A Duniyata Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   62 / 119

183K to 186K   out of 356.9K words

daya akan fuskarta. Wannan karon kasa jure kallonsa tayi,saita runtse idonta tana hade rai sosai.

"Banaso kana tabamin jiki.....bana so"

"Am addicted to you.......tabaki shine favourite thing a rayuwata gaba daya" Ya maida mata amsa kai tsaye yana me bata tabbaci ya kuma sake matso da ita sosai yana mannata da jikinsa.

Gigicewa tayi sanda taji ta saki ajiyar zuciya tare da tashi ajiyar zuciyar,kunya da wani irin takaici ya lullubeta,abinda taji haduwar jikinsu ya saukar mata ba zata iya shanyeshi ba idan bata bawa zuciyarta daman numfasawa ba......to amma kuma ta dauka a boye ta saki nata ajiyar zuciyar. Fitar sautin ajiyar zuciyar tata ya sakashi ware dukkanin idanunsa a kanta yana dubanta,duba ne na qurilla da son gane meye ya taba wannan zuciyar?.

A gaggauce gama shiryawa tsaf cikin Holland vlisco me asalin tsadar,an xuba mata dinkin manyan mata na buba,ta kuma cika wuyanta da hannunta da kayan ado na gold. Macace me son izza da alfahari,wadda idan tazo guri so samu kowa ya dusashe a gurin sai iya tauraruwarta kadai. Ta tsaya gaban madubi ta tabbatar komai yayi a shigarta sannan ta juya ta dauki wayarta tana nufin fita a dakin. So take ta kasa ta tsare......so take komai zai dinga wakana cikin gidan ya dinga kasancewa saman idonta,bataso tsakanin sabreen ko fu'ad wani yayi wani motsi da zai zarta ganinta da idanunta,wannan karon salon da zata bullo musu dashi na dabanne,har sai ta samu tabbatuwar nasara a gareta. Tanaso da iya dressing dinta kawai ameentu ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ameenatu ta sake tabbatarwa da kanta cewa ita din fa itace mahaifiya ga muhammad jadda.......ba wata mace a duniya ta biyunta.

Cikin takun isa take fita parlor din tana qarewa ko ina na parlor din kallo. Siyan gida a qasashen waje musamman gidaje irin wadannan ba abu bane da za'ayi maganan qananun kudade ba. Abinda ta lura dashi wasa wasa ameenatu ta maida mata yaro saniyar tatsa kenan,taja wata irin qwafa tana samun sofa guda daya ta hakimce a kanta.

Daga inda take ta sanya remote ta kunna tv,tayi sa'a tashar farko ta kamota a inda suke gabatar da abincij breakfast na yaren mutanen qasar china.

Minti uku kacal taji tunaninta ya koma ga kitchen din gidan,tanaso ta tantance dame dame ya jibge musu suke ci?,wanne irin gadara kuma ake gwadawa a wajen?,don haka ta miqe tsam tana maida flats shoe dinta tana nufar kitchen din.

Yau kam sai data shigo sosai sannan idanunta ya sauka a kansu. Mugun gigicewa tayi fiye da jiyan,saboda yanayin data gansu a yau din yafi na jiyan munin gani.

"Na shiga uku ni mariya!" Ta fada muryarta na rawa tana yunqurin juyawa,wanda saurin da take ta matsa a wajen santsin gurin ya debeta ta kusa zamewa,cikin taimakon Allah ta kama murfin freezer ta riqe tana tsaiwa saman qafafunta.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 94



94


Daga shi har sabreen din sai a lokacin suka dawo hayyacinsu. Ita ta fara zamewa ta tsakiya tana raba jikinta da nashi haushi yana cikata. Yana son lalla qarfi da yaji sai ya koya mata dabi'ar da ba tata ba......lallai lallai sai ya sanyata tana yin abinda ba halinta ba.......batasan me zata masa da zai sanyashi nesanta kansa da ita ba. Batason yadda yake warning nata kan bata isa ta raba kanta dashi.......a nata wajen ba wani abu me sauqi a wajenta sama da wannan din......zaman Maldives ya bashi wannan damar,isarsu Nigeria kuma zata yanke kowacce alaqa da yake tunanin ya qulla da ita.

Juyawa tayi tana fita a kitchen din ba tare data sake kallonsu ba. Qirjinta ne kawai yake bugawa da wani irin bacin rai da kuma rudanin abinda ta gani din.

"Wanne irin asiri tayi masa?,wanne irin asiri ne wannan?,maqale mata?" Ta dinga jerawa kanta tambayar da bata batasan amsarta ba. Yadda zuciyarta ke matsewa da bacin rai sai takejin idan tayi shuru tsaf zuciyarta zata iya bugawa......don haka ta soma sakin ruwan sababi.

