Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
sameni a Sheraton hotel, royal suit daki na uku yace ba matsala sai mun hadu.
Motar luku ne suka ta iso suka fito suna cewa ina president? Wai attack dinka ya tashi ko? Nan sukayi masa jaje domin suma an juyar da kwakwalwar su sannan suka koma side dinsu, kuma a daidai lokacin ne su zakiyya suka shigo ita da Jamal. Yazeed yayi shaking hannun Jamal yace gou are Jamal ko? Jamal yace yup ashe baka manta ba. Dariya yazeed yayi yace ai little sis ta fadamin tace idan naga balarabe toh shine cousin Dina jamal. Jamal yace tabbas kuwa amma ka daina damun kanka, uncle ya tafi babu abinda yake bukata sai addu'ar mu. Mummy ta fara share kwalla kamar da gaske.
A halin yanzu dai abinda suka nuna ma duniya shine baban yazeed ne ya hada jini da larabawa saboda kimanin yazeed da kuma Jamal idan ba haka ba ai mummy yar najeriya ce futuk dan haka basuda explanation shi yasa suka hado wannan karyar tunda dai a zahirin gaskiya mom ce balarabiya kuma sun batar da ita.
????
Koda su lado suka karaso layin su godiya sabi'u yayi masa tare da cewa ya tafi gida shima zai wuce haka suka rabu suna shirya yadda zasuyi mugun sabawa minal idan suka sameta.
Yana raba hanya haka ya shigo har ya wuce sai yaga kamar akwai wani Abu da bai Saba gani ba a gefen itacen mahaifiyar sa. Rakani kashin sa (Nokia) ya ciro ya haska sai ya tuna ashe gari ma ya waye kalla yayi dakyau yaga minal kwance tana bacci hankali kwance. Yace daidai kenan wato kin tagaiyara ni? shine ke kuma zaki kwanta kiyi bacci ko? Toh gashinan Allah ya kawomin ke har gida. Dariya ya fashe dashi Wanda yayi sanadiyyar farkawar ta babu shiri ta fada cikin gidan daidai lokacin ummu amina ta sauke kunun sayarwar ta tana kokarin dauko su mukubur din ta na tuyar kosai taga mutum ya fadi Mata gida salati ta rafka yayinda minal ta buya a bayanta. Daidai lokacin sabi ya fado cikin gidan yana fadin ina take ? Ina ta shiga? Ummu amina tace lafiya zaka biyo yar mutane ku fadomin cikin gida da sanyin safiya? Yace kalli, ummu kalli goshina. Wannan yar iskar ce taji min.
Kallon ta ummu amina tayi tace a ah yar nan Dama kece? Sabi yace kin Santa ne? Tace ai jiya da muka fita nemanku ni da uwani, sai aka fara ruwa anan muka hadu da ita.
Kai miko min kujerar can ta zauna, yace? tashin hankali ai indai ni zan dauko kujera ta zauna saide ta mutu a tsaye. Ba rantse da wallahi idan na shiga na fito bata bar gidan nan ba, zan muku hauka. Yana fadin haka ya banka dakin sa ya shiga. Ummu amina tace dadin abun nice uwar ba kai ba, daga nan ta shigar da minal daki ta zaunar da ita ta bata kunun sannan tace Mata ta shirya su tafi kasuwar gwanjo ta siyo Mata kaya, ta daga kai alamun toh nan dai ummu amina ta gane cewa minal bata iya magana.
Haka suka tafi kasuwa ta zabo Mata kala 5 masu arha da rahusa sannan suka dawo gida. Koda suka dawo sabi bayanan dan haka ummu amina tace ma minal tayi wanka ta shirya sai tazo ta karbi kosai a kofan gida.
??
