Author : Huguma Category : Complete Novels
mata,ta tako a nutse ta samu gefan sabreen din ta zauna tana qoqarin sakin fuskarta.
Ashar maamah keda muradin narka musu ganin suna hira qasa qasa a gabanta amma bakin yaqi buduwa,game kula kuwa zaiga yadda idanunta suka kada sukayi jajur,daga amna har sabreen ba wanda ya kula a cikinsu,don sabreen din nata qoqarin jan amna da hirar da zata sakata sakin jiki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
154
"Shekararta nawa tana fama da hawan jinin nan sir?" Likitan daya gaji da ganin abun mamaki tsakanin kwanaki ukun ya tambayi fu'ad. Kafadunshi duka biyun ya dage yana son gano dalilin tambayar.
"Ba wasu shekaru bane,idan ya dade wata daya....."
"Hamma duka baifi sati uku bafa" Musaddiq ya fadi yana duban fu'ad. Dauke dubansa fu'ad yayi ya maida ga likitan alamun
"Kaji amsar tambayarka?".
Kai ya jinjina cikin matsanancin mamaki. Tunda yake kaf a tarihin aikinsa bai taba ganin mutumin da jininsa yahau har haka kuma yake iya ci gaba da rayuwa ba. Matakin hawan jininta yakai mataki na qarshe,wanda daga wannan stage din saidai mutuwa bama stroke ba.....uwa uba kuma tun a kwanakin da aka kawota yake ta qoqarin ganin jinin ya sauka amma yana nan a inda yake,ba wani ci gaba. Ya gwada duk wata basira tashi da dabarun aiki amma abun ya cimma tura.
"Sir......munyi mata dukkan abinda ya dace amma ba wani ci gaba ko nasara koda alamunta kuwa,abinda yafi bani mamaki shine......yadda hawan jinin yayi mata wata mummunar rafkiya karo daya,nayi zaton tsohon ciwo ne ma,sa'annan duk wani hanya na sauke jinin wallahi yaqi sauka,abinda yake dada bani tsoro shine,ci gaba da qin saukar nasa zai iya zame mata sanadin matsaloli kala daban daban,don a yanzun haka tsoro nake kaman qodarta tana son harbuwa,bansan me yake faruwa ba,nidai ban taba cin karo da case me kama da nata ba tsahon shekarun dana dauka a bakin aiki.......amma abinda nake tunani.......anya ba wani abu babba data sanya a ranta?,ko wani goal da takeso ta cimma a rayuwarta?,wani matsala dake bata mata rai?". Wani murmushin takaici ne ya qwacewa fu'ad,wanda tunda suka shigo office din yana tsaye kawai hannayensa zube a aljihun wandonsa.
Likitan yayi tambaya a muhallinta,duk duniya shike da amsar wannan tambayar tasa,saidai abune da bai shafeshi ba,koda ya shafeshi ma labarin zai zame masa wani baqon labari da ko a duniyar hikayoyi bai taba jin irinsa ba. Uwa nason mallakar d'a kota mallaki abinda ya mallaka kota halin qaqa?,uwa nason tarwatsa rayuwar 'ya'yanta ta hanyar rabasu da abokan zamansu?......rabo na jikokinta dake manne a mahaifar surukarta kuma fatanta yabi rariya?,BURIN UWA TARWATSA RAYUWAR 'YA'YANTA ta rabasu da uwa da uban goyonsu da suka zamewa rayuwarsu suttura?,wacce irin uwa kenan wannan?,baya ga wasu boyayyun al'amura da fadinsu ma baida dadi koda a baki ballantana ga kunnuwa?.
"Me take buqata?,me ya kamata ayi?" Ya yankewa likitan dogon tunani da zallar mamakin daya fada
"Tana buqatar kulawa ta wurwuri......kulawa ta gaggawa saboda gudun rasa wasu bangarori na jikinta,kamar idanunta kunnuwanta ko qoda ko kuma hanta".
"Yanzu me kake gani za'ayi?" Ya sake tambayar likitan,yana jin wani tsoron girman Allah yana kamashi. Amsa kuwwar muryarta yakeji a shekarun baya yanzu haka.
