Author : Huguma Category : Complete Novels
a hankali ta miqe,ta taka tana fita zuwa parlor din.
Dukkansu suna zaune,kowa kusan wayace a hannunsa yana dannawa. Farooq kuma ya koma amsa waya. Rusunawa sukayi suka gaidata cikin girmamawa,ta amsa musu da danjin kunya da nauyi sannan tace musu.
"Hamma yana kiranku" Miqewa sukayi suna wucewa ciki,banda farouq daya daga musu hannu alamun yana zuwa. So samu su shiga ciki duka ta zauna ita a nan,don wala'alla wata magana zasuyi data shafesu,to amma farouq yana nan,ita kuma yanzu kunyarsa takeji,dole ta juya ta koma dakin.
Yana zaune still saman kujerar,ya miqe qafafunsa hannunsa da cup din ruwa yana sha. Gaidashi sukayi shima cikin girmamawa kaman yadda suka saba,ya jiye glass cup din yana amsa musu.
"Anni bata shigo ba?" Ya tambaya yana dubansu.
"Eh sai zuwa anjima kadan,abba ne yadan tashi da ciwon kai".
"Subhanallah,amma ba wanda ya gayamin a cikinku?" Ya fada cikin dan nuna bacin rai. Idanu kawai suka hada kowa ya sadda kansa,kota yaya zasu gaya masa bayan ko ganinsa basu samu yi ba.
waya ya dauka ya kira abban,suka gaisa yaji jikin bawai tsanani ko yawa yayi ba,yace suyi xamansu yau su huta,tunda komai yana tafiya lafiya alhamdulillah,sannan sukayi sallama ya aje wayar yana dubansu.
"A cikinku akwai wanda yayi magana da wani cikin abokai ko 'yan uwa sanda zamu baro madeena mu sauka a nigeria?". Daga kai sukayi suna dubansa,don tambayar tashi ta musu wani iri. Kai ya jinjina musu.
" Eh ina nufin ko a hira ba wanda ya bawa wani full details na ranan dawowarmu da inda zamu sauka?"
"Full details?" Musaddiq ya tambaya yana kallon hamman nasa. Kai fu'ad ya jinjina yana maida hankalinsa a kansa.
"Eh" Fu'ad ya jaddada masa.
"Akwai hamma" Musaddiq ya fada abinda ya faru a wancan ranar yana dawo masa. Ido fu'ad ya lumshe sannan ya budesu.
"Waye?" Ya tambayeshi kai tsaye.
"Maamah ta bani wani number na tura mata details din.....ban kawo komai a raina ba hamma......ban kuma yi tunanin akwai wata matsala da hakan zai haifar mana ba" Ido sosai ya zubawa musaddiq din,yana jin kanshi ya masa nauyi da ambatar sunan maamah a lamarin. Tsoro ya kama sha da fargabar kada sunanta ya fito cikin jerin sahun sunayen mutanen da suke da hannu a faruwar al'amarin fa.
"Me yasa zakayi haka musaddiq?......me yasa baka kiyaye wasu abubuwa?,kana tunanin ni dakai saddiq farouq amna dama duk wanda yake under jadda family ordinary human ne?" . Shuru yayi jikinsa yana yin sanyi. Tun sanda abun ya faru wannan abun yake a ranshi,jiki da zuciyarsa duka suna gaya masa akwai alaqa tsakanin abun da kuma wancan address din daya bada,wannan ya sanyashi tilastawa kansa zama tuno digits din daya turawa address din,ya kuma sake zaunar dasu tsaf cikin kansa.
"Baka riqe name din dake jikin contact din ba....koda bincike ne ta yaya kake tunanin za'a iya yinsa?" Fu'ad dake kallonsa da takaici ya fada.
"Na riqe digits din...." Shuru ya danyi yana ci gaba da kallonsa
"Really?" Kai ya jinjina masa,sai ya waiwaya ga saddiq.
"Ya baka digits din ka turawa saleem.....kace masa injini" Ya fada yana maida bayansa jikin kujera yayi relaxing.
