Chapter 11 Reading NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA HN Novels

NIMA 'YA CE Yar da Ta Boye By LEEMA

Author :  LEEMA Category :  KDP NOVELS

Chapter   11 / 35

30K to 33K   out of 103.7K words

isa haka kada a kar'ar mun da turare,uhmmm deeyah gori.?
Sauƙin abun dai nike saya idan ya ƙare zan sayo wasu design ɗin,suna tafi suna raha har table ɗin lokacin baby ta gama tana kokarin Kai plate da cup kitchen.

Sadeeyah ta amsa barshi kawai zo nan muje ki kwanta suka nufi wani dake dake opposite da wanda suka fito shirt d'in dake jikin baby ta cire tare da daura ta saman bai ruf da ciki yadda bayanta zai sha iska ta kuna mata fan,oya sleep like a baby sweet heart,rufe ido baby tayi dama ta gaji Bacci take ji,kofan sadeeyah ta jawo mata ta fito tana jin soyayyar baby cikin jinin ta.

Cikin so da kauna suka ciyar da junansu har suka kamala ta kwashe kayan ta wanke koda ta gama yayi dai dai saman three seater zuwa tayi wurin ƙafan shi ta zauna ta dauka kafafun shi saman laps nata a hankali take mamatsa kafafun nashi....

Can Kasan mak'oshin shi yace thank u deeyah...,rmtace for what.?
For everything, Allah ya maki albarka sadeeyah ina alfahari da samun mace mai natsuwa da tarbiya kamar ki....,murmushi taci gaba dayi cikin natsuwa ya kwashe duk abinda ya sani game da baby ya Sanar da sadeeyah,tun kafin ya karasa bata labari kuka take sosai hadda shesheka dasu ajiyar zuciya"tana imagining Wai yarinya karama Kamar baby za'a yiwa irin wanan duka saboda tsabar rashin imani,nan da na taji yaya Mallam ya fice mata a rai domin ta tsani mutum azzalumi musamman namiji mai zaluntar mace.

Tashi zaune yayi tare da rungumo ta zuwa jikin shi yana rarashin ta har tayi shiru tace"honey yanzu baka ganin idan ka mayar da ita zai iya mata fiye da hakan.?

Haka ne deeyah nasan halin Captain Aminu fiye da tunanin ki wallahi mutum ne mai mugun zuciya gashi da naci idan ya fadi magana baya canja wa sai ya aikata,zan so anjima da dare mu tafi tare da ke gidan ko Allah zai sa ya canza ra'ayi idan ya ganki!

Honey gaskiya zuciyata bata aminta da mu tafi da yarinyar ba kawai ta zauna mu tafi mu biyu idan ya hakura da safe mu dawo da ita,and wallahi ina sonta da zai bani ita...

Katse ta yayi kaji ki da wani magana daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki,baki san inda yarinya ta fito ba,sunan ta,dangan takar dake tsakanin su ba kawai kice ya baki yarinya "U Are sick in the head.

Murmushi tayi kawai domin tabbas yarinyar na matukar kama da Captain Aminu maybe younger sister shi ne.

Baby bata farka ba sai daf da magrib sadeeyah ta haɗa warm water tayi mata wanka sosai ta gasa mata jiki,baby na kuka tana bata hakuri har aka gama ta shafe mata jiki da deep relief cream Bata saka mata riga ba sai doguwar wandon ta data cire mata don wurin tasha iska suka fito palour lokacin Captain sadiq ya fita zuwa masjid.


Tunda Captain sadiq ya fita da baby Yaya Mallam ke Safa da marwa cikin palour yana ayana irin rashin mutunci da tuzarci da zai ma Captain sadiq cikin barrack d'in a yau,zuciyar shi sai tafarfasa yake yi har zuwa yamma ya rasa mafita saboda duk wani makirci da zuciyar shi ta saka mai ya aiwatar idan ya tuna da kyautatawa irin na Captain sadiq sai yaji ba zai iya aikata mashi hakan ba har aka fara kiraye kirayen magrib ya fita zuwa masjid.

