Author : Huguma Category : Complete Novels
kika fada". Fada ne ya kacame tsakanin sassan zukatanta guda biyu,daga qarshe taja qaramin tsaki,ta jawo landline ta soma neman number gidan anni saboda tata wayar a hannunsa ta barta.
Daya daga cikin masu aikin ce ta daga,cikin girmamawa ta gaida sabreen.
"Hadani da huda ko.nadra ko haneefa"
"Okay maa" Ta amsa mata a ladabce. Dukkaninsu ta kawo mata,suka bata lokaci sosai suna hira kafin suyi sallama.
Daki ta koma donyin wanka,sai a sannan ta lura an kwashe duk wani datti kwanuka data zubar. Mamaki yadan kamata,amma saita samu assurance na shine ya shigo din ya fidda kayan.
Tsaf ta gyare dakin,ta wadatashi da qamshi daya qarawa dakin wani irin sukuni da nutsuwa,sannan saita wuce tayi wanka. Tsaf ta shirya cikin wata chiffon gown maras nauyi,ta lalubo Malaysian hijab ta saka sannan ta fita.
Kaman ba zata haura saman nashi ba amma ta daure. Tasan bai kamata ta barshi haka bata gyara ba,kaman yadda bai kamata ta bari wani ko wata su hau ba.
Tsaiwa tayi tana qarewa parlor din kallo. Komai yana nan a zube inda yayi amfani dashi,da alama ma a nan parlor din ya kwana,saita taka tana tattareshi tsaf,ta kuma sanya vacuum cleaner ta tsaftace saman dukka ta gyare masa toilet din. Sanda ta gama azahar ta kawo jiki,cikinta kamar an mata yasa,dole ta sauko dining din qasa neman abinci.
Tunda lalurar nan ta kamata ma'u ta haddace,bata taba barin dining din wayam ba komai,kaman yadda bata barinta ta dawo sake cin abinci ta samu maimaici.
A nutse ta zauna ta zuba da nufin soma cin abincin amma kuma sai taji ta kasa. Azahar ta sako jiki sosai,ina yaje?,abunda tun fara shaquwarsu bai taba faruwa ba.
Ta juya abincin har batasan sau nawa ba amma ta kasa kaiwa bakinta,kaman ahakan ake jira ya faru sallamarsa ya ratso parlor din.
Duk da hautsine yake amma kallo daya tayi masa shigarta taji ta burgeta ta masa mugun kyau. Baqi da baqi a jikin fari,saidai duk da hakan saita wani basar ta dauke kanta tana amsa masa sallamar tan jira taga da wanne irin yanayi ya dawo gidan.
Tsam ta miqe sanda taji alamun takowarsa nan dining din,ta tura kujerar tana nufin wucewa,saiji tayi anyi mata wata Kyakkyawar damqa na tare da bata lokaci ba kuma ya mata wata Kyakkyawar runguma da ta sanya qamshin turarensa mai matuqar sanya nutuswa isa ga hancinta.
Saman wuyanta ya aje fuskar ta,kullum alfahari yake d wannan qamshin nata da yasha banban dana kowacce mace.
"Kina bisa wuyana oum triplets......a yafemin,na leqo kina bacci,banaso kuma na katse wannan daddadan baccin nan.....yaya babies dina" Ya fada yana zamewa ya duqa a gabanta yana yaye rigarta.
Maganganunsa daya saba yi da cikin nata yayi da nufin da yaransa yake magana,ta dauka zai tashi kaman yadda ya saba,sai kawai ya jawota yana tsokanarta ta cibiyarta. Janyewa tayi da sauri ya saki dariya.yana miqewa.
"Anga amna"
"Serious hamma....serous?" Girarshi ya dage mata,saita sauke ajiyar zuciya tana fadin
"Alhamdulillah alhamdulillah.....please hamma"
"Bani hug daya kawai ya isa tukucin yi miki albishir......tausar dare kuma itace tukucin kaiki wajenta"
"Zanyi hamma zanyi wallahi" Ta fada tana dan qaramin tsalle. Riqeta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanunta,da wata muryarsa can qasan maqoshi yace.
"Bi a hankali.....yarana" Ya qarasa fada yana dora hannunsa saman cikinta. Kunya ta kamata,ta kuma sanyata janye idanunta da sauri,daidai sanda kira ya shigo masa.
