A Duniyata Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   57 / 119

168K to 171K   out of 356.9K words

da babu wani abun burgewa qwaya daya tattare da ita.

"Tambayoyi ne zan miki su da bansan qwaya nawa bane,amsarsu kawai nake da buqata.......samun amsoshinsu sune kubutarki.......ki manta ubanki waye da farko.....sannan kema ki manta wacece ke......kiyi tunanin makomarki da abinda zai iya faruwa dake.......ki manta kin bawa mariya ahmad kudade don ta mallaka miki Muhammad fu'ad....." Ya fadi maganar yana jin wani d'aci yana tasowa daga qasan zuciyarsa,yana jin zuciyarsa kuma ta matse waje daya. Da wani irin zafin nama ta bude idanunta a kansa tana mamakin ta yaya yasan da wannan deal din?.

Sai daya hadiye abinda ya taso masan sannan yaci gaba da magana.

"Baki da wani ko wani abu da zai iya mallaka miki wannan muhammadun har abada" Ya sake fadi yana nuna qirjinsa da yatsarsa.

"Koda babu ameenatu sabreen a gefe na......ballanta tana cikin DUNIYATA tana cikin rayuwata....na tsere miki tserewa ta har abada.....bama keba,duk wasu mata ire irenki......WAYE YA BAKI DAMAN KIRAN MATATA DA KARUWA?.....WAYE YA BAKI WANNAN LASISIN?" ya mata tambayar farko da ita tafi tsaye masa a wuya fiye da kowanne abu.

Wata irin wutar kishi ta taso mata,ta kuma yaudareta da cewa ya zauna ne yaci fuskarta kawai......ta yaya tana cikin jerin masoyansa zai zauna yana mata tambaya akan wata mace da batajin ta fita komai?.

"Au bakasan karuwa kowa yake kiranta ba?,bakasan karuwa ka aura ba dama?". Ta fada tana danne tsoron dake taso.mata,saboda yadda zuciyarta ke qarfafa mata gwiwar idan yaga tsoro a idanunta to tabbas ta karya lagon kanta da kanta.

Labbansa na qasa ya cije yana kausa kansa daga fuskarta,kalamanta suna qonashi da wani irin zafi.

"Jordan" Akwai yace yana dunqule hannunsa waje daya,saboda bayason yakai hannunsa kan qazamin jikinta.

Taku daya jordan ya qaraso bayanta,wanda kwata kwata bata kawo komai a kiran nasa da yayi ba,ba zato ba tsammani taji an take yatsun qafarta an kuma murjesu da kyau har sai data fasa wata qara tana jin azaba tana ratsata,qarar yatsun kuma suka baqunci kunnenta da qas....qas.....qas...daya bayan daya,tabbacin qasusuwansu ne suke rarrabuwa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

EID MUBARAK TO YOU ALL

ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEN SUMMA AMEEN

SHUKRAN JAMEE'ANπŸ™ŒπŸ½πŸ™ŒπŸ½πŸ™ŒπŸ½πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 87


87


"Ka dagani......ka sakeni!qafata.....qafata" Ta fada a mugun rude kuka da fitsari dukka yana qwace mata lokaci guda,sake take dayar yayi sosai yadda itama yasan zataji a jikinta ba alamun tausayi sam a tare da jordan din. Sai daya kalli fu'ad sannan ya bada damar ya matsa baya,ya dauke qafarsa yana cewa.

"Kiyi magana dashi da manners.....kiyi magana dashi in a polite way......idan ba haka ba kafin bincike ya kammala duka sai na kusa dake sun kasa ganeki". Ko jordan bai fadi haka ba ta fahimci abinda ke shirin faruwa kenan.

" Shut up!" Fu'ad ya daka mata tsawa yana kallon yadda ta sauya launi tun karon farko.

"Wannan shine ya baki qwarin gwiwar buga sunana dana matata a jarida?.....bakisan ta fiki daraja ba?,ta fiki mutunci......ta fiki duk wani abu da mace ke jin tana taqama dashi ba......su wadanda suka baki shawarar aikata hakan basu gaya miki waye muhammad jadda ba?!" Ya jefeta da tambaya yana jin wani tururin bacin rai yana taso masa.

