A Duniyata Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   108 / 119

321K to 324K   out of 356.9K words

jurewa ba,idan kuma har na gaza jurewar komai ma zai iya faruwa" Ya qarasa maganar yana aje mata wannan zazzafan kallon nasa da taji ya tsarga mata itama tun daga tsakiyar kanta har tafin qafafuwanta. Daidai sanda kira ya shigo wayarta,ya matsa a hankali ya dauko mata wayar.

"Bibo da yarinyarta sunzo,saidai na hanata ganinki,don har yanzun ban gama nutsuwa da ita ba,bazan kuma bari kowanne abu da ban gama nutsuwa dashi ba ya iso gareku" Ya furta yana saka mata wayar a hannunta.

"Na tabbatar maka bibo tayi nadama zuwa yanzu,don ba komai yake damunta ba tuncan baya sai kishi da hassada"

"Zan duba na gani" Ya amsa mata yana takawa a hankali zai fita a dakin,ta maida kallonta kan wayar.

Kawu rufa'i ne,ta dan saki murmushi tana daga kiran.

"Sannu d'iyar arziqi......sannu d'iyar albarka......wadda aka haifa tsiya tana bacci". Dariya sosai kawun ya bata.

"Ina wuni kawu barka da dare"

"Barkanki kadai,an samu kai qalau?"

"Alhamdulillah kawu"

"Ubangiji ya rayasu yayi musu albarka......ai nace kinyimin daidai da kika bugo yara uku tun a karon farko......wa yaqi arziqi?,waye zaiyi sanya a gidan arziqi?,ina me miki wasiyya,duk sanda kika tashi haihuwa dinga ajiye masa hudu hudu uku bibbiyu,idan da hali karkiyi d'an d'aya ma sam". Dariya ce taso kubce mata,amna ta danneta,saidai hakan ya nuna a muryarta.

"To ai kawu abun na Allah ne,shi yake bada iya adadin da yakeso".

" Eh amma ai yace ku roqeni zan amsa muku ko?,qarshen watannan zamu shiga qasa me tsarki,farouqu xai fara cika alqawarinsa.......zam zage nayita roqo miki.haihuwar haka haka din" Wannan karon saida tayi dariya sosai.

"Kawu Allah ya bamu masu albarka wadanda zamu iya dasu".

"Ke!,kana da wadata da arziqi irin na mijinki harka dinga tunanin kalar yaran da zaka iya dasu?,yo ko yawan taron arfa kika haifa masa ai yana da abinda zaiji dasu". Kai ta girgiza tana murmushi.

"Kawu......tarbiyya ba'a nan take ba,kace ameen kawai"

"To ameen sarkin tsari......nace ba?" Ya fada yana komawa serious.

"Ina jinka kawu"

"Ina iya tahowa zaman dab'aro?". Idanu sosai sabreen ta bude dariya tana son qwace mata.

"Kawu kaifa kawuna ne,kuma namiji ne kai,ai mata suke zaman dab'aro,inama laifin ace inna A'i?(matarsa)".

"Ke komai yanzu a zamanance akeyinsa,ta yaya zan turo A'i gani?,bayan ba abinda bazan iyayi miki ba?,ni damuwata na kula da d'iyar ahmadu,na rama halascin da ya yiwa rayuwata" Ta fuskanci da gaske kawu yake,saita gyara muryarta.

"Kawu kada ka damu,mun dauko masu kula da yaran musamman,sannan kuma ga masu aikin gidan na ainihi".

"Duk da haka ba za'a barki haka ba,xan aiko A'in ta zauna miki kona kwana arba'inne na al'ada"

"To kawu Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci" Ta fada tana jin dadi qasam ranta. Ko ba komai zata ce ga wani daga dangin mahaifinta,duk da zuwa yanzu 'yan uwa ne kowa keta kutsowa da b'arkowa don nuna kulawarsa da bajintarsa akan haihuwar,tun suna madeena ma kafin sukai ga dawowa.

Wayar ta sauke tana murmushi sanda take tuno baya,drama dinsu da kawu wadda kusan kullum sai an yita,rayuwa kenan.....komai yayi farko said qarshe,kuma dukkan tsanani yana tare da sauqi tabbas.