Wani irin bacin rai ne yake ratsashi,maamah itace silar faruwar wannan abun?,to hadin baki sukayi da fareeda kenan wajen kasheshi ko goyon baya ta bata?,hakan yana da alaqa da hallarar kowa a asibitin da nuna zallar damuwarsa a kansa amma banda ita?. Kanshi ya samu da girgizawa,yana jin cewa sam maamah din ba zata aikata haka ba.
"Amma ta taimaka wajen kauda abbanku daga duniya?" Tambayar da tazo daga qasan zuciyarsa kenan,ta kuma sake taso masa da wani irin bacin rai.
β
A hautsine take duban mahaifin nata bayan ya gama gaya mata hanyar mabudin arziqinsa da yake hannunta,bisa tsari da kuma dokar da fu'ad ya bayar.
"Yanaso yayi humiliating dina ne abba......ta yaya zan fita gaban 'yan jarida na tonawa kaina da kaina asiri?....hakan kuma ba yana nufin na wanke kaina da kaina bane?,tamkar kenan na bawa shari'a daman yankemin hukunci da daukan mataki a kaina ta sassauqar hanya?" Ta fada tana jin cewa aikata hakan wani abune da bazai yuwu ba.
"Kina tunanin kina da wani sauran amfani a wajena ne fareeda muddin dukiyar dana kwashe shekara da shekaru zata salwanta ta sanadinki?......ruwanki kimin hanyar dawowar arziqina nasan hanyar xa zaki samu Sasaaucin hukunci.....ruwanki kiqi ni kuma da hannuna zan miqawa hukuma ke......daga rana irin ta wannan lokaci kuma ki tabbatar na cireki daga jerin 'ya'yana.....sunan.Khaled mustapha kuma ya saraya daga wuyanki.....na haramta miki amfani dashi haramtawa na har abada".
"Bazanyi abinda yace ba daddy.....hakanan kaima dukiyar ka zai dawo hannunka" Ta fada tana rarumar wayarta.
Number maamah take nema,hanya guda daya tilo da take tunanin zatabi don samun warwarewar komai.
Daidai lokacin da mota ke tsula gudu da ita saman kwalta,hankalinta yayi nisa yayi kuma zurfi a tunanin tun sanda ta baro wajen boka. Kora yayi mata fata fata akan kada ta sake zuwa masa muddin da maganar data shafi taurari biyu ne sabreen da fu'ad. Ya gama aiki a kansu har abada saidai ta nemi wani.
Sanda ta lallabashi da batun wata buqatar daban tazo da ita ba irin ta baya ba.....buqatarta dankwafar da cikin sabreen yayita zama a mararta ba tare daya girma ba bare a haifeshi,wannan kuma zai zama silar da zai zama karo na farko kuma na qarshe data samu ciki da fu'ad din,a sanya masa shakka kan qaryar ciki tayi dama tun asali.....maganar rabuwarsu kuma ita zataji da sauran.
Har ya soma buga qasa yayi wani zabura da saida qoqunan gabansa gaba daya suka hantsila,yaja baya yana gurnani da wasu surutai kafin daga bisani ya dubeta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 131
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
131
"Kinsan aikata hakan daidai yake da kiran mutuwarki da kuma gaggauto da ajalinki tu lokacin mutuwarki baiyi ba?" Sosai abun ya daure mata kai itama,tana kuma buqatar qarin haske.
"Kamar yaya?,ban fahimta ba?". A fusace yake.magana wannan karon fiye da fusatarsa ta dazu.
"Wannan yaran da suke cikinta......bake bama......duk wanda keda qudurin cutar dashi to tabbas ajalinsa yake kira......fiddasu daga mahaifarsu ko hanasu wanzuwa suyi rayuwa irin ta kowanne jariri kuwa,daidai yake da kiran ajali yayin da yake nesa da ruhi.....ki fita daga harkar wadannan taurarin......suna dab da karo da naki taurarin.......tazarar dake tsakaninku kadance,faruwar hakan kuma daidai yake da LALACEWAR RAYUWARKI!.......SAURA QIRIS!.....KI KAUCE KI BASU HANYA.....BA WANI ABU ME CUTARWA DA YA ISA YA TARE HANYAR SHAWAGINSU!" ya fada a tsawace yana nunata da yatsa.
