Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 45

33K to 36K   out of 134.5K words

banason jaraba

Dan Allah ni ka matsa mutum sai shegiyar mayata Wai........

Hankadeta yayi hakan yasa bata karasa fadar abinda tayi niyan fada ba sannan ta dubesa aiko hatta jijiyoyin kansa sun tashi saboda Bacin rai聽.

Kofa kawai ya nuna mata Da hannu danshi kanshi tsoran motsi yake dan gani yake babu abinda zai hanashi yiwa zakiyya dukan kawo wuka a darennan.

Zakiyya na ganin haka tasan ta kwabsa domin ko ta bata masa rai Wanda hakan ke nufin bazai hukunta minal Ba tunda dama ta bada Kaine saboda taci uban minal gobe never the less she enjoyed it.

Aiko dole ta gyara kafin reshe ya juyewa mujiya, matsowa tayi kuwa dashi yace out,tace bab....

Kofa ya nuna mata tare da maimaita mata Cewa tabar masa daki rungumosa tayi yace ke banson iskanci meye hakan? tace ban koshi bane .

Wani harara ya watsa mata irin me kika mayar dani kamin ya yakiceta ya fada bathroom yana mai jin zafin hali irin na zakiyya Sam Daga bukatarta ta biya to shikenan shikam ko oho

Son kai yayi mata yawa........ Haka ya dinga sake sakensa yayi wanka tare da wankan tsarki sannan ya fito

Koda ya fito Bai sameta Ba Dan haka ya Shirya abinsa yayi kwanciyarsa zuciyarsa cunkushe ga kuma wutar d茅j脿 vu dake addabarsa yanajin Kamar zaiyi hauka.

Bashi yayi bacci Ba sai wajen 2:30 domin juye juye yaketayi dayaga babu sarki sai Allah kawai sai ya fara kuka hawaye nabin kuncinsa ga wani mugu Abu mai zafi daya tsaya masa a zuciya gameda abinda zakiyya keyi masa.

Abangaren minal kuwa kwashe ceramic din take tana kukan takaici da bakin ciki ita yanxu a haka zata karashe rayuwarta cikin bauta?Allah ka kawomin dauki shine abinda take fadi tana gama kwashewa ta zubar ta gyara wajen sannan ta tafi dakinta wanka ta Shiga ta Dade Kamar yadda ta saba(ko me takeyi oho muje zuwa daganan zamu gano)

Fitowa tayi sannan ta tsaya a gaban madubinta taci gaba da abinda take yi a bandaki kullum tun tana gida har ya zame mata jiki in batayiba batajin dadi.

Bayan ta gama Shirye shiryenta tayi alwala sannan ta kwanta tana mai nazarin rayuwarta

Zakiyya ko koda taje dakin ta Fadawa gadonta tayi tana mai tsaki kana tace kaika sani Idan jarabarka ta matso ka zama kazo ne sannan ta bingire da bacci Ba tare da tayi ko tsarki Ba balle wankan tsarki ko makamancinsa(uhm Allah kyauta)

MORNING

Yau kam minal sai 7 tukunna ta fito yin aikinta Wanda takeyinsa bisa kwarewa bayan ta kammala ta Koma daki tayi wanka ta Shirya cikin atampa blue mai mai circle yellow sannan ta zauna a kan kujera tunda batada right din zama a gado tana karanta wasikar jaki.

Banko kofar dakinta taji Anyi take jikinta ya dauki rawa domin tasan cikin biyu daya ne ko mijin ko matar sa

Aiko yazeed ne yana wani yatsine fiska Kamar yaga kashi sannan yace wato ke gaki hamshakiya ko in bada umarni ki take

Sai yayi murmushin gefen baki to ai shikenan kinga ko Ba Komai zaki ragewa washing machine dina aiki Wanda ke nufin bill din nepa da kuma kudin gas zai ragu domin Daga yanxu聽 ke zaki dinga wankemin singlets and boxers dina Mara mutunci gold digger kawai.(uhm yazeed kenan sai kace kuddin bill din wani Abu yaje rage masa)

Zaki tashi kije dakina ki dibo su yanzu ko sai na wanke miki wannan shegiyar fiskannaki da tafi

Jiki na rawa ta mike zata fita yace "hold on! dakata" ta jiyo wannan karan ranta adan bace

Yace ya zama dole kibi umarnin matata

Batasan lokacin da tayi kicin kicin da ido tace wallah nanne kuma kayi karya na rantse......

