Author : Huguma Category : Complete Novels
ta hanyar basu ilimin addinin islama?,ya karbesu a matsayin 'ya'yan da shine yayi silar zuwansu duniya bawai uban riqo ba?,yayi musu gatan da ko 'ya'yan cikinsa bai musu ba?.....amnan dai itace d'iya ga ameenatu......ameenatun data dawowa auren hamza saboda yaran?,ameenatun data sadaukar da duk wata kulawa da lokacinta akan yaran?,ameenatun da bata yarda da wani abu me cutarwa ya rabesu ba?,ameenatun da idan kanaso kaga farincikinta.....ko kaga kirkinta ka yabi musaddiq.......ka yabi fu'ad......idan kanaso ku bata alaqarku taja baya ka zagesu ko ka kushesu.....ameenatun da ta sadaukar da lafiyarta saboda su su rayu cikin aminci?,taqi kwanciya ta huta sabodasu?,taqi ci saboda saboda basuci ba?,taqi sha saboda basu sha ba?......" Ya sake tsayawa saboda yadda numfashi ke masa wahalar shaqa.
"Laifin ameenatu rainon 'ya'yanki da tayi......laifin ameenatu inganta rayuwar 'ya'yanki.....idan duka haka ne ita kuma SABREEEN FA?!". Wannan tambayar daya jefa mata tafi kowacce gigitata. Sabreen?,ya tabbata ta qarasa bude mata aiki kenan kaman yadda taci alwashi?.
"Ni na kawota rayuwarka.....kuma a yanzu bani da buqatar kasancewarku......na nuna maka ta dukka hanyar data kamata amma saboda banda kima da martaba a idanunka ka gagara fahimta".
"Sai hakan yanzama license ya zama halaccin da zaki tura wani d'a namiji gidan aurenta.......dakin da d'anki ya gina saboda matarsa ta sunnah?.....yaje ya keta hurumin ubangiji?,.......kin auramin sabreen saboda ki.mallaki fu'ad......fu'ad din da bai mallaki wuta ko aljanna ba......fu'ad din da bai mallaki rayuwa ko mutuwa ba.......bai mallaki komai ba face wata aba da ake kira DUKIYA wadda ka iya zama fitina da jarrabawa ga bawa.......". Yana kaiwa qarshe ya jawo littafi da abun rubutun daya gani ajiye a gefe,ya jawo side table ya ajiye a tsakaninsu ya daga idonsa yana kallonta duba na kai tsaye.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 150
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
150
"Na baki dama......daga farkon littafin nan har bangonsa ki rubuta adadin kudin da kikeso......na baki dama ki rubuta adadin alatun rayuwar da kikeso......na baki dama ki rubuta tsarin rayuwarki na shekaru dari nan gaba idan har zaki kai sannan......ni kuma zan tabbatar miki da wannan mafarkin,muddin zaki zare kanki daga rayuwarmu.......muddin zaki fita salin alin daga rayuwarmu......muddin zakiyi nesa da rayuwarmu......indai kin amince zaki bar iyalin ameenatu su rayu cikin salama su kuma zauna lafiya........ina fada miki hakanne cikin harshe na girmamawa.......ina gaya miki hakanne saboda har yanzu sunanki MAHAIFIYARMU.......Duk da girman abubuwan da kika aikatawa mutanen da basuji ba basu gani ba......ina gaya miki wannan zabinne saboda shine zaifi mana sauqi mu dake" Ya qarasa maganar yana jin wani mulmulallen dutsen wuta yana tsaya masa tsakanin wuyansa da qirjinsa yana qoqarin turashi da qyar. Fata yakeyi inama ace wani ko wata ce can daban suka aikata musu wannan abun ba maamah ba?......inama ace wasu mutanen ne daban keda alhakin dukka wadannan abubuwan ba maamah ba?,ya rantse da Allah da sai ya ganar dashi kuskuren bari da yayi uwarsa ta haifesa zuwa gidan duniyar ma gaba daya.
"Fu'ad!.....ni kake gayawa wannan maganar?,ni kake cewa zaka rabu dani saboda ameenatu?" Ta tambaya tana jin wani irin tashin hankalin jahiltar matsayin ameenatu da tayi a baya. Ashe har zai iya katse alaqar uwa tsakaninsu saboda ameenatun dai?.