Tashin hankali!,kanta taji ya wani irin sarawa.....muddin ya kasa mata wannan aikin duk duniya bata jin akwai wanda zai iya yinsa
"Kayimin rai.....zan ninka maka abinda ya kamata a......"
"Dakata!" Ya fada a gigice.
"Wannan aikin ba kudi yake buqata ba.......aiki ne na tsira da rai........ran da muddin aka barshi ya dulmiya babu me iya fitowa dashi........KIBAR DA'IRATA HAR ABADA....KARKI SAKE DAWOMIN DA MAGANAR TSARARRUN TAURARI BIYU".
Wannan tunanin yana mata shawagi kiran fareeda ya shigo,ta saka idanunta akan kiran da wani irin yanayi,mamaki ya sanya batayi wani dogon nazari ba ta daga kiran tana sakawa a kunnenta.
"Ina kika shiga fareeda..... Ko kina shirin janyewa ne saga qudurinki?" Ta fadi tanajin kamar idan ta hada kai da fareeda din nasara zata zo mata da gaggawa cikin sauqi,dole tana da buqatar me tayata wannan yaqin.
Ba kalar neman da bata yiwa zuwaira ba amma ta kasa samunta......duk inda take tunanin idan taje zata sameta ta aika ba labarinta,abun yana daure mata kai.
"Ban fasa ba.....kuma sauka daga kan nufina ba.....hasalima tsakiyar aikin da nakeyi aka samu matsala da kuskure". Kanta ya sake sarawa,ta zauna sosai tana riqe wayar a kkunnenta sosai.
" Me ya faru kuma?". Sai data gyara muryarta da kyau sannan tayi magana.
"Nasa anyi attacking na matarsa.....cikin rashin sa'a aka sameshi.....yanzu haka anyi freezing komai na dukiyarmu......yasa kuma an dakatar da dad daga muqaminsa......yana maganar saina fito nayi iqirarin nina aika a kasheshi.....na bada haquri a media sannan zai sakar mana komai.....abinda yasa na kiraki.....inaso ki sakashi ya warware komai......ya janye kuma komai.....muddin wani abun ya sameni duk wani mmuradinmu zai tsaya cak.....don ina da babban shirin da zai kauda mana damuwoyinmu ni dake gaba daya".
Dif maamah din tayi,kwanyarta suna juya mata maganganun fareeda. Haka kawai taji hankalinta kamar ya kasa kama maganganun fareeda din,kaman akwai wani abu da ba daidai ba.
"Fareeda.....bansan qasar da suka kaishi ba.....yanzun haka matarsa ke dauke da cikin da nakejin gwara na nakasa da wanzuwarsa a tare da ita.......bansan inda suka ajeshi ba".
"Taiwan......yana wani asibitu na Taiwanese a taipei......ki kirashi tabbas zaki sameshi".
" Ki dakaceni tukunna.......fu'ad baya cikin mazan da akewa gaggawa haka kuma su karba da sauri".
"Me kike fada mariya?!" Fareeda ta fada a tsawace,a yanayin da take ciki bata qaunar sharhi qarin bayani ko dako......isar da saqonta da cimma burinta kadai take da buqata.
"Kinsan a wanne yanayi muke ciki da har zaki saka bataun JIRA a wannan zancan?......kinsan kowacce daqiqa guda da zata shude muna sake shiga hadari ne nida duk wanda ya dangancemu?......buqata ta gaggawa ce......kiyi hanzarin dakatar da d'anki daga aikata abinda yayi niyyar aiwatarwa......idan kuma ba haka ba to tabbassss bazan shiga uku ni kadai ba......zan shaidawa duniya da hannunki a cikin komai......dollars dina da kika karba kuma.....kada ki manta akwai evidence na amount account details date da time na yadda na saka miki komai.....saiki shirya maidosu" Daga wannan fareeda ta yanke kiran.
Wani sarawa kan maamah taji yayi......lallai idan fareeda ta ambaceta a wannan badaqalar ba abinda zaya hana mutane aminta dasa hannunta.....musamman mutanen dake da issue da ita irin ameenatu da sabreen.....sabreen din da har yanzu tana qarqashin awa saba'in da biyun data bata,awannin da batasan ta yadda zata fiddo fu'ad ba banda yanzun da kiran fareeda ya sanya tasan inda yake.
