Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
yar tasu.
Hawayen da ya gangaro kan kumatunta shi yasa ta sauke ajiyan zuciya
Tayi missing iyayenta,itakam Allah ya isanta da wannan oga sir me kama da aljanu
*Toooooh Anan zan dasa aya*
*kwana biyu kunjini shiru wallahi makaranta ne* *kunsan mu Yan 100 level dole mu zage dantse balle yanxu da muke second semester atayani dai da addu'a Allah yayi mini tsari da carry over*
*Seriously need your prayers!*
*Thanks for understanding me*
*Show some love by:*
*Sharing*
And
*Commenting*
10 July 2019
Mzz untichlobanty馃挄
*Karamarsu babbarsu ce.*
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮馃崁By @mzz_untichlobanty馃尮馃崁
*CHAPTER 15*
Fitowa falo yazeed yayi ya zauna tare da fara karanta wasikar jaki
Sallamar da mamy ta watso shi yadawo dashi daga Inda ya tafi
Ganin yanayinsa yasa tace son lafiya ya na ganka haka duk ka hada gumi ko bakada Lpy ne ?
Lumshe idonshi yayi yace lapiya klau mom kawai gajiya ne
Zama tayi kamin ta kira atine ta dawo mata ruwa da drinks
Ruwan ta kawo mata tare dasu coke da fanta da Sprite da maltina da 7up da ..........
Kallon duka drinks din tayi kamin tace son yaushe za'a kawo me aikin ne danni na gaji da wa dannan gases din
Yace wallahi mom an dudduba yawancin restaurant din ba'a samu Ba amma de had yanxu ana bincikawa
Cup mom ta dauka ta zuba ruwan kamin ta kurba zata kara kenan suka jiyo Jamal na suburbudo sallama
Mikewa yazeed yayi tare da ware hannunsa yayinda shi da Jamal din suka antayo a guje suka rungume juna Kamar wasu kananan yara
Sai alokacin suka fahimci yadda sukayi missing kuna
Ai kam gogan naka ya manta ma da akwai wani hallitar minal a gidan
Jamal yake Cewa ai Nayi fishi shine mukayi zaka daukeni amma naga sabanin haka
yazeed yace afuwan nawan wallahi wani abune ya taso
Jamal yace sunfini kenan
Yazeed yace bazaka gane bane
Jamal:
mom masa'ul khair
(good afternoon)
ina wuni?
Mom:
masa'ul noor khaifa anta ya ibny Jamal
(good afternoon how are you my Darling son jamal)
Lpy klau Ykk Dana Jamal?
Jamal:
ana bi khair wallah
(am absolutely fine)
Lpy na klau
Ain zakiyya ?
(where is zakiyya?)
Ina zakiyya?
Mom:
zahabat ilaaa boutikiha
(she went to her boutique)
Ta tafi boutique dinta
Jamal:
mata sa tarji'i?
(when is she coming back?)
Yaushe zata dawo?
Yazeed:
anta uskut tatakallam kaseer wallah walakin arafta annany annany karihtul dajij
(hey pls keep quiet,you talk too much while you know I hate noice)
Kai Dan Allah kayi shiru ka fiya magana bayan kasan na tsani hakan
Jamal:isbir ya sadiky la atakarir Insha Allah
(sorry dude I will never repeat it okay?)
Yi hakuri mutumina bazan sake ba
Yazeed :
khairullak
(better)
yafi maka
Point out shine abinda yazeed ya fada sai ga atine da salma sunzo suka tsuguna a gabanshi
yace do the right thing sumul sumul suka tashi suka koma kitchen gasu sundawo su biyar tare da kayan abinci iri iri Suna bin hanyar dinning room
sanda suka gama jerawa tukunna yazeed yace
Dan uwa muje kaci abinci ko?
Mom tace Toni bara in Shiga ciki Dan na gaji
Sukace to mom a huta gajiya
tace shukran
(thanks)
na gode
Dinning room din suka Shiga Jamal ya kalli abincin
yace Dude ya haka ina kasar waje inci wannan yanxu nazo Nigeria ina expecting tuwo sai naga abinda na baro.
Ya fadi hakan ne a accent dinshi na balabe sai hausar tayi wani zakwai da ita amma fah bai kai na yazeed ba.