Bai fasa sakata a jikinsa ya matseta ba sannan ya amsa wayar da cp ne ya.kirashi.
"Thank you.....gani nan fitowa" Sai ya katse wayar yana dubanta.
"Zanga baqi my world.....zan dawo shortly in sha Allah....ki kulamin da kanki" Ya fada yana kissing kuncinta duka biyun ya juya yana fita farfajiyar gidan.
Daki ne yalwatacce da aka shimfideshi da lallausan carpet milk color kaman kalan labulayen dakin.
Daga damansa bibo ce ita da zuwaira,sake maida dubansa yayi ga gabansa,mashkur ne shi da dan uwan tasa ta'asar.....mashkur din da gaba daya ya fita a hayyacinsa,tsufa sosai ya kamashi,wani irin tsufa na qarfi da yaji wanda wawulonsa ya sake tsananta munin abun.
Sauran duka ya bisu da kallo,amma kowannensu munin fuskar mashkur ta zarta munin da yake gani a fuskokinsu,bawai muni na fuska kawai ba.....aaah muni na zuciya.
Ma'aikatan gidan jaridar ya fara nunawa.
"Wadannan na gama da case dinsu......aje a hadasu da diyar ambassador......ranar shiga kotu a hadosu tare qarqashin shari'a guda daya,lawyer na zaiji da komai".
"Wayyo Allah.....mun shiga uku,don Allah sir kayi mana afuwa ka yafe mana,wallahi bamusan a kanka tace a buga labarin nan ba". Wani banzan kallo yayi masa.
" Okay,idan wanine bani ba kenan zaku iya tozarta masa iyali,idan wani ne bani ba kenan zaku iya wulaqantashi ku wulaqanta aurensa da shaidar zur.....CP.....bana son sake jin muryarsa a nan wajen" Ya fada yana takawa ya jawo wata kujera.
Kiiiii ya ajiyeta gaban bibo wadda jikinta ketsa tsuma,ya koma ya zauna sosai yana dora qafarsa daya kan daya.
"Nutsu sosai.....labari zan baki sannan na sallameki".
"To....to Allah yayi albarka".
" Ameenatu ahmad sabreen takai budurcinta gidan mijinta,wanda ni Muhammed fuad jadda na karbeshi da kaina....kuma mutanen dake rayuwa damu suka shaida hakan a lokacin". Dif wuta ta daukewa bibo duk yadda takeji da tsageranci sai taji maganar ta girmeta.
"Ke din uwace ko?,a kamatance bai dace na gaya miki haka ba ko?,saidai kash.....nidin bana yafiya bana kuma ragayya ga duk wanda yace zai taba rayuwar duniyata.....sabreen,a inda kuma aka samu akasi shine.....tuntuni kika sanya qafa kika take wannan girman daya kamata ki samu......to ina me!miki albishir.....sabreen takai bantenta......ba wani matsiyaci ko lusarin daya samu damar tsallake wannan shingen......yadda kika dinga yada jita jitan mutuniyar banza ce......na baki dama na biyu kisan yadda zaki wanke wannan sunan daga kanta....ki maida gurbinsa da kyakkyawar shaida,idan hakan bata kasance ba kuwa,a karo na biyu idan na daukoki batar dake zanyi bat.....a bude mata ta tafi gida". Bata tsaya tunani ko waiwayen tazarar nisar tafiyar da zatayi a qasa,ba tare da abun hawa ko kudin mota ba ta fice,tunda har ta samu nasarar shaqar iskar 'yanci kuwa......bataga abinda zai hanata hada lecture din wayar da kan al'ummarta kan muhimmancin mutuncin da sabreen ke dashi ba.
Idanunsa ya ware akan mutum uku.....mutum ukun da yakejin laifinsu yafi na kowa girma,ya sake aza idanunsa akan zuwaira wadda daga ita har bibo sunyi wani zuzzurmawa. Duk da ajiya ce kawai akayi musu irin ajiyar da take daidai da aljannar kare.
"Kamata yayi kema a hadaki da wadancan.....sashen manyan laifuka ko?..." Kuka ta fashe dashi tana hurwa tana neman agajinsa.