Aguje ta fice domin yunkurin da yazeed yayi zai kamota ya gwabe bakin da Kamar zai bita sai ya Fasa ya nufi dinning area yana mamaki Wai yarinyarnan ce ke masa irin wannan rainin wayon da fitsara?

Zuciyarsa ce tace masa what do you expect from a ghetto girl like her?inbatayi fitsara bama sai Allah ya tambayeta(fadi Gaskiya babana?

Dinning room ya Shiga abinshi ya hada tea yasha tare da cin plantain baifi 5 slice ba Sannan ya wuce gym room dinsa.

Minal ko data dauko kayan wankesu tayi tas聽 sannan ta shanya sannan ta koma ta nemi abinci taci

Zata koma dakinta taji ance ke!..ke!..ke! asararriyar baiwa zonan juyowa minal tayi a hasale kawai sai kalaman yazeed ya fado mata

Wani irin kallo takeyiwa zakiyya at any moment zata iya mata illa zakiyya ko dukda tana shakkun captain yayiwa minal din magana ko baiyiba amma bazata barta taci banza Ba

Zaki rama ne? Shiru minal tayi, zakiyya ta tabe baki kana tace zokiyi min tausa

Wani harara ta rafkawa zakiyyan aranta tace wallahi baki isa Ba saide mijinki ya kasheni

tasowa zakiyya tayi tana nufo minal domin dauketa da tafi minal ko rayawa take aranta irin rashin mutuncin da zata antayawa zakiyya Idan ta tabata Dan ita Ba jaka bace

Yazeed ne ya shigo cikin isa fiskannan Kamar bakin hadirin daya taso Daga yamma kamshin Cologne din da yakeyi ne ya Sanar da minal isowarsa

Atake kirjin minal din ya buga kana tsoro ya shigeta amma kunsanta da taurin kai bata nuna Ba saide tanaji jikinta har makarkata yakeyi

Wajen su ya iso ya watsawa zakiyya kallon me kikeyi Anan?tsaki taja ta wuce koda ya juyo ganin Inda minal ke tsaye聽 yaga empty,ta arce.

Zakiyya kam ficewa tayi Daga gidan tana Cewa malam sule idan ya dauko yaranta kar ya kaisu gida ya Kaisu su siyo cup cakes kamin ya kawosu boutique dinta Kamar yadda ya saba

Yace to hajiya Insha Allah ta wuce abinta ta shige cikin 4matic dinta ta wuce .

Don't forget to vote,share and comment pleeease because that is the only way zan gane yadda kukeson novel din.

Taku for life;karamarsu babbarsu wato

Miss untichlobanty馃挄

13th October, 2019.

馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

馃尮@mzz_untichlobanty馃尮

*CHAPTER 32*

Sama ya haura direct dakin minal ya Shiga ya sameta tana ajiyar zuciya yace follow me !

Ta dago idanunta ta kallesa domin neman karin bayani wani electric shock sukaji dukkansu biyu kamin ya waske ta hanyar Cewa ko bazaki iya zuwa bane kin kafeni da inu munafuka?

Shiru still tayi ya fice itama ta bisa subul subul tana mai gyara zaman yellow hijabinta

Koda ta shigo dakin akan coach ta samesa zaune ya daura daya akan daya yace bazaki iya karasowa bane?

Ahankali ta tako a tsure dukda bata bayyana hakan Ba ta tsaya a Dan gefensa

Yace closer tare da mata alamu da hannu ta Dan kara matsowa harara ya buga mata tare da Cewa cinyeki zanyi ta girgiza kai tana mai karasowa da Dan Sauri tsayuwa tayi a kansa

Ya kamo bakin hijabinta ya janyota kasa

Dan kara ta saki domin hijabin ya Dan kurji gefen wuyanta kana visa kuskure ta Dan taka kafarsa kamin ta zube,yace Dan kaniyarki haka zaki tsaya akan yayanki ta girgiza kai yace bakida baki ne tace a'a

Harara ya kwada mata yana mai hadawa da rakwashi kwas a tsakiyar kanta yace bakisan in antaka mutum hakuri ake basa Ba?girgiza kai tayi alamu tasani tana rarraba idanu Dan rankwashin ya shigeta