Dama idan suka tafi sai anyi sallar isha'i suke komawa gida,wani lokaci gidan Captain sadiq suke nufa ayita hira da sauran abokan su da matan su har zuwa 10pm kowa ya koma block nashi,wata rana kuma a tafi block na ɗaya daga cikin abokan su haka dai suke zumunci,idan kuma sun fita wani aiki matan nasu ke zumunci banda yaya Mallam da bashi da aure da wasu daga cikin abokan aikin su da matan su ke garu ruwan su cikin su akwai masu zuwa night party , Sunday Sunday,week end babey Q, cocktail,da dai bar kala kala cikin barrack d'in"su yaya Mallam Allah ya tsare su basa shaye shaye shida sadiq amma kam yaya Mallam akwai neman matan banza domin bashi da niyar aure gudun tonon asiri.


Bayan sun idar da Sallah sun fito ne yaya Mallam ya riƙe hanun Captain sadiq cike da ɓacin rai,"sadiq tun muna shaida juna ka dawo da diyar mutane taci gaba da punishment d'in ta tun kafin rayuka su ɓaci!!!

Murmushi yaya mai ciwo,Aminu yaushe ka koma mara imani da tausayi ban sani ba.?,duk hukuncin da kayi mata bai isa ba sai taci gaba.?,dama inada niyar zuwa baka hakuri tare da sadeeyah anjima shike nan zan dawo da ita idan kaga dama ka kashe ta...,ya wuce abun shi don ranshi ya ɓaci haka ya shigo gida sadeeyah na sallah ya jawo hanun baby bai ce da ita k'ala ba har kofar gidan yaya mallam nan ta duke tana wayyo Allah na mutu zai kashe Ni don Allah uncle kada ka mayar dani gidan kashe Ni zai yi ammie tace shine papa na Amma baya sona,Ni dai ka mayar dani wurin ammie cikin jirgi ita bata dukana kuma tana bani abinci....

Tausayinta ne ya kama shi amma bashi da wani option daya wuce ya mayar da baby kada abun ya zama babban magana cikin barrack d'in domin mutanen bariki basu iya samun gulma ba sai ayita ririta shi ana mayar dashi babban magana!,,door ɗin ya murda ya tura baby ciki ya jawo ya wuce abun shi.


Yana shiga gida sadeeyah ya samu tana kuka ina take.?,,na mayar da ita inda na dauko ta!

Kuka taci gaba dayi tana magiya akan yazo suje gidan su dauko ta jikinta na bata Captain Aminu zai hukunta baby...,banza yayi da ita ya shige bedroom d'in hankalin shi a tashe domin ya tsani kukan matar shi saboda bata da isasshen lafiya idan ciwon ta ya tashi wahala suke sha sosai shi yasa yake tsaka tsantsan wurin ganin bai bata mata rai ba.

Kukanta taci gaba da rairawa cikin palour ɗin can yaji alamar buɗe kofa...,da gudu ya fito sadeeyah ce ta nufi hanyar block din Captain aminu aguje ya rik'o hanunta yana haɗa ta da Allah ta koma gida amma ta turje sai ta tafi ta dawo da baby!!!

Cikin zafin rai ya wanka mata mari Nan take ta yanke jiki ta fadi tana fidda numfashi sama sama kamar mai chronic asthma,jikinta duk ya saki tayi nauyi duk karfi da jarunta shi ya kasa daga ta,ita kuma sai shure shure take yi nan take ya kira wasu sergent biyu mata suka cicibe ta tare dashi cikin na uku sai cikin gida,,"abunka da bariki har wuri ya cika ana kallon gulma domin tunda suke basu taɓa ganin tayi irin haka ba kowa a barikin yasan irin soyayya da kauna dake tsakanin Captain sadiq da matar shi amma yau aka ga saɓanin haka,,nan take wasu maza ke faɗin ai tun da rana suka Ganshi rike da wata yarinyar har clinic ya kai ta maybe karuwan shi ta haifa mashi suringa ta kawo ta gidan shine sadeeyah ta mata wanan duka har ya haɗa su faɗa...,can wani army doctor dake zama a hospital d'in cikin barrack ya bada tabbacin yarinya da Captain Aminu take kama ba Captain sadiq ba kowa yasan aminai ne duk yadda akayi Captain aminu keda yarinyar ......,haka akaci gaba da cece kuce har crut Peter yaji ya ruga sai BLOCK ɗin Captain Aminu yana son bashi labarin a bunda yaji ana yaɗawa cikin barikin,yana shiga yaci karo da baby tsaye cikin palour'n wurin labulee.....