"Ki rufen baki,don duk yadda raina yakai ga baci bazan iya zabgawa fuskar dakeda furfura mari ba,koda furfurar ta banza ce" Gum ta koma tayi sannna ya bude idonsa yana sake dubanta.
"Kina gidana kina qarqashin inuwata amma kina neman hanyar da zaa shigo a keta haddin iyalina?!.....abu guda ya rage miki ki gayamin......waye ya sanyaki boyesu a dakinki kika fiddosu da dare zuwa sassan matata!!!". Wata bahaguwar tsawa daya sauke mata sai data tattara gudawa me yawa a cikin mashkur,ya rasa wanne.ibtila'i da bala'i ne yake hanashi furta masa sunan.matar kowa ma ya huta?,fatansa daya wannan tsohuwar ta kira sunanta,wataqila ko kwatance da ka yayi akan shima ita ta dauki.nauyinsa duk da akwai nasa shirin.
"Mmm.......maamah ce" Sunan ya saukar masa cikin ba zata. Fuska ya yamutsa yana dubanta.
"Wacce kenan?"
"Hajiya maamah.....mariya mahaifiyarka" Komai ya tsaya masa na wasu daqiqu,sai daya koma daidai kuma kwanyarsa ta cika da wasi wasi.
"Cp.....janye matar nan,a hadata da wadancan mutanen". Kallo daya ya yiwa mummunar fuskar mashkur,wadda ta jima da tashi daga kyakkyawa zuwa asalin mummuna.
"Mariya ce nima!.....maamah ake ce mata" Ya fada da sarqaqqiyar muryarsa da bata fita yanzu tartar saboda fitar haqora sha biyar daga bakinsa.
Kaman ya dauki takobi ya jefeshi dashi haka yaji,duk wani jini dake jikinsa yaji yana neman daskarewa,kwanyarsa kuma tana shirin yi masa formatting da karan kanta irin na kota kwana,saidai kiran wayarsa yaso maida komai muhallinsa,ya daga kiran bawai don yana gane waye ke kiran nasa ba yana komawa kaman wani shashasha.
"Jordan ne sir.......sir an jona musu na'urar fidda bayanai cikin sauqi,sun kuma yi bayanin komai...."
"Me aka samu?" Ya tambaya cikin sarewa da jin komai.
"Am sir.....kayi haquri.....gaskiya bayanansu na qarshe kaman na'urar ta samu matsala.....sunce zaa sake bincikawa"
"Jordan please tell me.....ka gayamin ko waye ya sanyasu.....bana buqatar jinkiri a daidai wannan lokacin".
"Sir....sir" Sai ya kama inda inda.
"Tell me nace!" Ya fada a tsawace.
"Mariya......mariya ce maamah". Iya abinda fuad yaji kenan wayar ta sulale daga hannunsa ta fadi qasa.
Bai sani ba......jijiyoyin hannunsa ne suka daina aiki yadda ya kamata ko kuma qwaqwalwarsa ce?!.
Tashin hankali!
Allah ka rabamu dashi!
Me karatu sai ince muje
mu qarasa
Hugumanku ce
Na gode
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 149
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
149
Kowacce gaba ta jikinsa sai yaji tayi wani irin sanyi,sai ya dinga jin kaman bashi da wani sauran damar ya motsa ko ya sakeyin kuzari a daidai wannan lokacin.
"Mariya ce.....maaamah ce......itace" Sautukan suka dinga haduwa suna masa amsa kuwa a tsakiyar kansa.
"Are you okay sir?" Muryar cp tayi kutse cikin tunaninsa,wanda yaga lokaci daya fu'ad din yanayinsa ya sauya,wuta kuma ta dauke masa. Da qyar ya iya daga idanunsa ya kalli cp saboda wani dan banzan ciwon kai daya saukar masa lokaci guda.
"Yes.....am okay,akwai wadanda sukayi kidnapping 'yar alhaji hamza kibiya......za'a canzasu daga can inda suke a kawosu nan a hadesu......duk yadda ta kama ayi musu hukunci".
" Ma sha Allah....sunzo.hannu kenan?" Kai ya jinjina masa kawai. Bayason doguwar magana sam sam,don shi kadai yasan yadda kansa yake masa wani irin bala'e'en ciwo,yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa da wani irin mahaukacin fushi da yake tsoron kada ya illatashi shi a karan kansa. Da zafi zafi ya fita a gurin,ya samu abdulgaffar suna tsaye suna dakon fitowarsa. Hannu kawai ya miqa masa
"Bani key" Ya fada ba tare daya dubu abdulgaffar ba. Baki ya saki yana kallon boss din nashi,baisan meye haka da zafi ya tunzurashi ba ko kuma ya sauyashi.