"Wanne wacce irin masifa ce?,gida sai kace gidan arna?,to wallahi ni bazan lamunci wannan ruwan tantirancin da barikin ba ehe....dole kowa ya gyara zamanshi,ni ba shashashar uwa bace ko banzar suruka,kome mutum yazo dashi ina daidai dashi ne".

"Oops" Abinda fu'ad ya fada kenan yana dafe goshinsa da tafin hannunsa,zuwa yanzu yanajin anya zai iya rayuwa da mutane kuwa muddin yana tare da sabreen din?,anya gidan nan duk da haka bai musu kadan ba?,wannan zaman zai yuwu kuwa?. Duba daya sabreen tayi masa ta zare idanunta tana lalubar hanyar fita daga kitchen din ranta a bace.

Jiya tayi zargin giftawar mutum dama a kitchen din,koda suka fita sukaga sai ita kadaice a falom zuciyarta ta dinga raya mata ita ta shigo......amma ba kasafai ta fiya son dorawa dan adam zargi ba,don haka ta cire abun a ranta,qarshe ma ta gayawa kanta.

"Idanma itace ita ta jiyo......zaiyi mata dadi idan idanunta suka gani ta kuma tayata rabata da maqalallen d'anta. Dab da zata fice a kitchen din yayi caraf ya kamo hannunta yana sake janta jikinsa. Dubansa tayi idanunta na bayyanar da bacin da ranta yayi

"Bayan maamah din ko akwai wanda kakeso ya sake shigowa ya ganmu ne?" Ta masa tambayar da salon gatse kanta tsaye tana duban qwayar idanunsa duk da tsaurin da kallon yake mata.

"Yes" Ya bata amsa shima kai tsaye yana kallonta

"Saura anni.....anni ce akwai ta rage bata gani ba.....ita nakeso ta gani.....don ta hakanne kawai zata fahimci ina tsananin buqatar matata". Har tsakiyar kwanyarta taji yadda ya fidda sautin maganar,wani abu me kama da jin kunya da nauyinsa ya danso kamata,saidai tana ganin ya kamata ta fito masa a mutum don ya sasssuta yadda yake yawan hada jikinsa da nata. Da alama da gaske yake fadi....da gaske yakeson annin ta gani,tunda daga nan inda suke tsayen tana iya jin muryar annin na tambayar maamah

"Lafiya mariya?" Batajira jin amsar da zata bata ba ta soma kokawar qwatar kanta.

"Annin ma?" Ta fada tana ware idanunta cikin kallon me kama da harara harara. Yadda ta yiwa idanun nata kusan kasheshi yaso yi,hannunsa ya miqa a hankali ya nufi gashin idanunta da suka sake zara zara saboda buda idanunta da tayin,abinda yadan saukar mata da tsoro ta rufe idonta da sauri. Kusan dariya abun ya bata,ya zuba mata idanu yana ganin yadda zuciyarta ke bugu sosai tun daga wuyanta zuwa qirjinta dake lullube da hijabi.

"Bakisan harsashin da kika sake jefamin ba da wadannan idanun naki ba......a karo na gaba tsiwar nan zan cire gaba dayanta na maida gurbinta da zazzafar soyayya....." Ambatar soyayyar ya sakata bude idanunta a kanshi,tanason nuna masa tawayenta koda ta hanyar murguda baki ne amma tana kokwanton kada ta jawa kanta,sai kawai ta zabi zame jikinta daga nasa gudun kada annin ta samu isowar kitchen din. Still sake riqe hannunta yayi,ga mamakinta hankalinsa kwance yake janta zuwa falon kaman wani dan jagora. Daga can qarqashin zuciyarsa kuma wani kokwanto da mamaki ne fal ransa. Me yake tunzura maamah din a duk sanda ta gansu haka a tare?,bayan tafi kowa sanin igiyar aure ce ya hadasu?,me yasa yake ganin fushi kwance a fuskarta game da sabreen bayan a nashi tunanin zatafi kowa murna da farincikin kasancewar hakan?. Idan bar ba mantuwa yayi ba.....duka duka ba'a yi watanni biyu ba data masa kyakkyawan warning akan bawa yarinyar kulawa.....meye ya canza wannan?,wannan kadai yana sake bashi signal na AKWAI WANI ABU.

Dukka juriyarta da dakiyarta ta tattara sanda suka iso parlor din,kanta tsaye ba tare da tabi ya banbamin maamah ba ta wuce zuwa dakin anni. Ko wani bai gaya mata ba tasan maamah din ta bita da kallo ne,kallon da ita daya tasan ma'anarsa. Tana qasan shower tana jin yadda ruwan kebin sassan jikinta amma mayataccen qamshin nan nasa bai matsa ko nan da can ba,duk inda ya aza hannunsa a jikinta sai ta tuna idan takai hannunta,ta kammala wankanta tsaf ba tare da tasan yadda suka qare a parlor ba don ba damuwarta bane. Ta jona dryer nan cikin toilet din da busar da kanta,sai abun ya fado mata a rai.

