Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 45

9K to 12K   out of 134.5K words

daga kanta

Wai Wai Wai wannan dakyar in takai kafadansa ma tabdi

Ai bata lura gardi bane wannan sai sai basamude ma ai da batayi masa rashin kunya ba

ta wuce abinta salin alin babu wata hayaniya yanzu wannan Idan ya mata naushi daya ai har lahira.

Gaskiya dukda tana jibgar maza bazatayi koda kuskuren tunanin dukan shi Ba balle ta aikata

Yazeed yace ke wa kikeyiwa fitsara?

idonta ya ciko da hawaye a take tsoro take kar ya daketa Dan taga ya dunkule Hannu jikinta na rawa ta girgiza kai

Yace Nayi kama da sa'anki?

Tace a'a

Yace shine kike min rashin kunya

Tace ai kai ka jawowa kanka kana Abu Kamar baksan darajar dan Adam ba

Ya dalle mata baki da yatsansa

Tace Allah ya isa na wallahi bazan yafe makaba kuma bullukutut bakar mutuwa.

Yace ke zan canja miki halitta fatace Bismillahi

Daga hannu yayi Kamar zai mareta dashi bata dukan mata聽 tace wallahi kana marina zan kira Yan sanda kaga wayata?

Yazeed yace to sai me dankin kirasu?

Tace sai en sandan su kama ka

Yace idan ni kakansu nefa?

Tace sai sojoji su kamaka

Yace idan ni ubansu ne fa?

Tace da gaske nake fah zan kirasu inka tabani

Ya matso kusa da ita yace Bismillah

Tace a ah fa

Ya kara matsowa yace ki kira mana! Ya fadi hakan da kakkausar murya

cire dayan takalminta tayi ta rike a hannun dan ta lura zaliha da haske ta tafi tun dazun ta tafi tun dazu

Tace mai zubin samudawa da ido kulya kawa sannan ta Diba aguj

Bata tsaya a ko Ina ba sai gidan aunty fauziyya zata fada a guje taji gate a kulle ga wani mota shigen na yazeed ya shigo Latin take fitsari ya cika mata Mara take gumi ya fara karyo mata.

Bubbuga gara din ta farayi aiko zaliha na bude mata ta nufi ban daki tana mai cillo da takalmanta.

Bayan ta fito aunty fauziyya tace ina kika tsaya tun dazu muMun dauka kin Koma gidane ma kuma ya akayi kika bari fitsari ya matseki?

Labarta musu abinda ya faru tayi aiko sukayita dariya zaliha tace ai in kinsan wata bakisan wata Ba 馃槀

Nandai zaliha ke fadamata irin haushin data bata har ta tafi ta barta

Nan aka dago da zancen auren zaliha har minal take basu labarin baba nason ya mata aure amma yace sai mai Dan ilimi

Minal tace nidai indai gidan da abinci Toh shikenan banida damuwa kai amma fa banda mai warin hammata.

Aunty fauziyya tace har kura zatace da kare maye ?

Keda bakyayin minti uku kingama wanka? Harvwani bakison mai wari?

Zaliha tace ai ta gyara yau bakiga har kwalliya na mata Ba

aunty Fa'iza tace dallah dubi wani gira Kamar Anyi bakin fenti dukkanku Ba abinda kuka iya

Haka dai suka dinga hira suna kwasar dariya Kamar Ba gobe

Minal shaf ta manta dacewa Ba kwana zatayi Ba

Aunty fauziyya kuwa ganin a holiday suke kuma taga minal da katan jaka sai ta dauka kayanta ne aciki

Zaliha kuwa dama sati zatayi mata

Aunty fauziyya Ba laifi mijinta yanada rufin asiri mijinta Dan kasuwa yanada shago akasuwa

Itakuwa tana gyaran jiki,dasu makeup,da turaren wuta Wanda inna ce ta koya mata makeup kuwa

Training class tayi

Kuma Ba laifi tana samun alheri.

