Author : Huguma Category : Complete Novels
daya yana hautsinata ya koma qasan ita kuma ta koma sama ta maye gurbinsa.
"You're in charge now" Ya fadi yana dage mata girarsa. Wani kunya ya kamata,ta cusa fuskarta cikin ni'imtaccen qirjinsa da bata gajiya da wanzuwa akai.
"I give my self to you....i surrender to your will....play your role well" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi.
Duk yadda yake buri hakane ya kasance,duk yadda yake da buqata haka tayi masa. Abun ya gigitashi ya sanyashi fita a hayyacinsa,wasu maganganun daya dinga yi sai sukayi mata mugun nauyi,har ta dinga jin daga wannan ranar kaman ba zata iya sake hada ido dashi ba.
Wani sabon amarcin aka balle a asibitin tsakanin fu'ad da sabreen din,ba tare da kowa ya kula da lalurar da yake tare da shi ba.
Hankalinta ya tashi bayan komai ya lafa da taga bandages din hannunshi sunyi staining da jini.
"Ka gani ko?,dama bana gaya maka ba?" Ta fada a narke muryarta tana rawa tana shirin sakin kuka. Hannun nasa ya kalla ya saki murmushi yana jawota jikinsa sosai,duk qoqarin sauka da takeyi daga jikin nasa amma ya hanata.
"Please stay with me.....i could use some relaxation time......sai muyi wanka"
"Ciwonka fa?" Ta tambaya a mamakance tana kallon fuskarsa da tuni ya maida idanunsa ya lumshe yana fidda wani sassanyan murmushi.
"Forget about.....zasu gyara zuwa safe" Ta sake motsawa zatayi magana ya dora yatsansa akan labbansa.
"Shshshsh" Yace da ita,dole ta maida kanta ta kwantar,saidai hankalinta gaba daya yana kan ciwon.
Bayan sun idar da sallar asuba,tana kammala azkar dinta ta koma toilet don yin fitsari saiga jini. Ta razana sosai ta ware dukka idanunta tana duban jinin. Jikinta ta dauki rawa gaba daya,bata da wani qwarin daga murya ta kirashi,tana ma ganin kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani irin sauri.
Kansa ya daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware idonsa yana dubanta kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana tambayarta
"What's happening?.....relax.....gayamin" Pant dinta kawai ta daga masa,sai ya zare idanunsa waje kaman zasu fado.
"Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba daya ya gama firgicewa. Cikin kula da takatsantsan ya maidata gadonsa ya kwantar da ita.
"Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da sauri don yana ganin tsaiwa kiransa ta landline ma bata lokaci ne.
Su biyu suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana akan hannunsa amma bata wannan yake ba.
"Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies din" Likitan ta fada tana qarasawa gaban gadon sabreen din.
Maida dubansa likitan yayi a kansa.
"Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi fu'ad din wanda hankalinsa duka yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo na'urar scan wanda take a dakin permanently.
Kafin yace komai anyi knocking qofar an turo an kuma shigo. Farouq ne shida musaddiq dauke da breakfast da anni ke dafa musu.
Likitanne ya amsa sallaman,farouq ya qaraso dakin fuskarsa dauke da alamun tambayar abinda yake faruwa.
"Lafiya dude?" Farouq ya tambayi fu'ad yana qarasawa kusa dashi. Bai amsa masa ba,ya taka ya matsa gaban inda su sabreen suke ya jawo curtain divider ya rufesu daidai sanda yaji tana tambayar sabreen din
"Kinyi wani aiki me nauyi ne sosai?" Amsa mata tayi da a'ah....still ta sake tambaya.
"Ko kunyi mu'amala?". Shuru tayi tana jin kunya na dawainiya da ita,fu'ad da hankalinsa ke wajen ya sauke hannayensa daya goya a qirjinsa yana fadin.
"Kiyi checking baby din kawai madam"
"Okay sir" Ta amsa masa a ladabce.
Daidai lokacin wani ma'aikacin jinya ya qaraso yana tura medication cart dake dauke da bandages da sauran kayan dressing.
"Your hand sir" Dr din ya sake fadi yana duban fu'ad tare da masa nuni da abun zama.
Sai daya waiwaya zai zauna din suka hada idanu da farouq,kai ya dauke yana hade rai,sai shima farouq din ya basar yana girgiza kai.
Ana mata scan din likitan yana ware wancan bandage din a hankali,farouq yana daga zaune a gabanshi yana danne dariyarsa. Ya wani maze sai cin magani yakeyi?,karon farko da ya fuskanci fu'ad din baya son kallonshi. Koda ba'ayi bayanin komai ba farouq din ya fahimci aika aika akayi a dakin a daren jiya,saidai fatarsa daya babies dinsu ya zaman lafiya suke.
