A Duniyata Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   69 / 119

204K to 207K   out of 356.9K words

hankalinsa ke waya cikin yaren Dhivehi,har ta kammala ta juya ta fita tana basu guri.

Juya spoon din take kawai a plate din tana hadiye wani abu a qirjinta. Batasan meye ba amma ya tsaye mata a wuya. Bai ankara ba,sai daya gama uzurinsa da waya sannan. A mamakance yake dubanta.

"Start mana madam....banason wasa da abinci fa?".

"Itama fareedan ce?" Ta tambayeshi da wani salo daya sanyashi karantar zallar kishin dake kwance a idanunta,saidai kuma a sarari qwalla ce kwance saman oily eyes dinsa,sai suka qara wani sheqi.

Dariya yakeson mata saboda wani irin farinciki yaji yana lullubeshi,tun daga saman zuciyarsa yana sauka ta kowanne sashe na gangar jikinsa. Har ya fara winning haka da wuri? Ya tambayi kansa yana taya kanshi murna,amma a bayyane sai ya lanqwasa fuskarsa alamun tausayi.

"Me kuma nayi?". Muryarta na rawa kadan tace.

"Kunata magana da yaren da banaji.....tanata maka hira kana amsawa?". Wannan karon kam kasa boyuwa dariyarsa tayi,abinda ya tunzurata kenan.

" Karki wuce gona da iri sabreen,karki rudu ki fada soyayyar abinda ba yafi qarfin ajinki.....abinda yafi qarfinki,abinda baki da tabbas a kansa.....shin kin Manta maamah tana nan?". Tambayar data tarwatsa duk wani qwarin gwiwa da take qoqarin tattarawa kanta,taji kuma komai ya tsaya mata cak.

Dab da ita ya dawo ya zauna,ya kama hannayenta ya saka cikin nasa yana matsawa a hankali.

"Kin taba ganin mutum ya canza DUNIYARSA?" ya mata tambayar kai tsaye,qasa tayi da kanta don sai takejin tana son jefa rayuwarta cikin hadari ne kawai,muddin ta sakewa zuciyarta ta fada sonshi to ba shakka ta fada babban tarko......babban tarkon da zai bawa maamah daman walagigi da rayuwarta yadda taga dama.

"Amsar itace aah......ke duniyata ce,babu daman na sauyaki ko na hadaki da wata ko wani abun......ni muhammad jadda naki ne ke kadai,don ke kadai aka halicceni.....ki rubuta wannan ki ajiye"

_to zamu gani,anya hajiya maamah zata qyale kuwa???_


*ANNI*


Tun a jam'in sallar asuba da sukazo yi taga bata ga fu'ad ba.....still da tace farouq ya turo mata shi komin dare baizo ba,har suka gama waya da abba Alhaji hamza kibiya dake tashi umrar ta kwanta amma ba fu'ad din ba dalilinsa.

Sanda suka kammala sallar sai tayi zaune kawai tana lazimi,tunaninta yana rarrabuwa,bataga fu'ad ba......bataga sabreen ba,duka ina suka shiga?. Ta wata fuskar sai takejin relief na rashin ganinsu su duka biyun,don zuciyarta na qissima mata wani abu,ta wani bangaren kuma bataso ta sake jikinta akan hakan,saboda tasan wace mariya din.

Takwas saura farouq ya shigo gaidata. Yana daga zaune gabanta ya dan dubi amna dake kwance tana shirin komawa bacci

"Ta duba qur'aninta kuwa?". Kai anni ta daga masa

" Ta duba" Sai ya jinjina kai. Wani sabo ne da raino data musu dukkansu,dole kowacce safiya....komai uzurinka ko meye kakeyi ka fara duba qur'ani kafin komai.

"Kiramin fu'ad.....ka gwadamin dukka layukansa" Anni ta fadi tana gyara zamanta.

"Na gwada wani tun jiya a kashe,amma bari na gwada sauran" Farouq ya fada hankalinsa kwance,don shi kam ya gama hasashen inda aka haihu a ragaya ma. Baya tunanin ko maamah ta yiwa fu'ad farin sanin da shi yayi masa.