Da daddare suka dafa Dan malele

锟?

suna cikin sha

Minal tace Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Aunty da zaliha sukace menene?

minal ta side manjan dake bin mata hannunta kamintace na manta baba yace karnayi dare

Atare sukace dama Ba kwana zakiyi Ba ?

tace eh

Aunty fauzy ta kalli agogo pass 9 tace dare kuma yayi Tara ya wuce

Wayar baba tanananko?

Minal tace eh

Aunty fauxy tace yauwa bara na kirasa na fada masa

Nan ta kira baba tace minal zata kwana a wajenta

Yace to Ba Komai daganan ma ta kara mata fada akan tsafta Dan yau yaji dadin yanda ya ganta tace Ba Komai Insha Allah zata musu fada dukkansu biyu ma

Nan sukayi sallama

Anan suka tattara suka kwanta dama mijin aunty fauziyyan bayanan.

Yazeed's POV

Yazeed kuwa koda minal ta falfala a guje tsaki yayi yace idan na kama yarinyannan sai Nayi mugun saba mata sai ta gwammaci ba'a haifeta ba

Komawa mota yayi zakiyya nata dariya tace swthrt kaga bakinta kuwa itafa gani take ta kure kwalliya

Yazeed yace gaba zakky ke wato duk rashin kunyar da tamun Ba dameki bako? Tace wannan tsakaninku ne ai

Dear pls let's go !

Yace my zakky you will never change

Sannan ya kunna mota suka tafi yanata gungunin abinda minal tamai zakiyya sai dariya take Kamar tababbiya

Abin mamaki take basa zakky wace iriyar mutum ce?kawai yayi smiling.

At night

After sun dawo daga dinner dinsu

Suna hira a parlour mom tana fada masa Cewa she is planning on visiting her family

Wayan YAZEED yayi ringing it was his aboki,a brother as well Jamal

Jamal yace Hello captain.

Yazeed yace Dude how far?

Jamal:guy I have a surprise for you?

Yazeed: and what's that?

Jamal:gobe zan shigo garinku

Yazeed: are you serious?

Jamal: of course yes!

Yazeed:okay I will send habu(personal)driver to pick you up

Jamal: guy pls kazo da kanka

Yazeed: no need to plead with me I will come,by what time would u land?

Jamal:that's why I like you,emm we will land by 12:30pm Insha Allah

Yazeed: okay see yah

Jamal: bye

Yazeed: bye............

Hope you love this chapter?

Juma'at Mubarak

7 June,2019

Mzz untichlobanty馃挄

[1/11, 1:40 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒:

馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

馃尮by miss untichlobanty馃尮

馃崁CHAPTER 10馃崁

*Morning*

Koda su minal suka tashi akayiwa yara wanka

sukayi聽 karyawa suka ci Suma sukayi wanka suka danyi hira

Anan聽 aunty fauziyya tayiwa minal fada sosai akan tsafta sannan ta bata wasu yan turare tace tanayin aiki dasu

ta bata wasu sako ma ta kaiwa inna(nima bansani me acikiba)

Waje ta fice domin nemo almajiri ya kai mata gyaran takalmi aiko taci karo da kandala mai gyada wanka mata mari tayi tace ke kandala da ub*nki me kikazo yi nan unguwar iye? Kuka kandalar ta fara tana kokarin kwashe gyadatta daya bare tace wallahi saina hadaki da aunty salma minal tace inkin fasa kinki Allah ita kanta salmar tayi kadan balle ke banzar bazara kunun bayan ludayi. Dama itama Daga haka ta fara Daga talla ta fara bin maza unguwa unguwa yanzu ta zama magajiya adai juri zuwa rafi. Bankadeta minal tayi tace sh*giya jaka.

Gyaro mata takalmin akayi sannan ta kama hanyan聽 gida domin Azahar ya kusa pass 11:00am...........

Yazeed's POV

Yana tashi da safe after yayi all necessary things needed ya gaida mom sannan yadan fita.聽 motanshi fara tare da guards 2 kamin 12:00pm yayi ya dauko Jamal .

After yaje wani cafe yanashan favorite cappuccino dinshi phone dinshi yayi ringing.