Kwala kira ya fara yi oga AA where u dey.?
Dama aiki yake cikin desktop computer ɗin shi a daki,ya sauko sanye da jalabiya fari kal.

Peter ya riko hanun baby u see dis pikin wey resemble u,heeee she don cause big crowd for outside people for dis barrack no better at all...

Katse shi yayi ranshi a b'ace still Yana kallon baby kamar zai hade ta don baƙin ciki"tell me something peter what did they said about her.?

That one na big matter oga aminu,they just talk am say u and oga Sadiq give one lady bele,na the pikin whey she born ,she come carry her come to ur apartment so tey u bit the pikin black and blue,oga Sadiq come carry her to his apartment form there oga Sadiq start to they fight with his madam bcuz of this pikin"Yana nuna baby Wanda tunda yake bayani take zub da hawayi....,yaya Mallam ji yake kamar ya kama da wuta domin babban abinda yake gudu kenan gashi yau yau daga zuwan baby ya faru,tsinaniyar yarinya ta shiga tsakanin shi da babban aminin shi daga zuwan ta,shegiya iblisiya kamar yadda uwarta ta mashi shamaki da iyayen su haka baby KE neman mashi shamaki da sadiq din shi!

Sama ya aura a guje ya dauko jakar kayanta yayinda ya damki hanun ta yayi hanyar waje....



*KANO STATE,SHAGARI QUARTERS*

Tunda ammie ta shirya da alaji babu bata sake bari wani sabani ya shiga tsakanin su ba duk da abubuwa na cin fuska da wulakanci na faruwa a gare ta daga mijin nata wanda duk makirci uwar gidan shi hajia mariya ne hakan bai saka ta karaya ba Da taimakon Allah da taimakon ba'baa mairo dake daura ta akan hanya a kullum ta zame mata uwa da uba har take tunanin bata labarin rayuwarta ko da shawar wari da zata taimaka mata!

Lokaci na tafiya ta cinye satin ta ɗaya na amarci da daɗi babu daɗi domin dai wata rana ko breakfast alaji habu baya yi a gidanta,da ya tashi bacci zai wanka ya nufi gidan hajia mariya nan zai yi break fast ya nufi wurin aiki ita da saka shi a ido sai goma zuwa sha ɗaya na dare wani lokaci har sha biyu ya dawo da excuses kala kala wai ayuka suka mashi yawa a office ko meeting tun abun na damunta har ta hakura ta zuba ma sarautar Allah ido,,aka raba girki wanda biyu biyu amma sai ta share sati alaji bai kwana gidan ta ba sai ya leko ya koma,abun mamaki daya shigo zasu shiga faɗa kaman karnuka har sai ya bar gidan sai taji tana mugun son ganin shi...,abun duniya isheta wata rana ta shirya bada sanin shi ba ta nufi gidan su na da wurin Uwar masu gida nan shawara,,tsautsayi yasa alaji habu yaga fitowan ta daga mota ta shiga gidan ba ƙaramin ɓaci ranshi yayi ba domin ya jima zuciyar shi na saka mashi abubuwa da dama akan ammie bata daina bin mazan banza ba da auren shi shi yasa ma ya lura yanzu bata damu da nan hakkin ta a wurin shi ba,ai kuwa za ayita takare domin ba zai iya ci gaba da zama da k'aruwa ba!!!!



_Halimatus sadiya Muhammad_

*LEEMA*
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*NIMA 'YA CE*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~sensational Heart touching story~

*BY*
*LEEMA*

_DEDICATED TO KANO STATE_

*The whole book is dedicated to KANO STATE for their heartfelt support and contribution towards president MUHAMMAD BUHARI by re-electing him to retain his seat as the president of Nigeria for the second time,KANO STATE with the highest number of vote"ONE MILLION,FOUR HUNDRED AND SIXTY FOUR THOUSAND,SEVEN HUNDRED AND SIXTY EIGHT{1,464,768} KUDUS TO KANO STATE CITIZEN'S👍🏻*





*LITTAFAN MARUBUCIYA*

WATA RAYUWAR
QURUCIYAR JUMMAI
RIKICIN AURE NA
IYA KUƊIN KA..
HISHAM NAWA NE
NASREEN
NIMA 'YA CE LOADING..