Janyota yayi ya matse cute pinky lips dinta聽 yana kalla yace wato gani sarkin mahaukata ko ina magana kin bawa banza ajiyata

A hankali hannunta na rawa ta daura akan nashi alamun ya sake bakin zatayi magana idanunta ko ya cicciko da hawaye saboda radadin da bakinta ke mata shikuwa wani yaaaam yaji Ba shiri ya saki bakin kana ya kauda kansa gefe domin jin bananarsa na kokarin kawo masa raini

Ahankali cike da in'ina tace kayi hakuri na taka ka,tsika jikinsa suka mike gabadaya yayinda hawayen da taketa boyewa ya samu nasarar saukowa

Ba tareda ya kalleta Ba yace nace miki kimin wanki shine Dan kin rainani ki kamin jika jika ko?

Muryarta na rawa tace wallahi me kyau Nayi kaga hannuna ma ta nuno masa gefen hannunta yadda yayi jaa Kamar ka taba jini聽 ya fita tsabar yadda ta dirji kayan

Tsaki yaja yace raguwar banza dan kin wanke singlets 3 da boxers 3 Wanda nasa jiya shine zakina wani nokewa Kamar marainiya

Batasan lokacin da tace aide nafi wasu juyowa yayi adan zabure Dan baiyi expecting ta mayar masa da magana Ba

Hannu yasa ya bige bakinta yace zaki tashi kibar gefena ko saina maujeki in canja miki halitta.

Da Sauri tabar dakin tana mai zubda kwalla,lallai tayi kuskuren amincewa da zancen auren Ba tareda ta saurari ko Waye su baba zasu aura mata ba sai a yanzu ne take kara ganin wautarta

Dakinta ta koma ta tsaya agaban madubi tana kallon yadda tayi kyau dukda kuwa ko petroleum jelly bata shafa Ba balle powder amma idanunta sundan fada ciki sannan ta zama kalar tausayi babu walwala a tattare da ita.

Haka rayuwa taci gaba wa minal yanxu har tayi wata 3 a gidan captain聽 tanayin aikinta Kamar kullum once in a while sukan hadu da zakiyya inta gama banbaminta minal kawai ce mata take Allah ya baki hakuri sannan ta wuce itako zakiyya babu abinda ta tsana Kamar tayima rashin mutunci ka nuna bai dameka Ba Dan haka sai tayita kumfan baki tana cika tana batsewa

Minal ko gani takeyi Kamar zakiyya taci noti kuma tana bukatan Sabo hakan yasa bata tanka mata har tayi ta gama

Aunty fauzy ta kawo mata ziyara har sai biyu Inda take kara jaddada mata girman aure da kuma yadda zata zauna da abokiyar zamanta lafiya. Ita dai minal kunne kawai ta kasa Cewa komi aranta ko tana Cewa cab ai bakisan halin abokiyar zaman tawa da mijinta ba da ko zancenta bazakiso muyi ba.

Yau saura 3 days auren zaliha Inda gobe ne za'ayi kamu

Minal nason tambayar captain izini tun last 2 weeks amma tsoro take yau kam shahada tayi ta turo kofar dakin da yar sallama a bakinta aiko abinda ta gani shi ya Daga mata hankali captain ne ya fito Daga wanka Daga shi sai gajeren wando fari kal da bathrobe Wanda ya barshi haka ba tare da ya daure igiyan ba wanda yayi sanadiyyar Nuna dukkan ilahirin faffadar kirjinsa mai dauke da gashi kwance luf luf Wanda keda laushi hamar gashin kan jariri.

Rikicewa tayi a maimakon ta fita saita fada bandaki aiko ta sule sai a kasa Inda ta bige makunin shower sannan ta gurde kafanta salati ta sake tare da sakin wata gigitacciyar kara hawaye kuwa tuni sun Dade da fara ture junansu wajen saukowa yiyinda ruwa ya mata sharkab.

Captain da bai San ta shigo dakinba yaji ihunta atake ya nufi bandakin ganinta shame shame a kasa ta jike da ruwa jakab ya sashi Jan tsaki tare da Cewa ke Dan ubanki me ya kawoki cikin bandaki na bayan yau ba ranan wankewa ba?