Tayi matuqar rudewa,ta kuma girgixa qwarai da gaske. An gaya mata....ma'aikatan ma sun gaya mata,da qyar ta samu suka yadda zasuyi aikin. Sun jaddada mata waye jadda din,amma a sannan idanunta basa ji basa gani,burinta kawai ta bata mata suna......ta tona mata asirin da shi kansa baisan dashi ba,ta saka masa shakka da kokwanto me yawa a kanta.

"Su waye kika aika cikin gidana har dakin matata!?" Ya sake mata wata tsawar da sai da taji 'yar qwarya qwaryar gudawa ta hadu a cikin ta ta cure lokaci guda,glass doors din dakin kaman zasu tsage saboda yadda suka amsa.

Tashin hankali......kada dai ace ta taka sahun barawo?,da yaushe kuma aka shiga gidan nasa?......wata shigar akayi bayan wadda mahaifiyarsa tasa ayi?.

Da sauri ta fara girgiza kai tana dubansa da sabbin hawaye,don gaba daya yatsunta bata jinsu a gangar jikinta.

"Ban sani ba wallahi.....bani bace.....saidai.....saidai....." B'am bakinta ya bame ya kuma kasa kama sunan maamah kaman yadda take da marmarin shaida masa ita ce. Tanason gaya masa mahaifiyarsa ce,ga sunan a bakinta amma ta kasa furtashi waje,ta dinga kokawa da harshenta amma kaman wadda gabbai ko rassan maganarta suka samu matsala.

"Saidai me?" Ya tambayeta yana tsareta da idanu yanason samun ragowar tabbacin da yakeson samu.

"Na gidan jaridan......nice" Maimakon wancan bayanin ta sake bashi yaqini akan wancan tana sunkuyar da kanta,baqinciki da bacin rai yana cika zuciyarta. Me ya sameta ta kasa gaya masa sirrin da baisan dashi ba?,idan ita yasa an mata irin wannan mummunan dukan ita kuma da take uwarsa tana son taga ya zaiyi da ita.

Idanu ya zuba mata,yana ji a jikinsa akwai saura......akwai abinda yayi saura.....akwai abinda jikinsa yake bashi game da ita wanda ya rage bata fada ba.

Saman qafafunta ya maida kallonsa bayan yaja kujerarsa nesa da ita. Ta sauqaqawa kanta wahala......don ba qaramin bugu yaso Jordan yayi mata ba da qattin qwanjinsa. Yaso ya rage mata adadin yawan haqoran dake a bakinta ko zasu zame mata tunasarwar shigarta hurumin muhammad fuad anan gaba,ya kuma zamewa 'yan baya izina. Qafar ta tasa tayi suntum cikin qaramin lokaci,alamun mummunan targade ko karaya sun samu wajen zama. Banda ita din mace ce baya jin iya wannan dukan ya wadatar dashi,amma duba jinsinta yakeyi.....idan yace zai zazzage dukka muguntarsa a kanta ba zata wanye lafiya ba. Ya maida kallonsa ga fuskarta da har ta suntume,kamatunta sun tasa sun soma hayewa saboda munin marin daya sauke mata,idanunta har sun fara yin ciki

"Zan baki dama ta qarshe da zaki fice daga rayuwata.....ki kuma sanyawa ranki baki taba sanin wata me suna sabreen ba.....fu'ad kuwa ki saka a ranki a saqe saqen mafarki kika taba saninsa.......saidai kafin sannan......na baki wata guda kacal kije kiyi jinyar qafafunki da fuskarki,zan sake waiwayarki......ba kuma waiwaye na arziqi ba. Sa'arki daya labaran ba inda suka fita.....yau da newspapers dinnan sun fita...." Sai ya kada kai daga hagu zuwa dama

"Ko buzunki ba za'a samu ba ina me tabbatar miki da wannan" Ya qarasa fada yana nunata da yatsa.

"Kije kiyi jinya kafin amsa tuhuma ta gaba......ruwanki ki gayawa babanki......ruwanki ki rufe bakinki wannan matsalarki ce......amma inaso ki rubuta ki ajiye.....idan ma kina da plan na guduwa wani guri da kike tunanin zaki samu tsaro to ki sani.......lahira ce kawai zaki tafi ki kubuta daga tuhumar muhammad jadda" Daga haka ya miqe tsam yana takawa yana barin dakin.

