Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
/>
Wannan hali nata tunba yauba inna ke fama da ita na cillar da hijabi ta ko'ina Ba tare data ninke Ba acewar inna wata rana Zara wulla kan Dan aljani
A hankali ta karaso izuwa bakin gadon sannan ahankali ta janyo bargon dake kan gadon kamshin yazeed ne ya daki kofar hancinta Wanda yasata lumshe idanu tare da kara bude kofofin hanci domin ta shaki kamshi
Wani Abu taji yana mata yawo ajiki amma ta share Dan a halin yanxu bata bukatan wani distraction
Abangaren yazeed kuwa kallonta ma kawai yake takaici ya cika masa zuciya Kamar ya mata suka ya rasa yadda zaiyi
Wani karago ne ya tsaya masa a makokoro flinching and unflinching fist dinsa kawai saiya Komai cikin dressing room din nasa
Minal ko ninke bargon tayi sannan ta ajiye badan ranta yaso Ba sai Dan kada hawan jini yazo ya tarar da ita a dakinsa (aikin gama ya gama)
Gadon ta fara gyarawa sanda ta gyara tsaf sannan ta kalli gadon gaji batada burin dayawuce ta kwanta akai
Kunji mutuniyar Ku fa na dakinta ma anhanata hawa balle na oga kwatakwata
Aiko kankace me,saiga minal ta tsuguna a gefen gadon sannan ta daura fuskanta akai tanashafa gadon da hannunta mai dauke da baby fingers masu tayi da laushi Wanda suka sha lallen amarci
A hankali ta mike sannan tayi abinda ya kawota dukda Cewa dakinnasa Ba wani datti bane dashi domin yazeed dinma Ba baya bane wajen tsafta.
Tas ta gara Komai sannan ta dibi kayan aikinta tayi gaba tare da manta hijabin nata adakinsa.
Shiko yazeed koda ya fito ya kalli Inda ta ajiye hijabin kwafa yayi dabadan dukan mace baya birgeshi Ba da babu abinda zai hanashi gyara mata zama,aiyana irin zaman dazaiyi da ita na halin ko in kula acikin gidan yake. Daga karshe ya tashi ya bude wani kofa na daban Wanda shi kuma balcony dinshi ne.聽
Mika yayi tare da furzar da iska yana mai shafa lallausan sajen dake habarsa Wanda suka a kwance luf luf.
Wayansa ya zaro a aljihunsa sannan ya latso number mahaifiyarsa domin taci ace sun isa yanxu amma yaji shiru bata kirashi ba.
Ringing uku yayi zuwa hudu ta dauka aiko atake yazeed ya shagwabe fuska Kamar tana ganinshi
Haba sweetheart dina ace kin isa tun yaushe amma shine聽 ko ki kira Babyn ki kiji yanake?
Dariya mom tayi sannan tace Allah sarki baby na ai Nasan yanxu akwai wacce zata kularmi. Dakai shiyasa kaga hankalina kwance Ashe har ka task Daga bacci.
Kwabe fiska ya dad'a yi yace haba mommy ni tun dazu na tashi yafadi hakan yana mai tura baki Kamar mom din na kallonshi.
Mom tace ai na dauka yau sai an hada da duka tukun zaka tashi saboda angwanci
Muryan kuka yazeed yayi yace "moooooom!"
Dariya mom ta karayi yace mom yaushe zaki dawo ? Tace aini son bazan dawoba har sai mun kusa sauka. Yace what!? Tace dagaske nake fa shiyasa na Baku space ma idan Ba kawomin labarin danakeson ji Ba tofa bazan dawoba yace haba mana mummy na! Tace uhm kai yazeed ni kaga tafiyana kit yaji ta kashe wayan.
Yasan Cewa she is very serious da abinda ta fada tunda har ta kirasa da sunansa na asali amma shi the last thing he wants to do on earth shine ko hannun yarinyar nan ya tana Allah ma ya kiyaye bara kawai yaje wurin zakiyya su samawa Kansu mafita.
Allah sarki fans Nayi missing dinku inaso inyi updating Mr. Romantic and I amma babu time
Karku manta dayin voting, sharing and commenting.