Zakiyya:swthrt awhile naga fita ko?pls if you don't mind kabiya restaurant da mukaje jiya ka siyo mana pizzan naga akwai a menu dinsu kaga sai ka daina siyowa a dayan wajen kasan yaufa Thursday

She said all of that in not more than 2 breath

Yazeed: haba dear!can't you atleast say good morning, u didn't ask about my well being or anything all you care about is the pizza which we will eat later at night ?

Zakiyya: sorry good morning

Hope zaka siyo pizzan ?

Yazeed: naji

Zakiyya: and also kafin ku dawo kudan biya ta boutique dina Ku karbo min wani sako( legendaries), bye love you tiiit

Yazeed:love yo.....

Oh god,bukatanta ya biya she can't even wait for me to say bye

He called the waiter,paid for聽 cappuccino dinshi

And went out security men dinshi guda biyu na biye dashi

Kofa suka bude mai ya Shiga motan sannan suka rufe daya ya Shiga drivers seat dayan kuma front passenger seat

Na driver's seat ne ya kunna motan ya kama hanyan airport

yazeed yace we are going to zakby unique boutique聽 before going to the airport

Drivern ya karya kwana sukayi hanyan boutique

Minal POV

Tana cikin tafiyarta tana er wakenta akan babban titi wasu en shaye shaye suka hangota

Thug 1:boss kaga wata er shila kuwa

Thug 2:kunama yarinyannan tayi

Thug 3:boss kawai mu sankacota mana

Thug 4:boss nifa inason sidin kwano

Thug 2:goje(thug1) Ku kai min ita

Mansion amma kuyi ahankali Dan yarinyar ta Shiga raina

Thug 1:lallai yarinyannan ta Shiga ranka boss tunda har sai an kaita mansion baza'ayi Anan Ba

Boss:banason maganan banza ni har kishinta ma fa ya kama ni

(Kaji min rashin kunya irin na Dan tasha Wai kishinta ya kamashi ni yama bani haushi)

All thugs:hahahahaha boss kenan mude in an gama a aiko mana

Boss:zundum me kuke jirane Ku dauko min amaryata

Minal tana tafiya taga en shaye shaye sunyo kanta fuska tayi taci gaba da tafiya

Goje ne yace amaryar mu ji mana

Bata kulasu Ba amma tana fake dasu

Scorpion ne yayiwa Goje alama da ido akan su kamata basu ankare Ashe Amaryar su ta Dade da arar kafar kare acan nesa suka hangota ta auna a guje suma da gudu suka bita

Gudu take batasan inda take wulla kafarta ba wulan keluwa (kwana)tasha inda ta hango booth din wani mota a bude da gudu ta daga kayan ciki ta Shiga kasan kayan yazeed yaji聽 jijjigar motan kuma baiga fitowan su ezikel Ba a karo na biyu hakan yasa ya leko

Alokacin su scorpion Suna arean motan minal ta bace musu ganin yazeed ya fito daga motan gashi wandon sojojinshi yasa da farin T-shirt Ba shiri suka bar wajen shikuma da baiga kowa Ba kawai sai ya koma

Su ezikel ne suka fito da guntun kayan suka saka a booth din kamin suka rufe

minal tana hangosu suka daura mata kaya gashi ta gansu da kaki atake wani mugun fitsari ya matseta聽聽

Yazeed ya Duba agogo yaga 11:45 sai yace kawai su kaiwa zakiyya kayan sai su wuce airport

Dan ko su Jamal din sun iso kamin su sauko, kayansu ya taho, ya fito zai bata lokaci shi kuma bayason jira

Sai yace muje gida mu sauke kayan

Driver ya kunna mota suka nufi gida

Minal tanajin an kunna motan tace shikenan za'a kaini barikin sojoji na Shiga uku na lalace.

AT JEEDMAR

Suna shigowa yazeed ko fita daga motan baiyiba yace su sauke kayan daga motan su shigar gida

Sukace yes sir

Booth suka bude fara Ciro kayan lukman na daga Leda taga Kamar kafan mutum

Ahankali ya radawa ezikel "be ready something no dey right here

Ezikel ya Ciro AK47 dinshi ya saita daidai minal

Lukman ya ajiye ledan hannunshi ya daga daidai na kanta

Wata yar kyakkyawa ya gani mai cute pinky lips tana bacci babu Komai a fiskanta sai uban man baki Kamar zai digo

Suka furta wow a tare

Kallon juna sukayi Suna magana da ido akan yanda zasu fadawa boss

Lukman ya gyada kai alamun zaije ya fada

Kewayowa yayi murya kasa-kasa

yace boss an sami matsala

Yazeed: meaning?

