Author : Huguma Category : Complete Novels
Batasan me yake tsarga mata ba duk sanda ya kirata ta DUNIYATA ba,wani irin feeling takeji yana motsa zuciyarta,wanda tun tana qaryatawa har ta soma yarda tana jin wani abu a ran nata duk sanda ya ambaci sunan. Yafi mata dadi ya kirata DUNIYATA akan ya kirata my world.
Susutacciya ya maidata yadda ta fahimci ya soma maidata a wadannan kwanakin,lallai so yake sai ya matso komai a kansa dake cikin zuciyarta. Ta sani tabbas muddin zaici gaba da wannan salon......muddin zaici gaba da tafiyar da ita da wannan tsumammen yanayin to ba shakka zata gaza boye duk wani abu dake zuciyartata kuwa.......yana kuma dab da maidata mahaukaciya da gasken gaske,zata rasa duk wannan dauriyar tata da basarwa da takeyi.
D'aya bayan daya ya dinga zare hair pins din da dama shi ya zauna ya jera mata su,duk daya idan ya zare yana ware gashinta me tsaho baqi da santsi,wanda zuwa yanzun hair mist dinsu shi da ita ya zama guda daya,kaman yadda mayataccen mouth fresh dinsu ya zama products daya. Kusan komai nata cikin kwanakinnan ya canza mata zuwa kalar wanda yakeso,qamshinta,creams lip gloss da komai ma......komai kuma me tsada ne fiye da tunaninta,ranar data duba kudin perfume din daya sauya mata zaune kawai tayi tana binsa da kallo ba tare da yasan ma me ake ba. Su huda na wata duniyar duk da tayi imanin suna cikin kulawa......amma ita tana nan tana rayuwar da take ganin tafi qarfin matsayinta?.
Sai daya zare mata duk pins din,sannan ya kutsa yatsunsa cikin sumarta yana barbazata yadda yakeso,ta fahimci tana daya daga cikin abubuwan da suke matuqar burgeshi ga diya mace. Kaman yasan abinda yake saqawa muryarsa me kama data mashaya ta sauka a kunnenta
"I love it duniyata......kina da komai da nakeso..... Please ki sake bani dama na gina miki wasu dabi'u.......na dade ina kame kaina daga kallon Haram da kuma zina.......i only want my pure halal.......please ki qarasa mallakamin kanki da rayuwarki gaba daya I want the best from you,i want the best relationship with you" Ya qarashe maganar yana mata wata kyakkyawar runguma kafin ya fara maidata birkitacciya yana cireta daga ainihin tunani nutsuwa da saitinta. Batasan wanne abu daban yake buqata daga gareta ba.....batasan wanne best yake nema ba bayan duka fitar da ita daga tsarinta da yakeyi. Yana sakata jin wani irin nauyi da kunya da bata taba tsintar kanta a ciki ba.
Ko yanxun da qura ta lafa tana gaban madubi yana tsaye a bayanta yana bata dan kunnenta tana maidawa daya bayan daya,ya kafeta da idanu murmushi na fita daga kan fuskarsa qasa qasa. Idan yana kallon fuskarta a irin wannan yanayin sai komai ya dinga dawo masa. Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa kaman zai fashe don tsananin cika da qaunarta da sukayi,yadda yakeji a duk sanda suka kasance da juna.....yasha imagination abun idan tana participating itama,yana kwadayin yaga wannan lokacin.
Taku uku ya qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya dora fuskarsa saman kafadarta yana dubansu a tare shi da ita ta fuskar madubin.
"Idan Allah ya bamu 'ya'ya......wanne irin kyau xasuyi my world?". Wani kunya ya saukar mata,tayi qasa da kanta qaramin murmushi yana subuce mata. Shima murmushin ya saki,a duk sanda kunya haka ta bayyana saman fuskarta tana mata wani irin kebantaccen kyau na musamman.
"DUNIYATA.......Why aren't you responding?" Idanu ta daga alamun tambaya ba tare data yarda ta kalli tsakiyar idonsa ba. Ya fahimci haka,sai yasa yatsunsa yayi gefe da gashinta yana cusa bakinsa ta kunnenta abinda ya sanya tsigar jikinta tashi.
"On bed dear......" Ta fahimci inda ya dosa,don haka bata bari ya qarasa bama ta soma neman inda zata boye fuskarta. Ire iren rashin kunyarsa suna sakata jin wani irin nauyi ba kadan ba.