Yazeed yana zaune a dakin sa, ayush tana hada masa shayi yace little sis banida Mata ne? Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah tayi Mata rasuwa bayan ta haifi safwan. Shiru yazeed yayi kamin yace safwan din ?ana ne? Ayush tace eh shi da yayan sa safwan. Murmushi yazeed yayi yace no wonder nakeji kamar ina missing wata ashe marigayiyar Mata ta ce. Ina yaran suke? Tace sun tafi school is already 8am fah. Yace kikace nine president na jeedmar group ko? Tace ofcourse bro Yace toh gobe zan cigaba da fita aiki. Tace okay but bro kasan ban Dade da dawowa daga karatu ba and you said zaka bani GM kace zaka shirya papers din kuma sai wannan abin ya faru. Yace no problem tomorrow zaki iya fara fita kece general manager na advertisement department. Tsalle ta daka tare da rungume shi tace thank you brother, ya shafa kanta yace you are welcome sweetheart.? Kanshi ne ya Sara jin kalmar sweetheart hakan yasa ya rike kansa. Tace bro lafiya yace nothing ki turomin sahir da safwan din idan sun sawo in gansu. Dariya tayi tace kaji ka fa bro wai ka gansu. Sai kace irin an siyosunnan yace toh ai na manta shiyasa. Dariya kawai tayi ta fice, tana fita daga side dinsa ta daka tsalle tare da fadin yes! Komai yana tafiya yadda nake so.
.......
Ummu amina tana cikin tuya minal ta fito ta zauna a gefen ta, Murmushi ta Mata tace har kin fito kenan? Minal ta daga kai kosai ta zuba Mata ta fara ci tana Mata hiran yadda takeson Allah ya bata diya mace. Tace sai gashi Allah ya bani ke, kinason ki zama diyata? Minal ta daka kanta.
Abinda basu sani ba yan anguwa duk sun taru, labari ya ratsa ko ina akwai sabuwar budurwa kyakkyawa a gidan ummu Amina kuma tana da ciki. Saurayi dake siyan kosan ne yace ummu amina wai a ina kika samo wannan kyakkyawar budurwar? Ummu amina tace kai banason maganar banza diyar nan tawa ce da na Dade ina rokon Allah ya bani ya kawo minaita har gida, kuma harma ina sa ran samun jikoki. Sunan ta Amina.
Kallon minal yayi yace wow nide minal baby zan dinga kiranta sannan yayi kokarin riko hannun minal din. Wani irin kallo ta banka masa tare da Jan dogon tsaki tana mai yin kicin kicin da idanu.
Yace tofah, ummu ai baki sanar dani cewa amina taki batada kunya ba ashe uwar tsiwa ce. Wani kallo minal ta aika masa ta ajiye kosan a gefe ta dafa kasa ta Mike. Wato za'ayi cakwakiya kenan, daidata tsayuwarta tayi ta dun?ule hannu wata Mata dake keken abinda ke faruwa ta window tace tooo, ashe aminar ba ta arziki bace wannan aminatun yar jagwal ce.
Take kan minal ya Sara 'aminatu yar jagwal' ke Mata yawo akai kamin ta yanki jiki ta fadi.
_Nan fa...nan fa...nan fah. Au ashe ruwan biro na ya kare shiyasa na kasa ci gaba da labarin?_
Karku manta kuyi SHARING sannan kuyi COMMENTING hakan ne zai nuna min tsananin kaunar da kuke wa littafin nan da ma mai littafin da kanta.
One love ? from your KARAMARSU? BABBARSU
Miss Untichlobanty ?
30th March,2020.
*??KURUCIYAR MINAL??*
?by miss Untichlobanty ?
INSTAGRAM : miss_untichlobanty
WATTPAD : miss_untichlobanty
TWITTER :miss_untichlobanty
TIKTOK: Untichlobanty
*?CHAPTER 80?*
*RECAP*
Yace tofah, ummu ai baki sanar dani cewa amina taki batada kunya ba ashe uwar tsiwa ce. Wani kallo minal ta aika masa ta ajiye kosan a gefe ta dafa kasa ta Mike. Wato za'ayi cakwakiya kenan, daidata tsayuwarta tayi ta dun?ule hannu wata Mata dake keken abinda ke faruwa ta window tace tooo, ashe aminar ba ta arziki bace wannan aminatun yar jagwal ce.
Atake kan minal ya Sara 'aminatu yar jagwal' ke Mata yawo akai kamin ta yanki jiki ta fadi.