"Wow......unbelievable" Muryar likitan ta fita da wani irin sound da yaja hankalinsu su duka. Kasa jurewa fu'ad din yayi,ya dagawa likitan hannu.
"Wait..." Sai kawai ya miqe yana danne sauran bandage din da ba'a gama cirewa ba.
Kai tsaye ya kutsa tsakanin curtains din ya shiga.
"Triplets ne sir" Likitan ta sake fada da wani kwantaccen murmushi saman fuskarta. Idanu kawai ya zurawa na'aurar qirjinsa na harbawa,wani bahagon farinciki yana son bugar dashi. Zooming na scan din tayi,sai gashi ya nuna wasu gurabe guda uku.
"Gasu a nan sir......congratulations" Ta fada tana sakin dariya cikin nishadi.
"Alhamdulillah.......alhamdulillah" Farouq da yakeji kaman yayi tsuntsuwa ya shigo a nuna masa shima ya fada yana murza hannayensa bakinsa ya gaza rufuwa.
Idanunsa ya lumshe sannna ya budesu,yana so yaji mafarki yakeyi ko kuma idanunsa biyu.
"Subhanallahi wabu hamdih.....subhanallahilazeem,Alhamdulillah......alhamdulillah hamdan kaseeran dayyiban mubarakan fihi....." Ya fada yana yin qasa da kansa yana jin wani abu yana taso masa. Wanne abu zaiyiwa Allah ubangiji da zai da dadawa Allah?,wanne abu zai yiwa Allah mafi soyuwa a wajen ubangiji.....duk da ya ambaci wadancan kalmomin,masu sauqi a harshe.....masu nauyi a mizani.......masoya a wajen Allah(subhanallahi wa bi hamdih,subhanallahil azeem,kada ki wasa da yawan maimaitasu,kalmomi ne masoya a wajen Allah,wato wadanda Allah yake sonsu qwarai,ga nauyi a mizani,zasu qarawa ayyukanki nauyi ranar qiyama,ranar da ake auna ayyuka akan ma'auni).
"Thanks.....thank you so much" Ya fada yana isa inda sabreen din take. Hannunsa ya dora saman kanta yana ranqwafawa a samanta,sai a sannan ya dauke idonsa daga kan screen din yan jin kamar zaiga yaran be baro baro a ciki. Idanunsu suka hadu waje daya,saita fara sakar masa murmushi. Kai yake jijjigawa kawai ya kasa magana,sai ta miqa masa hannunta shima kai tsaye ya bata nashi,ya sunkuya yana sumbatar mararta.
"You're my world sabbrrrr.......da nace ke DUNIYATA ce da gaske ke din duniyata ce.......ya rabbb......ka tsaremin wannan baiwar taka da irin tsaronka ita da duk abinda take dauke dashi......yadda mahaifanta suka haifamin alkhairin rayuwata......ubangiji ka shimfida musu aljannarka cikin qaburburansu........"
"Allah ya hada da abba daya zama nagartaccen uban daya nunawa yaransa muhimmancin mace" Ta tari numfashinsa tana jin zuciyarta na karyewa da irin addu'arsa akan mahaifanta wanda bata taba jin irinta ba. Wata kyakkyawar runguma yayi mata wadda ta sanya likitan ficewa daga cikin labulen ta basu guri. Wannan karon ba fu'ad kadai ba.....hatta da sabreen saida fuskarta ta jiqe da hawayen farinciki. Ya fita jarumta a wannan karon,don shi ya soma janye jikinsa yana goge mata fuskar.
"Kada ki tashi hankalin babies dinmu......ya isa.....is okay ko?" Ya fada bayan ya gama goge mata fuskar ya sunkunya ya sumbaceta a goshi.
"Sir......zaa qarasa duba ciwon?" Likitan yace dashi,sai ya miqawa sabreen daya hannun nasa ya dagata ta zauna ya yaye labulen bayan ya tabbatar ko ina a jikinta a rufe yake.
Hugging nasa farouq yayi wanda ya kasa zama saboda farinciki,fu'ad ya dan bubbuga bayansa yana murmushi
"Congratulations dude....." Kai tsaye ya taya farouq din murna,don ya sani suna raye ko basa raye,zai amsa sunan mahaifinsu ne kawai wanda yayi cikinsu,amma sunan uba farouq keda wannan matsayin.
"Thank you dude.....na gode" Farouq ya fadi murmushi yana qin barin fuskarsa.
Likitan yana duba ciwon daya doctor din tana sake yiwa sabreen bayani.
"Duka fetuses din suna lafiya qalau,ki zauna sosai ki huta yau gaba daya,zai tsaya nan bada jimawa ba....sai prenatal medication dinki da zaki ci gaba da sha da kula dasu.....ina miki fatan haihuwa sassauqa da lafiyayyun Yara".