"Shi hawan jini ai baka rabuwa dashi sai ya lalata maka ji gani qoda ko hanta.......kai kam gaskiya kaman bakayi sa'ar rayuwar duniya ba?,daga wannan sai wancan?" Tayi maganar tana tsaye a kan abban nasa sanda duniya tana tsaka dayi mata zaqi da gard'i. A lokacin shi kuma yana tsugunne a gabansa yana qoqarin ballo masa magungunansa saboda hakin daya sarqeshi ba qaqqautawa.
"Ina ganin me zai hana ku fita da ita waje?,suna da kayan aikin damu bamu dasu,zasu sake bincikarta sosai ko akwai wani abun daban da yake jawo wannan matsalar bayan......."
"Kayi magana da dukka asibitin daya dace ace an kaita din,ka tura adadin abinda za'a buqata daga dawainiyar asibitin da komai ka sanarmin ta waya" Ya fada kawai a gajarce.
Yana ji a jikinsa komai daya kama na neman lafiyarta zaiyi mata shi,bayan ya tanqwara zuciyarsa wadda kowanne taqi tana tuna masa da yanayin nata action din akan mahaifinsa sanda yake jinyar ajali. Ya sani idan zai biya ta wannan ko paracetamol maamah bata cancanci tasha ba ta hannunsa.....to amma har yanzu huduba da tarbiyyar anni tana yawo a jininsa.
"Uwa uwa ce fu'ad,duk lalacewarta ba wata madadinta" Wannan maganar ya jima da haddaceta daga bakin annin.
★Cikin sati guda komai ya kammala na fitar da maamah din qasar Egypt. Fu'ad da kansa yace musaddiq yayi zamansa su samu hutu sosai da amna,don itama amna din har yanzu yana ganin kaman bata gama sakin jikinta ba bata warware gaba daya ba. Sanda yake shirin tafiyar sabreen ta sameshi a daki,ya daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta. Sosai cikinta yake sake bayyana kanshi kowacce rana. Sosai cikin ke qara mata wani kyau,shi kansa zamanta a jikinta kyau yake mata. Hannuwansa ya harde yana kallonta da sassanyan murmushin nan nasa. A kwanakin gaba daya ta sake sauya masa,wani abu me sunan tattali da kulawa da bai sanshi ba yake samu daga gareta. Wani irin respect take bashi,bai taba jin bashi respect yana burgeshi ba kaman a kanta,ta maida kanta qasansa sosai,komai zatayi tana nuna ita din a qarqashinsa take,ita din mallakinsa ce.
"Sun hanaki bacci halan so abbee dinsu suke jira yazo tayasu hira" Ya fada yana bude mata hannayensa. Bata tsaya wani bata lokaci ba ta taho ta fada ciki,ta kuma lafe abinta. Ba wani guri da takejin tsananin aminci kaman qirjinsa,ba wani guri da take ji take kuma samun cikakkiyar nutsuwa irin qirjinsa,wani guri ne na musamman da takejin duk duniya bata da kamarshi.
"Na gama shirya nawa kayan fa hamma" Ta fada a shagwabe. Dan dagata kadan yayi daga jikinsa yana duban fuskarta.
"Zuwa ina kenan adda?".
" Egypt mana" Ta fada a shagwabe tana maqale kafada. Kai ya girgiza yana sakinta sannan ya fara takawa yana barin wajen
"No.....zaki zauna a nan har mu dawo,kinsan yanayin da kike ciki ai ko?,ko kin Manta wani hutun nake shirin baki ma?". Batace masa komai ba har ya qare zancen,saita sauke hannayenta data harde a qirjinta tana takawa a hankali zuwa inda yake zaune yana basarwa ta hanyar qirqirar wani aikin.
Dab dashi ta zauna har jikinsu yana gogar na juma,tasa hannunta ta jawo fuskarsa zuwa inda take kaman yadda shima yakeyi mata.