_Alhamdulillah Allah ya albarkaci daya daga cikin member na brilliant WRITTER'S ASSOCIATION"UMMU FARHANA" ta haifi baby girl,Allah ya sanya wa abinda aka haifa albarka ya ba mai jego lafiya da ƙarfin jiki amin_






~🅿27-28~




Janta yake a ƙasa hanun shi ɗaya jakan ta ne har block ɗin Captain sadiq ya tura kofar a fusace tare da cillo baby tsakar palour'n,a lokacin kira'a ke tashi cikin palour'n Captain sadiq rungume da matar shi yana shafa mata turaren fusuqu (dama tana da matsalar jinnu),koda aka cillo baby ji kake garam ta haɗe kai da royal cushion dake palour'n tunda ba nauyi ne dashi ba suka yi baya tare....


Captain sadiq ya ɗago jajayen idanun shi yana kallon yaya mallam cikin ɓacin rai,shima kallon nashi yake yi har zuwa wani lokaci Captain sadiq ya ɗauke idanun shi yana ci gaba da tofa ma sadeeyah adu'oi.

Yaya Mallam yace"saboda kai yau suna na ya ɓaci cikin barikin nan,a dalilin abinda ka aikata mutunci na ya zube a barikin nan.!,ka buɗe kunu wanka da kyau kaji abinda zan faɗa maka tunda ka mun shishigi cikin lamura na zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne,gata nan na kawo maka daga yau babu Ni babu ita kayi duk yadda kake so da ita tunda ban isa tayi laifi in hukunta ta ba Ni da d'iya ta a mun iko da ita,baka san komi a kanta ba,baka san lokacin da aka haife ta ba,baka san pains and agony da nayi going through cuz of her "Yana nuna baby a dalilin ta na rasa family na kowa nawa na zama mara ya na karfi da yaji wanan,wanna shegiya tsinaniyar yarinya wace ba zata gama da duniya lafiya ba wallahi yadda kika saka na aikata abun kunya a duniya kema sai Allah ya nufe ki da aikatawa sai kin haifa kin goya da yardan Allah!!!

Kai kuma na dawo kanka wallahi idan ka sake koda wasa ka tunkaro Ni da maganar wanan idiot d'in WALLAHI hukuma zata raba mu,ya juya fuuuuuu!!!!!


Baby CE tabi bayan yaya Mallam a guje..., Captain sadiq ya daka mata tsawa"where the hell are you going to.?

A razane ta dawo ƙasa ta zauna sai da tayi fitsari a wando saboda rude wa...

Ya ɗauki lokaci mai tsayi Kafin sadeeyah ta dawo hayacin ta bacci yayi gaba da ita,koda ya duba agogo 9:40pm daukan ta yayi zuwa bed room nasu ya gyara mata kwanciya,sanan ya dawo wurin baby dake dunkule gefe ɗaya,alama yayi mata da hannu da tazo...,cikin kad'uwa ta kara su wurin ta zauna ƙasa lokacin ya lura tayi fitsari a zaune fasa magana yayi"ga daki can ki dauki bag naki idan kin shiga ki fara yin wanka sai ki canja kaya ki kwanta.

Mikewa tayi ta kama hanya zuwa d'akin....,kwanciya yayi saman carpet Yana tunanin maganganun yaya Mallam domin sun kunshi wani sirri mai girma da yake boye wa,iya tsawon shekarun da suka kwashe dashi bai taɓa sanin kowa nashi ba abu ɗaya ya sani baban shi ya rasu baya ga wanan bai san asali ko wani dan uwa nashi ba idan har ya fahimci inda maganar ya dosa ciki yayi ma wata kenan ta haifa mai yarinya a dalilin haka ya rabu da iyayen shi bai sake waiwayen su ba,idan har hasashen shi ya zama gaskiya ba'a son ranshi ya taho da ita barikin ba shine dalilin da yasa yake kokarin boye ta kada kowa ya sani"murmushi yayi babu komi insha Allah zai rika baby ya mata gata kamar ko wace d'iya domin ITAMA Y'ACE CE wace yasan nan gaba sai anyi alfahari da ita,wanka yayi sanan ya kwanta bacci.