Daya bayan daya yabi layukansa yana kira amma kowanne gaya masa ake a kashe yake,sai ya daga ido kawai yana duban anni da fuskarta ta shiga damuwa.

"To ina ya shiga?,ina kuma sabreen?". Dariyarsa ya danne yana dan saka alhini a saman tasa fuskar shima

"Karki damu anni in sha Allah jikina yana bani suna tare,bari na tura masa email da SMS duka" Ya fada yana fara rubuta saqonnin ya kuma aike masan kaman yadda yace,duk da yasan zai wahala ya gani a kwanakin nan,lallai indai ya samu nasarar dauke sabreen ne tofa sai baaba ta gani.


*MAAMAH*

Idan tace hankalinta a kwance yake daga daren zuwa safiyar tayi qarya. Ta kirashi ta kirashi har batasan adadin sau nawa ba. Tabbas ta sani,a yanxu duk duniya idan ameenatu tace itace mahaifiya ga fu'ad,kuma tana tuhumarta batan sabreen ba wanda ya isa ya hana a daureta,ba wanda zai fiddata idan ba fu'ad din ba,da sauran mutuncinta,bataso wasan ya qare a haka,saidai hakan ya sake ninka qiyayyar anni sosai a ranta. Ita daya taketa shawa kanta alwashin saita yiwa ameenatu abu mafi munin da ba zata tabawa mantawa da ita ba,idan don tayi wannan ne don ta nuna mata iyakarta ne ganin suna qasar da ba tasu ba.....to tabbas ita kuma zata bar mata wani babban tabo a rayuwarta da ba zata taba mantawa dashi ba.

Musaddiq ta kira ta sanyashi nema mata fu'ad din,saidai shima kiran duniya wayar sunqi tafiya.

"Maamah wayoyinsa a kulle suke" Maganan data sake sakata a taraddadi da tunane tunane iri iri.

"Kada fa ya zamana ameenatu ta salwantar mata da yaro ne takeson tayi garkuwa da ita akan batun haka da wuri?" Wannan shine tunanin daketa mata kai kawo.

"Ya kamata ki xama cikin shiri.....ki xama a ankare.....karki nuna mata tsoronki,ki tabbatar mata da.naki zargin kema" Abinda zuciyarta take nanata mata kenan,wanda shine kuma ya bata qwarin gwiwa.

Cikin kwanakin sai ya zamana wani irin zama ake a gidan,kallo kallo kawai akeyi tsakanin maamah da anni din. Duk da maamah tana cikin d'ari d'ari da tunanin inda fu'ad da sabreen dinma suke......amma ta azawa ranta wani dakiya. Ta fannin annin kowanne taku na maamah din saman idanunta yake,ba komai take dubawa ba sai idanun yaransu da suke rayuwa guri daya,zai zame musu wani abu na daban kuma na tashin hankali idan suka ga wani sabani muraran a tsakaninsu,banda hakan a shirye anni yake akan maamah wannan karon.....duk da tana danjin relief idan farouq na bata tabbacin fu'ad da sabreen din suna lafiya.

Farouq din ya fahimci abinda ke faruwa,saidai bai nuna musu komai ba,yayi ma kaman bai sani ba,saidai time to time shima yana neman fu'ad din ta waya,amma dif kakeji ko sau daya bai taba katarin samunsa ba.....a haka sannu a sannu sai gashi an kwashe sati guda cif ba wanda yaji motsinsu ko yasan inda suke.

Zuwa sannan hankalin anni ya tashi sosai,kusan kullum sai tasa farouq ya kira mata shi,mafi qaranci sau biyu a rana,saboda kwanakin barinsu Maldives kusan za'a ce yayi,kwana uku ko hudu suka rage musi,gashi babu shi ba sabreen din.

Tun tana yiwa maamah din kara har abun yaci tura,ranar daya rage kwanaki uku subar qasar,da wani yammaci suna parlor. Amna ke mata kalba saman dogon gashinta da tafi masa kalba akan kitso,maamah tana daga gefe zaune tana kallo cikin tv. Ta tsiri wannan zamanne kawai don ta nunawa anni ba abinda zai tsoratata,hakanan itama me cikakken iko ce,duk da cikin rashin cikakkiyar nutsuwa itama take. Ba sabreen ce ma damuwarta ba danta shine damuwarta,idan tana da damuwa akan sabreen din bazai wuce na yadda take gudun kada anni ta fake da wannan ta tozartata a idon duniya ba.