"Nasan me kake tunani,nasan abinda yasa ka fadi haka kuma.....amma kada ka manta.....har yanzu maamah uwa ce.....kuma nidin nayi alqawarin riqe hannunka gam,zamuyi tafiya bisa tafarkin rayuwa a tare,da dadi ko babu dadi right?". Kansa ya daga a hankali yana dubanta,ya rasa wadanne irin mutane haka Allah yayi masa rahama da ni'ima dasu?,sam basa duba sharri sai alkhairi a tare dashi,duk da irin uwar da Allah S W T yayi masa jarrabawa da ita.
"Koda maamah zata kasance me laifi a waje na.....nikam na yafe mata,har abada babu wata uwar da zata iya haifamin muhammad jadda sai ita.....ta kuma haifamin din,ina da abinda zan iya saka mata dashi?". Idanunsa ya lumshe kawai yana jin yadda soyayyarta ke tsatstsaga jikinsa. Addu'ar mace ta gari da yayi Allah ya bashi ma sama da abinda ya roqa din,yana jin kunyar idanun kowa......yana jin kunyar sanyasu su yiwa maamah wani hidima bayan dukka tarin sharrance sharrancenta a garesu,wanda har zuwa yanzu shikam yana ji a a jikinsa maamah din bata hau sirad'al mustaqeem ba da gasken gaske.
Hannunta ya riqe sosai cikin nasa da wani irin taushi.
"Na gode sosai my world......na gode duniyata". Murmushi ta sakar masa
"Ba godiya tsakanina dakai.....kome nayi maka kafi qarfinsa a wajena".
Tafiyar sai ta kasance me sassauci a tare dashi,don kasancewar sabreen a tare dashi cikin kowanne motsi a rayuwa ba qaramin qarfafa masa gwiwa yakeyi ba. Sun isa Egypt bisa jagorancin Dr awwab,an kuma gabatar da maamah ga qwararrun likitocin asibitin,wadanda suka dauki kwanaki suna dukkan bincike da gwaje gwaje.
To sakamakon dai guda daya ne,hawan jini ne me tsanani da har a Egypt dinma dai bai sauka ba,sai kuma wani abu data qulle a zuciyarta da suke ganin kaman shima yana barazanar taba lafiyar zuciyarta.
Sabreen ta girgiza matuqa,jikinta kuma ya sanyaya,ta qara cika da mamakin maamah,ta kuma sake sallamawa lamarinta,ta qara yarda da imani da yaqinin lallai wanda Allah ya shiryayye......ba wanda kuma ya isa ya shiryar da wanda Allah ya batar. Daga idanun maamah da kallon da take binta dashi duk da kalar hidimarta gareta ta karanci ba wani rusunawa ko nadama a tattare da ita......qaddararren ciwon daya zama jarrabawa game hankali ne kawai yayi mata cikas ya hanata duk wani sukuni.
Daga qarshe sun yanke zasu ci gaba da bata kulawa har na tsahon wata guda suga abinda hali yayi. Da taimakon qwararun nurses dake kula da maamah din aka soma dorata akan magunguna da therapy kala kala. Duk da akwai masu kula da ita din sabreen bata zauna ba,saidai ko yanzun sabreen ce zata bata abinci ba zata karba ba. Da idanu take kafeta,wani abu yana sake mata ciwo,duk sanda ta kalleta zuciyarta tana gaya mata.
"Yarinyar tayi winning a kanki,ke gaki a zaune saman wheelchair ko yatsarki baki iya dagawa". Rana ta farko da zuciyarta ta gaya mata haka bayan sun gama zama da ita ne sun wuce masaukin da suke kwana.
Kuka sosai ta dingayi,hawaye shabe shabe daya na bin daya,hawayen zallar baqinciki faduwa da kuma asarar da tayi.
Hakanan nurses din dake kwana da ita suka taru a kanta suna lallashinta,amma taqi tsaida hawayen tamkar ma suna tunzurata. Haqurin da suke bata ma sake bata mata rai yakeyi,ta rantse inda bakinta yana magantuwa su kansu da sai sunji magana iya magana.
Jirigi guda musaddiq da amna,farouq da fannah......saddiq da huda wadda ta soma murjewa ta fara qiba suka shigo Egypt duba maamah din.