Yazeed shima cikin accent nashi na larabawa-larabawa turawa-turawa kuma cikin sanyin murya
yace yanzu muka gama maganan da mom soon har sai wannan kazantar taku ta isheka.
Kallonshi Jamal yayi irin kaji dashi kamin yace
Ka kiyaye watarana abinda kake Cewa kazanta zakazo kanaci harda santi
Yazeed ya tabe fiska Kamar yaga danmalelen da yara suka jagwalgwal yace Allah ya kiyaye
Jamal yace munanan dakai zama sukayi suka ci abincin Suna hiran yaushe rabo
Bayan sun gama ci suka tafi side din yazeed domin yin alwala su tafi masallati
Amina da taci kuka har tayi baccin wahala ta tashi sanadiyyar fitsarin daya matseta
da gudu tayi hanyar wata kofa data gani wadda take sa ran toilet ce
aiko tana afkawa taja waya super sanadin kamin ta bude kofar ya Dan bata wahala Duba da batasan irin kofar Ba
hakan ya taimaka wajen fara saukar fitsari wadda ya hadu da tiles yayi sanadin zamewar tata
Ihun data rafka kamin ta suma shi yasa yazeed da Jamal yin hanyar dakin aguje domin shi yazeed shaf ya manta da ita a side dinshi Suna Shiga dakin sukaga jini jini akasa
Sai a lokacin yazeed ya tuna da Amina na dakin
Tsayawa yayi abakin kofa yayinda Jamal ya jiga bandakin Dan ganin meke wakana
Ganin Jamal ya fito jikinshi a sanyaye yana kallon yazeed hakan yasa yazeed ya dauka ko minal ta kashe kanta
a hankali minal ta fito jikinta duk jini tana dingishi sanadiyyar zamewan da tayi wani ajiyar zuciya yazeed ya sauke ganin tanada rai
Ko kallon Inda yake Jamal baiyi ba ya fita fiskannan a daure Kamar hadari
Sai kuma ya jiyo yace me nake gani?
Cukumosa yayi tare da masa tsawa yace yazeed kayimin bayani Idan Ba haka Ba mum ta sami labari
Yazeed ya kalleshi yace mai karka fasa fada yana Dan murmushin gefen baki don't atunaninsa wasa Jamal yakeyi
Juyawa Jamal yayi ya fita
Direct side din mom ya wuce a lokacin har ta fara bacci Kamar a mafarki takejin yadda ake buga mata kofa hakan yasa ta bude ido
Adan tsorace ta bude kofar ganin jamal fiskannan tayi jaa tace son lapiya?
Kamo hannunta yayi sai part din yazeed hankalinta a tashe Dan tadau wani abunne ya samu danta daya daya
A Abangaren su yazeed kuwa harara ya banka mata kamin yaje ya kwanta akan gadon yace tayi knee down
Tayi tsamo tsamo da ita a cikin fitsari duk ta zama abin tausayi kwalliyan duk ta cabe
Kinyin tayi illa ma turo baki da tayi alamun gardama saukowa yayi daga gadon ya daga hannunsa zai dalle bakin
Puuuuuumm aka bugo kofar dakin duk suka kalli wajen
Abangaren su inna kuwa hankalin kowa ya tashi aunty fauziyya sai kuka take acewarta laifin tane tunda a hanyarta na dawowa daga gidan tane ta bata
Baba kam ya ma kasa yin Komai Dan jinya ce ta kamasa rif daya Ba abinda yake furtawa sai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un
Kowa hankalinsa ya tashi abin dai Ba dadi gashi ya Abubakar saura 3days ya dawo
*Anan ne ink din bairo na ya kare bara insiyo wani domin rahoto muku labarin kuruciyar minal*
*Ku Muna Mani soyayya ta hanyar commenting*
*Sannan Ku nunawa kuruciyar minal soyaiya ta hanyar sharing.*
*Love u wujiga wujiga*
10th July 2019
Karamarsu babbarsu ce fa
Mzz untichlobanty馃挄
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮馃崁by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 16*
Kallon wajen dukkansu biyu sukayi
Minal hawaye da majina duk sun chabe mata fiska
Jan majinan tayi kamin ta mitsitsika hanci sannan ta goge a hijabin daya hada launi daban daban kama daya kalarsa da kalar jini,da jurwayen fitsari tare da kanzon majina馃槀
Takowa tayi cikin dingisawa ta tsuguna tace ina kwana au ina yini hajiya
Dan Allah kicewa oga sir ya mayar dani gida wallahi yunwa nakeji gashi Nasan hankalin iyayena ya tashi.
