Author : Huguma Category : Complete Novels
saceta ba tare data sani ba.
Bakwai da rabi ta bude idanunta a hankali,qamshin jikinsa ya tunasar da ita a jikin wanda take. Murmushi ya qwace mata,ta furta
"Alhamdulillah" Tana tuna daren jiya,yadda ya baibayeta da wata zazzafa kuma tsumammiyar soyayya......tana kuma tuna yadda dare daya ubangiji ya tsamesu daga taskun da akaso jefasu,amma har yanzu ta gaza ajiye tunanin Who's the one behind the scenes?.
Bataso ta zama mace me yawan sanya ido tambaya ko bin qwaqwafi akan kowanne lamura,wannan ya sanya bata tambayeshi akan hakan ba,ta sani koma meye ba wannan ba kadai,akan komai da komai ma idan ta cancanci taji zai gaya mata.
A hankali a hankali ta dinga zame jikinta daga nashi. Daren jiyan tasan baiyi wani bacci me yawa ba,ta dade tana jinsa yana mutsu mutsu kafin baccin ya daukeshi.
Tas ta samu nasarar zare jikinta daga nashi,ta kuma maida gurbinta da pillow,saita waiwaya tana kallon fuskarsa kawai. Wata fuska dake dauke da tarin nutsuwa da kamala.....wata fuska dake da wani irin sassanyan kyau da zata iya rantsuwa bata taba ganin irinsa ba.....wata fuska da Allah yayi mata baiwar kwarjini da haiba. Samun kanta tayi da addu'ar Allah yasa yaranta suyi kamanninsa.....zatafi son haka akan su dauko nata kamannin.
A hankali ta dora hannunta saman mararta da yau takejin kaman an ajiye mata dutse a ciki,ta motsa labbanta tana karanto addu'o'in tsari sannan ta sauka a hankali daga kan gadon.
Dakin ta kintsa duk da dauda ko tarkace,still ma akwai masu aikin da zasu shigo suyi maka duk abinda kake da buqata. Ruwan zafi ta kunna a dispenser incase ko zaya buqaci wani abu,duk da shima akwai kitchen da zaka kira direct a kawo maka komai da kake buqata. Wanka takeso tayi,amma saita zauna ta tura list na breakfast din da suke buqata zuwa kitchen sannan ta dawo ta shiga wanka.
Tunic blouse ta saka da straight leg trousers,sannan ta saka madaidaicin Malaysian hijab da ya qawata fuskarta da wani irin calmness.
Luggage dinsu ta gyara ta maida cikin cabinet,a hankali ta waiwayo sai idanunta suka sauka cikin nasa. Mamaki ya kamata,tun yaushe ya farka amma baiko motsa ba bare ya nuna mata?,wataqila a gabansa ta saka bra ta saka kayanta ta taje gashinta duka.
"Kinyi kyau" Ya furta yana motsa labbansa a hankali,wanda banda tabi motsin bakin nasa ba lallai ta gane me yace ba.
Kunya ta sakata kau da kanta ta soma takawa zuwa wajen sofa ta rusuna tana fadin.
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya my super girl?" Ya fada cikin kulawa yana jin kwadayin jin dumin jikinta da kuma qamshinta gaba daya,tsumin daya tayar musu jiya yana qoqarin kunna kanshi a yanzu.
"Alhmdlh...jikinka fa?" Ido ya lumshe mata sannan ya bude
"Am fine and good....tunda gani ga duniyata" Murmushi ta sake sakar masa. Shi duka hakan bai masa ba,ya fahimci idan ya barta kuma a banza wannan kyan saidai ya ganshi a ido,don haka yace mata.
"Zaki taimakeni ki daga ni?".
" Why not?" Ta fada da tattausar muryarta tana isa gareshi. Gadon ta haura,kaman jiya ta bashi hannunta saiya noqe kafada yana kallon idonta.