*CONTINUATION*
Mikewa ummu amina tayi tana rafka salati tace na shiga uku aminatu lafiya? Fallawa saurayin Mari tayi tace kai ilu me kayi Mata? Uwani ta Kira ta taimaka Mata suka shiga da minal cikin gida.
Sabi yana karyo kwana yaga taron mutane, baya baya suka fara ja lokacin da suka lura yana tunkaro su. Ashar ga danna yace kai me kukeyi anan wajen? Yaran ne suka ruga da gudu yayinda samarin suka watse suna gunguni? su kuwa Mata yan tasha yan gulma suka dinga Watso magana ta batanci. Matar nan dake leke ta window tace kai sabi'u bamason iskancin banza, kai da uwarja bakuda aiki sai hada tarzoma. Yatsa ya nuna Mata yace ke talatu billahillazi la ilaha illa huwa idan kika kuma kirana sabi'u zanci... tam.
Kofar gidan su ya bankade da kafa har sanda ta karye ya shiga tun daga zaure yake dannawa mahaifiyar sa kira. Ummu! Ummu! Ummu! Tace kai wai lafiya kake Kira na haka sai kace kana bina bashi dalla ka fice kaje ka tuya mini kosai banson shirman banza.
Yace ummu ba nace kar na dawo na samu yarinyar nan a cikin gidannan ba? Tace tunda kai ka haiho ba. Wallahi sabi idan baka fice ka toya kosan nan ba zan fito daga dakinnan in ci maka mutunci. Uwani tace waikai sabi bakada tarbiyya ne? Mahaifiyar ka tana magana kana mayar Mata yace ke uwani babu ruwanki, kuma idan rashin tarbiyyar ne ai gara akan danki.
Juyawa yayi ya fice yana fadin mutane sai shisshigin masifa ko uban me ya kawota gidan oho. Kuma wallahi idan ba'a cire wannan yarinyar a gidannan ba zan muku hauka zan muku bari.
Koda ya fito zama yayi a kujeran yana suya yana banbami wai tsabar an rainashi za'a hadashi da suya. Wallahi babu abinda zai hanashi ketawa minal rashin mutunci.
??
Safina! Safina!! Safina karki fita a gidannan nace ko. Wacce aka Kira da safina ne ta ja tsaki tare da kada kai tayi ficewar ta.
Motar kawarta dake jiranta a bakin kofa tayi shigewarta tare da cewa babe yau? Sheraton zamu je. Kawarta me suna rafisa tace kamar kinsan zuciya ta Dan naji ance this week akwai guests sosai. Figar Motan sukayi bayan sun sake kida kamar a club.
Suna cikin tafiya rafisa ke cewa gaskiya babe mum dinki bata kyauta miki ace big girl kamarki bazata iya using mota ba? Haba this is not right. Tsaki safina taja tace kede bari ai wata rana saina gaurawa wannan matar Mari.
Reception suka Shiga lokacin da suka iso hotel din nan suka tambaya kuma aka sanar dasu cewa yau akwai baki sannan ma ana party.
Nan suka tafa tare da biyan kudin daki saboda kar a hanasu shiga.
Daki Dali suka fara bi suna kafa kunne idan sunji alamun namiji ne kadai a dakin sai suyi knocking idan an bude sai sugani, idan Dan hannu ne shi da kansa zai musu tayi idan ko ba Dan hannu bane sai su basa hakuri suce batan kai sukayi.
Saide fa yau da matsala Dan basu samu customer ba gashi anfara complain cewa wasu Mata na damun baki.
Shawara suka Yanke idan suka duba room dinnan ba customer toh zasu nufi wajen party ne.
Knocking sukayi ba'a bude ba har suna shirin wucewa sukaji alamun motsi hakan yasa suka gyara tsayuwa tare da sake budo wasu bangare na jikinsu. Ana budewa suka saki murmushi amma me zasu gani ayush ce ta bude kofar. Wani kallo take binsu dashi da yake itama safina tanaji da kanta harara ta mayar Mata. Aiko babu bata lokaci ayush taci kwalarta tare da wulla ta chiki daki. Sauri rafisa tayi itama ta fada tana kokarin ceto kawarta yayinda itama safina ta ci kwalar ayush nan fa dambe ya kaure tsakaninsu suna zagin juna uwa da uba.