Dagota mom tayi ta Shiga dakin tana takawa idon ta cikin na yazeed Wanda ya kasa fassara yanayin mahaifiyar tas
Bai ankare Ba yaji saukan mari
Wani tashin hankali ne ya saukar masa tunda ya mallaki hankalin kansa bai taba ganin bacin ran mahaifiyarsa akansa Ba balle ta dakesa.
Hakan yasa lokaci daya zazzabi ya rufe oga sir Dan baima lura da Cewa yana ha'bo ba
Zama yayi kan gadon jagab Ba tare da yace Komai Ba kuma bai motsa Ba kwakwalwarsa ce ta daina aiki
Baki mom ta bude ta fara magana dukda ko zuciyarta ta girgiza ganin ta fidda jini Daga jikin Dan nata amma abinda yayi ya wuce wannan.
Haba yazeed ban taba tunanin irin haka daga gareka Ba dukda Nasan irin zaman da kakeyi da matarka ban taba tunanin ko da wasa zaka Ra'bi zina Ba
Bama a zina ka tsaya Ba zinar ma fyade kayi?
Amina jin bata gano Inda mom ta dosa Ba kuma da alama mom ta saba layi Dan da alamu bata fahimceta Ba sai tayi saurin Cewa Hajiya dama oga sir da ya fita fyade yayiwa wata?
Juyowa mom tayi fiskanta da alamar tambaya domin kanta itama ya daure shima dai Jamal hakan ta kasance masa.
Domin duk Wanda yaga minal a yanayin da take kuma acikin side din yazeed to lalle Abu na farko da zaiyi tunani shine fyade yazeed yayi mata
Duba da yadda shi Jamal din ya samota a bandaki a sume sannan tana tashi abinda ta fara yi shine kuka to lallai abinda zaizo kanka kenan.
Mom tace yata dama Ba fyade yayi miki bah ?
Minal ta gyada kai kamar kadangaruwa atake nadama ya saukarwa mom kawai sai ta kama hannun minal tayi side din ta da ita domin jin Karin bayani.
Abangaren Jamal kuwa dakin yazeed yaje ya dauko cotton sannan ya dawo zauna a gefen yazeed,cotton din yasa ya goge masa jinin sannan ya tura wani a hancin ya ruko hannun yazeed din.
Rumgumesa yazeed yayi ya fashe da kuka mai sauti Kamar maraya gaba da baya me karancin shekaru.
Jamal bai hanasa kukan Ba illa ma bubbuga bayansa da yake yi alamun lallashi
Saida yayi mai isarsa sannan ya tashi zai fita Jamal yayi saurin rikosa tare da mikewa tsaye Suna fiskantan juna yace lallai mudin abokai ne amma abokantakan ya ya karfafa Yan uwantakan mu lallai nidin na kasance mai kuskure d............
Hannu yazeed yasa ya rufe masa baki tare da girgiza kai yace lallai nine me laifi da ban sanar dakai Ba kuma ai sanda kace zaka kawo mom saina mata bayani,na dauka wasa ne Kamar yanda ka saba Dan nima baizo kauna Cewa zakuyi min mummunar fahimta Ba saboda yanayin yarinyar. Lallai kaidin amini ne na Gaskiya saboda alkhairi kake sona dashi Dan haka karka bani hakuri.
Rungume juna suka kara yi kowannensu na hawayen farin ciki kamin kuma suka fashe da dariya suka tafi domin yin sallh Dan lokaci ya tafi.