"Ko sai randa aka yanke shawarar ana sona ko ba'a sona?" Ya sassauta muryarsa yana fadi qasa qasa gami da riqe hannayenta da kyau qaramin murmushi yana subuce masa.
"I hope wannan ranan zata zo soon.......na matsu,ko akwai wani abu da ake buqatar nayi da za'a gayan I LOVE YOU MUHAMMAD FU'AD JADDA?....." Ya tambayeta da gasken gaske,har qasan zuciyarsa yana sha'awan jin ta fadi hakan. Kai ta girgiza tana basarwa,neman tserewa takeyi ya kuma fuskanceta,don haka ya sunkuceta kawai yana nufan stairs din da sukayi dakin qasa.
Idanu ta fitar waje,har ha Allah tsoron dakin qasan nan takeyi,yatsa ya saka ya lakuce mata hanci yana girgiza kai.
"Relax.....you're safe my world.....bazan taba yin wasa da DUNIYATA ba fa". Kasa ce masa komai tayi sai idanu data lumshe tana shaqar daddadan qamshinsa daya cika mata hanci,ta kwantar da kanta a qirjinsa tana jin bugun zuciyarsa. Batasan me yasa ko yaushe bugun zuciyarsa daban yake ba,wani bugu ne me sauri sauri wanda tasan qa'idan bugun baikai haka sauri ba. Idanunta saman dakin duke kallo,yadda ruwa yake gudu saman kansu tare da kifaye kala kala ba tare da ko damshin ruwa ko qwaya daya ya tabasu ba,ta dauke idanu tana tasbihi ga ubangijinta.
Saman lafiyayyen gadon dakin ya ajiyeta,ya dawo gabanta ya tsugunna yana zagaye hannuwansa da qugunta.
"Muhammad fuad jadda.......d'an alhj Muhammad ne,haifaffen bafulatanin mambila......,ta gefan mahaifiya kuma...." Sai ya danyi shuru yana hadiyar numfashi.
"Mariya da akafi sani da maamah itace mahaifiyata.....bafulatanar mayo belwa ganye local government" Hannuwanta ya riqe a tausashe cikin nasa zuciyarsa na karyewa.
"Lokaci na farko da zan bude bakina na fasawa wani dan adam daban rayuwata.....waye ni?....me naji me na fuskanta?.....sabrrrrrr.....abbana......abbana yana cikin jerin sahun mutumin da nafiso nafi qauna kaf cikin rayuwata.......saidai mun rasashi a sanda mukafi qaunarsa......mun rasashi a sanda mukafi buqatarsa......mun rasashi saboda wa'adinsa ya cika.....amma da taimakon maamah". Kai ta daga tana dubansa,tana ji yana tayar mata da wani mikin ciwo dake zuciyarta.
Kai ya gyada mata idanunsa suna sauya launi.
"Ta shayar dashi guba......ta dura masa miyagun maganganu da suka qarasa illata gangar jikinsa da zuciyarsa,suka Haifa masa da ciwon zuciya......kalmomin bakin maamah su suka jefa abba na a matsanancin ciwo......ciwon da haquri ya gadar dashi dashi,ya kuma ci gaba da tara masa guba na maganganun da suka zama silar fashewar zuciyarsa daga qarshe. Tun a gaban idanunsa muje ganin qasqanci da wulaqanci,ba wanda yake samun tausasawa ko kulawa daga gareta,daga shi mijinta harmu 'ya'yanta......bazan boye miki komai ba......bamusan dadin uwa ba,bamusan wani abu da ake kira dadi tsakanin mahaifiya da 'ya'yanta ba,mun rayu tamkar irin rayuwar da bawa zaiyi a hannun ubangidansa,walwala 'yanci da farinciki dukka yayi mana qaura,mun rayu tamkar agololi kuma 'ya'yan riqo......abbanmu kuma ya zama tamkar wani yaro gida bame gida ba......ba abinda tafi bawa mutunci da kima sama da KUDI sama da tayi KUDI sama da abbanmu dole ya zama me KUDI ya nemo KUDIn da zatayi kalar rayuwar da takeso,yayi lafiya ko kada yayi......ya rayu ko kada ya rayu,muyi lafiya tarbiyya ilimi mu tsaftatu mu qoshi duk basa cikin lissafinta,abinda ya dameta shine KUDI.....sabrrrrr..... Mun rayu cikin qasqantacciyar rayuwar da al'umma suka gaza janmu a jiki a garin da bamu da kowa,kowa yana ganin tunda wadda tayi silar zuwanmu duniya ta gaza tallafawa da tausayawa rayuwarmu,lallai mudin akwai wani abun