"Fu'ad!.....ka saurareni da kyau!......."
"Jaffal qalam" Ya fada yana miqewa daga gabanta. Zuciya da shaidan dukka suna kusa,duk sanda zai kalli fuskarta fuskar mahaifinsa yake kalla a tayi watsi dashi cikin tsananin ciwo bayan ta gama illatawa luguiguita lafiyarsa cikin mugunta.......duk sanda zai kalleta saiya tuna sanda take cida Mahaifinsu da abubuwan da aka hanashi ci ko sha saboda hakan zai iya zama sanadin komai.....ciki harda MUTUWARSA.......duk sanda ya kalleta saiya tuna sanda JADDA ta mutu saman cinyarsu saboda rashin gata suka kwana da gawarta ba wanda ya ko leqosu sai bayan wayewar gari......duk sanda ya kalli fuskarta sai ya tuna sanda musaddiq ke kwana yana kuka harda shidewa cikin kewa da qauna yana kiran sunanta.....burinsa shine kawai ya ganta......har yanzu kunnuwansa sun gaza manta yadda aka saka abun rushe gini ake dukan ginin gidan da mahaifinsu ya wahala da dukka qarfinsa ya ginashi don su rayu a ciki......ta badashi a mazaunin jingina ta karbi kudaden ta nausa zuwa duniya
"Wannan dama ce a wajenki cikin girmamawa da kuma baki abinda kiketa harin mallaka din tsahon shekaru kina fadi tashi.....ki rubuta!....ki rubuta!!.....ki rubuta!!!!....ki gayyato wasu ma su tayaki rubutun?!!!,wannan damar ce kawai ta rage......'yanci muke nema!!!!,yanci muke buqata....." Sai ya hade hannayensa alamun roqo
"A wannan karon da kanmu muke roqarki ki tafi ki barmu kaman yadda kikayi a baya". Sai ya fara tafiya da baya da baya idanunshi a kanta yana barin falon. Irin kallon da ya jima baiyi mata irinsa ba. Ya dade rabon daya sanya idonsa cikin nata,ya dade rabon daya iya daga kai ya dubeta,tana hango abubuwa da yawa cikin idanunsa.
"Idan kika rubuta hakan yana bawa ameenatu tabbacin kinbar mata su dama dukkan wata dama ko matsayi da zasu sake takawa a gaba.....kinbar mata su da dukka wani arziqi da zai sake habaka nasu......kinbar mata dukkan wata alfarma ta amsa sunan UWAR ME JADDA har abada......iya abinda kika samu daman rubutawa shine kawai naki rabon har abada.....baki da wani sauran dama ko rabo a jikinsu saidai idan sun rigaki MUTUWA" Maganar da shaidaniyar zuciyarta ke gaya mata kenan sanda yake dab da fita a falon,abinda ya sanyata zabura ta miqe,sai wani irin jiri ya taso mata,amma cikin tsananin taurin rai dana zuciya ta cije ta kuma soma takawa tana binsa da hanzari gami da qwalla kiran sunansa.
Turus yayi ya tsaya gaban gate din gidan yana kallon tarin 'yan press da suka cika qofar gidan maqil.
"Da gaske ne kenan yallabai.....mamarka itace tayi kidnapping d'iyar alhaji hamza kibiya dake kwance a asibiti a yanzu tana jinya?,yanzu haka ma akwai d'iyar qawarta a cikin gidan nan da tayi!kidnapping nata tsahon watanni ba'a sani ba me suna laila?" . Wani abu yaji yana neman kayar dashi,abu daya ya saka masa sassauci ganin yadda dukkaninsu suka sauke cameras dinsu a kanshi cikin nuna masa girmamawa.
Kasa magana yayi cikin tsananin mamakin yadda akayi!maganan ya fita?,waye kuma ya gayyatosu?,amsar da ya sameta kai tsaye daga bakin wani dan jarida.
"Mun samu half details na cikakken labarin daga wajen aminiyarta hajja harira......ta kuma bamu tabbacin zamu samu full din daga bakin hajiya mariya ahmad" Ya qarashe fadi sanda maamah ki fitowa da sassarfa tana qwala kiran sunan fu'ad din.
