Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   44 / 45

129K to 132K   out of 134.5K words

da daya ya basu dukda cewa karami ne shekarun sa bakwai. Amma har yau fa jiya I yau ne kullum sai sunyi rigimar nan dai tasu.

Minal an cakare anci ado sai walwali take tana ta zirya tsakanin kitchen da dinning room zakiyya ce ta shigo da abun koyar tafiyanta Dan shekara 15 a zaune ba wasa bane. Mashkur yace suma gode Allah akwai hope zata iya taka kasa Dan yanzu leave shima ya dauka yazo zai Dan zauna da su yazeed a sake karfafa zumunta da shakuwa.

Hira suka fara ita da minal suna jimamin ko? ina ayush ta shiga? Zakiyya? tace ke ni bar banza AI wallahi ma taje Allah kiyaye hanya. Minal tace uhm uhm fa idan kuma taje ta bata rayuwar wasu yanda taso yi wa namu fa? Zakiyya tace? kuma fa maganarki gaskiya ce toh amma... bata karashe ba sanadiyyar Umma hani da ta shigo da saurin ta tana? fadin uwar daki akwai matsala banga hajiya ba. Minal tace ai hajiyoyin maki yawa garesu wacce ? Tace hajiya babba mana na duba...... hayaniyar da suka jiyo ta window din kitchen yasa ta yin shiru kamin suka fita.

Aikuwa mummy ce ta tattare zani tana sharar gudu kamar mota sharon.kai kace standby generator aka jona Mata ga security da masu aiki sunyi ca sai binta suke amma ta file musu.

Waje ta fice ta ari titi suna bin ta a baya.?? Ba komai take fadi ba sai kai jama'a ga mutuwa ga yan boko haram, ku gudu.

Irin yan acabar nan sun taru dama kawai sukaga Mata cikin kaya mai tsada harda sarkin gwal tana gudu tana fadin ga mutuwa shiyasa kafa me naci ban baki ba? Gudu suma suka fara, wasu nayi adungure su diro daga machine din suyi kolin koli su kwalu da kasa sannan su Mike su cijewa rigar su iska. Irin stop stop dinnan na yan napep suka wuce shugaban wajen sunan shi dogo me babban Riga.

Ana cikin cakwakiya da shi akan kudi ya sakami mai napep kenan zai nana da kasa yaga taron mutane ana gudu cuceshi kawai ake wani fiwt ! Fiwt ! Kakeji abinda akee fada yaji aiko ya sako mai napep din dam a kasa ya fita da gudu shine a gaba gashi yafi kowa tsayi rigar iska ta cikata ji kake fafar? fafar baka ganin komai se babbar rigarsa yayinda yake sambado gudu zundum zundum.

Inyamurai masu saida doya sukazo wucew inyamurar ka bajin hausa suke ba amma sunji Boko haram take suka bi ta Kan doya yayin da mamar su tsohuwa kafa ya hau mazari ji kake curr ta saki fitsari.

Haka suka dinga kwasar mutane, me shayi ne, masu kasa irin kayan marmari a titi ne.... sanda akayi gudu iya gudu aka gaji aka tsaya hutawa dogo yace wai ni wa ya gansu ne samrin nan sukace wannan hajiyar ce.? Yace wai to ma a ina kika gansu ne? Dariya tayi tace zakusha mamakin inda na gansu. Cikin mafarki nagansu in fada muku. Ashar irin ta yan daba ya danna yace wannan matar ta ma raina mana hankali wallahi kai kuyi Mata na jaki.

Rufeta akayi da mugun duka matan inyamuran nan suka zage dantse suka kiranta kamar sun Sami sakwara. Akayi Mata ruf dubu aka jijjibge ta. A TAKUCE de daga nan itama tasan inda dare yayi Mata domin haukace wa tayi dalilin da yasa haukace kuwa shine saboda lokacin da za'a tsafin anyishi ne cewa in dai ayush tana raye mom din yazeed bazata taba yin hankali ba toh yau da safe ayush tayi gaba sanadiyyar cinye gaban ta da aljanin yayi domin satin ta daya a gidan wasu halittu masu Lama da kuda suka fara fitowa daga kasar ta suna cinye Mata fata. Atakaice de tayi mutuwar wulakanci iya wulakanci ga bata sallah ga shirka ga zalinci ai kowa ma yasan makomar ta.