aibu ne a tattare damu. Taji a rant ba zata iya rayuwa damu ba,ba zata iya zama damu bs,ta watsar damu da abba dake buqatarta saboda matsanancin ciwon zuciya dake sake kwantar dashi....duk inda abba bai qwallafa rai a soyayyarta ba,tayi nesa dashi shi yafi alkhairi,kunnuwansa xasu daina kwana su wayi gari da jin munanan kalmominta a kansa wanda hakan shizai bashi lafiya da wuri.....saidai kuma sonta ya zame masa jarrabin rayuwa,ya kasa haqura da nesanta kanta damu da tayi,ya sake zame masa silar hauhawar ciwonsa. Nayi kwasar kashi......nayi aikin bola da hannuwana duk don na kula da musaddiq da abbana......nayi sharar kasuwa nayi ta kwata har bansan iyakarsu ba kawai don na samo abinda xan kula da abbana da musaddiq.......munci abincin bola saboda gudun yunwa kada ta halakamu.......na kwana da GAWAr abbana.......na kwana da gawar mahaifiyar abbana JADDA saman cinyata dukkansu ba tare da nasan mutuwa sukayi ba ko bacci?,naci gaba da gadin gawarsu ba tare da nasan ya akewa gawa ba?,a shekarun da duka duka baifi a koreka daga bakin gawa ba idan kana da gata don kada kaga abinda shekarunka basukai ba. Jadda tazo mana da wani irin gata da muka dinga tunanin wahalarmj ta yanke......ta saida duk komai nata don tazo ta kula damu......ta bamu wani jin dadi wanda ko maamah da tayi silar zuwanmu duniyata tsahon shekarun da mukayi tare da ita bata taba bamu irinsa ba. Saidai sanda muke tsaka d wannan tunanin ashe ragowar kwanakinta na rayuwa yazo qararwa tare damu ajalinta yazo mata a kusa.....ta sake kwanciya ta barmu a wani irin yanayi. Daga sannan muka sake gane meye ma'anar rayuwa?,muna ta tunanin maamah zataji labarin komai......zataji tausayinmu ta dawo garemu amma inaaa......wanda yayi nisa bayajin kira........wata kalma da maqocinmu ya fada a kanta sanda ya dawo daga kudu yace mana ya ganta a can.......taqi barin raina da zuciyata.......har yanzu da ita nake kallonta.......bansan ranar da zata bar zuciyata ba.........maamah dinnan dai da daga qarshe naji duk duniya ba wani abu da nake qyamatar ya kusanci inda muke......itace silar mutuwar abba......ke daya kikasan wannan a duniya......na kamata har sau uku tana ciyar dashi da abubuwan da likita ya hanashi ci saboda suna tunzira ciwonsa.......suna kuma iya sanyawa komai ya faru dashi ciki harda rasa rayuwanshi......a dukk ukun nan dana kamata tayi alqawarin ba zata qara ba.....mantawa takeyi ne......na fahimci abinda ya sanyata take aikata haka ta hirarta da qawarta da har yanxun nake tunanin kamar matar nan harira da suke tare ne......so take ta kashe auren,so take abbanmu ya saketa shi kuma yaqi......tace tana buqatar tayi arziqo,tana buqatar freedom amma yaqi sallamarta....wannan shine dalilinta......shine kuma silar tunzurar ciwonsa har ya kaishi ga kushewarsa......ba ita ta kasheshi ba kenan sabrrrrr?" Yayi mata tambayar da wani irin yanayi daya tsorata sabreen qwarai da gaske.......yanayin da yake tabbatar mata wani abu ne guda daya da yake masa ciwo har yau har gobe a zuciyarsa......salon tambayar data tabbatar ya jima yana so ya yiwa wani dan adam ita......amma rashin jin kowa a matsayin na kusa da zuciyarsa sosai ya sanya ya gaza furtawa kowa,yadda yayi tambayar kaman hankalinsa na neman gushewa daga jikinsa sai ta kama kafadarsa da kyau tana riqewa kuka yana shirin qwace mata......tana jin ashe suna da yawa irinsu wadanda suka rayu cikin wulaqantacciyar rayuwa?......amma dashi dake da sauran uwa a raye........dasu da ba ko daya ga dangi masu tsananin jifa da zumunci waye yafi rashin sa'a.