Lukman: dama...em da Muka..mukaje Ciro kayan....shin........

Yazeed: hope Ba Barin kaya kukayiba ?

ya fadi haka adan tsawace

Lukman: a a dama acikin booth.....

Ezikel ne ya tsindumo baki

Ezikel: boss lukman dey shy for u ooo,wani Yaro ne beauuuuutiful

Muka ganshi asikin booth yana bassi

Yazeed: ezikel what nonsense are you talking about ?

Ezikel: boss if adey lie,thunder fire me

Yazeed: let me go and see

Futowa yayi yazo wurin booth din minal ya gani tana bacci hankali kwance

Tabbas bazai manta wannan fiskarba

Wannan yarinyarce Wanda tamai fitsara jiya dole ya shaidata kodan man bakinnan lebensa na kasa ya gatsa

Sannan ya dakarkare ya daka mata duka a gadon baya yaga ko motsawa batayi Ba

Aranshi yace lallai wannan yarinyar ni zata nunawa jarumta

Kwata kwata bekawowa kansa Cewa zai iya yuwuwa suma tayi saboda babu ninfashi ba Wanda haka abin yake suma tayi Saboda rashin ninfashi inba hakaba minal ko cinnaka ya cije ta an Shiga uku balle soja ya watsa mata tafi.

Ciki ya Shiga babu kowa sai mai shara yace ta kawo masa chilled ruwa gora biyu

Jiki na bari ta dauko ta basa ya karba ya fita

Zuwa yayi ya kalli minal tana kwance yanda ya barta su lukuman a tsaye

Gora daya ya mikawa ezikel

Sannan ya bude dayan

Ezikel yace boss ruwan akwai sanyi sosai fa

Yazeed yace na fika sanin haka

Kamin ezikel ya kara magana

Yazeed ya juyewa minal ruwan sanyi..............

Ina sonku irin sosai dinnan

9 June,2019

Mzz untichlobanty馃挄

2 - CHAPTER 11-20

馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

By miss untichlobanty

*馃崁馃尮CHAPTER 11馃尮馃崁*

A zabure ta wantsalo daga cikin booth din tana salati ta fado a gaban lukman ta kurje hannunta

Bude idon da zatayi taga takalmin soja

sai alokacin ta tuna mai ya faru kawai sai idonta ya ciko da hawaye

Fitsarin da takeji dazu ya dawo ya cika mata Mara taf

Yau tasan ta Shiga uku kashinta ya bushe ta Shiga hannun soja

Tsawa yazeed ya daga mata ke mike tsaye ?

Allurar ta motsa

Ba ita kadai Ba har su lukman Saida suka tsorata

fitsarin da takeji聽 atake yabi jikin skirt dinta tana zazzare ido

tace kuyi hakuri walla.....

Bata karashe Ba yazeed yace shut up my friend, kalleni!

Sai alokacin ta kalleshi babu shakka wannan basamuden datayiwa rashin kunya ne jiya itakam ta shi uku Ashe soja ta tsokalo

Duka kam yau zata shashi harda na sadaka

Tace Dan Allah kayi hakuri ka yafe mini wallahi bazan kar....

Yace shhhhh yimin shiru

Yazeed yace Samuel inasu doggy suke ne?