Love you all馃槝
Karamarsu babbarsu ce
Miss untichlobanty馃挄
7th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 29*
Bai tsaya yin wata wata Ba ya koma cikin dakinshi direct laptop dinshi ya dauko ya haye gadonsa sannan ya kunna CCTV dinsa domin rabonsa da ya Duba meke wakana acikin gidansa run shekaranjiya domin baya bukatar cin karo da kayan bakin cikin da baki ke aikatawa
Koda ya kunna forwarding yayi har izuwa na jiya tukunna ya tsaya
tundaga jiya da yamma ya fara kalla har izuwa Inda aka kawo minal zaliha ya hango tana rawar kai,tsaki yaja cikin ransa yace dubi wata me bakin fiska sai shegen rawan kai Kamar tsohon keke.
Kalla ya cigaba dayi har izuwa sanda mom ta kawoshi wani tsakin yaja tare da yatsine fiska sannan yadan kamo gefen lip dinsa na kasa yana tsotsa saboda takaici forwarding yayi har izuwa yau da safe
Bangaren masu aiki ya kalla yaga suna ta zirga zirgan su once In a while tunda asuba ne yawanci ma alwala Duke kamin sukayi wanka na minal ya Duba yaga ta tashi tana tafiya ahankali Kamar kazan da kwai ya fashewa take tafiya domin baccin bai isheta Ba .
Cikin nutsuwa yaga ta Shiga toilet sanda ta Dade bata fito Ba ran yazeed ne ya kara back a hanklai yace shegiya kome takeyi aciki haka oho...
Can saiga minal tafito tayi sallh ta fita
Duba parlour yayi yaga banan yaje Ba Dan haka ya Duba na kitchen aiko anan yaganta tana neme neme
Tsaki ya kara ja yana mai cizan lebensa na kasa,can yaga tayi murmushi ta dauki tsintsiya ta fita abinta. kwafa yayi wato ma aikin dadi yaje mata tasaba kenan Ba irin zakiyya bace.
Zuciyarsa ce tace masa yo kai what do you expect from a low class human being like her.
Girgiza kai kawai yayi irin zai San abinyi.
Ganin shiru bata dawoba yasa yasan Cewa ta fara aikin Dan haka bai bata lokaci Ba ya canja izuwa na dakin uwar gida sarautar mata.
Yawwnci Ba Komai bane sai yadda take kuka lokaci zuwa lokaci da yanda su sahir ke sha'aninsu hankali kwance illa in sunga tana kuka su tambayeta matsalarta in tace聽 babu sai su goge mata hawaye suna masu jin tausayinta hardai izuwa jiya da akakai minal wajenta da kuma sanda yazo dakin da yadda su kayi fada har yau da safe.
Da wuri yaga ta tashi Wanda hakan yabashi mamaki matuka Dan shidai yasan Ba sallah take akan lokaci Ba yayi magana,yayi fada,yayi fishi har ya hakura amma yau ta tashi da asuba Alhamdulillah shiryuwa ya samu matarsa ta fara gyarawa.
To his disappointment wanka tayi ta Shirya tsaf shirinta na zuwa office Kamar yadda ta saba wani ras yaji a kirjinsa,bakin ciki yayi masa kaluluwa a zuciya,wato ba'a yaban Dan kuturu saiya shekara da yatsu. Ganin ta dauki jakanta DIOR yasan Cewa ta tafi hakan yasa ya koma kitchen yayi playing Daga Inda ya tsaya sannan ya fara forwarding a hankali can yaga su atine sun Shiga Suna hayaniya ba'ajin me suke Cewa saboda yadda muryansu ya kacame Kamar gidan Suna
Parlour yaga sun nufa Dan haka yayi pausing yaje yayi playing na parlour ya fara forwarding aiko atake yayi playing yana mai kara hade fiskaganin abinda ya tsana ta fito tana tafiyar nan nata Wanda ke kara bata masa rai saboda yadda zuciyarsa ke bugawa aduk lokacin daya gani
Shara yaga ta fara tana aikinta cikin nutsuwa da kwarewa,shi kansa idan yace batada kyau yasan San zuciyane kawai amma ai she is not his type worse of all she is a gold digger. Mtswww wani wawan tsaki ya kara ja sannan taci gaba da kalla su binta yagani sun shigo nan yaga sun fara yiwa minal murmushi Suna magana tare kokarin karban aikin duk yadda yayi kokarin jin me suke Cewa ya kasa saboda yadda suke maganar kaman marasa Gaskiya can yaga sun kara hanyar kitchen hakan yasa yayi pausing tare da komawa na kitchen yayi playing aiko gaji yayi sun Shiga kafin suka fara aikin tare sunata hira minal nata musu murmushi
Aransa yace lallai yarinyannan wato ta rainani ko?wato har wani nasu aikin da nasata take kuma har tana murmushi lallai rayuwa batayi mata kunci Ba tukunna kwafa ya kuma yi yana kara gyara kwanciyarsa tare da janyo laptop dinnasa sosai sannan ya kashe Dan takaici ya masa yawa. Ruf da cikin yayi yana mai lumshe rikitattun idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya.
