadda za'a yi ya bari ammie ta yi tafiyar wanda dama ta faɗa mata kudirin ta nason zuwa kasa mai tsarki domin neman gafarar Ubangiji akan abubuwan data aikata na sab'on Allah,ta nuna ma ammie idan har taga bata samu zuwa ba awannan shekara Allah ne bai kira ta ba,GODIA suka mata sosai suka tafi gida.



Cikin ikon Allah a hankali laulayin yayi sauki sai shirye shiryen tafiya suke yi har lokaci tafiya yayi dole umma kano tazo saboda ta nan jirgin su zai tashi, cikin yan rakiya yadda ya hydar da mama ladi murna makar zai kashe ammie yau ga umman ta da ɗan uwan ta a gidan ta,basu wani yi baccin kirki ba a ranar saboda farin ciki ammie wurin su ta tare wanda ba haka alaji habu yasu ba dole ya daga mata k'afa ,da safe tunda wuri suka gama shiri hajia mariya da kanta ta kawo ma su umma abun karyawa wanda hakan ya faranta ran umma sosai,basu wani bata lokaci ba suka nufi airport bayan an gama abinda ya kamata jirgin su ya daga zuwa ƙasa mai tsarki.
Hadiza karama gidan hajia mariya ta kowa saboda karatun ta.



____Baby bata da damuwar komi yanzu data tashi tayi sallah zata yi shirin schl bata jiran kowa ta kama hanya idan sherrif yazo da abinci tare suke ci,idan anyi darasi wurin da bata gane ba ya ƙara fahimtar da ita,inda bai gane ba ta fahimtar dashi lokacin cin abinci idan yazo da kuɗi ya saya masu abu su ci lokacin tashi tare suke jerawa da an kai titi ta shige gida yaci gaba da tafiya.

Wata ranar juma'a ta dawo daga schl kenan tana zaune d'aki taji sallamar mutane ana Barka da zuwa,Barka da zuwa ana shigo da kayan abinci niki niki,sai da taji hayaniyar ya lafa ta fito,"wata farar mace mai jiki da matsakaici tsayi ta gani tasha

17 / 35