A ranar taga baqar ranar da zata iya cewa kaf fadin rayuwarta bata taba ganin irinta ba. Kowa yana zaune da qugunsa......yana takawa da qafafunsa....hannu kai da qafufuwansu dama bakunansu gaba daya suna aiki amma banda ita?,banda nata?,ita kadai dai komai a kanta ya qare?. Wannan tunanin ya sake sakawa ta dinga fitar da hawaye,har numfashinta ya sarqe saida likita ya shigo ya mata allurar bacci.
"Har yanzu akwai wata danqararriyar damuwa a ranta.....kuma indai bata cireta ba treatment dinmu bazaiyi aiki ba,jininta bazai taba sauka ba.....tana da ciwon tun asali tayi wasa da magungunanta har sai daya zame mata haka,qodarta ta fara nuna alamun failure.....duk yadda zakuyi ta cire damuwa a ranta". Bayanan da likitan yayi musu kenan. Dukkaninsu sunsan wani abune me suna gaibu tilasta maamah ta cire damuwa a ranta,damuwar da dukkaninsu suka kasa gane ta meye idan ka dauke fu'ad sabreen da musaddiq.
A nasu hasashen it's high time ace maamah ta cire komai a ranta,so ba damuwar dabi'unta bane na baya,saidai fu'ad sabreen da musaddiq sunsan cewa HALI ZANEN DUTSE......BARIN HALI KUMA SAIDAI MUTUWA.
*_TURQASHI.....WAI ME KARATU NACE BA.....WAI SAI YAUSHE NE MAAMAH ZATASAN ANNABI YA FAKU?,SAI YAUSHE NE HALINNAN ZAI CANZA?_*155
★Cikin wata gudar nan da suka dauka mata ba wani kalar treatment da ba'ayi mata ba. An kashe kudi sosai anyi amfani da engine da fikira da fasahar dan adam a kanta amma ba wani canji ko qanqani da aka samu. Duk wata lalurarta saidai ayi mata,bata tsinanawa kanta komai don ko yatsanta bata mallaka ba,bata isa ta juyashi ba bare sauran sassa na jikinta. Idanu da kunnuwan ne kawai suke aiki,banda su za'a iya cewa komai a jikinta ya tsaya a aiki idan ka cire ZUCIYA.
Wannan zuciyar dai da annabi yake mana gargadi da jan kunne a kanta,wannan zuciyar dai da yake gaya mana idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci dukkan jiki ya baci. Wannan zuciyar dai wadda da ita ake gwada nagartar bawa.....wannan zuciyar dai wadda da ita ake ganin qarfin mutum,ba qarfi na jiki ba ko qarfi na dukiya ko qarfi na mulki ko qarfin iko ba.
(Ubangiji don girman al'arshinka kasa mufi qarfin zuciyarmu,ya Allah kasa mu mallaki zukatanmu don hasken fuskar manzan Allah,wallahi wallahi duk wanda kaga yayi qarko to tabbas ya mallaki zuciyarsa ne......yafi kuma qarfinta,ya haneta aikata abubuwa masu yawa daba daidai ba,dukkaninmu kowa yasan daidai yasan kuma ba daidai ba,kubutacce a cikin mu shine wanda ya mallaki zuciyarsa yaji tsoron Allahnsa akan komai na duniya da lahira,yake kuma aiki da nasa hankalin).
Dole hakanan don ba yadda za'ayi mata suka tattara suka koma gida nigeria da sauran tarkacen kayan therapy din da za'a iya siya mata,wadanda zasu dinga motsa mata gabbanta,kaman yatsun hannu da sauransu.
Ma'aikata dole ya sanya aka samo masa ya dauka,wadanda zasu kula da ita da komai nata. Wankanta,cin abincinta,sallarta tsaftar kanta data jikinta. Already tana da masu aiki dake tsaftace gidan suyi girki,akwai guard kuma a gaban gida da farfajiya masu kula da gidan gaba daya.