Bayan yayi sallar la'asar ya dawo gida tundaga mai kofan parlour yajiyo kamshin abinci wani kurrr cikinsa ya bada sauti aiko yana dago Kansa karaf ya hango minal tana saukowa Daga stair case sanye take da black short bun da white t shirt sai dogon hijabi mai hannun Dan haka baya iya hango abinda ke jikinta.
He was expecting her takoma da gudu Dan ta buya amma to his surprise yaga tana pretending Kamar bata ganshi Ba
Itako minal kokari take ta Koma kitchen domin Duba abincinta,Dan haka da Dan sassarfa take saukowa,wani Abu yaji ya tokare masa numfashi saboda bakin ciki taga alamun yarinyarnan zata kawo masa rainin sense,Dan haka shima da sauri ya fara yawa aiko minal bata ankare Ba taji tayi karo da gini amma abinda ya bata mamanki shine irin kamshin da gadon yazeed keyi irinshi taji ya bigi hancinta
Taga taga tayi Kamar zata dadi yazeed yayi sauri rikota aiko tsayuwarta na daidai tuwa taji tassss! Ya dauketa da mari wutanta ne ya dauke na Dan wani lokaci.
Yazeed ko baice komaiba kawai sama yayi abinsa ya nufi side dinsa hankali kwance Kamar Ba shi ya kaftawa har mutane mari Ba.
Minal Kam sanda ta daskare awurin for almost five min kafin hawaye ya tsiranyo a idanunta
Ahankli take Daga kafafunta har ta isa zuwa kitchen ta samu har atine ta kashe mata Dan haka kawai tace wa atinen su dibi nasu domin dama yam porridge tayi
Aiko atine tace to aunty Amarya sannan ta diba musu Dana securities din da'ake bawa abinci guntun ta juye a flask takai dakin minal da sallama ta Shiga amma bataga kowa Ba Dan haka ta ajiye kawai ta fice abunta zuciyarta kal yawunta har tsinkewa yaje tana Allah Allah taci abincin minal Dan bazata manta sanda taci tuwo Ba.
Minal ko tana dawowa daki toilet ta fada tabaje akasa sai kuka
Jin alamun antaba kofar dakinta yasa ta sassauta murya
Tanajin anfita ta kara bude makokoro ta sha kukanta Kamar umarni Daga Allah.
Da daddare.......
Show some love by voting and commenting.
Sauri nake so bye, love you all馃槝
Miss untichlobanty馃挄
9th October,2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 30*
Duk Wanda kuke karantawa bakwayin commenting ko voting ina kallonku.
馃ズidan kuka karanta bakuyi voting Ba kuna nufin bai muku Ba kenan.
Asha karatu lafiya
Da daddare minal na zaune a dakinta idanunta da suka kumbura sanadiyyan kukan da tayi dazu sun Dan sace sai ajiyan zuciya takeyi.
Wani azababben yunwa ke nukurkusatta Kamar me Dan haka ta dauko flask din da atine ta kawo mata aiko tana ganin abinci mutuminta ta manta da Komai Kamar Ba ita ta gama sharar kuka Ba
Yam porridge dinta ta cinye tana mai side hannu kamin ta dauki flask din tayi kitchen domin ta wanke
Kitchen din ta Shiga ta wanke flask din kamin ta fito jikinta a sanyaye
Shigar jikinta na dazu ne saide yanzu ta daura zani domin Ba hijabin dazu bane
Zanin atamfa ne mai kyau Wanda ta dauko acikin kayan nata. Wani taku takejiyowa na isa da takama da nuna isa da kuma nuna kowa Ba kowa bane.