"Sir.....muje na kaika duk inda zaka je.....like kaman baka cikin mode din da za'a barka kayi driving".
"Just give me the keys abdulgaffar.......ko mutuwa zanyi a hanya kana da asara?........wanda ya kawoni duniya ma bashi da asara ballantana kai!" Ya fada da wata irin tsawa data bashi matuqar mamaki. Salin alin ya miqa masa key din,saidai kuma ya yiwa sauran team nashi alama da ido,don haka fu'ad din yana tada motar yana fita suka bishi a baya cikin salon da bazai gane shi suke ba. Suna matuqar qaunarsa da kula da dukka abinda zai cutar dashi,suna matuqar jinsa a jiki irin kusa kusannan,suna jinsa tamkar wani babban yayansu da yake da ruwa da tsaki a rayuwarsu,inda suna da hali tabbas ba zasu bari ba ko quda me cutarwa ya sauka a kansa ba.
Wani mahaukacin gudu yake zubawa wanda ya sake tabbatar musu da ba lafiya ba,hankalin abdulgaffar akan motar yana duban wanda ya bawa yayi driving.
"Ka kula sosai,kada ka matsi bayansa da yawa kada kuma ka bari ya kufce mana" Ya fada yana gyara zaman Bluetooth din kunnensa yana magana da na motar baya.
Shi kansa yasan gudun da yakeyi ya wuce qa'ida.......amma a irin zafi da bugun da tasa zuciyar takeyi sai yakejin ba wani gudu yake ba shi din. Idanunsa fes bisa kwalta amma tunaninsa yayi nesa sa gangar jikinsa. Baisan kuka yakeyi ba saida yaji iska na fifita hawayen daya silmiyo masa,karon farko tun bayan tafiyarta ta barsu.....karon farko tun bayan wasu shekaru masu yawan gaske da ya share wani abu bai sakashi kuka ba......a yau a zagaye na biyu ta sake zama silar kukanshi. Hannunsa daya ya saki dava steering din,ya shafo hawayen yana kallon su,a wannan lokaci yana jin ta gama sanyashi kuka......yayi kuka qarshe a rayuwarsa saboda ita. Tsananin kunyar anni da abba yakeji,da wanne idanu zai kallesu ya shaida musu mahaifiyarsa ce ta aikata ma diyar cikinsu autarsu haka?,da wanne bakin zai musu bayani?,wanne shine kalar sakayyar da suka cancanci su samu makwafin alkhairin da sukayi mata?.
Wani birkitaccen parking yayi qofar gidan,parking din da ya tada qura,ya kuma ja hankalin malam sa'adu dake zaune daga cikin gidan a bakin qofa yana jan tasbaha.
Da sassarfa yake takun nasa,kaman me gaggawar cimma wani abun. Security na farko ne ya hangoshi,ya kuma taso ya bude masa da sauri kafin yakai ga qarasowa.
Kusan ba sosai yake gani ba,fatansa kawai ya cimmata......fatansa kawai ya isa gareta......ya kuma tambayeta dukka akan me?,me yasa?.
Da sauri me aikinta dake saukowa daga samanta taja baya tana zubewa sanda taga shigowarsa.
"Barka da warhaka yallabai?" Sam ba gaisuwarta bace damuwarsa,bai kuma damu ya amsa ba
"Tana ina?" Ya tambayeta kai tsaye yana jin jikinsa ko ina yana rawa.
"Tana sama" Ta amsa masa tana rabewa ganin yadda ya nufo saman da sauri bata ko dire statement dinta ba.
Matakala bibbiyu ya dinga hadawa har Allah ya kaishi saman. Dab da matakalar qarshe sautin muryarta ya sauka a kunnensa.