Abangaren su mom kuwa wani daki ta kawo minal sannan taje dakin zakiyya wardrobe din ta ta bude Dan tasan pin din taga duk babu laces da atamfofin
Wani kofa acikin dakin聽 ta bude dakine girman sa Kamar store babu Komai aciki sai akwatina 5 wasu takalma masu kyau amma zakiyya tasa a store Wai sun tsufa alhalin Kamar saga kwalinsu aka cirosu ko kurar arziki basuyi ba
Akwatinan mom ta bude ta dauko wani lace mai kyau da takalmi da kuma hijabi sannan ta rurrufe wurin ta kawo dakin da tabar minal
Ajiye kayan tayi sannan ta kalli minal wacce ta zauna a kasa tace Yan mata tashi ki zauna akan kujera mana ayayin da take nuna mata sofan dake dakin
Girgiza kai tayi tace Ba Komai nan ma yayi
Mom ta kamo hannunta ta zaunar da ita sannan tace
ya sunanki?
Tace Amina
Mom tace ya akayi kikazo gidannan kuma me hadinki da Dana
Kallon mom minal tayi kamin ta fara kwararo mata bayani cikin nutsuwa,kamunkai da tarbiyya Kamar da gaske tun daga fitowarta daga gidan aunty fauziyya har izuwa yanxu
Not telling her that this is not the first time she met yazeed
Shiru mom tayi tana nazarta maganan
Da ta tambayi yazeed kamin ta mareshi amma ai kowaye yaga yanayin aminan abinda zai ce kenan kuma ko Ba Komai soyayya ta jawo hakan ai Dan masoyinka ke hukuntaka akan laifinka
Makiyinka ne zai ganka kana Abu Ba daidai Ba ya barka ko ya kara ma kwarin gwuiwa
Kayan ta mika mata sannan tace tayi sallah za'a kawo mata abinci kamin ta fita tana tunanin lallai yazeed bai kyautaba na azabtar da minal da yayi Ba tare da yaji mai ya kawota motansa Ba sannan taya za'ayi ta miyar da minal gida a wannen yanayin?
smiling tayi wadda ke nuna ta samo mafita
Masu aiki ta aiko da kayan abinci
Lokacin minal ta chakare tayi das da ita har taji wani fresh a jikin ta murmushi tayi tace tsabta dadi
Dakwalin ta dauko zata daura saita fasa kawai tasa hijab
Zama tayi a bakin gado tana kalon tsarin dakin
Ya mugun tafiya da imaninta
Abincin aka kawo duk babu Wanda zata iya ci sai shinkafa haka ta daure ta tuttura taci rabi Dan ita shinkafa Ba gwanarta bace
Doctor mom ta kira aka da mata su bandage a inda taciwo aka Duba kafarta targade tayi aka daure mata shima likita yace tanajin wani ciwo tace a ah Dan tasan da tace eh to tasan allura ne馃槀馃槀
*(People like me and minal come and gather here lets know our selves)*
*Karamarsu babbarsu ce fa kai yau Nayi rubutu chapter har uku fa kuma ina tunanin kara wani*
*oya ku kirawo kawayenku da Yan uwanku masoya karatu suzo su yar da zango Anan.*
Mzz untichlobanty馃挄
Au Ashe bansa date Ba
10 July 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 17*
Abangaren yazeed kuwa suna dawowa daga masallati dakinshi ya koma ya kwanta domin zazzabine ya kamasa sallan ma daurewa yayi
Gawani tsananin tsanar minal dake taso masa
Wai yau shi mom ta Mara akan wannan kazamar bagidajiyar? Kuma har ta fidda masa jini?
Lallai sai ta gane kuranta a haka bacci yayi awon gaba dashi yana nazarin yadda zai yi maganinta minal.
Haka ta kasance Abangaren Jamal domin shima zaki ya nufa yayi d'are d'are a saman gado harda cire Riga sannan ya Lula duniyar bacci.
Abangaren su inna jikin baba Ba laifi ya Dan warware amma daka gansa kasan yana cikin damuwa.
Inna ce ta dinga yi masa nasiha tana kwatar masa da hankali har ya hakura ya fita domin zuwa gidan radio da jarida ayi sanarwa ko Allah zaisa a ganta
Aunty fauziyya ma ta daina kukan,mijinta yanajin labarin yayi gida haka zaliha ma ta tattara ya nata ya nata tayi gidansu.
Sanda mahaifiyar zalihan wato iyata sami labari kafafun ta kasa riketa sukayi.