Har yakai qofa sai ya dakata,ya juyo ya watsa mata wani kallo sannan yace.

"Daga yau.....na yanke duk wata alaqa tsakaninki da maamah......idan kuma baki yarda ba ko kina doubting akai......ki sake koda kiran layin wayarta ne.....koda sau daya ne" Ya furta yana daga doguwar yatsarshi dan manuni,sannna ya sanya qafa ya fice abinsa.

Tunda tazo duniya ba'a taba gwada mata azaba irin wannan ba......tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin qasqancin d'a namiji ba irin na jadda. Inda wanine yau yayi mata wannan abun ta tabbatar bazaisha ba a hannun daddynta dama ita kanta. To amma.muhammad jadda fa?,ta sani farin sani cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. Alfarmarsa ta wuce duk yadda ake tunani,duk arziqi da alfarmar ubanta da take taqama dasu bai wuce yaron jadda ba. Ta sake tsinkewa da lamarinsa sanda daddynta da kansa yake bata labarin yadda fu'ad din ya soke masa wata kwangilar millions of naira,wanda gwamnatin tarayya taso bashi amma jaddan ya fahimci cin hanci da rashin kyan aikin yayi yawa. Ya fusata a sannan baisan waye jaddan ba,ya kuma bazama da zummar a nemo masa wayeshi a hada musu zama....saidai randa ya soma yi masa ganin farko ya kuma zauna dashi da qyar ya qwaci kujerarsa ta ambassador. Har qasa yakai yana hurwa da neman ya rufa masa asiri,ya barshi ne bisa sharadin komai zai dinga tafiya bisa adalci da amana,ya kuma tsaya da iya muqami da dukiyar da Allah ya bashi. Tun daga ranar suka yiwa juna farin sani,labarin da daddyn nata kuma ya bata ya sanya mata tsananin son mallakar fu'ad din. Tanason namiji me qarfin izza da mulki gami da iko takowacce fuska,a duk inda ya tsaya yayi magana za'a dakata a saurareshi,a duk inda yayi umarni dole za'a bi.....to amma sai gashi dare daya komi ya watse komi ya wargaje mata daga hannunta.

"Zan iya barinsa kuwa?" Ta tambayi kanta sanda wata zuciyar ta fara mata saqa da mugun zare.....zuciyar ta fara ayyana mata daukan BAQAR FANSA da kowanne irin hukunci daya kamata ta zartar kawai a kansa.

_uhmmmm,nidai nace wanda baiji bari ba yaji hoho_


Ido farouq ya zuba masa sanda yake dawowa wajen. Sai a sannna hankalinsa ya kawo abinda fu'ad din yayi masa. Cikin dakewa da kuma basarwa yace yana zama.

"Sarkin noma.....na dawo" Sarai yasan magana ya gaya masa,amma ganin ma ya zaro wayarsa ya soma lalubar wata number sai kawai ya qyaleshi da duk abinda zaice dashi,illa dai yace masa.

"Ina fatan baka rabata da numfashinta ba"

"Ta samu wannan tsiran saboda batayi musu ko gardama ba" Yana kaiwa nan ya saka wayar a kunnensa yana magana da daya bangren.

Ya kusa mintuna talatin yana amsa wayar kafin daga qarshe ya rufe da

"Aikinka na kyau CP.....good job,akwai zuwaira......akwai harira ko something hajja......yes......yes" Daga haka sukayi sallama.

Zazzafar numfashi ya sauke yana aje wayara a gabansa gami da watsa idanunsa saman glowing beach din da ruwansa ya fara komawa sea of stars,hakanan yashin dake kwance a wajen ya soma glowing sosai kaman an warwatsa taurari a qasan wajen.

"Wai wanne irin kame kake ne dude?.....har mutum nawa zaka saka a kulle maka?". Idanunsa da suka masa nauyi saboda tunanin daya cika zuciyarsa ya janye ya maida kan farouq,ya kafeshi da idanu sosai saboda tunaninsa ba'a wajen yake ba. Gaba daya tunaninsa ya ta'allaqa a kanta,yana jin a yadda yanayin wajen ya masa kyau da dadi kamata yayi ace tana tare dashi yanzu haka a gefansa,ya shaqi daddadan qamshin jikinta.....lallausar fatar nan tata me wani irin dumi me bawa zuciya da gangar jiki nutsuwa.