Farouq yayi bacci,saita ajiyeshi kusa da dan uwansa hamza,ta miqe ta soma shiryawa,tana yi tana duban fuskokinsu. Ita kadai murmushi yana subuce mata,tana jin qaunar yaran har a cikin jininta. Duk sanda ta kallesu su ukun a jere reras saita samu kanta cikin mamakin yanzu wadannan din daga jikinta suka fito?,yanxu wadannan din 'ya'yanta ne?,mallakinta ne?,yanzu wadannan din jininta ne?,jinin muhammad fu'ad ne?.

Sanda ya shigo tsaiwa kawai yayi yana qare mata kallo,tayi wannan sassanyan kyau cikin shigar atamfar data yafawa mayafi onion color. Sautin sauke ajiyar zuciyarsa shi ya dawo da hankalinta,tadan juya ido a shagwabe

"Ka tsoratani hamma.....ka iya sanda ka tsaya kayita qaren kallo.....so kake kyauna ya qare?". Bai amsa mata ba har sai daya iso inda take,ya rungumeta ta baya sassanyan turarukansu suna gauraya waje daya.

"Bakisan kina sake qara shekaru kina sake qara kyau a waje na ba?,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan halittar ya kuma mallakamin ita a matsayin halaliyata......kuma uwar 'ya'yana" Luf tayi itama a jikinsa,tana jin yadda soyayyarsa take hudata tako ina.

Mota uku kawai tayi musu rakiya zuwa gidan maamah din,wadda tun a bakin gate masu da guards na gidan suka taso,kowa barka yakeyi masa da nuna farincikinsa.

Shi ya dauki farouq da hamza,ita kuma abba ne a hannunta wato almustapha. Yana gaba yayi sallama tana biye dashi. Mutum daya suka samu a parlor din wato saratu,ta miqe tana musu sannu da zuwa,ta kuma karbi yaro guda daga hannun fu'ad din tana musu barka da addu'o'i sosai.

"Yanzu muka kai hajiya ciki,munga kaman ta gaji da zaman bacci takeso tayi"

"Har yanzu ba batun magana?". Kai saratu ta girgiza cikin jimami.

"Ba abinda ya canza har yanzu" Shuru kadan yayi yana juya al'amarin,a irin kulawar da take samu physically and mentally yaci ace an samu ci gaba sosai,amma yana mamakin yadda komai yaqi canzawa koda qanqani kuwa.

Daga saman gadon da take zaune jingine da fuskar gadon ta daga idanunta sanda suke sallama cikin dakin. Idanunta ta zube fes a kansu kowanne dauke da yaro guda. Saratu ce ta fara isa gefanta ta aje hamza tana juyawa ta fice a dakin.

Da wani irin kallo taci gaba da binsu ba tare data dora idanunta akan yaran ba da takejin ba zata iya kalla ba,zuciyarta ta fara zafi tana jin gumi yana fara keto mata.

Kaman hadin baki suka isa gabanta a tare,fu'ad ya ajiye mata farouq a gabanta,ya karbi almustapha ya ajiyeshi shima kusa da farouq,ya dawo da hamza kusa da yan uwansa still idanunta akan fu'ad din yake. Yatsarsa ya sanya ya nuna hamza.

"Ga hamza......wanda ya zamemin tsanin zama muhammad jadda din da ake kirana dashi a yanzu,hamzan daya bani dakin kwana......ya bani sabuwar rayuwa,ya bani sabon ahalin da zan rayu dasu,na kuma kallesu a mazaunin nawa,ya kashemin kudinsa,yayi amfani da lafiyarsa don sama mana abinda zamu rayu dashi cikin aminci.......ga farouq,wanda ta sanadinsa nakai ga hamzan daya zama qashin bayan ilimina da tarbiyyata gaba daya........ga kuma abbana..." Ya nuna almustapha yana tsagaitawa wanda da alama wani abun ya hadiye.