Tafiyarta ta cigaba dayi Ba tare da ta waiwaiya Ba domin wani bacci dake dibanta saboda gajiyar da tayi
Staircase ta kama za'a hau gaji an fincikota....Taga taga tayi kamin ta dai daita tsayuwarta da taimakon ginin dake gefenta wani nauyayyan ajiyan zuciya ta sauke kana ta hade ranta ta dago domin ganin wani uban ne yayi mata irin fincikar nan aiko tana dago idonta tage zakiyya ta hade rai tayi kananu da idanu
Ke Dan ubanki ankawoki aiki shine kikewa mutane yawo agida sannan bakisa uniform Ba kuma kinajin alamun mutane baki iya gaisuwaba? Tukunna ma urban Waye ya baki damar hawa sama?oh Ashe ankawo kaskancacciya yar uwarki Wanda batasan dokokin gidan mutane Ba tazo tana tsifo mana iyayi
Ganin minal ta kafeta da idanu Ba tare da tace komaiba yasa tace idan baki dena kallona da wannan shanyayyun idanun naki Ba sai naci ub*nki common get out of my sight useless human being. karbi kikai min wannan sama tunda abinda kikeso kenan.
Atine Wanda ta Shiga domin yiwa uwargijiyatta ta 2 Kumar amaryar oga yazeed tajiyo abinda zakiyya ke Cewa Shigowa tayi ta russuna tana mai Cewa sannu da zuwa aunty.
Zakiyya dake kallon minal ta kallo atine kamin ta kuma kallon minal tace haka ake gaidani agidannan.
Atine ne ta aro wani jarumta kana tace rankin shi Dade ai wannan itace amaryar.
What!?wannan abar me zubin aljanu?
Jikin atine na rawa ta gyada kai kana tace Allah bamu alkhairi ta fice tana mai zazzare idanu alamar kidimewa Dan bata bukatar rashin hankali ana zaune lafiya
Minal kam shiru tayi Kamar wata kulya ta dunkule a lungu daya takaici ya hanata yin komai
Zakiyya da mamaki da kuma kishi ya cikata yasa batayi wata wata Ba tace au Ashe Kece wannan dabbar wacce talauci ta dama akayi auren jari ai da kin sanar dani Cewa kuna bukatar kudi na baki Wanda za'a ciyarda danginki baki daya bawai Kiyi kokarin hada kanki dani Ba JAKAR BAIWA kawai,wuce ki hadomin tea kamin na saba miki.
Minal kam yau da badan sharadin da yazeed ya gindaya mata Ba da babu abinda zai hanata shukawa zakiyya rashin mutunci amma tana tsoro kada wancen azzalumin ya kasheta Dan tasan sojoji Ba mutunci bane dasu bare imani ko tausayi.
A hankali ta koma kitchen din sannan ta hadomata shayin domin atine ta nuna mata Komai da yadda zatayi amfani dasu.
A bakin kofar dakinta ta tsaya ta kasa Shiga zakiyya ko tana Shiga dakinta ta fada kan gado ranta na wani irin kuna
Can wajen 10min taji shiru Dan haka ta fito domin ta antayawa minal rashin mutunci aiko daidai lokacin minal ma ta aro jarumta minal na daura hannunta akan handle din zakiyya ta bude kofar a zafafe aiko take kofin shayi ya watsu musu dukkansu biyu Wanda yamafi zubowa minal din sannan ya fadi ya fashe
Wani wawan mari zakiyya ta kwasheta dashi kamin tace kan buhun bala'i ! ke wace iriyar dakikiya ce dabba kina Abu Kamar jaka!saboda tsabar bakida hankali bare lissafi shine zaki kama ki zuba mini tea ajiki?
To Dan matsiyacin ubanki ki gyara nan wurin sannan ki hado Mani wani kamin in fito Daga wanka.