Tunda suka tashi sallar asuba ya lura da zazzaɓi ta tashi don haka bai fita Masjid ba a gida yayi sallah ya mata wanka tare da haɗa mata tea Tasha tare da magani sanan ya gyara gidan,koda ya leka d'akin baby ta tashi tayi sallah yace ta dawo wurin sadeeyah zai fita...,ya shirya ya fita cikin barrack domin suna da aiki.

Ganin Baby yasa sadeeyah ya warware sosai ta tashi suka shiga kitchen tare suka haɗa abinda za su ci,bayan sun kamala tayi ma baby wanka itama tayi tare da cin kwaliyya suka dawo palour suna kallo"can tace wai ya sunan ki..?,tace baby!

Murmushi tayi baby ai ba suna bane,tace tunda aka haife Ni baby ake ce mun har schl ma da sunan nake amfani...,ok kin taɓa yin schl ne..?,eh a Kano lokacin ina wurin ammie na!

Yanzu ina ammie ta and me yasa ta bari kika dawo nan.?

Ammie na kano ta canja gida ne mai kyau tayi aure shine mijinta yace a mayar dani wurin papa na"lokacin ta fahimci lallai ba ta hanyar aure aka haifi baby ba shi yasa da mahaifiyar ta zata yi aure ta dawo da ita wurin Captain Aminu babu shakka shine mahaifinta kenan!!!

Amma menene dalilin shi na nuna mata kiyayya haka.?,wanan amsa a bakin mijinta za taji idan ya shigo...,tambayoyi ta shiga ma baby akan karatun da tayi,ta gane baby Nada kokari sosai ta fanin addini kuwa babu abinda ta sani!

Zuwa azuhur ta shirya abinci cikin basket ta d'aura abaya saman English Wears dake jikinta ta yane kanta da ƙaramin veil din shi...,baby ki zauna zan kai ma uncle abinci office yanzu zan dawo kin ji.?

Tace tau sai kin dawo aunty..,Koda sadeeyah ta Isa office din nasu suna fama da aiki ta gaisa da sauran abokan aikin mijin ta cikin wasa amma banda yaya Mallam wanda ko gaisuwa ta bai amsa ba bare ya biye wa shirmen su.

Bata wani bata lokaci ba ta aje mai abincin ta dawo gida saboda baby dake ita ɗaya a gida,koda ta shigo baby na zaune tana kallon cartoon Network inda ake Film ɗin"Sofia the first",sai dariya take kyalkyala ganin ta haka ya faranta ran sadeeyah sosai.

Sai zuwa yamma Captain sadiq ya dawo bayan yayi wanka ya ci abinci suka tattauna da sadeeyah akan yadda yaya Mallam ya mashi jiya kma ta bashi goyon baya ɗari bisa ɗari na su riƙe baby da amana har take sanar dashi ta fara karatu kuma she's very brilliant ,sai dai fanin karatun addini bata da sani!

Yace what's ur suggestion now?,,fuskan shi ta shafa,honey tunda akwai schl cikin Barack and she can read and write Kawai ta shiga cikin yan primary6 suyi common entrance exmas tare kaga idan ta dawo zuwa 4pm ta rinka shiga masallaci tana daukan karatu tare da sauran yara.

Murmushi yayi saboda abinda ke zuciyar shi kenan,ok zuwa gobe zan yi komi ta fara zuwa insha Allah.

Abunka da akwai kuɗi ƙasa Captain sadiq yayi duk wani shige da fi ce cikin kwana aka sama ma baby admission a "COMMAND PRIMARY SCHOOL" da yake suke bada uniform da writting material yasa ba'a wani bata lokaci ba ta fara zuwa abunta..,ranar farko abun ya zame mata sabon abu tunda ta kwana biyu bata shiga class ba,sanan wanan private ne akan wanda tayi a kano government schol

11 / 35