Farouq ne ya shigo da sallama,kaman yadda suke koyi da tarbiyyar anni da umarninta,ya yiwa maamah barka da gida,ta amsa masa a d'age kaman yadda ta saba. Mugun haushinsa takeji.....tana ganinsa a asalin tantirin munafuki tun daga quruciyarsa kawo yanzu,kai tsaye zata iya cewa shine kanwa uwar gami da yaja mata yaro cikin gidansu ya hadashi da mayun iyayensa da suka kasa sakar mata kurwar d'a,suka hanata taci arziqin d'anta yadda ya dace. Ko a yanzun gani take cutar fu'ad kawai yakeyi yana amfana da arziqinsa,yana tatsarsa ne shima.....ba wani tare da suka samo arziqin,ba kuma wai iya harkar noma da kayan abinci yake wannan fantamawar ba,dukiyar gold da diamond din d'anta ce.

"Farouq......kwanaki uku suka rage mana mubar Maldives.....ka samomin 'ya'yana?" Tayi maganar cikin salon son isar da saqo ga maamah.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 104


104


Kalmar 'ya'yana din kuwa ta daki zuciyar maamah da wani matsanancin kishi. Wato har fu'ad dinma ya tashi daga sunan dan riqo ya koma danta?.

"Aah anni....inata dai qoqari" Ya amsa mata yana fahimtar inda saqonta yasa gaba. Kai ta jijjjiga

"Zan sabawa fu'ad kuwa muddin qafafunsa yasa ya tafi bai sanarwa iyayensa ba.....idan kuma wani keda hannu kan hakan....na rantse da Allah ko waye bazan barshi ba.....tashi kaje,tsakanin yau da gobe nakeso ka lalubomin shi" Kai kawai kada mata yana tashi,maimakon ya koma daki sai ya juya yana sake ficewa a gidan.

Yau din Jordan ya nema kai tsaye,shima ya gaya masa tun randa suka fita tare bai sake ganinsa ba. Ci gaba yayi da bibiyarsa ta waya amma a banza,sai ya koma ya lalubi system dinsa da yakan ajiye schedule nasa da komai. Yasan password nasa da komai don haka kai tsaye ya bude ya shiga. Zallar aminci ne da yarda da kuma dawwamammiyar qauna,shima iya abinda yaje nema ya shiga ya duba kawai ya fito. Bai samu bayanin komai ba,hasalima bai ajiye inda zashi ba banda ranar da sukayi zasu fita din satin baya daya wuce ranar daya bace kenan.

Awa daya ya bawa ransa zai sake kiransa,idan bai sameshi ba kuwa aikin safa da marwa ya sameshi cikin tsibirin Maldives,wala'alla sai yayi hayar boat ko skis ya gewaye tsibirin Maldives ya nemowa anni 'ya'yanta.

"Oops.....wannan soyayya taku nima ta jefani kwale kwale.....where are you?.....anni ke kika jawo,da kin damqa masa matarsa salin alin dani kaina ban tsinciki kaina a halin da nake ciki ba" Ya fada yana furzar da iska daga bakinsa gami da yin relaxing jikin kujera yana lumshe ido. Murmushi ne kuma ya qwace masa saboda hango fuskar maamah da yayi,tayi wani laushi da yaushi ba tare data fahimci hakan ba

"Wato anni kema kinsan takan tsiya?" Ya fada qasan ransa yana komawa ya kwanta sosai saman sofa din.


β˜…Gaba daya ya wani narke saman sofa din bayan ya miqe qafafunsa saman table din gabansa daya dora system dinsa. Tun dazun ya kunna system din amma ya gaza saka mata password ya budeta. Sai yau yakejin ya kamata ko farouq yasan inda yake,don yayi imanin ko kowa bai nemesa ba anni zata nemesa,zata kuma damu da rashin ganinsu.