Waiwayawa yayi ya zube idanunsa a kanta a sanda sam bata lura da taron da dama ita suke kwadayin gani ba.....malam sa'adu ya tsaidasu da qyar ba,sai kawai ya dauke kanshi ya kuma dubesu da dakakkiyar muryarsannan dake qara masa kwarjini,wadda a yau take cakude da bacin rai yace.
"Ku bani hanya....bani keda labarin ba". Tsakiya suka buda masa ya fara wucewa da sassarfa,bayajin akwai wani abu da zaiyi mata.....ba wani abu da yayi saura da zai iyayi mata shi
"Fu'ad......a matsayina na mahaifiyarka ina me baka umarnin........"
"Yauwa.....shikenan ma.....gata nan ta fito" Yaji muryoyin wasu a cikin su suna fadi gami da kunna cameras dinsu suka saitasu sannan sukayi kanta.
"Kada ki damu,wataqila sun soma fahimtar kece mahaifiya ga fu'ad din.....girman ya fara dawo miki,wataqila ameenatu ta sallama ne" Wata zuciyar ta gaya mata,don haka ta dake tana dubansu sanda suke yowa kanta yuuu.
"Ranki ya dade......samun tabbaci da neman sahihancin rahotanni yasa mukazo gareki.....da gaske kece mahaifiyar muhammad fu'ad jadda?.....mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources?" . Wani murmushin alfahari ya kubce mata,murmushin da ya dusashe duk wani bacin rai da tashin hankalin data tsinci kanta yanzu yanzu a cikinsa.
"Qwarai da gaske.....nice"
"Ma sha Allah......kina tare da laila d'iyar qawarki kenan?". Da farko tambayar ta mata banbarakwai,amma zuciya batan basira da neman suna suka gina mata tunanin wataqila suna kallon ita din uwar kowa ce da take riqon yara turmus,don haka ta daga kanta kawai tana cewa.
"Eh haka ne".
"Yauwa.....mun samu cikakken labarin qawancenku......yadda kikayi silar hada auren d'anki da matarsa ta yanzu sabreen da dukkan wasu hujjoji na riqe qannenta a bisa cikar wannan buri naki.....kidnapping diyar alhaji hamza da kidnapping tata d'iyar wato laila da a yanzu kika bamu tabbacin kuna tare....". Wani jibgigen abu ne taji ya saukar mata tsakiyar kanta wanda ya sanya numfashinta yaso riqewa iya wuyanta.
Ita hajja zata yiwa haka?,ita hajja zata wulaqanta?,ita hajja zata jajibowa taron manema labarai?,ita hajja zata tonawa asiri?,ya akayi ta manta da ita bata sanyata mutum ta uku daya kamata ta shafe labarin su ba,me yasa bata b'atar da ita ba?,me yasa ta barta taci gaba da shaqar iskar 'yanci?.
Juyawa tayi kawai don komawa ciki,saboda tana jin bai kamata tace komai ba gudun tonuwar asirinta gaba daya wanda ta fahimci fiye da rabinsa ya yaye.
"Ranki ya dade ya zaki koma kuma?" Zaqaqurin dan jaridar ya fada. Waiwayowa tayi ta zube masa wani kallo.
"Ni ba uwar qaramin mutum bace,bani da lokacin magana daku kai tsaye haka.....idan ka matsa kuma kasan waye d'ana,ba aikinka kawai zaka rasa ba.....har....." Sai kuma ta dakata tana kwabar kanta duba da irin cameras din dake fuskantarta. Kallon kallon suka farayi tsakaninsu,don kowa da abinda ransa ke raya masa da yanke maganar da tayi bata qarasa ba. Ganin ta dauke musu wuta gaba dayansu saita taka tana komawa ciki cikin jan qaqqarfan tsaki.
"Akwai batun aika b'ata gari da kikayi gidansa don yiwa matarsa fyade da sunan baki sonta.......wannan batun gaskiya ne?". Wani irin suka maganar tayi mata a qirjinta,har batasan sanda ta saka hannu ta dafe saitin zuciyarta ba. Haki ta soma yi tana jin kamar qafafunta ba zasu dauke ta ba,dole ta fara kiran sunan laila saboda tasan duk 'yan aikinta yau basunan cikin mancewa da tarin 'yan jaridar da suke neman tabbacin lailan tana tare da ita kaman yadda cikin rashin sani ta basu tabbacin.