"Duk wanda ya taba kiranta da karuwa......duk wanda ya taba yi mata sharri ko qazafin zina ko neman maza......bazan qyale kowa ba farouq". Kallonshi sosai farouq yakeyi yana kallon yadda idanunsa suka jirkice da wani irin giyar soyayya me qarfin gaske. Ya karanci wani muguwar kwankwada fu'ad ya yiwa giyar soyayyar sabreen din,ta kuma bugar dashi fiye da yadda ya kamata.

"To amma ai sai ka hada da kanka da kanka a kullewar ko?" Ya fada yana dage masa girarsa duka biyun sama. Kallon days jefeshi dashi ya tabbatar masa b'arna fu'ad zai masa,ya sanshi yasan abinda zai iya aikatawa,don haka yaja kujerarsa baya da sauri yana dariya. Qwafa yaja yana gyada kai,baisan abinda yakeji ba tabbas farouq da bai qara masa ciwo akan ciwo ba.

Barinsa yayi yaci dariyarsa me isarsa kafin ya kira sunansa.

"Yes sir" Ya amsa masa har yanzun lamarin fu'ad da gaske yana bashi dariya. Yana sassauta masa ne kadai saboda yasan bashi da wani gurin samun sassaucin sai wajensa.

Sai daya ware idanunsa a kansa sosai sannan ya tashi ya zauna yana dubansa.

"Me yasa soyayya take haka ne?" Yayi tambayar sounding serious......saidai kuma abun ya bawa farouq dariya amma ya danneta.

"Me tayi maka kuma?" Ya tambayeshi yana matse dariyarsa da kyau. Kasa magana yayi don baisan ma yadda zai kwatanta masa ba,sai kawai ya dora hannunsa akan qirjinsa da yakeji zuciyarsa na azalzalarsa akanta. Ya dauki wasu sakanni kafin ya iya buda bakinsa a hankali da wani irin calmness.

"Bansan adadin Lokacin da na dauka ina sonta ba......amma inaji a jikina ba sai bayan abun nan ya faru ba na fara sonta.....kaman wani dadadden so ne daya saba dashi.....na taso dashi,aka kuma haifeni dashi". Sosai maganganunsa ke ratsa farouq......da gaske ne fu'ad din yana sawun mutanen da suke iya boye so ba ko su daukeshi da sauqi ba.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 88




88


"Kayi qoqarin koya mata yadda zata soka........ta fahimceka.......tasan ainihin waye kai da kuma rayuwarka,daga nan komai zaizo da sauqi......zan baka kowanne kalan goyon baya da kakeso.....nayi maka alqawari......amma nima kayimin uzuri daya alfarma daya" Ya fada yana kama hannun fu'ad din.

"Fadi muji dude" Ya fada yana sake jin qaunar farouq da kimarsa tana ratsashi.

"Duk sanda naga taka kalar haukan soyayyar ka yiwa Allah karka hanani inyi dariya......i swear wallahi kai babanmu ne ta nan.....nayi imani da gaske irinku masu shuru shurun nan kunfi kowa zurmawa da iya rikita mata". Danawa bayan hannun farouq dake cikin nasa duka yayi yana zame hannunsa sannna ya miqe.

"Ka lallabani farouq......kasan Allah zan daga aurenka?".

"Iyeeee.....eh ai kayi haka mana,tunda kai ka samu kanka ka zazzage lalurarka ta shekara da shekaru...."

"Idan bata haukatani ba farouq kai zaka haukatani" Kawai yace dashi yana yin gaba abinsa. Da sauri farouq din ya tashi yabi bayansa,don yasan tsaf zai iya tafiya ya barshi a wajen. Tuni suka gaya masa an biya kudin komai da komai tun kafin suzo ma,harda qarin wasu kudin spare da yayi ragowa idan suna buqatar qarin wani abun.