Samuel:Suna cage ne fah

Yazeed: bring them out

Samuel: yes sir

Minal taji ance su doggy kuma ance cage sai ta dauka

Cage din da yake kai masu laifi nan zai kaita

Tafara Cewa oga sir kayi hakuri karka hadani da arna a caji office dinka wallahi na dena

Gashi idonta ya ciko da hawaye amma sunki su zubo tayi tayi sunki su zubo

Shi kuma yazeed abinda ke kara bashi haushi kenan takiyin kuka ita a dole jaruma

Haushin karnuka ta faraji a take ta kara tsula wani fitsarin

Wasu kosassun police dog ne guda biyu

Tsalle tafara tana ihu innalillahi wayyo inna na Shiga uku na lalace amma still babu hawaye

Alokacin duka masu aikin gidan sun taru

tsabagen muryarta shiyasa inna batason minal tana kuka ta kwammaci dije tayi sau goma akan minal tayi sau daya

kowa na tsoran bada hakuri kar a hada dashi

wasu kuma na mamakin mai ya hada oga da wannan yar kyakkyawar innocent yarinya Dan basu taba ganinsa a wannan yanayi Ba

dukda sunsan Cewa bayada sakin fiska ayanzu

Gashi mom batanan taje gidan friend dinta balle tasa baki

Madam zakiyya ma batanan ta tafi wani get together da sukeyi ita da business partners dinta Wanda yazeed bai Masan dashi Ba

Da minal tayi hawaye yazeed zaisa amayarda karnukan ganin takiyin hawaye tana ihu kawai yasa yake ganin pretending takeyi

besan tsananin tashin hankali yasa ta kasa hawaye ba

Kallonta yayi yace ke al'amarinnaki bayan tsiwa harda taurin kai ko ?

Tace wallahi oga sir Ba taurin kai bane

Yazeed yace release them!

Atake Samuel ya sakesu sukayo kanta babu shiri ta antaya a guje

fitsari nabin skirt dinta domin ahalin yanxu ta tsula yakai sau biyar聽

Gudu take Suna binta har suka iso wurin swimming pools.

Toh anzo wurin minal nason wasan ruwa amma bata taba Shiga mai yawa Ba gashi Ba tashin kauye tayi ba balle ta iya nitso da linkaya

amma kuma ga karnika nan Suna tunkarota kuma wa dannan bazasuyi mata da kyau ba

Dan ga bakinsu har yawu yake zubarwa

Kawai sai ta yanke shawara gwara ta fada ruwan koba Komai gawanta zatayi mutunci

Finndumm!!

ta fada swimming pool din Samuel kuma da gudu ya riko karnikan Dan karsu bita cikin ruwan

Yazeed Wanda ke tafiyan kasaita har ya iso wajen

Alokacin lukman na shirin fadawa ruwan Dan ya cetota Yazeed ya dakatar dashi

Rigarsa ya cire sannan ya fada ruwan alokacin har tasha ruwa nimfashinta ya kusa daukewa

ya daukota

Akunnenta ya rada mata bashi聽 sannan ya fito da ita

yacewa masu aiki su hada mata shayi mai zafi tasha sai su nuna mata side dinshi Tasameshi acan

sannan su lukman suje su dauko jamal kuma

karkowa ya sake ya fadawa mamy ko Jamal abinda ya faru

Ya wuce side dinshi

Wet trouser dinshi ya cire sannan

Ya saka wani tare da farin T-shirt kamar Wanda ya cire sannan ya fada gadonsa yana tunanin abinda zaiyiwa minal Idan ta farfado batayi kuka ba

Domin yaga sanda ta suma a hannunshi........

Am feeling so sleepy yet typed coz of the love I have for u guys

Show me some love as well

11 June 2019

Mzz untichlobanty馃挄

[1/11, 1:44 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

By miss untichlobanty

*CHAPTER 12*

minal kuwa shayin dazai taimaka mata da condition din da take aka hada mata

Kamin suka samo bowl da ruwan dumi da tsumma

Sannan suka dauko first aid box domin ciwon dake hannunta har yanxu yana zubda jini

duk ya bata mata hijab dinta

Tabawa dukkan maids da securities din gidan tausayi hatta sojojin domin duk rashin imanin wasu daga cikinsu sunsan Cewa minal ta horu

What so ever her fault is?

They all look at her pitifully, how young she is,yet going through all these sort of troubles

First was her hiding inside the Booth,

Then passing out due to lack of oxygen,

Then woken up by a chilled bottle water !

Then fear of being in an army's house as an offender!

Then the blood cascading from her hand making her clothes

4 / 45