Hala kishi maamah take da ita?,hala maamah tana tsoron kada ta karbe mata yaro?,qila maamah tana zaton mallakarta ce ita sabreen ke niyyar qwacewa?. Siririn tsaki ta saki a ranta tana fadin

"Inda tabi a hankali ma wannan rayuwar tasu batamin ba......dab nake da bar mata d'anta" Tayi zancan cikin ranta saidai idanunta na kallon fuskarta ta madubin dake gabanta. Dif sai kuma tunaninta ya tsaya cak tana sake maimaita furucinta na qarshe.

"Idan shi zaki iya barinsa.....zaki iya barin anni da amna?" Tambayar data tsaida duk wani tunaninta kenan,sai ta samu kanta da neman tabbacin zata iya ko ba zata iya ba?.

"Su nadra huda haneefa sunfi muhimmanci cikin rayuwata" Ta gayawa kanta a gaggauce tana kunna dryer din da hanzari tana son binne wannan tunanin daga ranta.

Idan banda rudin zuciya ma duka duka yaushe ta sansu?,yaushe ta fara rayuwa dasu da har zata shiga shakkar iya barinsu?.

A nutse ya shirya cikin riga da skirt na sakakkun English wears. Basu kamata ba amma sun mata wani irin dan banzan kyau,musamman sata daure gashinta data gyarashi da kyau tsakiyar kanta. Wani qaramin hijabin ta samu ta sake dorawa saman kanta,saidai wannan din da kadan ya rufe saman qirjinta.

Tana jin amna na mata tsiya

"Wannan kwalliyar adda bazan iya cankan nawa hamma zai siyeta ba......kullum sai na dinga jin inama nice ke adda....inama nike da kyanki?" Harararta tayi

"Zageni da kyau amna.....har kina iya cewa wai na fiki kyau?".

" Da gaske nake adda....ke kam ba zaki gani ba tunda a jikinki yake"

"Bazan gani ba dai saboda kin fadi abinda bashi bane.....matsamin kada lokacin walaha ya kubcemin" Ta fadi tana sanya dogon hijabinta,da wannan suka rabu amna ta shiga wanka ita kuma ta tayar da sallar.

Tana shafa addu'o'inta anni ta shigo tana dubanta.

"An gama breakfast.....lokacin cin yayi....ki fara yin gaba kafin amna ta gama nata laqai laqai din" . Kanta ta daga ta dubi anni,tanason gaya mata ba zata fita ba..batason sake fita kwata kwata bare taga matar,maganganunta na dazun sun mata zafi data dangantasu da kafirai,amma kome zatayi tana duba musaddiq ne. Bataso taci gaba da kusantar inda take har hakan ya jawo musu matsala,amma sai taga kaman bai dace ta gayawa anni ba zata fita ba.

Abun sallar ta nade,ta rage hijabin saman sannan ta sanya tattausan bedroom slipper din tana fita a dakin.

Kowa yana saman dining din a zaune kan tashi kujerar,wanda ya rage kawai ita anni sai amna. Cook din na tsaye tana serving kowa da kalar abincin da yafi sha'awa. Hankalinsa yana ga farouq wanda ke gwada masa wani sabon app da suka qirqira don manoma. Musaddiq da saddiq na nasu hiran saidai qasa qasa,sai ya zamana maamah din ce kadai zaune tana qarewa abincin alatun kallo tare da jin bacin ran kudin da aka narka tun daga hiring me girkin zuwa kudin kayan abincin.

Maamah dince mutum ta farko data fara ganinta,kallo daya tak da sabreen tayi mata ta fahimci abinda ke kawo a ranta. Batason irin wannan kallon haka......saidai ta bawa kanta tabbacin indai wannan dabi'ar na tare da matar zai wahala su rabu lafiya. Ba komai zata iya dauka daga gareta ba,abinda ta dauka a baya ma ya wadatar.....yanzun tana jinta 'ya me cikakken 'yanci ne da bata qarqashin juyawar kowa.

Cikin jikinsa yaji alamun wanzuwarta a wajen,ya daga kansa a natse yana duban sassan da take tahowa. Fuskarta tayi masa kyau kaman ba dazu ya ganta ba,tafiyarta me cakude da nutsuwar nan tana tsananin burgeshi,tun a wani lokaci can baya ba tare da yasan da hakan ba.

