Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
think u are ?ke asuwa kunun bayan ludayi....just a zero behind a decimal point....ran mom yayi mugun baci
Iyee, its all my fault da bansani Anyi wajen dake Ba kamin a Shiga da ita, shiyasa kika sani bakin magana. Listen to me very attentively! Idan kika sake kikayi mana tashin hankali a gida ki tabbata zaman ki ya Kare. Banason in zama sanadin daba aure amma abin naki ya isa. Kin fara wuce gona da iri.
Yazeed ne ya riko mom yace calm down sweetheart bade aure bane Anyi angama karki damu kinsan I love u ko?muje dakikinki. Haka ya tisa mom a gaba har dakin ta. Tanaji Kamar ta yarfawa zakiyya tafi amma batason ta zubda girmanta.
Zaunar da ita yayi ya bata ruwa sannan yayi assuring dinta Cewa ba mai hanasa aure sai Allah daganan ya fita...
Zakiyya kuwa tasan ta tabo Dan yadda taga ran mom ya baci babu abinda zaihana tasa a saketa she must calm herself down. Taso tayi musu hauka amma bazata iyaba saboda tanason igiyan aurenta
Haka taje dakinta aguje tahau watsarda abubuwa tana fasawa hannunta na jini kamin ta fada kan gado ta fashe da wani matsanancin kuka.....
Yazeed ne ya turo kofan dakin ya shigo
Tasowa tayi attachment dinnan duk ya wargaje tana sending masa murderous glare ahankali yazo ya zauna akusa da ita being conscious with the glasses kar ya taka.
Hannunta ya riko ta warce ya kara rikowa zata warta ya rike gam yace haba my zakky uhm....yanxu shine kikaje kikayi fada da mum kinsan mahaifiyata ne tanada hakki akaina ya kikeson Nayi kinaso na haukace ne?
Rungumeta yayi kamin yaci gaba da fadin na dawo ko kiss ban damu sai kihau yima mahaifiyata fitsara kin kyauta kenan?a hankali ta girgiza kanta yace ai kinsan ko Nayi auren ke nakeso waccan zabin mom ne ko?ta gyada kai yace promise me zaki bawa mom hakuri tace on one condition idan kayi auren bazaka hada gado da matar ba yace ai wannan ko baki fadaba kinsan haka yake Insha Allah.
Tace to nima zan bada hakurin yace good daganan aka Shirya kuma akayi wani duniyar.
Jamal kam sune kirjin biki bai samu haduwa da yazeed ba sai Washe gari Inda za'akai lefe
Your one and only karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty馃挄
8 SEPTEMBER, 2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 24*
Kamar yadda kuka sani yau za'a kawo lefen minal
gidansu ya cika taf da dangi,Yan uwa da abokan arziki kai har makiya ma sunzo domin asamu abin fadi acikin gari
Ana zazzaune akaji sallaman kawayen mom da aunties din yazeed sun iso firfitowa akayi ana musu maraba tare da shinfida musu dardumai
Gaggaisawa akayi da fara'a da mutunci Yan gulma da tsurku tundaga ganin masu kawo lefen sunsan minal ta cafka tayi sa'a zata Shiga gidan da akwai gida mai maiko
(Wannan yana daya daga cikin kuskuren da mutane keyi Suna ganin idan har ka auri me kudi ko me kyau Toh kayi sa'a saide abin Ba haka essential qualities da ake bukatan mutum ya lura dasu shine:
1.shin wannan mutumin ya kwantamin ?
2.shin yanada addini?
3.zai iya ciyaddani da halal?
4.shin 'ya'yana zasuyi alfari dashi amatsayin ubansu?
5.shin zasu gode min na zabanshi amatsayin baban su?
6.shin yanada akida mai karfi
7.is he loving and caring?
8.will always support me?
9.am I ready to live my whole life with him?
10.Does he respect my family
if those questions are satisfied then you are good to go,bawai idan ka auri mai kudi,handsome shine kayi sa'a Ba pls and pls Yan mata take note Ku core San duniya aranku Ku sank duk mijin da kika zaba Ba kanku kadai kika zabawa ba har da yaranku.Ku guji ranan da 'ya'yanku zasu kalleku suce muku kun cucesu kun zaba masu mafi munin uba.