Harga Allah minal yarinya ce mai Shiga rai dukda ko bata daukan raini ga tsiwa da tasha tayi tatul.
Hankula Kam dan banace hankali Ba sun tashi, yan anguwan su minal ma sunji tashin hankali,Yan matan nan ko da minal tayi musu saitin hamma da gyaran kafureto kwanaki sai Cewa suke Allah ya kara.
Wasu daga cikin Yan anguwan sun yi farin ciki,wasu na yada jita jitan ai iskanci ta tafi,mafi yawanci kuma na tausayawa baba saboda shidin tsoho ne mai dattako kuma ansan yadda yakeson minal shiyasa Idan tayi wasu abin ma ake boye masa.
AT NIGHT(after magrib)
Minal tana zaune a daki tayi zugum gashi bata Masan Inda wayanta yayi Ba abin duniya ya taru ya mata yawa.
Ko wani hali iyayenta ke ciki?me zata ce musu?
Kofan dakin aka turo laraba ce tace Wai hajiya tace kizo.
Amsawa tayi da Toh sannan ta dauki hijabin da aka bata tasa ta fita.
Da dingishi sannan ahankali take saukowa daga upstairs saboda tsoro da kuma rashin Sabo amma inka ganta zaka dauka damuwa ce.
Mom ce tace sauko kizo wajena kinji my daughter.
Karasa saukowa tayi taje wajen mom ta zauna a kasa. Mom tace zo zauna gefena kinji hira ta fara janta dashi itakuma sai nokewa take.
Mom tace ki saki jikinki babu abinda za'a miki kinji kai ta gyada Kamar Kadangaruwa sannan ta Dan saki jikin nata.
Suna fira kawai alarm din 8 ya buga da gudu minal ta tashi mom tace relax is time for dinner.
Batade gane me akace Ba amma ta zauna tana zazzare ido.
Maids dinne suka fara fitowa da abinci ana kaiwa dining table.
Mom ta kamo hannun minal tace muje ko Ba musu ta bita suka he wajen dinning table minal de mamaki take Wai Ashe a duniyannan akwai masu rayuwa Kamar a aljanna masha Allah dama nida su inna nane.
Sai kuma tayi chuckling to the sound of her calling inna innana.
Warmers din suka fara budewa one by one minal taga duk batasan abincin bama.
Mom tace wanne za'a sa miki minal tayi shiru domin bataso tacewa mom bazata ci Ba.
Mom ta fahimci batason abincin daga yanda tayi da fiska sai tace atine kuje kitchen tare Ku kama mata ta dafa duk abinda takeso.
Suka amsa da toh hajiya.
Mom tacewa minal tashi kije kinji kunya ne ma ya kamata taga ya akeyi Wai manya suke ramfo ka duk wayon ka ?
Tashi tayi suka Shiga kitchen din tace musu sunada dawa gyararre wanda zatayi tuwo su kace ah'ah semovita ne kawai pack daya shima ya Dade bari su Duba ko yayi expire dubawa sukayi sukaga beyi ba sai suka bata.
Tace akwai wani Abu da zata iyayin miya Kamar kuka,kubewa,ogbono,taushe sukace a'ah amma akwai ganye tace to subata nan dai ta dinga fada musu abubuwan da take so Suna dauko mata saide bata bari Susna mata hannun ba.
Haka ta fara aikinta cikin kwarewa Inda ta dafa tuwo miyan ganye ya sha kayan hadi yaji kaza tun kafin ta gama yawunta ke tsinkewa Dan mugun yunwa takeji ga kamshi daya mamaye ko ina.
Mom tana kallo a parlour ta jiyo kamshi smiling aranta tace yarinyannan ta iya data shinkafa Dan tasan yamatan yanxu akwai maitar shinkafa(Nide ahalin tuwone馃槈)
Koda ta gama warmers
(foodflask) suka kawo mata madaidai ta.
Tuwonta Mara(malmala) 3 ta saka a ciki sannan tace su bata wani flask din Malmala 5 tasa a ciki sannan ta basu tace suci nasu ne ladan tayata aiki.
Godiya suka rinka mata yayin da suke satar kallon junansu me ma'ana