"Ki hada hannu biyu.....baki da wani qwari.....ina tsoro kada ki Fadi nayi laifi ace da fuska biyu nayi hakan" Yadda yayin ya bata dariya,saidai ta karkada kanta.
"Zan iya"
"Really?" Ya tambaya yana daga girarsa,saita jinjina masa kai alamun bashi tabbaci.
Kai tsaye ya miqa mata hannunsa guda daya,ta cafe a nata,saidai kuma tashin farko tayi kyakkyawan masauki a qirjinsa.
"I love you" Ya fadi da sauri cikin wani karyayyen amo cikin tsakiyar kunnenta.
Murmushin dole ya qwace mata,ta yadda da gaske da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,ta kuma sallama fu'ad daga jiyan har yau wayau ne kawai yayi mata,don haka bata da sauran inkari itama ta motsa pink lips dinta da suka fusgi hankalinsa tace
"I.....love you.....more" A rarrabe da wani sound daya sanya ya gaza jurewa yakaiwa lips dinta kiss. Janye fuskarta tayi tana cewa.
"Asibiti ne fa hamma.....yanzu ida....." Bata qarasa ba aka murda qofar,abinda ya sanyata hantsalawa gefe tana neman maboya. Maida qofar akayi da hanzari aka rufe,muryar farouq ta bayyana.
"Na shiga uku....wallahi daga yau bazan sake zuwa asibitin nan ba". Maganar tayi tsananin bawa sabreen dariya,ta cusa kanta a kafadar fu'ad tana boye dariyarta.
"Rabu da tuzurun banza......waya aikeshi?...sa'idon farouq yafi qarfinsa"
"Hamma baka kyauta ba gaskiya".
"I'm only selfish when it comes to you.....zakiyimin wanka?" Ya fada a narke a kuma shagwabe. Ido ta zaro waje,tanason duban idanunsa tana tsoron kada ya narkata da kallon nan nasa.
"Please" Kai ta girgiza.
"Why?" Ya sake jefa mata tambayar a tausashi. boye fuskarta ta sakeyi cikin pillow.
"I can't.....bazan iya kallonka ba". Wani murmushi yayi mara sauti yana fidda idonsa shima
"Am all yours babe....alright,hadamin komai i will do it by myself" Hakan taji yafi mata,saita tashi da sauri ya wuce toilet din don ya gama shiryawa da wuri kada subar su farouq a parlor suna jira,ya bita da kallo yana jin kamar zuciyarsa ce a waje take tafiya da qafafunta.
Har cikin toilet din ta rakashi sannan ta fito tana ja masa qofar. Tana tunanin yadda zata fita su gaisa da farouq da wanne ido zata kalleshi taji an bude qofar toilet din.
Ido ya zuba mata ba tare da yace komai ba,har sai daya gama tsumata da kallonsa yadda yakeso sannan ya motsa labbansa.
"Towel madam" Janye kallonta tayi zuciyarta na qara gudu,tanajin kaman akwai towels a bandakin,amma bata da energy din masa bayani,don haka ta taka a hankali hannun sofa ta dauko masa wani.
Miqa masan da zatayi ya hado harda hannun nata ya jawota cikin toilet din ya maida qofar ya kulle.
Sabon wanka ya sakata ta sake bayan ya gama jagwalgwalata. Tabbas banda ciwon hannunsa ta Tabbatar barna za'ayi a asibitin ba jinya ba. Ya aza mata wani nauyi da ta sakejin ta gaza dubansa harta kammala shiryawa ta canza wasu kayan zuwa riga da wando saqar india. Rigar ta kawo gwiwa haka wandon budadde ne sosai,yalwataccen mayafin kayan ta ware tana rolling dashi,sai ya tako a hankali ya tsaya a bayanta.
Hannunsa guda dayan ya dora saman qugunta,ya daidaita tsahonshi da nata hana dora fuskarsa a kafadarta.