β˜…Karo na kusan barkatai ya qara daga fuskar wayarsa ya kalla yana hadiye wani abu me tauri a maqoshinsa. Kwanaki kusan takwas kenan rabon daya sanyata a Idaninshi,tun ranar da sukeja Vaadhoo Island shi da farouq bata sake bari yaga face dinta ba.

Da farko yayi tunanin zai jure,kwana daya biyu uku hudu ana biyar din yaji bazai iya ba,yakai bango kaman numfashinsa na shirin masa qaura. Ba ganin face dinta ba kuma jin muryarta?. Koda ya shiga dakin da nufin gaida anni tanajin alamunsa take shigewa duvet ta kwanta abinta. Ya fuskanci kaman tana garkuwa ne da anni wadda ba lallai ta fahimci abinda yake faruwa. Yana jin nauyin anni yana jin kunyarta,amma ta fara kaishi bangon da yakejin yana dab da ajiye kunyar a gefe.

Wayar amna ya soma kira yana sanyata ta bata wayar. A kunnensa yakejin sanda amna take bata wayar amma saita karba ta kife taci gaba da sabgarta. Idan ya kira amna ta wayar anni tana bashi tabbacin wayar na hannunta,sai mintuna suyita tafiya babu ko motsinta bare tarinta. Da yaga haka saiya koma kiran annin yasa a bata,still dai haka take masa,kwanaki uku kenan yau tana masa haka,adadin kwanakin da lissafinsa yake gaya masa jibi ne yarjejeniyarsu da anni na zuwa daukota daga macca.

Bazai iya jure wannan ba......da kansa ya sanya order din wayoyi har guda biyu aka kawo mata,Falcon supernova iPhone 6 pink diamond edition irin wayar dake hannunshi kenan. Sai iphone 4s elite gold. Dukkaninsu wayoyi ne masu tsananin tsada da ba kowa yasan da zamansu ba,saboda ba kowa keda qarfin tattalin arziqin mallakarsu ba. An qera jikinsu ne da diamond da kuma gold masu tsananin daraja.

Yana jin cewa idan ya bata wayar ya zamana tana da tata mallakin kanta dole idan ya kira ta daga din.

Har ya gama shirin kwanciya tun goma na dare amma kewar nan da yakeji ta hanashi kwanciyar,ya tashi ya sanya pyjamas dinsa light blue da suka amsheshi sosai ya sanya flipp flops dinsa ya kwashi wayoyin ya wuce dakin anni.

Tana zaune abinta qasan carpet dauke da littafin hadisinta da yafi mata dadi akan komai a yanzun. Tayi kyau kaman wata 'yar baby cikin milk color din Indonesian hijab me haske sosai daya fidda fuskarta.

Tunda taji sallamarsa wani abu ya tsarga mata,ya shammaceta sosai,yau ko qamshin turaren nan nasa da takeji bata jishi ba.

"Barka da dare anni...." Ya fada cikin girmamawa yana zama saman sofa din dake opposite dinta,kansa tsaye yau duka idanunsa suna kanta. Ji yakeyi kaman yayi shekara takwas ne bai ganta ba bawai kwana takwas ba. A yau din har anni ta ankar da hakan,tadan dauke kai kaman bata gani ba cikin jin nauyi tace.

"Barka kade me babban suna.....mun yini lpy?"

"Alhamdulillah" Ya amsa mata yana maida dubansa ga amna data tsugunna tana gaidashi.

"Lovey dovey.....barka da dare"

"Barka kadai hamma". Sak tayi,bata da niyyar magana kowacce iri ta hadasu,amma gaisuwar anni data amna ta daureta,dole ta gyara zamanta daidai sannan tace

"Barka da dare,ina yini?" Kowanne gaba ta jikinsa sai data amsa sautinta,bai taba sanin yayi masifar kewar muryarta kawai bama sai yanzu,amma duk da haka ya dake yana hade fuska.

"Bazan amsa ba.......sau nawa ina kira a wayar amna nace ta baki?.....sau nawa ina kiran wayar anni a baki saiki ajemin waya.....saboda kin rainani?". Dukka duf dakin yayi,nauyi ya kama anni da kunya......yayin da sabreen din wata masifaffiyar kunya nauyin anni da fargabar kada ya ballo

57 / 119