"Ta yaya akayi saken da har wani yasan inda suka boyeta.....wanne irin hauka ne wannan?,baisan muhimmancin yarinyar nan a hannuna ba?,subucewarta da kuma kamasun da akayi yasan irin asarar da zai jawomin?.....bani da haufi akan zasu iya fadar sunana......duk da boka baiyi aiki a kansu ba amma kudin dana musu alqawari da alqawarin dana musu akan koda tsautsayi ta gifta zan fiddasu....iya wannan bazai bari su fadi sunana ba" Ta furta cikin bawa kanta tabbaci da yaqini da gaibu da qaryar daka iya fidda bawa daga ainihin imaninsa.
Wani abune ya fusgeshi sosai,da sassarfar data jawo hankalinta daga wayar da takeyi. Wani irin duba take masa me cike da tsoro da kokwanton ya jita ko bai jita ba?,zuciyarta gaba daya ta kasa bata nutsuwar bai jita din ba saboda wani irin kallo dake fita daga idanuwan da suka sauya launi suka jirkice,daga fararen qwayar idanuwa zuwa kalar makuba kaman an diga jini.
"Why maamah.....why amna?!" Ya furta da wani irin sauti me cike da razani mamaki dake cakude da karyewa yana wara hannuwansa da kuma watsasu kaman wanda yake dakon kama wani abu.
Wani irin shock taji,wanda ya kusa sanya numfashinta dakatawa na wucin gadi.
"Me yasa maamah?.....me yasa?,idan ni kinyimin.......d'anki ne.....idan kin yiwa musaddiq.......d'anki ne......amma amnah fa?!" Ya fada da wata irin murya dake neman fara rawa saboda tsananin sarewa da dukkan komai,ya kuma qarasa maganar yana nuna waje da yatsarsa.
"Me amna ta aikata maamah.....meye laifinta?" Ya kuma fada da yanayin mutumin da ya soma zarewa.
"Idan kika bada kai bori zai hau.....idan kuma baka iya kama barawo ba saishi ya kamaka" Wani sashe na rubabbiyar zuciyarta ya sake bijiro mata da wannan shawarar,shawarar data qarfafi dukkan gabbanta,ta soma qoqarin tattaro kowacce nutsuwa tata,sannan kuma ta hana kanta shiga d'imuwa.
"Kai fu'ad.....kalleni nan da kyau,idan kana cin qasa ka kiyayi ta shuru....ni dinnan nice uwarka,baka da sama dani.....ohhhh,wato kaje an karanto maka abinda zakacemin da kalar rashin kunyar da zaka yimin.....dukka ameenatu ta yo maka katunsa shine zakazo ka saukemin?!"
"Ameenatu ameenatu dai?,ameenatun da batayi miki komai ba face alkhairi?,ameenatun da ta rungumi yaran da kikaji cewa baki buqatarsu?,ameenatun data yarda ta zauna ta kashe tata rayuwar saboda ta 'ya'yan da kika watsarwa duniya?,akwai wani alkhairi sama da wannan?,akwaishi......wata can daban tayi abinda uwa ta gaza yi?,wata can daban tayi abinda uwa take ganin ya zame mata babban aiki?" Ya qarasa fada yana zuba mata ido,qirjinsa yana sama da qasa yana jin kamar ciwon zuciya ne yake shirin kamashi.
"Kin dawo kin sake kashemu a karo na biyu bayan wancan kisan da kika yiwa rayuwarmu.......me mukayi miki haka?,laifinmu ne da kika haifemu alhalin baki buqatarmu?" Ya fada a tausashe da wani irin rauni daya sanya idanunsa fitar hawaye
"Daga kowanne bangare......cikin binciken kowanne laifi Maamah dai mahaifiyar fu'ad?,mahaifiyarsa?.....maamah dai?,wadda tayi silar zuwansa duniya?,maamahn ita ta dauke amna?,amna diya ga hamza kibiya?,mutumin daya zame musu uba......bango madafarsu?,ya tallafesu a sanda duniya tayi watsi dasu,ya rungumesu,a sanda ita da take Mazaunin uwar data kawosu duniya ta sanya qafa tayi wancakali dasu?.....ya rungumi farincikinsu da baqincikinsu?,ya rabu da duk wanda zaice baya sonsu?,ya qara zafin nemansa saboda su.......yayi musu riga yayi musu wando?,yayi kawar da dauda da duhun jahilci daga qwaqwalensu?,ya daga darajarsu a idanun duniya ta hanyar haskasu da hasken ilimi?,ya maidasu mutane