"Na gode" Sabreen din ta fada tana murmushi. A yau din jinta take wata ta daban,jinta take ta musamman,yau ita sabreen itace a mazaunin uwa?,wadda zata kawo wasu rayukan cikin duniya?,wasu halittun da suka kasance jininta?,jinin muhammad fuad dukka a cakude a jikinsu?.
Duk bayan minti daya sai ya daga kai ya kalleta,daga qarshe parlor suka koma don Dr din ya qarasa dubashi,sai yake jinsa ba tsaro,gani yake kaman yana kalle masa ita.
"Amazing....haka kake da quick healing?" Likitan ya tambaya da mamaki yana murmushi sannan ya dora.
"Nayi mamakin ganin saurin warkewar ciwon,kadanne ya rage banda an bashi pressure me yawa ba da bazai fidda jini ba.....za'a maida sabon bandage amma dan kadan.....please next time kada a matseshi da yawa hakan zai bashi daman warkewa da wuri".
" Ai basai ka fada bama likita,ni nan zanwa tufkar hanci" Farouq ya fada yana bubbuda hanci. Harara fu'ad ya watsa masa,sannan ya maida harshensa zuwa hausa.
"Kada kiyi gigin cewa zaka kai qarata wajen anni....muddin ka rabani da duniyata saina maida maka naka hannun agogon baya" Ya fada sounding seriously.
Dariya farouq ya tuntsure da ita,baisan ya akayi ya dagoshi haka da wuri ba
"Ko bankai qararka wajen anni ba nasan nayi dakai ai" Ya amsa masa yana miqe qafafunsa nishadance yana duba saqon fannarshi daya shigo masa.
Sai da likitan ya kammala komai ya fice sannan ya kalli farouq.
"Bani abinci malam.....haka ake jinyar?" Ya fada yana hararasa.
"Zan baka mana....kai banda ka fanshi kanki jiya zaka sake ganin face din angon fanna ne?" Yadda yayi maganar ya sanya murmushi subucewa fuskar fu'ad,yakau da kansa kawai yana murmushi.
Ya zuba masa komai amma sai yaga yayi gefe da wani babban mug.
"Wancan meye a ciki". Da hannu farouq ya nuna masa.
"Wannan?,maca and ginseng tea ne".
"Zubashi a nan" Ya fada yana nuna masa wani glass mug. Nesa farouq ya qarayi dashi.
"Kai ina......kaida wannan ai ba yanzu ba wallahi......kana wannan barnar xan barka kaci gaba da shan wannan?,kayi haquri ku haifemin yarana lafiya....to daga nan har china kuje saikun dawo". Idanunsa ya janye kawai bai ko musawa farouq ba ya dauki mug din daya zuba masa normal black tea ya fara kurba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 135
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
135
So take ta zama kaman kowacce mace.....wadda ke dauke da responsibility na mijinta,kula da duk wani welfare nashi da al'amuran da suka shafeshi,bawai ta barshi shi yayita hidima haka da ita ba,don haka koda suka qarasa bedroom din towel ta ajiye masa sannan ta zarce toilet din.
Water heater ta kunna wanda in minutes ta kashe kanta da kanta alamun ruwan ya tafasa,saita kunna tap din duka guda biyu na famfunan,ta cika masa bathtub da ruwan me dumi sosai sannan ta saisaitashi ta health faucet saboda kama ruwa da sauransu.
Ta kammala tana waiwayowa da nufin fita tace ta gama sai ji tayi an sake sama da ita an tsumbulata cikin ruwan sannan ya biyo bayanta.
"Bansan sai yaushe zakiyi nauyi ba....kosai kin fara turtsi bulli irin na masu ciki?" Ya fada yana qanqameta cikin ruwan.
"Me yasa da bakya hadamin ruwa me dadi haka?" Ya sake fada yana sake matso da ita yana shanshana sumarta data fara jiqewa. Bare baki tayi ta soma masa kukan shagwaba,akan meye zai jiqata bayan ba yanzu zatayi wanka ba. Dariya ya dinga mata kafin daga bisani ya fuskanci kukan ya koma na gaske ya lalace wajen lallashinta.
Mintuna arbain kafin su fito,tayi daurin qirji da towel tanata goge kanta daya jiqe. Curling iron din data dauko ya karbe,ya soma tsaga gashin yana nade mata shi da style din da takeso.
"Hamma.....ana jiranka fa"
"Tare zamu sauka sabrrrr,bazan sauka na barki ba" Karbe curling iron din tayi ta ajiye
"Mu shirya na rakaka kaci abinci ka fita.....kace kana da hidiman bikin BB naka.....yaushe ka gama ganawa da mutane ka maida hankalinka akai?". Hancinta ya lakace mata.