Kuka kawai take kamin tace Dan Allah ka taimaka mini wayyo kafata tsaki yaja da Kamar zai fita amma yadda take kuka yasa yaga bazai iya barinta ba yasa ya miko mata hannu aiko hannunta ta mika ta rike nasa take sukaji Kamar sun taba wayar wuta ba shiri ya saki hannun ji yayi jijiyarsa ta fara harbawa Wanda yasashi Cewa kaide kayi asara yazeed acikin zuciyarsa

Sake miko mata hannun yayi ya Dagata

Dingishi ta soma har zasu fita yace dakata !me kike nufi?

Kallonsa take alamun Neman Karin bayani yace au dake a haka kike nufin zaki Shiga dakina ki jika mini da ruwa saboda Yan garinku basuda lissafi?

Bata fiska tayi cikin rants tace badai garinmu ba wallahi

Yatsansa yasa ya dalle mata baki yace dani kike tayi saurin girgiza kai alamun a ah hannun yasa zai cire mata hijabin dake jikinta ta rike kyam kiciniya suka fara aiko yazeed ya riko hannunta duka biyu da hannu daya sannan ya zame hijabin da hannun daya yayi Ciro dashi

Kallonta ya farayi Inda idonsa ya tsaya kyam akan cikakkun breast dinta Wanda doguwar Riga jikinta da ta like mata har nipple dinta ana kallo wani yawun jaraba ya hadiya 'kutt kana ya kalli fiskanta aiko shi take kallo and she caught him staring at her boobs red handed

Waskewa yayi ta hanyar tabe baki sannan yace yanxu dama wadannan tsiyar ake boyewa?uhm aike yarinya bama kida abin boyewa danko tsirara zakiyi yawo bakikai akalleki ba uhm kwaila lamba daya kawai sannan ya fice ya barta a wurin minal ko tabe baki tayi tanacewa jeka dai Nasan borin kunyace kawai kumanima ai jikina tafi karfin mugu sannan ta murkuda baki

After Kamar 1min saiga yazeed ya shigo rike da wata T-shirt dinshi fari kal wulla mata tayi sannan ya fice yana yana mai Cewa yi Sauri kibar Mani daki

Domin alokacin har wani hajijiya yakeji tsabar sha'awa

Dan Rabon da yayi harka sati biyu kenan amma yanagudun abin kunya kuma ai yarinyar gold digger ce so he should be very careful kar mazakutassa takaishi ta baroshi.

Minal ko tsayawa kallon Rigan tayi wai me mutuminnan ke nufine Wai ko bazai bata wando bane?

Jin shiru bata fito ba yasa yace Wai Dan kaniyarki bazaki fita bane kullum kika Shiga bandaki Kamar mai haihuwa

Sauri tayi ta saka rigar tana mai Cewa ko yaushe ya taba ganin sanda nake Shiga bandakin oho mutum sai shegen fi'ili

Iya cinyarta rigar ta tsaya Dan haka ta fito tana jajjan rigar domin rufe jikinta

Aiko yazeed na ganinta sanda yaji numfashinsa yadanyi seizing

Kana ya dawo

Ganin yadda takeyi da fiska ya bashi dariya amma taci mur

Muryarsa Kamar yasha giya yace zonan

Zuwa tayi ta zauna a kasa domin bata manta da abinda ya mata ba sanda ta tsaya masa akai yace me yakawoki dakina ?

In ina ta fara tace dama Ami..niya..ta..ce zata..yi aure shine....nakeson naje

Tabe baki yayi yace naji zaki iya zuwa amma ko gidanku ban yarda kije ba

Kallonsa tayi alamun lafiya kake kuwa ?

Baibi takanta yace zaki iya bar mini daki kuma kitabbata kin kwashe tsummokaranki

Fita tayi tana nazari acewai mutum rabonshi da iyayensa kusan wata 5 amma Dan rashin imani ace bazashi ba ALLAH YA ISA

captain yazeed zaune a bakin聽 gadonsa yana buga game din chase a laptop dinsa Kiran mom ya Shigo dauka yayi

yace salamu alaiki ya habibaty

Mom tace Ameen wa alaikas salam son yakake?