Gilmawarta kadai a gabansa yana debe hankali daga gangar jikinsa,a kwanakin nan shi kansa yasan mahaukacin so yake mata wanda baisan adadinsa ba. Idan ya kebe yana salla,yana yawan tuhumar kansa wanne irin so yake mata wannana?,abu daya ke sanya masa relief addu'o'in daya debe tsahon rayuwarsa yana yi akan.

"Ya Allah,idan ka tashi dasamin soyayyar wata 'ya mace.....ka jarabceni da soyayyar da zan iya.....ka dasamin soyayyar macen data dace dani ta dace da rayuwar 'ya'yana,macen da zata soni itama sama da yadda nakeson kaina....macen da ni karan kaina takeso ba abinda na mallaka ba.....macen da zata fifitani sama da kowa da komai....tsaftatacciyar mace.....kamila aaqila....aabida,ya Allah,kada ka jarabceni yadda ka jarrabi mahaifina......ubangiji ka azurtani nida dan uwana da matayen da zasu rufe ciwukan da suke cikin zukatanmu kaman yadda kayi mana baiwa da samun anni". Idan ya tuna wannan addu'ar sai yaji son da yakewa sabreen din ba komai bane.....yayi imanin Allah bazai wofantar da addu'ar da aka dauki tsahon lokaci ana qwanqwasa qofarsa saboda ita ba.

Duk wasu kaya nata tunda sukazo wajen tayi bankwana dasu,daga kayan safiya zuwa na dare duka tana shigarta ne a bisa zabinsa. Tun tana dojewa har ta fara ragewa,don idanma tace zata musa shi zai tubeta ya kuma sanya matan. Yayi amfani sosai da damarsa......yayi amfani da tsoronta da gurin ya mata wani irin sabo da kwana a jikinsa,ya sanya wata shaquwa me qarfi a zuciyarta da wannan. Ranar farko da hakan ta fara kasancewa.....
Tayi wani irin bacci da idan zata iya tunawa irin baccin qarshe da tayi saman cinyar ummenta ranar da asthma dinta ya tashi. But bacci cikin jikinsa yana da wasu qa'idoji da ta kasa kiyayesu har yanzu. Wani sabon abune kwanciya hakanan ba tare data rabawa jikinta komai ba....shi kuma kullum sai ya maimaita mata bayan ya maidata yadda yake

"That's my rules". Daga qarshe wayo yake mats,wayon da yake sanyawa washegari ta tashi da matsananciyar kunyarsa da bata iya hada idanu dashi.

Duk yadda taso ta gano yadda yake iya cimmata ya firgitata ya fiddata daga saitinta ta kaucewa wannan abun amma ta gagara......wani lokaci har jira takeyi yayi wani motsi don tayi masa tawaye.....to amma da an iso gurin sai ya sanyata ta manta wacece a ina kuma take?,sai bayan qura ta lafa ta isheshi da kukan banza da qorafi. Wani lokaci ya biye mata ya lalace wajen rarrashi.....wani lokaci kuma yaja hancinta

"Har yanzu baki fara koyan maida martani ba......am dreaming about it,saikin gama kwashe alkhairan kuma ayitamin kukan abunga...." Gulma tason yakeson cewa,fadi ne kawai bazaiyi ba.

"Sabrrrr" Ya kirata jikinsa yana sake macewa. Wani irin Palazzo ne a jikinta da wata 'yar top data zauna mata sosai a jikinta,ta kuma bayyana masa albarkatun qirjinta yadda yakeso. Kanta yasha hair pins wanda shi ya zauna ya shiryata,ya kuma gyara mata kan yadda yakeson gani.

Yasha wahala sosai wajen nesanta kanshi da mata,ya kame kansa,ya runtse ganinsa ya kuma kiyaye al'aurarsa.....wannan ya sanya yaci alwashin ko meye dake burgeshi game da mace sai yayi qara'insa a jikin matarsa......sai ya kalla yadda ranshi keso. Yana ankare da ita a takure taka,yasan zaayi hakan,don shima ko sau daya bai bari idanunsa sun huta da kallonta ba.

Duk sanda yaga dari darinta akan sakin jiki ga d'a namijin da ya kasance mijinta sai yaji wani qunan rai da bacin rai ga wadanda suka dinga sadakar mutuncinta,suka kuma dangantata da sunan KARUWA.