Kome takeyi,komai girman bacci ko uzurinta muddin maamah ta kirata saita bar komai. Kaman yanzun da take zaman cin abinci haka ta watsar dashi ta kwaso da gudu. Fitowar tata ta sake maida hankalin mutane kan laila din da dukkanin kamanninta da hajja harira da suka fito.
"Lafiya maamah?,me sukayi miki?,me ya faru?".
"Kamani muje ciki" Ta bata umarni a tsawace,abinda ya sanyata kamata dukka jikinta suna rawa.
"Da gaske kece diyar hajja harira?" Wata cikin su tayi caraf ta jefa mata tambayar sunason tabbatar da maganar juya mata hankali da sukayi.
"Eh 'yarta ce......amma yanzun daidai nake da baiwa wajen maamah......yadda takeso take buqata haka zanyi,koda ya kama na rabu da ita hariran"
"Ke laila kama bakinki mu wuce ciki!" Maamah ta fada da hanzari gudun kada tsananin mallaka ya sanyata nunawa duniya abinda zai sake zame mata abun fada.
"Laaaaa haila ha'illallahu.....muhammadurrasulillahi" D'aya daga cikin mata 'yan jarida dake wajen ta kasa daurewa abinda ya farun ta saki kuka tana tafa hannu.
"Wallahi 'yar hajja harira ce,da gaske ne,da gaske aikin juyar da hankali tayi mata bayan tayi kidnapping nata......da gaske ne,gashinan diya tana neman mancewa da uwarta?" Wannan kalaman sun sauka daidai kunnen maamah,wanda hakan ya sanyata runtse ido,tsananin jin zafin hajja yana sake ratsata tare da alwashin daukan fansa a tare da ita.
"Ki gayawa malam sa'adu ya fidda mutanen nan,idan ba haka ba zai fuskanci fushi na" Umarnin data bawa laila kenan,ta kuma saka kunne tana jiran daina jiyo hayaniyarsu daga nan inda take.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 151
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
151
Tsahon mintuna talatin ta sauke idonta akan takardar da fu'ad ya ajiye mata,ta zubawa littafin idanu tana lissafa adadin yawan shafukan da yake dasu. Ya fadi cewa zata iya cika littafin harma ta qaro wani....tayita rubuta dukkanin abinda takeso.......wannna babbar dama ce a gareta kenan na zama Mulitibillonier?. Murmushi ta saki ta soma yunqurin daga hannunta ta miqashi don dauko littafin,amma abun mamaki sai taji hakan ya gagara. Ta sake yunqurawa a karo na biyu da zummar gwada daukar nan ma shuru ne hannun yaqi sarrafuwa.
A zabure ta maida dubanta ga hannun nata cikin wani irin kidima da dimuwa tana kallonsa. Hannunta ne dai......hannunta ne data sani shekara da shekaru......hannunta ne da ba wani abu daya canzashi.........amma meye ya kawo qin daguwarsa?.
A karo na uku ta tattaro dukkanin qarfinta zata dagashi ya sake motsuwa koda wasa,a birkice ta maida hankalinta kan daya hannun tana qoqarin motsashi shima.
Still shima abinda dan uwansa yayi shi yayi mata. Matuqar qololuwar tashin hankali taji ta shigeta,wani irin mahaukacin gumi ya yanke mata.
"Me hakan yake nufi kenan?,wani ne yayi min asiri?,ko wani ne yayi min tsafi?" Ta tambayi kanta da kanta.
"Kai inaaaa.....a irin wannan lokacin?,a lokacin da dama tazomin?" Ta sake tambayar kanta a fili kaman wata tababbiya.
"Bazai yuwu ba" Ta fada tana qoqarin miqewa don ta gani ko qafafunta suna aiki?.
Miqewar datayi aniya jikinta ya gaya mata bashi da wani sauran motsi me qarfi,qafafun suma suka shaida mata basu da wani sauran qarfin da zasu dauki nauyin gangar jikinta ta hanyar warbar da ita ta zube a qasa tana kifawa saman fuskarta.