"Ki bani lokacinki.....ko zana rayu a duniya.....ki bani tabbacin zamana dake kinji masoyiya....nidai nidai nida nake son ki nafi kowa jinki a zuciya" Murmushi ya qwace mata,ta rufe idanunta tana miqa hannunta ta shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Muryarsa ta mata wani mugun dadi,asalin sound din yana tasowa daga parlor dinne yana ratsowa ta cikin dakin,tsakaninsu musaddiq batasan waye yakejin waqar ba,shi kuma yabi waqar da tattausar muryarsa da tafi ta mawaqin dadi.
"Am starving" Ya fada yana sansanar wuyanta. Muryarta da mugun sanyi tace
"Muje parlor na baka" Kai ya girgiza da sauri yana dauko wayarsa dake saman table din ya soma budeta.
"Farouq ya fusata.....idan kikaji yana jin waqoqi definitely ya fusata......yana kewan fannah dinsa" Ya fada yana dan jin wani sashe na zuciyarsa yana tausayin farouq din,don ya yarda da gaske soyayya mahaukaciyar abace....kewar masoyi kuma wani abune daka iya kassara mutum komai jarumtarsa.
Murmushi me sauti ya kubcewa sabreen,batace komai ba don fu'ad da farouq sunfi kusa.
Ya cika da mamakin ganin tarin uban miscalls din ambassador khaleed mustapha,ba kiran bane ya bashi mamaki,saboda yana expecting hakan dama,yawan adadin kiran da ya masa na fitar hayyaci shine abun mamakin. Qaramin tsaki yaja yana share dukkanin kiran,ya lalubi number saddiq.
"Shigo dasu ciki" Kawai yace yana kashe wayar. Cikin second uku ya turo ya shigo dakin da wani kyakkyawan basket. A girmame ya gaida sabreen ya gaida fu'ad yayi masa sannu da jiki,sannan ya ajiye basket din ya juya ya fice.
Mayafin data rola ya saka hannu ya cire pin din sannan y wareshi tas yana dubanta.
"Let me behold this beauty....i want to take a look at this loneliness....i wannan see this " Ya qarasa fada yana shafar sumarta zuwa gefen fuskarta. Zamewa tayi tana murmushi,ta qarasa gaban basket din ta tsugunna a nutse ta fara zuba komai yadda ya dace,har zuwa sannan kunnuwansu na sauraron waqoqon soyayyar da farouq ya ware volume abinsa yanaji. Fes waqar ke fita da baituka na zallar soyayya,su duka kunnuwansu suna jinsu,har ta gama ta tako a nutse tana juyawa a hankali da wani irin nutsatsen taku dake bayyana surarta da zubin halitta me kyau da Allah ya azurtata dashi.
Sosai ta ajiye plate din a gabansa,ta zauna kaman yadda taga yayi ta tanqwashe qafafunta. Hannu ya saka ya cire spoons din,ya gyara hannun rigarsa yana fadin.
"Oya bismillah" Idanunshi zube a kanta. Zobanta ta canzawa yatsa sannan ta saka hannun nata kaman yadda ya buqata.
Wani irin shuru ne ya ratsa tsakaninsu,sai kallon kallo da yaren zukata da suke fitarwa ta cikin idanunsu,irin yaren daya gagara zuciya ta furta.
Zuwa lokacin waqar abdul hassan ta meerah ta soma tashi. Komai sunaji kaman a nan aka kunnata.
Kowanne baiti dake fita daga bakin mawaqin sai yakejin kaman ya wakilceshi ne.....tamkar furucin da rarraunanniyar zuciyarsa ta gaza bawa bakinsa daman furtawa ne yake fiddasu daga zuciyar tasa. Ita dinma waqar ratsata take,ta daga fararen idanunta tana kallonsa. Ya dakata kwata kwata da cin abincin,ita yake kallo. Karon farko data yarda da cewa,da gaske ne idan soyayya tayi qarfi masoyi yana iya qoshi daga jin yunwa daya ganin masoyinsa kawai(kin taba fuskantar hakan?....musamman irin yunwar da batayi worst ba....da gaske ne hakan yana faruwa).