Suma mazan idan kun aurensu zasusan Dan me kuka auresu Dan kudi ko Dan allah.
Shiyasa yanxu rate of zaurawa ke karuwa soboda tun kafin adaura aure an rusa ta an kasheta auren a mace tazo. AKIYAYE)
Abokan ya abubakar ne suka fara shigowa da akwatuna har aka Shiga da 6 akwai nasu Kate ba,7,8,9,10.........18 set uku kenan Wanda Duke da kalar fari,baki sai sky blue ga stones farare masu kyau ajikin ko wanne
Wasu set shida aka shigo dasu Wanda suke kalar brown guda 3 na inna,2 na baba sai 1 na kawayen Amarya
Kaya aka fara budewa hmm abin ba magana atamfofi 50,laces 30,material 25,an dinka goma goma atamfofi kuma ashirin ,English wears 25,Arabian gowns 30,sleeping dress 20,pants da bras dozen uku uku,takalma da jaka set 20,cosmetic traveling bag daya,gold jewellery 5 sets
Inna tace kayan sunyi yawa a rage Rabi sukace ah ah ai kaya sunzo in zasu koma to saide in ankawo amarya
Haka inna ma ta nasu tukuicin ban girma ;cin-cin,bakilawa,cake,doughnut, alkali,meat pie da samosa buckets buckets Wanda aunty fauzy ta bayar amatsayin gudun muwa sannan tahada musuda turaren wuta
Haka aka watse kowa yana farin ciki da annashuwa
THE WEDDING DAY
yazeed ne tsaye abakin mirrorn dakinshi zakiyya makale dashi tana wani shashshafa fuskanshi zuwa wuyanshi baby Wai da gaske auren zakayi,yace Toh zaky ba maganannan an gamata ba meye na dago da ita,zakiyya tace Toh naji amma kar ka manta kace bakasonta kuma bazaka hada gado da ita ba yace ina sane da wannan,happy now?tace yes
Fesa turare yayi kamin yayi mata peck a kumatu ya wuce
Zama tayi abakin gado tace koma wacece ke to kisani zaki kawo kanji cikin masifa ne Dan kishi dani sai an Shirya yanda ba'ayiwa uwata kishiyaba nima bazan zauna da ita ba馃槇
(Wannan banziyar akida ce mutum yace Wai Dan ba'ayiwa mahaifiyarsa kishiya ba shims ba'a masa ba karku manta Allah madaukakin sarki yace acikin suratun nisa'i
"Wa in kiftum all芒 tuksid没 fil yatam芒 fan kihu ma d'aba lakum minannisa'i masna wa sul芒sa war ba'a,fa'inkiftum all芒 ta'adil没 fa wahidatan au ma malakat aimanukum zalika adn芒 all芒 ta'ul没" 3:3
Allah madaukakin sarki ya umurci maza da su auri mata biyu,ko uku,ko hudu,idan bazasuyi adalci ba to su auri daya
Kinga da auren biyu ma aka fara kamin uku kamin 4 shikuma daya karshe
Kisani idan mijinki yace zaiyi aure kikayi adawa to kisani badashi kikeyi ba da Allah ne tunda Allah shi ya umarci ayi hakan
Dan Allah mata mu tashi munemi ilimi kuma muyi aiki dashi kodan gudun ranan da yayan mu zasu tambayemu Abu akan addini mutsaya muna zare ido mu Shiga kunya.
Ba'a tsufa ko girma daneman ilimi,idan bakusamu kunyi da yarinta ba lokaci bai kure ba tunda har yanxu kuna shan numfashi.
Kusaka yaran Ku amakaranta na boko da addini kodan suyi alfahari daku
Abin kunya ne ace Wai semi yar cikin Ku da Kanwarka bayanku ne zan Samar daku abinda ya dace.
Ku Duba abinda nake iya rubutawa?I am just 14 years, 11 months,20 days kuma ina university sannan na haddace takaddun addini turum. what do u expect idan nakai 18?what of 20? ba cika baki nake ba amma kuma kunsani akarancin shekarun da nake dashi inada tunanin manya.
Abin kunyane ace yar cikinki ko kanwar bayanki ta Fiki zurfin tunani.