"Sabrrrr" Ya rigata sakeyin magana duk da tana buqatar magana dashi.
"Idan kika gwada yimin abinda maamah ta yiwa abbana......nima mutuwa zanyi kaman abba.......saboda na fahimci zuciyata irin tashi ce......bamu iya soyayyar qarya ba,bamu iya soyayya da wasa ba,bamu iya yiwa masoyi qaramin riqo ba.......a halittarmu yake.......wannan ya sanya na tsani soyayya na kuma tsani kowacce 'ya Mace......anni ce mace qwaya daya data fara samun qauna irin ta uwa daga gareni bayan faruwar komai......amma hatta da amna bata samu komai daga gareni ba sai sanda naga tana shirin mutuwa ta barmu........bazan jure ba sabrrrrr idan kikace zaki gujeni......bazan iya dauka ba idan kika ce zaki barni sabrrrrr,da gaske nake nima mutuwa zanyi" Ya qarasa fada muryarsa da dukkanin jikinsa suna wani irin rawa,tabbacin ya tabo mikin da baida kamarsa a rayuwarsa.
Gaba daya sai ta rude,ta rasa yadda zatayi dashi,ga wani irin ciwo daya tayar mata wanda baida magani illa itama tabar hawayen idanunta su sauka ko xata rage abinda takeji tsakanin qirjinta zuwa zuciyarta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 106
106
"Kasan wace sabreen din da kake muradin ta tabbata a matsayin taka?". Ta fada muryarta na yayyankewa. Wani kyakkyawan riqo yayi mata yana sakata cikin jikinsa.
"Na sani......na sani,iya abinda kuma na sani a kanta ya isheni yanxu haka......abinda ya ragemin ME YASA WANNAN TSAYAYYAR SABREEN DIN sauri bada kai ta yarda da wannan muhammad jadda din?,shima bana fatan kiban labari,da kaina zan lalubo......duk wanda keda hannu wajen maida sunanki wancan mummunan sunan baxai shaba.....sai na hukuntashi" Ya fada jikinsa na daukar rawa gaba daya.
Luf sukayi a jikin junansu,kowa yana qoqarin controlling yanayinsa,sannu a hankali yanayinsu ya fara daidaita,saidai kuma a hankali taji jikinsa yana daukan wani irin dumi......kafin kace meye wannan zazzafan zazzabi ya rufeshi me tsananin zafin da har cikin fatarta da tsokarta takejin zafinsa.
Rudewa tayi sosai,ta fara qoqarin zamewa daga jikinsa tana fadin.
"Zafin yayi yawa......yayi yawa ka bari a samo magani".
"Banaso ki kira mana kowa a gida.......inason kwanakin nan biyu da suka rage nayisu dake.......banason kowa ya shigo tsakani" Ya fadi dumin numfashinsa yana saukar mata saman goshinta. Kai ta girgixa hankalinta yana tashi.
"Jikinka yayi zafi da yawa...akwai buqatar temperature din yayi qasa". Sake sanyata yayi a jikinsa ya lullubeta da kyau
"It's not......haka fever na yake......zai sauka" Ya fada yana lumshe idanunsa duk kuwa da cewa yau zazzabin na daban yake jinsa,don har kusan cikin qasusuwansa yakeji kaman ana karyasu,saidai kwanciyarta a jikinsa yafi masa komai a yanzu haka.
β
Shi kadai ya dinga dariya sanda saqon fu'ad ya tarar dashi. Hannu yasa yana shafa kwantaccen sajensa yana duban saqon yana sake karantawa. Wato ko yaya kusanci yakai tsakaninka da iyaye akwai sanda soyayya da matar aure ke diban nasu kason idan kusanci yakai kusanci. Bai taba tunanin akwai sanda fu'ad zai nemi kebewa shi daya ya barsu tsahon kwanaki ba tare da ya buqaci kowa yasan inda yake ba....ko ya rabi kowa ba. A nutse ya maida masa amsa sannan ya juya akalar motar yana komawa gida don bawa anni saqon d'anta. Fitarsa dama kenan daga gidan yana tsammanin zai iya samunsa a wani gurin,amma yanayin amsarsa kawai ya tabbatar masa ba zai ganshi ba koda ya shiga neman nasa.