"Abbana.....sanadi na......abbana da bani da wani abban daya haifeni wanda zai sake maimaituwa irinsa sak" Yana kaiwa nan ya miqe,ya damqi hannun Sabreen

"Gasunan maamah.......gasunan ki kallesu,kiga waye bakiso a ciki?,waye yayi miki wani laifi na rashin kyautawa?.....ki.kallesu jikokinki ne......yaran da suka fito daga tsatson fu'ad.....dan da kika dauki cikinsa wata tara,d'an da kikayi naqudarsa tsakanin mutuwa da rayuwa" Yana kaiwa nan ya fara jan sabreen din suna fita a dakin.

Bugawa kawai zuciyar sabreen takeyi,don tace akai mata yaran ba hakan yana nufin su fita a dakin subar mata su ba,zuciyarta ta kasa nutsuwa ko amincewa da hakan

"Hamma......"

"Shshshsh" Kawai yace da ita da qarfi.

"Hamma yara na....." Ta sake fadi a gigice wanda sautin da reaction din yakai kunnen maamah dake zaune a dakin.

Suna fita a dakin ya kama kafadunta dukka biyun ya riqeta da qarfin gaske.

"Relax sabreen.....ba abinda zai faru......ba zata iyayi musu komai ba......inason zamansu a dakin ya wanke duk wani daci da tsanarsu da zata iya ji a nan gaba......ban isa na sanya ta soki ba kota soni......amma definitely!.....dole!......dole taso wadannan yaran" Qwarin gwiwar da take gani tsakiyar idanunsa shine ya bata relief,ta bishi xuwa falon suka zauna.

Tana iya jin zaman yaran kusa da ita har cikin jikinta,tana iya jin wanzuwarsu sosai a tattare da ita,saidai kuma ta gaza daga idanunta ta kallesu. Zafi takeji a ranta,zafin sabreen sosai takeji,tana ganin kamar itace silar komai da komai.

Sun dauki mintuna masu yawa a haka,iyayen basu dawo sun daukesu ba,abinda ya dinga bata mamaki kenan. Me yasa suka iya dauke idanunsu akan yaran?,me yasa suka iya bar mata su suka fice abinsu?. Motsin da hamza ya fara yi shine ya fusgi hankalinta ba tare data sani ba takai dubanta kansu.

"Subhanallahi" Ta fadi a ranta tana mamakin zallar kamannin dake fuskar yaran. Kamannin da suka tuna mata da fu'ad din sanda yake tsumman goyo kaman haka. Idanu ta zuba masa shi kuma yana ci gaba da motsinsa,a hankali har ya fara qushin qushin din kuka,abinda kuma ya tashi sauran 'yan uwansa kenan.

Mutsu mutsu suka fara yi su duka ukun,kafin kuma a hankali su kece da kuka.162



Hannun fu'ad ta riqe da kyau tana ji kaman ana matsa zuciyarta sanda sautin kukan nasu ya isa ga kunnuwanta. Jikinta duka ya dauki rawa,ta daga idanu tana kallon fu'ad. Qin kallonta yayi,kuma kaman ta fahimci yana sane yaqi kallon nata,sai kawai ta sadda kanta qasa tana sake jin yadda zuciyarta ke tsananin bugawa.

Cika mata kunne sosai kukan nasu yayi.

"Ya isa....kuyi shuru" Ta fadi tana jin ciwon yadda furucinta baya fita a sanda ta yishi,saidai kuma ga mamakinta sai almustapha ya fara rage sautin kukansa,a hankali dukkaninsu suka rage kukan kafin kuma suyi shuru. Mamaki taji ya kamata,ta sake xuba musu idanu wanda kaman sunsan da hakan sai hamza ya soma bude idanunsa. Tarwai qwayar idanunsa,kai ba zakace jariri bane dan sati biyu kacal,tana waiwayawa ga sauran suma duk idanunsu sun bude,kuma ita suke kallo.

Batasan me yasa ba ta samu qaramin murmushi ya subuce daga fuskarta,ta samu kanta da yunqurin miqa hannunta ta kamo hannun koda d'ayane a cikinsu.