Kasa dauke idanunsa yayi daga kanta,yana fatan ta dubeshi da fararen qwayar idanun nan nasa. Ta gefe yaji an taboshi,sarai yasan farouq ne don babu me masa haka saishi

"Ina fata ba idanunka ne a kanta ba?" Ya soma tambayar farouq din ba tare daya dauke idonsa a kanta ba ko g waiwayo ya dubeshi ba. Can qasan zuciyarsa dariya ta taso masa ya danne,shi bama ta dalilin tabashin yake ba,abinda ya dameshi kawai kada ya kalle masa mata?. Ya manta saman table din akwai mamansa?,sam kaman baisan da wanzuwarta ba?,ita yake qoqarin ankarar dashi,don tun fitowar sabreen din maamah din ta fahimci mayataccen kallon da fuad din yake binta dashi,abinda ya sake tunzurata,ta dinga kokawa da zuciyarta da kuma fuskarta akan ta shanye amma ta gagara yin hakan.

"Ni bazan kalli haram ba.....don soon halal dina na tafe......amma dai ka gyara idanunka akwai iyaye a wajen" Shaf har kuma ga Allah ya mance da maamah din a wajen,furucin farouq din ya ankarar dashi,sai kawai ya zare idonsa akan sabreen din yana dojewa kallon maamah,don shine hanya daya da zai kaucewa tuhumarta ko bacin nasa ran.

"Ta yaya zamu rayu a wajen nan?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin idanun maamah a kansa saidai yaqi yarda ya kalleta ko sau daya,sai ya jawo tab din gabansa yana ci gaba da duba taswirar da suke magana akai kafin fitowarta shi da farouq.

"Matsa kusa da mijinki kiyi serving nashi". Furucin anni kenan daya sauka a kunnensa bayan fitowarta daga daki tayi joining nasu a dining table din.

Sosai maganar ta anni tayi masa dadi,ya murmusa can qasan ransa yana addu'ar a daren yau ta bashi matarsa. Yana jin yakai taki maqura tako ina,muddin kuma akaci gaba da tafiya a haka baisan me zai faru ba.

Satar kallonsa tayi kaman yadda maamah ta saci nasu kallon. Har ta buda baki zatayi magana sai wata zuciyar ta tunasar da ita,wawa shike saurin fasa abinda ke cikinsa,sai taci gaba da juya abincin tana noticing kowa.

Ganin baiko kalli sassan da take ba bayan annin tayi magana sai ya bata qwarin gwiwar miqewa,ta matsar da kujerar dake kusa dashi a hankali ta yiwa kanta wajen tsaiwa.

Cikin takatsantsan take zuba masa komai,don ya tattara komai ya ajiye ne ya zuba mata idanu yana bata order zuba kaza,rage kaza,kaza kadan zaki zuba. Wannan yaso daburtata,don sau biyu yana kai hannu yana riqe serving spoon din da take zuba abincin dashi da zummar kada ta zuba masa mayonnaise da man farfesun naman kan ragon daya dan taso a sama. Ita daya sai kuma maamah suka fahimci yana sane yake hakan,don duk riqewar sai ya hada da hannunta cikin nasa.

Da qyar ta samu ta kammala zuba masa din,sannan ta aje komai a gabansa. Dubawa take tana neman plate din da zata zuba nata abincin,duk da tasan zai wahala ta iya cin abin arziqi,don ya sanyata a gaba da idanunsa da suke sake zama marasa kunya marasa jin nauyin jama'a. Tun asali ta tsani yawan kallo,to amma shi din ta fahimci ya qware sosai wajen wannan dabi'ar,abinda yafi bata mamaki shine......kana iya wuceshi baisan waye kai ba.....kana iya gama sabgoginka a kusa dashi baima tantance me kakeyi ba......amma ita me yasa yake sha'awar sanya mata idanunsa?.

"Zauna muyi squatting.......wannan abincin ina zan kaishi?" Ta tsinci muryarsa katsam yana fadi gami da gyara mata kujerar dake kusa dashi.

Yadda wuta ta dauke mata haka wuta ta daukewa maamah,kaman kuma hadin baki wajen duka sai ya dauki shuru,sake tura kujerar yayi kusa da ita,bata da wani option sai janyota da tayi ta koma a sanyaye ta zauna a kai. Tayi zaton shikenan,zai tsaya iya haka ne,a'ah......sai daya sake janyo tashi kujerar ta zama kusa da ita sosai har gwiwoyinsu suna gogar na juna.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 95

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*

*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*

*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_*

*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*



*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*

*lace*

*kowanne nau'in shaddodi*

*yadika na maza da mata*

*mayafai*

*lafaya*

*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana*

*sarqoqi da agoguna*

*under wears*

*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*

*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?_*

*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*

*Sassauqan farashi me ban mamaki*

*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_*
_______________________________


95



62 / 119