Wani abin da ke bani haushi shine 'Yan mata masu shekaruna yanxu Kansu rawa yake,yanzu ne suke ganin Suma sun girma baza'a barsu a bayaba,Suna ganin sunyi boobs Kansu daya da uban kowa,basuda burin daya wuce ayi shigan tsiraici ana yawo a gari ana karya ka'ida da iyakar Allah,ana kara yada zina acikin alumma,tun daga fitanta har dawowanta mala'iku na tsine mata,manzon Allah ya tsine mata,bayin Allah salihai na tsine mata, ai tundaga nan ya kamata ta fahimci ta Shiga ukku,ta gama yawo ta lalace wallahi Mu kiyayi haduwar mu da Allah abin kunya ne kaje gaban Allah kana mai saba masa ka wulakanta a duniya ka wulakanta alahira.
Su mazan da suke ganinku suce u look breathtaking,u look sexy,u look hot ke tun daganan ansami matsala hot fa akace ba cool ba kinga ko anfada miki Inda mala'iku zasuyi dake ne in baki canja hali ba. Ancemiki zasu aureki ne ?babu mai aurenki lalataki zasuyi suyi gaba,wallahi ku ji kunyan randa zaku tsaya gaban Allah ana miki shari'ah keda iyayenki. Mu rufawa kanmu asiri mu nemi ilimi muyi aurenmu cikin rufin asiri har Allah ya karbi rayukan mu.)
Lovelies kuyi hakuri yau duk Mun kare a lecture wallahi rainane ya baci da abinda ke faruwa,duk mutane sun kwashe kayansu daga gaban annabi,amma karku damu I will make it up to you馃槈 Ku tayani da addu'a inada test guda biyu tomorrow masu zafi ne aradu; chemistry and Arabic thanks for your love
Your one and only favorite yobe girl,karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty馃挄
8 September,2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 25*
An daura auren minal da yazeed akan sadaki naira dubu 50,Yan uwa da abokan arziki NATA taya murna makiya ma na hassada
Allah ka barmana makiyanmu kodan su zama dalilin da zamuyi nasara. Kai jama'a Imagine life without munafukai Allah barmana Ku Yan wuta馃槀
Mom ta aiko da kayan abinci da abubuwan da za'ayi walimah Dan babu wani event da za'ayi. Saboda abin yazo a kurarren lokaci ko mai wa'azi ba'a sami daman kira Ba.
Bayan la'asar akayi da mom Cewa za'a daukan minal around 5 pm inji ango(mom anya wannan magana kuwa zan yarda da ita?).
Hakan yasa aka fara shirya Amarya around 3:50 bayan Anyi sallar la'asar.
Liffaya mai kyau tasa wadda aka siyo mata awajen reemah's collection. Wani sarkan gold akasa mata Wanda yake na inna ne family necklace dinsu. Babbar ya ake bawa in za'a kaita dakin miji. Kuma ba'ayarda ka siyar Ba amma zaka iya upgrading.
Kyansa yananan Dan haka ba'amayi upgrading din Ba.
Dayawa daga cikin Yan makarantansu sunyi attending, ciki kuwa harda heedaya Muhammad da ma'ani yerima Wanda suke mutunci sosai.
Yan matan ne adakin minal yayinda aketa tsokananta itako sai cika take tana batsewa wai ita batason adinga zancen batsa a gefenta.
Hidaya ce tace Nide sake fuskannaki in gama kwalliyan yayinda ma'ani ke Cewa nikam yau sai na cika camera ta da hotuna, inajin ma inna sami dama zanje in karanta photography馃槈
Heedaya ne tace oh mude zamuzo muji ya aka Kare a Daren farko.
Harara minal ta ballo mata,aka fashe mata da dariya Ashe ta shaka,zaliha tace kai Ku rabu da ita bari ayi Daren farkon wannan Cuno bakin da take duk zata dena saide muga mutumiyar ka an zama miji dadi
Alamun zatayi kuka muryanta yayi tana Cewa wallahi zaliha karki bari na kamaki shegiya yar.....
Innace ta shigo tace inkika karasa sainaci ubanki.