? Ganin abin yaki karewa yasa goje shiga tsakani tare da fadin wai sweetheart me ya hadaku fada ne tsawa ta daka mishi tare da cewa banza munafuki wato abinda? kakeyi a bayan idona kenan ko? Wato kanada wasu yan? Mata ko? Safina tace ke munyi miki kama da kananun karuwai irinki ne? Wani kallo ayush ta Mata kamin yace ke shegiya ki iya bakinki wannan din miji nane. Kai kuma.... ta juyo tare da sake kallon goje saide kamin taci gaba yayi saurin cewa haba wifey hotel dinnan fa ke kika kama kuma nasan zakizo toh meyasa zan kirawo yan Mata? Sannan da banida gaskiya bazan bari ki bude kofa ba saide ni in bude ince musu su jirani ko wani Abu. Tace ehhh kuma fa hakane amma ya akayi cikin duk dakunan hotel dinnan sukazo dakinnan? Yace tayaya zanyi na sani? Kallon Safinan tayi tare da cewa karamar ka..... safina ce tayi saurin cewa wallahi kina karashe wa saina tsinka miki Mari. Karuwa tana bin maza ne dan kudi Niko ina binsu ne Dan biyan bukatata. Ni safina Usman nadabo nafi karfin kudi wallahi.
Ayush tace what ke yar gidan Alhaji Usman nadabo ne? Safina tace kwarai kuwa. Murmushi mai sauti ayush ta fara tare da fadin yar uwa ai bakiyi bayani bane da wuri, toh amma me yasa kika zabi wannan harka bayan dukiyan da babanki yakeda shi? Tabe baki safina tayi tace wannan harka ta ce babu ruwanki.? Ayush tace hmm malama safina kenan ai yanzu? batun rigima ta kare a tsakanimu ai mun zama yan uwa dariya rafisa dake kefe tayi tace kai jama'a duniya juyi juyi anayi inajin dadi kamar ba yanzu kuka gama fada ba. Ayush tace kinga babu ruwanki ehe, kawai kina nema ki shiga tsakanin yan uwa.
Safina tace malama ya da sauri haka yaushe na zama yar uwar ki? Ayush tace kede bar wannan sanar dani ansar tambayan ki. Tabe baki tayi tace saboda kawai in biya bukatata. Ayush tace toh kiyi aure mana. Safina tace lokacin da nakeson ayimin AI ba'ayi ba yanzu ko ban bukata Dan na Saba da maza dayawa guda daya bazai isheni ba.
Dan tunani ayush ta shiga yanda zata rike safina Dan idonta akan kudin mahaifinta ne. Aikuwa sai ta tuno lokacin da zakiyya ke raki akan jarabar yazeed hakan yasa tayi saurin cewa idan kuma na samo miki Wanda yakeda komai har wannan fa? Safina tace ai babu bata lokaci zan bar bin maza.
Ayush tace rest your case hajiya ta kin samu bani numbarki kawai. Sharing number dinsu sukayi suna ta jin dadi kowa bukatarsa zai biya sannan suja rabu.
Koda safina ta koma gida carko carko ta Sami iyayenta. Baban ta na ganinta ya daka Mata tsawa ke me sunan mama daga ina kike? Nace cabdi,wannan shine ihu bayan hari. Turo baki tayi tace daddy wai kaima irin momy zaka zama ne? Yace shashashan yarinya ayimin shiru. Wallahi idan baki fito da miji nanda 3 months ba babu ni babu ke. Bubbuga kafa ta fara tare ta haye sama tana fadin lokacin da nace ayimin cewa akayi banida kunya yanzu kuma za'a dameni. Mum dinta ne tace idan kika bari na sameki wallahi zan ballaki.
Kallon Alhajin tayi tace Alhaji kaga abinda nake fada ko lokacin da kake bata ta, tazo tace tanason aure kace Sam sai tayi karatu saboda tayi taking over business dinka. Toh gashi yanzu ita auren ma baya gabanta.
Zama yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace hajiya ki yafemin na lalata rayuwar diyar mu guda daya tak. Maganin hawan jininsa ta Nemo masa duba da yanayin sa tasan zai bukace su.