"Yes maaa.....da alama ina da personal assistant me hazaqa,anya bazan sallami saddiq ba?" Murmushi ta saki tana cewa.
"Ba ruwana,kada yace nasa an koreshi".
Sai data tabbatar ya qoshi sannan ta taka masa har inda yake ganin baqin da suka zama dole,baqinsa na jikinsa sosai wanda ita kanta batasan da wajen ba sai a sannan. Zata juya kenan daya daga cikin guard dinsa suka qaraso.
"Malam ne yazo"
"Har sai an nema masa izini?,kace masa ya shigo qasan rumfar can" Ya fadi yana juyawa yana fasa shiga sitting room din. Hannunta ya kama.
"Muje ku gaisa da malam.....mutumin kirki wanda ta silarsa ne na samu ilimin addini". Bata musa masa ba suka taka zuwa farfajiyar da aka qawata da kujerun zama.
Tun daga nesa ta gane malam dinta,mutumin kirki na gasken gaske wanda kusan zata iya cewa tafi fu'ad sanin hakan.
Mamaki sosai malam yayi sanda yake zama saman dayan kujerun dake wajen. Ta zame tana gaidashi kaman yadda fu'ad yayi.
"Ashe da gaske rumaisa take?,sanda take gayamin ke kike auren muhammadu ba dauka shirmenta ne kawai.....muhammadu kayi sa'ar mata da gasken gaske" Malam ya fada yana maida dubansa ga fu'ad. Sabreen fu'ad din ya kalla sannan ya maida dubansa ga malam.
"Tana da tausayi da taimako......tana da yawan sadaka da kuma kyauta,bata wata batayi sadaka ga mabuqata ba......marainiya ce muhammadu......nasan halinka kai dinma.....muna da kyakkyawan zaton nagarta daga gareka......ka riqeta hannu bibbiyu,lada biyu gareka,ladan riqon maraya,ga kuma ladan kula da iyali".
"In sha Allah malam" Ya fada yana sadda kansa qasa. Inama ace malam yazo a sanda yake tsaka da fara cusgunawa rayuwarta?,inama ace malam yazo a sannan ya ceceshi daga feeling guilty da yakeyi a duk sanda ya tuna yadda ya mu'amalanceta a baya?.
Duk da cewa ba laifinsa bane.......yayi dukkanin binciken da zai yi a matsayinsa na dan adam.....kuma abinda ya samu kenan. Da gaske ga a inda kudaden da duk take diba sukafi tafiya kenan fiye da jikin 'yan uwanta,sai yakejin wannan din dama ce ta sake samun wasu labaran a kanta ta wajen malam din.
Hira kadan tayi da malam tana tambayarsa inna ta bada saqon gaisuwa ga rumaisa da shaida mata sun dawo sannan ta koma ciki.
Da kanta ta shirya abun motsa baki ta kawowa malam din,duk da ma'u tace ta barshi amma tace sam malam yafi gaban haka.
Qarfe tara tayi shirin bacci,don tunda ya fita ba sake jin motsinsa ba,ta tabbatar zai wahala idan ba baqin bane suka sha masa kai. Ta dawo parlor din farko da nufin daukan madarar shanu ma'u na fitowa a kitchen da alama ta gama komai na yau sai gobe kenan.
Tana mata sallama amma idanunta akan kwalin hannun mau,tsirfa da tsarabe tsarabe irin na musu ciki haka kawai taji yawunta ya tsinke.
"Amma fa ma'u meye wannan?" Kallon farin box din tayi tayi murmushi.
"Wallahi amna ce ta aikomin dashi,wani doughnuts ne da ta taba ban guda daya ta yafi dani,sai tace zata sake sakawa a kawomin".
"Mu gani" Sabreen ta fada tana matsowa,bude mata ma'u tayi take yawun bakinta ya qarasa tsinkewa gaba daya.
"Don Allah ma'u ko guda daya ne" Ta fada tana narke fuska idonta akan doughnuts din da aka yiwa wankan madara.
Dariya ta qwacewa ma'un,tasan halin ciki yafi gaban haka,bataga abinda zata samu ta hana sabreen din ba,bare wannan da nan da nan idan sunason wani za'a sake kawowa.
"Jeki da kwalin gaba daya" Ta fadi tana tura mata kwalin. Har wani dan tsallen murna tayi,ta amshe tana godiya ta haura saman dashi.
Gudu gudu ta gama shiryawa,ta ware gashinta saman bayanta ta haye sofa tana bude kwalin. Lashe baki tayi tana jin kaman ya mata nisa ta tsaya bude ledar a daidai