Rayuwa duk yadda kayi haka za'a yi maka,Allah da kansa yace wadancan kwanakin sune muke juyasu tsakanin mutane,kwatankwacin karin maganar bahaushe da yake cewa YAU GAREKA GOBE GA DAN UWANKA.
Wata babbar dama ce ta samu ga wadannan ma'aikata da aka dauka,sabbi da kuma wasu daga cikin wadanda suke cikin gidan. Bude cin karensu babu babbaka sukayi,kowa yayi abinda yakeso a sanda yakeso,a kuma yanayin da yaga dama. Bata da bakin magana sai idanu,sai tarin baqinciki da takeji kaman zai kasheta.
Idan tayi bayan gida ko fitsari,muddin fu'ad ko musaddiq basa nan sai ta gane kurenta. Don zasu barta da abinta sai sun gama sharafinsu sannan suzo su wanke su gyarata bayan sun gama tsaki toshe hanci da harara da baqar magana. Tanaji tana gani duk wani abu da yake mallakinta ita keda iko dashi sunayin yadda sukaga dama,da sunji alamun zuwan musaddiq ko fu'ad harma da sabreen......yanzun nan zasu dawo gabanta su zauna suna nan nan da ita. Takan yawaita kallon fu'ad din,tanason gaya masa irin abinda suke aikata mata amma ba wannan damar,ba bakin magana,tana ji tana gani zasu gama abinda zasu yi mata su fice,su kuma su dora daga inda suka tsaya.
Duk abinda mutum yake akwai ranar da dubunsa zata cika,khairan au sharran......muddin kaga ka dade to Allah yana qara maka lokaci ne yaga ko zaka tuba?,ko zaka gyara kurenka?.....ko zaka gano kanayin ba daidai ba?....kaman yadda bahaushe yace komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girma gona akwai kunyar qarshe.
A irin wadannan ranakun Allah ya kawo sabreen katsam. Basuyi zaton zuwanta ba,don ba lokacin zuwan nata bane. Yanayin da taga sun watsar da maamah din ya daga hankalinta sosai. Hawaye kawai ta dinga yi tsoron Allah ita kanta yana sake shigarta,wato dan adam ba kowa bane.....kaman yadda yake ba'a bakin komai ba. Girman kai dagawa da mugunta dukka idan kaga mutum yana yi Allah ne ya ara masa lokaci,dama ce wadda idan yaga dama ya qwaceta shikenan ta tafi kenan har gaba da abada.
Ko a mafarki akace mata maamah din zata dawo haka ba zata gasgata ba......ko da wasa aka ce mata akwai lokaci me zuwa kaman haka ba zata yarda ba......matar dakeji da dukkan wani izza taqama da gadarar qarfin iko,yau gata zaune waje daya,ko ruwa bata isa ta bawa kanta ba idan ba'a bata ba.
Kaf ma'aikatan gidan ta tattara,bayan ta gama jin ta bakin amintaccen malam sa'adu,wanda ya gama karantar halin kowa. Da kanta ta yanke hukunci ta sallami dukkan wanda lambarsa ta fito na baqin hali da mugunta. A ranar tayi kuka tayi kuka,kukan tausayin kanta a matsayinta na 'yar adam wadda itama haka tana iya kasancewa a kanta. Tun fu'ad na lallashinta har ya rasa ta ina zai bullo mata. Ya dafe habarsa kawai yana kallon yadda tasa ciki a gaba tana kuka. Kuka akan maamah?,duk sanda ya tuna da wannan abun yana bashi mamaki.
Baiyi zaton koda mutuwa maamah tayi ba hakan zai d'a d'a sabreen da qasa ba
"Ya ilahi......wacce irin zuciya ce da ita?" Ya tambayi kansa da kansa yana sake jinta har cikin qasusuwansa. Ya tabbatar kyakkyawar zuciya kawai baiwa ce......baiwa ce da ba kowa Allah yake yiwa ita ba,baiwar da tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi.
"Ya isa haka sabrrrr.......ya isa.....babies dinki karsu dauka nina taba musu maamah fa" Ya fada cikin damuwa. Shi kansa ba jin dadin ganin maamah a haka yakeyi ba,to amma yasan cewa duk wani