Minal kuwa tana bude idonta tace idan baka da hankali tabani kaga ikon Allah.
Ummu ce tace ke amina tu magana kikayi koko kunne nane sai alokacin itama minal tayi magana hakan yasa ta rungume ummu tanajin dadi.
Ummu tace aminatu yaya sunanki na asali? Minal tace amina ne kuma banda sunana babu abinda nake tunawa. Ummu tace kenan bakisan me cikin jikinki ba? Ta daga kai. Ajiyan zuciya ummu ta sauke tace ina kyautata miki zaton mutumiyar kirki amma da alamu kinada zafi. Nikam zan ajiye ki idan har kika haihu ba'a nemeki ba toh zan aurar dake, kinaso? Minal tace ni banason a rabani da ummu na. Ummu tace karki damu ko gidannan bazaki bari ba.
Fita tayi tare da karbar tuyanta a hannun sabi tana fadin shege ja iya abin arziki amma bakayi da tuyar kakemin kana samun albarka befi maka ba? Tashi yayi yana fadin ko ki karbi wannan abun ko na barar da komai. Kuma na dauki naira dari biyu tace nide karka sake kayimin shaye shaye da kudi na. Yace ke kika jiyo tare da bazata cikin gari.
??
Safwan ne da sahir suka shigo dakin yazeed da gudu suna fadin daddyn mu ya jikinka? Murmushi yayi tare da rungume su lokaci daya suka kwanta mai hakan yasa babu shakku ya yarda cewa yaransa ne.
Ayush ne ta shigo tana fadin kai kuyi ahankali kunsan daddyn ku bashida lafiya.
Dariya sukayi sukace daddy kaji aunty ayush ko? Wai muna damunka ? dariya yayi tare da cewa yaushe yara na zasu dameni?
Ayush ne tace brother akwai abin da nakeson in fada maka. Gyara zama yayi yace kaga dai yanzu 7 years kenan da rasuwar mummy sufwan ya kamata ka kara aure ko Dan su. Jin Jina kai yayi yace wannan gaskiya bari zan Nemo musu mummy, kunaso ko? Suka daga kai da sauri tare da fadada murmushin su amma dai sahir abun bai kwanta masa ba.
Ayush tace AI na samo maka kanason ka hadu da ita? Shiru tayi kamin yace
KO BAN GANTA BA NASAN ZABINKI YAYI DON HAKA ZAN AURETA!
*GENG! GENG!! GENG!!!*
Cabdi akwai cakwakiya fa jama'a.
Me zaku iya cewa gameda CHAPTER dinnan? Ya kuke ganin za'a kaya ne wai.
Karku manta kuyi VOTING tareda FOLLOWING Dina.
Ina matukar kaunarku! Daga taku KARAMARSU BABBARSU
Miss Untichlobanty ?
5th April, 2020.
[4/10, 20:39] Miss untichlobanty Writer: *??KURUCIYAR MINAL??*
?by miss Untichlobanty ?
INSTAGRAM : miss_untichlobanty
WATTPAD : miss_untichlobanty
TWITTER :miss_untichlobanty
TIKTOK: Untichlobanty
*?CHAPTER 80?*
*RECAP*
Yace tofah, ummu ai baki sanar dani cewa amina taki batada kunya ba ashe uwar tsiwa ce. Wani kallo minal ta aika masa ta ajiye kosan a gefe ta dafa kasa ta Mike. Wato za'ayi cakwakiya kenan, daidata tsayuwarta tayi ta dun?ule hannu wata Mata dake keken abinda ke faruwa ta window tace tooo, ashe aminar ba ta arziki bace wannan aminatun yar jagwal ce.
Atake kan minal ya Sara 'aminatu yar jagwal' ke Mata yawo akai kamin ta yanki jiki ta fadi.
*CONTINUATION*
Mikewa ummu amina tayi tana rafka salati tace na shiga uku aminatu lafiya? Fallawa saurayin Mari tayi tace kai ilu me kayi Mata? Uwani ta Kira ta taimaka Mata suka shiga da minal cikin gida.