Qarar wayarsa ta katsesu dukkaninsu shida ita,ya sauke nannauyan numfashi yana saka qwayar idonsa kan wayar.
Ambassador ne,sam bashi da niyyar sauraronsa a lokaci na kusa har haka.....saidai kuma yana jin baida lokacin da zai bashi da zaiyita damunsa har hakan,wannan ya sanya ya daga kiran ba tare daya dauki wayar ba ya sakata a hands free yana maida idanunsa akanta don bai gaji da kallon kayarsa ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 130
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
130
"Ex ambassador khaleed mustapha" Kalma ta farko da fu'ad ya fara fada bayan ya daga wayar.
"Ranka ya dade sir......tuba muke.....tuba muke,ayimana afuwa,ayi mana rai" Ambassador khaleed ya fada cikin matuqar qanqantar da kai da kalmasa harshe.
"Wani abu ya faru kenan" Fu'ad ya fada cikin halin ko in kula,abinda ya sake daga hankalin ambassador kenan. Yafi kowa sanin illar wannan shariyar tasa,har gwara ya fito maka a mutum,yayi maka duk yadda yakeso,yayi maka kalar hukuncin da yaga dama.
"Ranka ya dade sir.....ina me baka afuwa......ina me baka haquri......don Allah.....don Allah a dubeni,ayimin rangwame". Gyara zamansa yayi tare da yiwa sabreen inkiyar ta matso taci abincin. Kai ta langabe masa,sai ya matsa da kansa ya soma diban abincin ya miqa mata yana tambayar ambassador.
"Hala bakasan abinda yarinyarka take aitawa ba.....bama a kaina kadai ba,har kan mutanen da take taqamar matsayinka da matakin da kake kai sun tsaya mata sun kuma siya mata ticket na cin mutunci da qasqanci ga kowa?". Ya masa tambayar sanda sabreen ta saka hannu ta karbe spoon din ta maidashi bakinsa,ya bude bakin ta saka masa abincin sannan ya mata sign na itace next da zataci.
Shuru ambassador yayi,yana juya irin amsar da zai bawa muhammad jadda. Yasan wayeshi farin sani ma tass kuwa.......yi masa qarya tamkar tafka wani babban kuskuren ne,hakanan gaya masa gaskiya kuma bazai taba zama mafita ba.
"Ko ka sani ko baka sani ba wannan kai zaka bawa kanka amsa......".
"Am really sorry sir......ayimin afuwa.......na yarda da kowanne hukunci ya kamata kayi mata koka dauka a kanta,na aminta da hakan ranka ya dade sir". Fareeda dake durqushe waje daya ta daga kanta da sauri,a mamakance tana duban mahaifinta. Shi da kansa yake sallamawa me jadda ita?,shi da kansa yake miqata izuwa gareshi kan yayi duk kalar hukuncin da yaga dama?.
Ci gaba yayi da cin abincinsa yana kuma morewa kallon duniyarsa. Kaman bazaice komai ba....kaman bazai amsa ko ya sake magana ba......har ambassador ya fara sarewa gami da fidda rai kafin yace.
"Zabin dawowar dukiyarka qwaya daya ne tak........tsaffin kudaden qasar nan da ka danqaresu a France.......zamuyi yarjejeniyar dawo dasu gida kuma qasata Nigeria don amfanin al'ummar qasar". Wani razani ya sake kama ambassador,wanne irin mutum ne fu'ad din?,kamar wani maye me gani har hanji?,kudade ne masu ciwo nauyi da yawa da yayi imanin koda iya su kadai iyalinsa suka tsira sun rabauta,amma har ya akayi ya ankara dasu?.
"Ina fata kana saurarena?" Fu'ad ya tambayeshi yana cirar tissue yana goge bakinsa don abincin ya isheshi haka.
Sai daya goge gumin fuskarsa da habar rigarsa sannan yace.