Karasashinta ya dawo da wani irin sanya ran lallai tana da dama.....damarmaki har guda biyu.....damar sanyashi ya janye kaman yadda fareeda ta buqata,a yadda duk wata kadara tata data mallaka ta narke daga auren fu'ad da sabreen......da kuma neman hanyoyin da zata rabasu batajin tana da adadin dollars din da zata maidawa fareeda kudinta.
Lalubar number dinsa ta fara yi tana jin yadda kanta yaketa sara mata da ciwo. Kira uku tayi,ana hudun sabreen data dauke wayar don ya sake samun nutsuwa taga kiran.
"Maamah" Da sunan yayi serving ba kaman sunan anni da yake suna na daban cikin wayar tasa ba. Qaramin murmushi ta saki,sannan ta taka zuwa bandaki a hankali ta maida qofan ta kulle.
"A yanzun yana buqatar hutu daga dukkan wata takura da zullumi na rayuwa.....yana buqatar yin nesa da kowacce kalar damuwa" Kalaman sabreen kenan da suka sauka a kunnenta suka sanya wayar hannun nata kusan subucewa daga hannun nata,kanta kuma yayi wani dummmm na wucin gadi kafin ta tattara qarfin halinta waje daya.
Magana takeson mata amma ta kasa furta komai,wacce irin HATSABIBIYA ce yarinyar?,a yanzun haka kenan tana taiwan tare dashi ta barta bata cikakken bacci?.
"Duk yadda kike tunanin cin nasara.....kina yiwa kanki qarya ne.....ni mariya a duk sanda nayi nufin cimma nasara akan wani abu.....ba wani wanda ko wani abu daya isa ya dakatar dani daga wannan nasarar....."
"Sai ubangijin da yayi ni yayi ki,ya kuma halicci nasarar........shin da gaske ne kuwa?.....anya ke kika haifi muhammad da musaddiq?" Sabreen tayi mata tambayar da bata taba tunanin zata iya mata ita ba....amma yau ta tsinci kanta da tambayar tata.
Wutace tsaf ta daukewa maamah tana jin jiri yana kamata daga zaune.
"Idanma ya tabbata ke dince.....to ki saka a ranki kin haifawa masoyansu ne su.......sun tashi daga mallakinki.....sun tashi daga ababen kulawarki,ubangji ya musu musaye da masoyansu na haqiqa....."
"Ki dakata da wannan shirmen......ki hadani da d'ana dashi nake buqatar magana" Sabreen bata tsaya sake sauraronta ba ta kashe kiran,ta kuma kashe wayarma gaba daya.
Iska me zafi ta furzar daga bakinta,mamakin maamah yana sake kasheta,a yanzun dai ya tabbata dari bisa dari......dukiya takeso......arziqin take da buqata bawai 'YA'YAN BA.
Mummunan tashi hankalin maamah yayi,ta soma sake gwada kiran number amma a kashe.
"Allah ya tsine miki......muddin banyi sanadinki ba a rayuwa nayi asara" Shine abinda maamah take maimaitawa sanda take yunqurin sake maimaita kiran number fu'ad din ana gaya mata a kashe layin yake.
Sam Allah ya dauke mata basirar kiran musaddiq......tunaninta yafi karkata ga ME ZAI FARU bayan awannin da fareeda ta debar mata tana jiranta?.
*_Hajja_*
Tun sanda suka gama wancan wayar da maamah ko sau daya taqi bawa kwanyarta hutu na neman mafita da hasashen abinda zai wakana......hakanan ta gaza dauke kunnuwanta daga jiran isowar jami'an tsaro gareta suyi awon gaba da ita kaman yadda take hasashe,duk kuwa da bokanta ya shaida mata ba wanda ya isa ya shigo ya kamata muddin ta tabbata a cikin gidanta,saidai idan qafa ta sanya ta fita.
Ta sake amanna da maganarsa ganin kwana dayar har biyu shuru,sai wannan ya bata daman zama tana tunanin matakin da zata dauka akan maamah.