Minal dago rinannun idanunta tayi ta nuna zakiyya da Dan yatsa kana tace ahir dinki duk haukarki ta kare a kaina tunda dani kike kishi amma kada ki kuskura ki kara sako da iyayena.
Kuma baza'a hado shayin Ba inga abinda zakiyi tana fadin haka tasa hannu ta fara kwashe glass din.
Zakiyya ko a harzuke ta nufi side din yazeed Kamar wata zakanya聽
Bude kofar tayi tagansa ya fito Daga wanka da alama kwanciya zaiyi.
Yazeed ko mayatar ce ke cinsa ya kasa jurewa,yayi azumin,yayi addu'an,yasha magani amma desire nanan Dan haka ya yanke shawarar gara yaje ya samu zakiyyan ko kadan ne ya samu da babu gara Ba dadi. Gwara yaje yayi yanda ya saba ya danyi maneji abinsa Dan shikam hakuri kawai yakeyi shekara da shekaru bawai dan yana gamsuwa Ba Dan tunda sukayi aure da zakiyya baifi sai 3 ya zama satisfied domin Daga tazama satisfied to shikenan fa zata fara raki Wai ta gaji.
Sai gashi Allah ya aiko masa ita tsuntsu gasashe Daga sama
Ganin yanayinta yasa yace Matas ya akayi ne yana mai kashe mata ido tare da fara takowa izuwa gareta tsaki taja domin ta gano me yake bukata kana fara huhhura hanci tana jijjiga tace "baby kaga irinta ko? kaga abinda mom tayi ko?gashinan ai yanxu ta aro maka wata kaskancacciya kuma ma abin haushin Wai Dan tsabar fitsara har ta dubi idona Wai nasata aiki Wai bazatayi ba kuma harda nuna mini Dan yatsa
Rungumota yazeed yayi danshi bayason irin yanda takeyiwa mahaifiyarsa shiyasa duk sanda ta fara zai yi kokarin kawqr da maganan inata dage to saide suyi fada
Turesa ta fara yi ni Dan Allah cikani kai ko wani lokaci sai ana serious Abu sai kazo kawani hau kakabe kakabe ni banson jaraba.
Kallonta kawai yake tare da murtuke fiska Kamar basho yagama mata kalar tausayi Ba sannan ya hankadeta kadan Daga jikinsa yace zakiyya yanxu akan hakkina zaki kirani jarababbe, Toh gashinan nabar maki ki jika kisha nima zan rike abina.
Rigan baccin daya ajiye kan gadonsa ya dauko ya zura sannan ya kwanta tare da Cewa inkin gama zaki iya rufemin kofar daki sannan ya juya
Baiji sanda tahau gadon Ba kawai ji yayi an rungumosa ta baya.................
馃幍i am waiting for your comments
Don't forget to vote
Miss untichlobanty馃挄
11 October, 2019.
4 - CAHAPTER 31-40
馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
馃尮by @mzz_untichlobanty馃尮
*CHAPTER 31
Baice mata kala Ba yanaji ta fara tattabasa tare da masa wasu abubuwa ahankali wani mugun kuma jahilin feelings ke taso masa amma ko dar baiyi Ba a hankali yaji ta fara zurfafawa tsaki yaja kamin yadan matsa gaba kadan still hannunta na jikinshi
Matsowa itama tayi tanakai hannunta kan........ ai babu shiri ya mike tare da cire hannunta yayi wulli dashi
Kana ya fara magana a harzuke Wai me kika daukenine eh?ko kin dauka jarabata har takai nazama banida zuciya ne?ince P kuma nace banaso
Hannunta takai zata riko nashi yace karki kuskura ki tabani kinji na fadamiki.
Tace haba baby kayi hakuri mana kasan raina abace yake lokacin shiyasa na fadi hakan harara ya watsa mata kana ya kwanta Wanda yasa ta fahimci Cewa ya Dan hakura Dan haka ta fara aika masa sakwanni masu birki kwakwalwa aiko dama gogan naku ma a hanu yake Dan haka baiyi wasa da damarsa Ba ya bada kai bori yahau. saide kash zakiyya na zama satisfied ta fara nifa baby na gaji yazeed najinta kuma ransa na kuna danshi ko Rabi baije Ba ta cigaba da cewa ni ka barni na gaji please