Tunda ake hirar bansa baki Ba ina zaune a gefe ina typing a wattpad dina saboda kar ace na fiya rashin kunya sai alokacin na sako baki nace "assha!inna kin bata goma boyar bata gyaru ba in ita batayiba aike kinyi"
Dakuwa tayimin tace ingo naki yar jakan uban yarinya da baki cau cau Kamar babba kodan kinganki cikin Yan mata shiyasa kika falle ko?kinsa niqabi kamar da gaske ashe dai.......shegiya Da I damu Kamar na Yan chaina
Kafin ta karashe nayi Sauri nace wallahi Nide Ba yar China bace ina turo baki,aiko inna tayi kaina na fita a 360 har inacin karo da mutum Ashe ma sakina ce da habiba (from the nemesis of sakina)yi hakuri kawai nace kamin na 'buya a zaure ina haki sannan na sauke niqabi na,na saka gilashi na saboda naga alamun maza a waje.
Ciki su sakina suka Shiga aka gaggaisa kamin suka wuce domin mazajensu na jiransu.
Kanwar dad din yazeed aunty nafeesa da Umma habiba wadda take step paternal grandma ga聽 yazeed sai kuma aunty nina Kanwarka mom Wanda suka iso yau da safe sune sukazo daukan Amarya tare da motoci 3 kacal saboda basuso bidi'an tayi yawa
Aiko nan aka fara tashin hankali minal fa da taga da gaske tafiya za'ayi da ita kirjinta ya fara lugude duk dadin da takeji taji babu shi ya tafi kawai sai ta fara hawaye wiwi Ba magana nanfa聽 wattpad fans dinta sukayi CAA anata bata hakuri amma ina kukan karuwa yake tunba sanda sukayi sallama dasu inna Ba dasu baba da ya abubakar.
Inna da baba hawaye suke hankali kwance yayinda idanun yaya abubakar suka ciko da kwalla deeje Kam an jika gaban riga ma da hawaye da majina sai alokacin na lura da kwalliyar da tayi kominta yayi matching da kayanta hatta Jan baki da eye-shadow, da brows din duka blue ne. Abin dai sai kun gani. Nikam share kwallan da zai zubo min Nayi domin tausayi. Rabuwansu was heart touching haka aka kwashemu mu 10 aka kaimu gidan amarya.
Tundaga kofa akayi mana maraba,kai Mun sami tarba me kyau dakin zakiyya aka nuna mana muka kai minal Dan bada amana mu Yan mata 8 da tsofi 2.
Ba yabo ba fallasa ta karbemu. Amma ni dai hankalina bai kwanta ba kuma naga alamun hakan a fiskan wasu daga cikin mu amma dai sai Nayi shiru. Kar aji mutuwan sarki a bakina.
nuna mana dakin minal akayi Wanda yake part din baki ne na sama kuma acikin sashin zakiyya yake ada amma an daba kuma an gyarashi kai ya hadu. Allah dai ya kyauta ya Kare Daga sharrin makiya
Aikuwa hidaya ta cika alkawari Dan photo kam gida yashashi har minal dinma sanda akayi mata pic amma sanda ta sake ado tukunnan.
Haka dai har dare yayi munata shewa da tadi kamin aunty Nina ta shigo tace mana motocin tafiya najiran mu haka Muka tattari kafufun muka tafi minal Kam kukanta ta bude sabon shafi Dan ta manta da Cewa ita daya zamu bari(saima ankai mutum kabari zai San kadaici. Allah dai yasa muyi dariya a kaburburanmu.).
Hmm ai batamasan gidan wa aka kawota Ba saboda kanta na cikin gyale har muka kaita daki kuma ai batasan yazeed Nada mata Ba kuma bata tbna Shiga side din zakiyya Ba Dan haka bata gano ba.
Lokacin ko da akayi musu maraba kuka take ga hayaniya Dan haka bata gane muryan mom ba.
Aunty nafeesa da mom ne suka shigo,mom tayi Sauri taje wajen minal yayinda ta dago chin dinta tana mai Cewa " 'yata me ya sameki?"
Kuka minal ta kara fashewa dashi ta rungume mom Dan ta dauka mom tayi attending bikin ne
Tace "mom Ashe an gayyaceki?mom Dan Allah karki tafi ki barni kamar yadda su zaliha da untichlobanty da ma'ani da nasreen da hidaya da..."