"Ina jinka......na fahimta"
"Good......secondly diyarka......rashin kyautata tarbiyyarta wannan matsalarka ce.....damuwarka ce.....haduwarka da Allah kadai ya isheka barazana.......tayi attempting kasheni......inaso ta gaggauta fita da kanta media television da magazines ta tabbatarwa duniya da tayi yunqurin aikata hakan,tayi apologize nawa......tayi na matata.....ta tabbatarwa da duniya cikakken mutunci da darajar da iyalina ke dashi.......wannan muqulli ne kawai na budewar daskararru da kuma qwatattun dukiyoyinka......hukuncin yunqurin kisan kai kuma ita da hukuma.....sunsan matakin da yafi kamata su yanke a kanta".
Ba fareeda kadai ba.....hatta da sabreen hukuncin ya mata nauyi,tayi zaton iya hakan da zatayi ya wanke duk sauran laifukanta...
"Amma sir.......na dauka duka hakan zai wakilci kowanne laif......"
"Khaleed!" Fu'ad ya kirashi a tsawace cikin fushin da har sabreen dake zaune a wajen sai data daga kai tana kallonsa,tana kallon yadda kamanninsa ke sauyawa alamun bacin rai ya fara tasiri a zuciyarsa.
"Magana ake ta kisan kai bisa ganganci da niyya......magana ake ta bata mutunci da daukan hayar gidajen jaridu suyi batanci ga iyalina......kasan nawa ta kashe don kawai a buga sunan matata ta sunna da sunan KARUWA?,waye yake bata kudin?,a ina take samosu?,a gaban waye take dukka kalan rayuwar da taga dama?......wannan hukuncina ne ba wai shawara bace ko alfarma.....kana da right na cewa ba zatayi ba gaba daya......wannan ya rage naku.....dont contact me again indai akan wannan issue dinne.....i finalized the matter"
"Please sir......please....."
"Khaleed,Not my problem to solve......Could you please stop calling me?". Shuru ambassador yayi,ya tabbatar ba wani abu da zai sanya fu'ad canza wannan hukuncin nasa,abinda ya bawa fu'ad daman yanke kiran yana jan wani dogon tsaki kaman zai tsinke harshensa.
A tausashe ta karbe wayar,ta sakata a DND mode ta ajeta gefe. Kamo lallausan tafin hannunsa tayi ta saka cikin nata tana lalubar qwayar idanunsa,cikin nasara ta samosu,saita kafeshi da idanunta tana kallonsa tana kuma murza tafin hannun nasa.
Cikin minti biyar ya sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,abinda ke tabbatar mata ya samu relief na bacin ransa. Hannunta ta dora saman cikinta tana nake fuska a shagwabe.
"Suna tsorata sosai idan abbee dinsu yana cikin irin wannan fushin......sunce na bashi haquri,na gaya masa komai me wucewa ne,komai watarana zai zama sai labari". Murmushi ya subuce masa yana lumshe idanunsa,ya saka hannunsa ya dagota,ya dorata saman cinyarsa,tura hannunsa yayi saman cikinta a nutse ya aza tafin hannunsa akai.
"Dukiya jarrabawa ce me zaman kanta....kaman yadda talauci take shima jarrabawa ne,duk wanda Allah ya jarrabi bawa dashi akwai nasa kalan qalubalen.....ki fadi musu daddynsu yana nan yana fighting akan yadda zasu rayu cikin aminci ba tare da sauran qaya ba akan hanyarsu.....i love them more than i love myself....."
"I hope I'm still your number one?" Ta fadi a narke tana kyabe baki. Dole ta sanya wani murmushi me sauti ya subuce masa,ya kama kumatunta yadan riqe yana girgizawa.
"You're filled with jealousy......madam.....ke din DUNIYATA ce fa gaba daya". Murmushi tayi yana boye fuskarta a kafadarsa.
" Kiraminsu Musaddiq" Ya fada yana komawa normal mode dinsa. Zamewa tayi a jikinsa