Suna dab da kammala kalbar da amna kewa annin ya shiga parlor din,yadda ya barsu a daxun haka ya samesu,kowa zaune yana sabgar gabanshi.
"Anni.......sai kisa haquri,ba zaki samu ganin yaronki ba sai Thursday a airport,haka yacemin" Ya fada yana daga kafadunsa. Maganan farouq taja hankalin maamah duk da bata waiwaya sashensu ba bata kuma nuna taji abinda suke tattaunawa ba,ta riqe waya kawai a hannunta kaman tana daddannawa amma maganganunsu take saurara.
Qaramin murmushi anni ta saki,iya bada saqon da yayi a gaban maamah dinma ya wadatar mata,tabbas zai isar mata da wani muhimmin saqo,duk da ta san farouq din ya fadi ne kawai ba tare da wani nufi ko wata manufa ba,ya fada ne kanshi tsaye.
"Indai suna lafiya alhamdulillah,lafiyarsu tafimin komai" Sosai maganar ta soki maamah,ta tattaro wani yawu me tauri ta hadiye da qyar tana qoqarin daidaita numfashinta.
"Na rantse da Allah yadda kika dasa baqinciki cikin rayuwata.....saina dasa miki fiye dashi a taki rayuwar......indai har ban aikata haka ba lallai ba shakka ni mariya 'yar zina nake" Ta fada cikin zuciyarta wata wutar daukan fansa tana ruruwa cikin zuciyarta. A yanzun inda za'a bata bindiga.....aka ce ta kashe maqiyinta qwaya daya da tafi tsana a duniya.....to xata nemo harsasai guda biyu ne,ta kashe Alhaji hamza da ameenatu.....harsashinta na ukun kuwa muddin ya samu to sabreen ce ta gaba. Tayi imanin bariki ce zallah......zallar barikice ta sanyata janye mata yaro,wannan dukka plans din yarinyar ne,ita ta shirya ta tsara ta kuma gabatar,amma indai da numfashi a gangar jikinta saita gaya fahimtar da ita tazarar shekaru a rayuwa ba qarya bace,dukkan wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.
Har tana niyyar miqewa ta wuce dakinta,don ba abinda take gani a parlor din face abinda zai daga mata hankali yakuma sake tunzura mata zuciya,sai ga musaddiq ya shigo. Ta dauka itace mutum na farko da zai fara gani,tayi zaton itace ta farko da zai fara zarcewa wajenta,saidai gaba daya hankalinsa yana kansu anni.
"Lalala....waye ya saki kitso?" Musaddiq ya fada yana fito da idanunsa waje ba tare daya lura anni takewa kitson ba. Kwabe fuska kuwa tayi tana nuna anni da bata ganinta da comb din hannunta.
"Nice nan dan gidanku" Anni ta fada tana hade rai,saidai kuma qasan hade ran nata murmushi ne boyayye a kwance da zaka iya karantarsa.
"Ai banga ke bace" Ya fada yana shafa kansa yana saukar da ganinsa qasa gami da qoqarin boye damuwarsa.
"Maza ka qarasa sakaltata.....tunda shi wancan yayi gudun hijira......nidai wallahi karku sakani cikin masu yiwa mijin da zata aura bayanin sangartacciyar da zai aura ahto" Farouq ya fada yana miqewa gami da jifan musaddiq da harara.
"Basai kun wahalar da kanku ba BB.......mijin yafi kowa fahimtar wacece ita.... Lafiya qalau ba wanda zaiji bari ya gani" Musaddiq ya fada kansa tsaye yana aje dubansa kan fuskar amna. Maganan yadan tabata,sai ya hade mata da jin nauyi,bakinta yayi murus tayi qasa da idanunta tana tsaga kalban anni din. Ganin haka sai shima ya juya xai fita,sai a sannan subutar bakin da yayi ya dawo masa.
"Kan uban buhun babbakun bala'i" Maamah ta fada tana jin numfashinta kamar zai tsinke daga hunhunta yayi qaura yabar gangar jikinta. Ba ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen ya dauki haske,saidai nasu kyawawan zukatan cika sukayi da farinciki duk da basu nuna hakan kai tsaye ba.
"Kai musaddiqu!" Maamah ta fusgi sunansa da wani irin sauti sanda yake bin bayan farouq