Yace lafiya kalau mom i missed you amma ke naga baki damu da Babyn ki Ba

Dariya mom tayi tace Dan Allah dubeka wani kato dakai Wai baby na kai Wai bazaka barwa 'ya'yanka shagwabar bane?

Kwabe fuska yazeed yayi yadda yara keyi inka kwace musu alewa yace ai kowa da matsayinsa nidai Nasan ni Babyn ki ne ya kashe ido Kamar mom na kallonsa

Mom tace Allah ya kawo masu albarka sannan tasa serious tune tace yazeed naji shirufa bawani labari gashi har kunyi kusan wata 5 da yarinyannan kuma kasan dai daya Daga cikin abinda yasa naso maka aurenta kenan tunda naga kaida zakiyya bakuda tsarin haihuwa kusa ni sai mai shirin Haifa ta haifo mini

Hade rai yayi yana yatsine sannan ya tabe baki yace ai mom yarinyan ce tukunna ina Duba natsuwarta da hankalinta sannan inga ta dace ta zama uwar yayana koko?kuma kinga bata gama wani girma dazan daura mata nauyina Ba.

Sakin baki mom tayi jin abinda yazeed din yace

Yazeed kuwa jin tayi shiru yasa yace mom kina jina?

Kamar Wanda aka watsawa ruwan sanyi mom tace d'annan dama duk zaman da kukeyi da yar mutane Ba bata hakkinta kake ba? Kai a haka zaka rike mata biyun yazeed ?kana danne mata hakki?ja'iri shine harda wani Wai bazata iya daukan nauyinka ba sai kace wani abin arziki ka ajiye acikin wandon naka?to bara kaji yarinyar da kake renawan tsab zata daukeka harda guntu Dan jakar uba kawai........

Sai alokacin yazeed ya gane ya kwabsa Sosa 'keya ya fara kana yace mummyyy kiyi hakuri zan gyara Insha Allah

Mom tace karma ka gyara kai ka jiyota kuma zan dawo kasar inyi sati a gidan naku kamin na Koma gidana na Abuja saboda association Suna bukata na dama Hutu na dauka

Nan dai mom ta surfo masa kwadokwandon bala'i kamin tayi masa wa'azi ta kuma tunasar dashi hakkin matarsa dake kansa sannan ta kashe wayarta tana mai jinjina al'amari irin na tilon Dan nata shiko yazeed tabe baki yayi yace Allah ya kiyaye ni dayin abin kunya da jawakai raini

I will be waiting for聽 your comments

Miss untichlobanty馃挄

13th October, 2019.

[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮

*CHAPTER 33*

Saukowa yakeyi Daga stair case domin zuwa masjid phone dinshi ya dau ringing

Dubawa yayi yaga mom yace yau nadebowa kaina

Picking yayi yana Cewa sweetheart har kinyi missing dinane ?

Ta dayan bangaren mom tace dan Allah ni matsa mini ka rufen baki ka sadani da dadiyata

Marairaice fuska yayi yace haba mummy abin fa baikai nan Ba mom tace yama wuce nan. Zaka hadani da ita inji muryarta koko? juyawa yayi ya fara komawa sama kana ya nufi hanyar dakin minal sallaya ya gani a hannunta alamun sallah zatayi harara ya banka mata sannan ya kika mata wayan yana mata kallon kashedi alamun inata kwafsa zaici ub**ta

Karba tayi jiki na rawa muryar Kamar zatayi kuka tace sallam alaiki, mom?

Ajiyan zuciya mom ta sauke tace wa alaikis salam diyata yar albarka yakike?

Dashi ke wayan a hands free yake聽 captain na jinsu tabe baki yayi yana mai lumshe idanu

Minal tace lafiya kalau mom tace ya hakuri da mijin naki?minal ta dago idanunta ta kafeshi dasu kana ta sauke tace Alhamdulillah

Mom tace sai hakuri kinsanshi baudadden mutum ne ga taurin kan masifa sai kina hakuri kinji tace Toh

Nanfa mom ta fara mata magana akan rashin hada gadonsu ita da yazeed itakam batasan Inda mom ta dosa ba Dan haka koda mom ta karashe kawai Cewa tayi Insha Allah za'a gyara Kiyi hakuri

Shiru ne ya Dan ratsa gurin jin shirun yayi yawa yasa mom tace da

12 / 45