Cikin wani irin ba zata da mamaki sai ga hannunta ya motsa,ta maida dubanta ga hannun,ta sake gwada dagashi xuwa gaba,ga tarin mamakinta sai hannunnata ya isa ga almustapha ta riqe yatsunsa hannun nata yana wani irin kakkarwa.

Wani abu da batasan meye ba ya soma ratsa zuciyarta,hawayen da batasan daga ina suke ba suka tsinke mata.

Wacce irin baiwa ko hukuncin Allah ne tattare da yaran?,abinda ta dinga maimaitawa kanta da nacewa da tambaya kenan idanunta akan fuskokinsu dukka su ukun. Sun zame mata waraka daga wani bangaren ciwon ta kenan?. Tambayar da tana ajiyeta fu'ad ya murza qofar ya shigo a hankali shidaya,don gaba daya sabreen ta gaza miqewa bare tayi jarumtar biyoshi,kawai zuciyarta tana gaya mata shikenan,shurunsu wani abun ne maras kyau ya samesu.

Hannun nata yabi da kallo yana mamaki shima wanda har yanxu yana cikin yatsun almustapha,ya qarasa gabanta ya tsugunna yana duban hannun yana kuma duban yaran.

"Hannunki ya motsa yau?" Ya tambayeta,saita gyada kai a hankali hawaye yana silmiyo mata daga idanunta. Qasa yayi da kansa yana tasbihi ga Allah,sun jima a haka sannan ya fiddo wayarsa.

"Ubangiji ya tabbatar da lafiya" Ya fadi a taqaice yana kiran sabreen zuciyarsa ta nauyaya da girman zatin Allah.

Tana kallo suna ficewa da yaran a dakin,sai ta samu kanta da gaza dauke idanunta a kansu har suka kammala ficewa. Tafi qarfin awanni uku bacci bai dauketa ba,tana jin kamar dakin nata ya koma kango bayan fitar tasu,kamar ba wani abu daya rage a dakin sai ita kadai.

Abun mamakin shine,kwana tayi tana mafarkin yaran,cikin mafarkanta na daren gaba daya sune kewaye da ita,harda wanda suke magana da ita,saidai ta kasa bambance me suke fadi.

Ajiyar zuciya kawai ta dinga saukewa sabreen din tana tariyo abinda fu'ad ya gaya mata na yadda ya shiga ya samu maamah din.

"Ya Allah.....ka jefa matsananciyar soyayyarsu a zuciyarta ninkin ba ninkin yadda ta tsani mahaifiyarsu" Ta samu kanta da wannan addu'ar.


*_NAMING CEREMONY_*


Katafaren kuma qawataccen guri ne na alfarma,aka aka shirya sannan aka tsarashi musamman saboda gabatar da radin sunan. Komai na gurin kusan fari ne,farin ma irin qal dinnan me daukan hankali da kuma daukan idanu. Tun daga farkon shiga gurin har zuwa ciki wasu irin manyan hotunan ne na jiraran design daban daban suke welcoming naka.

Kana shiga gurin zakasan guri ne bana wasa ba.....guri ne da akayi barin dukiya,irin barin da zai gaya maka ba'asan zafin kudin ba,don an nemesu a sanda ya dace an kuma tarasu.

Komai a tsare yake,don guri na musamman aka tanada saboda ajjiye yaran. Kowa xai qarasa ya gansu,me buqatar basu gift ko wani abu makamancin hakan amna da huda suna kusa,don sune iyayen yaran gaba daya.

Cikin tsari aka soma gudanar da taron,sabreena maman yaran wadda ta koma hajiya sabreen,tayi wani irin razanannen kyau cikin wani dan banzan lace da aka warewa milliyoyin kudi aka bada order saqashi a india. Ba iya lace din jikinta kawai ba......hatta da lace da atamfofi da manyan luxury warmers da aka raba a gurin duka container guda akayi musu.

Tun kana lissafa adadin kayan ciye ciye da shaye shaye da aka tanada a wajen zaka gaji ne kawai,don kuwa tsarin serve yourself kawai akayi,debi da kanka,kaje ka zaba ka zuba koka aika a debo maka,ko ka kira daya daga cikin ma'aikatan dake wajen ka bashi order din abinda kake da buqatar ci.