Ya isa bazan tafi in barki ba mom ta fada hakan tana me daurewan kai ?kode batasan wa ta aura ba?kai maybe de tsoro takeji saboda first encounter dinta da yazeed wasn't good.
Shafa bayanta mom聽 tayi tana bata soothing words har tayi shiru tana shessheka (sobs).
Kinyi sallahn Isha'i ? mom ta tambayeta tace a ah. Mom tace to tashi kije Kiyi kinji
Shiga toilet din tayi taga irin na wannan dakin da aka kaita ne sansadowa tayi kamar barauniya Wai Dan kar fanfo din yaji motsinta ya bachi da gangan har zatakai hannu ta bude saide ta fasa
Fanfon dake jikin toilet irin na tsarkinnan tace ta matsa tayi alwalanta Dan akwai irinsa a gidan aunty fauxy so ta iya aiki dashi har wani smiling take irin itama ta Waye dinnan.
After tayi alwalan bata mayar da dankwalinta ba ta fito Dan ta manta da cewa ma su mom sunanan
Smiling suka mata ta miyar musu kafin mom tayi introducing mata aunty nafeesa sannan ta tada sallah
Aunty nafeesa Kam yaba Kyan聽 minal take tunba gashinba shi yafi dauke mata ido.
After ta idar mom ta zaunar da ita ta mata wa'azi ya tsumata sosai.
Abinda ta fada last ne yasa minal shock.
"Daughter Dan Allah ki rikemin Dana dakyau kuma iyayi miki wani Abu ki sanar dani"
"Kina nufin oga sir?"minal ta tambaya hankali tashe.
"Kwarai shi"mom ta bata amsa. Atake minal ta.........
Yey! Alhamdulillah馃拑馃帄馃帀馃巻 is my birthday your girl is finally 15years old 馃拑馃徏馃拑馃徏馃拑馃徏
love you all馃槝
Karamarsu babbarsu ce
Miss untichlobanty馃挄
*18TH SEPTEMBER,2019.*
[1/11, 1:53 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 26*
INTRODUCING NEW CHARACTERS SAFWAN AND SAHIR
Sahir and safwan 'ya'yan yayar zakiyya ce Wanda ta rasu two years ago ana kiransu sahboy and safboy tashin turaine su. An dawo dasu wajen zakiyya ne last two month acewar mamanta Wai idan yazeed bashida matsala to su zauna awajenta tunda babansu irin sugar daddy dinnanne dama dan kudi yayar ta auresa kuma sanda sukayi sharadi inta sake ta haihu tofa yaran nata ne shi babu ruwanshi Dan baya bukatan yara.
To ta haifi sahir (6 years old) and safwan (4 years old).
Yaran are very sweet kuma sun saba da zakiyya Kamar mamansu adan zamansu tare tunda dama Ba aiki take zuwa yanxu Ba kuma already sun saba kawai shakuwa suka karayi.
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
Atake minal ta sauke wani ajiyar zuciya aranta tace na Shiga ukku na lalace, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un sunana聽 death.
Da badan tana cikin matsala Ba da tayi smiling domin ta fadi kalmar death daidai
Bude baki tayi zatayi magana kawai sai taji ta kasa Cewa Komai sai hawaye mom kuwa bata kawo Komai a ranta Ba ta dauka minal tana kukan yadda dare daya Allah ya sauya rayuwanta ne(eh tabbas sauyin Shiga tashin hankali ba).
Mom tace bari inje intaho da angon naki Dan Nasan yanxu haka yana hanya idanma be karaso Ba kenan.
馃尮
Abangaren yazeed kuwa tun kayanshi na daurin aure ne ajikinshi dama shadda ne fari kal.
Yana shigowa gidan side din matarsa(I think yanxu matansa zance) ya nufa dama haka yakeyi tunda suka Shirya da zakiyya inya dawo sai yaje ya taho da ita dakinsa wataran idan a sama yazo ma to Anan za'a yada zango. Watarana kuma ya samota already a dakinsa.
Yana shigowa ya kalli right dinsa wani iri yaji aransa Wai yanxu matarsa ne a part dinnan left dinshi yayi ya tura kofan dakin zakiyya gaji abude.......
馃尮zakiyya tayi wa Kanta alkawari bazata biyewa yarinyar (Kamar yadda taji su mom sunce)da za'a kawo mata Ba tunda