Wani irin matsanancin ciwon kai yakeji,wani irin yanayi da yakejin kamar jikinsa yana dab da gazawa. Yana dafe da kanshi tsahon mintunan da suka dauka suna tafiya a motar,har zuwa sanda ya buda bakinsa a hankali yayi magana da driver din
"Badawa zaka kaini......ba gida ba" A yanzun ba abinda yafi buqata irin ya kebe,so yake ya kebe shi daya,bayason magana da kowa bayason kuma hayaniya.
Karya kan motar yayi suna komawa daya hannun. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu m,already yasan gidan,gida ne madaidaici daga waje,saidai kuma daga cikin yana da yalwa da wani irin yanayi da aka tsara me tsananin burgewa. Yakan jima baizo gidan ba,yana ma mantawa dashi sau tari,saidai duk sanda yake buqatar ya kebe ko ya huta a nan din yake zama har zuwa sanda ya gamsu da yanayinsa ya koma normal mode dinsa.
Tun a parlor din ya zube,karo na farko da yaji yana buqatar yayi kuka,karo na farko da ya buraci inama ace shi din yana cikin sahun mutanen da hawaye ke fita a fuskarsu da wurwuri?. Hawaye yake da buqatar ya zubar sosai saboda qirjinsa dama zuciyarsa sun gaji da daukan abinda suke dauka din. Koda zai iya hana kanshi fitar dasu to ba a irin wannan lokacin ba,a yanzun kuka yafi buqatar yayi bawai yaci gaba da nuna jarumtarsa ba.
"Astagfirullah ya Allah......astagfirullah" Shine abinda labbansa dake motsawa suke maimaitawa yana jin yadda qirjinsa ke sake suya idanunsa suna sake d'aurewa da wani irin zafi da kuma radadi.
Wani sabon babi ya bude na tariyar rayuwarsu,tun daga sanda ya bude idanunsa ya zama mutum cikakke zuwa yanzu. Bai tsinci komai tattare da maamah ba banda haihuwarsu da tayi......ko a sanda take rayuwa tare dasu,yadda take mu'amala dasu haihuwarsu ta zame mata kaman wani nauyi wahala ko dawainiya.....abbansu kusan shine komai nasu......abbansu shine duk wata wahala da dawainiya tasu,abbansu shine wankansu abincinsu,shirin makarantarsu da komai na dawainiya......yayi a gida ya fita yayi a waje ya kawo musu. Zuwa yanzu baisan sadaqaul jariya na abubuwa daban daban dubu million nawa yayi saboda shi ba......yana fatan ko a ina yake ya bishi cike da samun salama cikin kabarinsa da rayuwarsa ta barzahu.
Da taimakon ambaton sunan Allah da yakeyi ya samu nutsuwa ta fara dawo masa. Yayi amfani da wannan damar ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala. Dawowa yayi ya kunna ya kunna TV din dake kashe,ya lalubi tashar saudi qur'an ya qaro volume din ya karade parlor din gaba daya.
Cikin kujera ya nutse,idanunsa a lumshe yana sauraren karatun gami da bin ayoyin tare da shaik abdurrahman assudais. Yana karatun yana fahimtar ma'anar ayoyin,abinda ya sake taimakawa wajen bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa.
A nan gurin yayi sallar la'asar,magariba ma ta ruskeshi duka ba tare da ya sani ba. Itama magrib din a nan yayita,ya jima saman abun sallah yana addu'o'i har baisan adadin lokutan daya shafe ba,yadai duba ya tarar da lokacin isha'i har ya shiga.
Isha'i dince ya fita a daddafe zuwa masallacin dake cikin layin cikin shiga ta bad da kama,baya son kowa ya tsaidashi don bazai iya dogon magana ba. Ana idarwa ya taso shida jordan sukayo gida,jordan din ya dan dubeshi cikin matuqar jin tausayinsa qauna da kuma kulawa.
"Sir......ko za'a aika a karba maka abinci gurin madam?,if not a maka order daga wani eatery din?". Kai ya girgiza,a halin yanzu bayajin yunwa,still kuma bayaso ma sabreen ta ganshi a yanayin da yake ciki. Tashin hankalin da take fuskanta ita kanta yayi yawa,tunda ta dauki cikin nan bata huta ba,tana stressing kanta da yawa akan duk abinda ya shafeshi......is over,ya kamata ta huta hakanan,ya kamata ta samu peace of mind......yana shawarwarin