Guri na musamman aka tanadarwa jama'ar DUNIYATA,don a idanun sabreen mutane ne masu kima mutunci da daraja,wadanda suka taimaka qwarai wajen bawa dangantaka dama soyayyarsu gudunmawa.

A gurinne fannah ta gabatar da kyautar da BB ya yiwa takwaranshi,wato kyautar sabon company dinsa na sarrafa auduga da fiddashi qasashen waje.....daukan nauyin duka wani abu da ya shafi rayuwarsa,tun daga karatu lafiya sutura da sauransu,yace kawai abbanshi ya zuba masa idanu,don shi aka haifawa umar din. Bama umar duka ba.....dukkanninsu yana jinsu a zuciyarsa,saidai yace bazaiyi qarya ba umar din na dabanne a wajensa.

Abba baiyi qasa a gwiwa ba shima ya aiko da nashi saqon ta hannun amna,estate guda ne me dauke da gidaje dari ya mallakawa nasa takwaran. Ihu aka dinga yi a wajen,saboda yadda abun ya qawatar da mahalatta taron,wato dai gasa ce ta gasken gaske tsakanin kowa da takwaranshi. A sannan fu'ad din yana daga can gidan hutawarsa,yana kallon yadda taron yake gudana kamar a gabanshi,ta hanyar cameras da ya saka aka zuba sosai a wajen,aka kuma miqa ragamar monitoring dinsu a hannun qwararrun security dinsa. Saidai duk da haka yaji yana sha'awar zama,yayita kallon duniyarsa da yanzun ta rarrabu da wasu hadakar qananun duniyoyin har guda uku.

Murmushi ya saki yana gyada kai,shi za'a yiwa wariyar launin fata kenan a ware masa abbansa?,kawai sai ya dauki waya ya kira musaddiq da nashi saqon.

Sanda musaddiq ke sanar da bada kyautar JADDA WINGS ga almustapha kusan kowa sai da yaji shock,kafin daga bisani gurin ya kaure da tafi.

"Sannan nima ina gabatar da tawa qaramar kyautar motar" Ya fadi yana fiddo maqullin motar daga aljihunsa ya dagashi sama ya kuma isa gaban abban nashi almustapha ya ajiye. Motace me bala'in tsada new model,wadda har yanzun ko cikin masu kudi ba kowa bane ya samu nasarar mallakarta ba. Tabbas abban abba ne,kusan yafi kowa a cikinsu tashi da gwaggwabar kyauta.

Kafin abar gurin fu'ad ya sanya qaramar musabaqa ga yara masu haddan qur'ani a wajen,daga shekara goma sha biyu zuwa qasa,koda izu uku ke gareka kuwa. An gwabza musabaqa me kyau,abinda ya sake janye hankalin sabreen taji a duniya bata da burin daya wuce yaran nata su zama mahaddatan alqur'ani.

Sai da aka kammala komai sannan anni itama ta gabatar da nata kyautan. Motoci ne masu kyan gaske guda uku iri daya sak,dukkaninsu farare qal,amna kuwa wani babban box ne da ba wanda yasan ainihin meye a ciki. Fannah ma ba'a barta a baya ba,itama da nata gift din,haka dai kusan duk wanda yazo wajen da nasa alkhairin da zai gabatar,

Muhammad fu'ad jadda ba qashin yarwa bane,komai arziqinka komai kuma babunka ba zaka taba cewa baka amfana dashi da komai ba,wannan ya saya ma yaranshi dama matarsa wata irin soyayya da qauna.

Taro ya tashi lafiya,yara kuma sun tabbatar da sunayensu na ALMUSTAPHA MUHAMMAD JADDA(FAWAD). HAMZA MUHAMMAD JADDA(FAUZAN). da babban aboki amini kuma dan uwa UMAR MUHAMMAD JADDA(FAWWAZ). Yaran sunzo da wani irin yanayi a dangi gaba daya,yan uwa dama wadanda ba 'yan uwa ba kowa

108 / 119