"Zo kiji" Ya fada a galabaice yana miqa mata hannunsa sanda tazo gilmashi. Baima bata lokacin tunani ba ya sanya hannunsa ya jawota saman cinyarsa yadda ya saba mata. Sam bata masa nauyi wajen dauka ko jawowa,kaman wata leda yake daukanta.

Matseta yayi a jikinsa yana rungumeta sosai,ya kuma dauko system din ya aza saman cinyarta yana saka password dinsa.

"Massages nakeson dubawa amma gaba daya kin hanani sukuni.....sai rarrabamin hankali kike,gwara ki zauna mu duba tare,wataqila nafi samun nutsuwar dubawar"

"Me nayi kuma?" Ta tambaya a shagwabe. Hancinta yaja yana kashe mata idanu

"Aah hajiyata....komai mafa kinyi.....satar da kikayi a gangar jikin muhammad fu'ad.....zuciyarsa dinnan ta tafi kenan,bana jin zata dawo masa har abada" Ya fada yana sakinta gami da fara buda saqon farko wanda ya sakashi sakin murmushi ganin saqonnin farouq a jejjere a jejjere. Na qarshen ya fara budawa wanda bai wuce mintuna talatin da turowa ba.

_"You're rocking the boat,you're fanning the flames.......dude.....ka shiga hankalinka ka dawo gida.....yaqi zai barke tsakanin ummominka.....am serious dude"_ shine saqon qarshe daya gani mintuna talatin baya. Dan murmushi ya saki yana tabe baki,yasan abinda farouq zai masa qarya.....ya kuma san wanda bazai masa qarya ba,wannan statement din nashi yasan real ne ba wasa yake masa ba,sai ya danna replies ya soma bashi amsa

_"Step back BB.....leave them.....nasan anni ba zata biye abun yayi worst ba.....ina nan ina neman hadin kan DUNIYATA.....zamu hadu a airport ranar Tuesday to makka in sha Allah"_ yana tura masa ya koma duba ragowar saqonni masu muhimmanci yana ragewa,saidai kusan bayan kowanne minti daya sai ya tura kansa cikin rigar ta. Tureshi tayi har sau biyu,ana ukun yayi warning nata

"Idan kika sake ban yafe ba" Idanunta dukka ta fidda idanunta waje tana dubansa a mamakance,rai ya hada

"Yes....aikin karanta walau alattanur ko wajen rumaisa?" Qasa tayi da kanta tana tunawa da hadisin,ya kuma aza mata wata irin kunyarsa sosai. Yadda yaga tayi ya masa dadi.......da gaske karatun yana kama zuciyarta har haka,tsaf fa zai iya komawa wajen malam ci gaba da daukan karatuttukan da zasu sanyashi sake sanyata ta sake zama sassanya.....buqatar maje haji sallah. Yadda tayin ya bashi daman dauke hannuwansa daga can system din ya maida inda yafi muradi da wani tattausan yanayi yana sake shigewa jikinta.

"So kike na zama dan is......" Batasan ta saka tafin hannunta saman bakinsa ba.....batasan sadda hakan ta kasance ba sai data tsinciki narkakkun idanunsa cikin nata,hakan sai ya zama kaman wani lasisi ta bashi kenan daya sakashi yunqurawa dauke da ita,daidai sanda saqon farouq da mamakin fu'ad din ya kasheshi ya shigo system din,ta baya ya saka qafa ya tureta ba tare daya damu da idan ta fadi zata iya fashewa ba

"Just leave me have this moment,don't dampen the mood" Yayi maganan kaman wanda yasha giya ya maku,saidai duk da hakan abun mamakin shine,sanda ya mata masauki saman tattausan gadon da harshensa dake hardewa yace da ita.

"Let me relish this moment,and then I'll tell you more about fu'ad. Ya kamata kisan waye fu'ad......am ready to make you DUNIYATA da gasken gaske.......inason kisan komai nawa da gaske......".




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 105


105


_Barkanmu da dawowa,fatan munyi sallah lpy,ubangiji ya maimaita mana cikin lafiya aminci da kwanciyar hankali_




69 / 119