Laila itace burinta......laila da ita take kwana take kuma tashi,yantuwar laila shine muradinta kafin ta waiwayo ga hanyoyin tozarta mariya.
Tsai tayi da ranta tana bitar kalaman da sukayi musaya a wayarsu ta qarshe,ta tsinci tsoro kadan da razana a muryar mariyan,ta yiwu akwai wani abu daban da batasan dashi ba.....ta yiwu ba mmariya bace ta fidda hotonsu.....ta tabbatar tunda hoton maqale yake da nata....duk da fuskarta bata fito sosai ba amma zai wahala mariyan tabari ya fita. Wata shawara ta tsirga mata.....taji a wannan karon ta shirya ayi tone tone tsakaninta da mariya muddin autarta zata dawo cikin hayyacin rayuwarta,wayarta ta dauka kanta tsaye ta fara kiran layin wayarta.
Kamar ana jira ta tsagaita da kiran fu'ad wani kiran ya danno mata waya. Hajja harira,ko kadan kiran bai sakata fargaba ba har sai data daga wayar suka fara musayar magana.
"Da baki wahalar da kanki kina tambayata meye yasa nayi kiranki ba......fuskata da sunana sunyi tambari a bakunan al'umma da kuma kowacce jarida......kina tunanin akwai wani faruwar abun kunya da zanyi shakkar fitarsa?....abun da koda ya fita tawa kunyatar qarama ce akan ta mahaifiyar data sadaukar da mutuncinta da rayukan 'ya'yanta saboda ta mallaki abun duniya?". Kaman babu jini cikin jikin maamah haka takeji......a yanzu takeson solving wannan issue din batabataso hajja ta afko cikin wannan da'irar.....tanaso a sanda hajja zata buqaci a fafata yaqin ta gama da issue din fareeda dana sabreen harma da ameenatu,a sannan zata gwadawa hajja yadda ake wasan kura da rayukan dan adam.
"Hajja......karki tunkari.fadan da bazaki.iya qarasashi ba......ki lallaba masarautar cikin gidanki dake gareki,ki qarasa mulkinki sannu a hankali,ki kuma jirayi randa naga damar 'yanta miki d'iyarki"
Wata dariya data saka numfashin maamah tsaiwa na wucin gadi ta saki,sai da tayi me isarta sannan tace.
"A a'ah......mariyatul kibdiyya......wai ni bakisan abokin mutuwa nake nema ba?....,to bari kiji.......daga yau zuwa gobe na baki ki maidomin da d'iyata gaba na,ko kuma wannan boyayyar fuskar dake gefena a bugun shafin farko na jarida da kowa keson ganinta ta bayyana kanta da kanta.....aikin fahimta ko?" Daga wannan hajja bata jira komai ba ta kashe kiran.
Daga zaunen da take amma sai taji tana jin jiri.......me yasa komai yake neman ya kwabe mata lokaci guda?,kowa adadin awanni yake deba mata cikin umarni da kuma gadara?,wai me yake faruwa ne?.
Daidai nan taji muryar driver dinta yana fadin.
"Mun iso gida.hajiya" Kanta ta daga tana kallon gidan,batasan sanda suka iso ba kaman yadda batasan sanda suka shigo gidan har ya iso parking lot ya tsaida motar ya kuma kasheta ba.
Hannu ta saka ta bude murfin motar,a hankali taja jikinta tana fita a motar,saidai ko Cilakken tsaiwa batayi ba ta yanke jiki ta fadi a wajen hankalinta yana gushewa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 132
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
132
Da sallama farouq ya shigo,sabreen dake tsugunne gaban fu'ad din tana gyara masa nails dinshi na qafa duk da fes suke.....amma tsabar bayason tayi nesa dashi ya tsiro mata aikin ta matsa kadan tana amsawa.
"Sannu da aiki addanmu" Ya fada yana jawo kujera ya zauna yana dubanta. Murmushi tayi a kunyace tana amsawa.
"Yauwa BB....sannu da qoqari....Allah y qara zumunci.....ya saka da alkhairi".
" Ameen dai.....dama wani abun saboda ke akeyinsa ai ba