A gida kuwa safina fadi take nikam yanzu komai nawa ne nayi baje baje kawai abinda yamin saura shine na fitar da wannan kucakar matar tasa.? Waka take tana rangaji daure da towel zata shiga wanka saboda ance za'ayi baki kar su kawo Mata raini.

Bude bandaki tayi tana rangaji da juyi. Jijjiga tayi zatayi juyi, juyin ta ke da wuya santsi ya kwasheta ya hada da gini sannan ta fadi ta baya ta doke da toilet sit a take a wajen jini ya cika kwakwalwar ta sai barzahu.? Allah yaji kan mu'umini ameen!

Motar su zaliha ne ta faka a cikin gidan su minal.? Da sauri yaransu me suna kabir ya fito yana fadin wow daddy! Gidan uncle dinnan ya hadu. Kace ya ma sunanshi? Luku yace sunan shi uncle yazeed. Ciki ya shiga da gudu yana fadin kowa ya fito , king kabir yazo. Nine sarki kabir Dan lukman dariya minal tayi tana saukowa tace maraba sannu da zuwa Dana sarki kabir.

Alamun tunani yayi kamin yayi sauri ya riko hannun minal yace kece wannan kyakkyawa matar uncle handsome ko? Murmushi tayi masa sannan tace kaima AI kyakkyawan saurayi ne kabir Dina. Yace toh ya akayi kika sanni? Tace mommyn ka ne ta tura min hotonka.

Dadai lokacin su zaliha suka shigo rurrungume juna akayi aka Dan zubda kwalla abin ka da Mata. A one sitter? zata zauna shima luku na yayi kokarin zama. Tureshi tayi shima ya ture ta. Ture ture suka soma kabir ya girgiza . Dan in da sabo ya Saba ya samu guri tare da fara latsa tablet dinsa yana shan alewa. Sahla ne ta sauko da tayi bulbul da ita tana dauke da juna biyu karami shekaran jiya suka San hakan fadi Dan samri Kaine kanin namu? Dago kanshi kabir yayi yace wow! Kaga mata kyakkyawa fara sol idan na girma yar ki zan aura.

Zaliha ne ta zauna a kujerar luku ya ciccibeta ya dagata shi ya zauna. Dariya tayi tace daidai kenan ta dake cinyarsa. Wani tunani ne yazo masa Dan haka ta kasa kasa ya fara tattaba Mata jiki ganin zai nemi ya tsinkata gaban yara yasa ta tashi kuma duka abinda sukeyi akan idon minal.

Sahla kam tuni game ya 'bage tsakanin ta da mutumin ta kuma sirikin ta acewar sa fa kenan. Hira su minal suka kafa yayinda luku yace ina mutumina ne? Minal tace na barshi a daki yana shiryawa yaci ace ya sauko ma yanzu.

Daidai lokacin yazeed ya fara saukowa yana fadin my man ! Tare da fadada murmushin sa. Rungume juna sukayi kabir kam ajiye game yayi yazo ya kewaye yazeed sau uku sannan ya kalli baban sa yace daddy zan iya zama gidan uncle dinnan Dan inyi kyau? Luku yace kai de da masifar kyau dinka. Indai Abu na da kyau toh kai shikenan kabi ka damu mutane kenan akai.

A mota kuwa tunda zayya ta shiga take ma wa sahir magana amma ko inda take bai kalla ba Dan yasha alwashin koya Mata hankali.

Tace wai me nayi maka ne kawai murmushi yayi Mata yace .......

......

A gidan sabir da bushra ba laifi ana Dan zaman lafiya,yana Dan aikinsa saide me ya lura tunda sukayi auren bushra tayi sanyi dayawa bawai tuban bane kadai akwai matsala hakan yasa yauwa kamar kullum ya tisata a gaba yake tambayar ta matsalar ta. Da Kumar ya samu ta budi Baki zatayi magana ta "ance ana bukatar bone marrow transplant cikin gaggawa da a lissafi na yanzu kwana 20 yayi min saura."

TO WAI SHIN ME SAHIR ZAICE MA ZAYYA ?

KUNASON KABIR KUWA?

YAYA ZA'A KAYA DA JINYAR BUSHRA ? ZATA MUTU KO ZATA RAYU ?

Takuce KARAMARSU BABBARSU,? Jared Ku manta da VOTE, follow And? comment .

Miss untichlobanty ?

https://my.w.tt/WGgiLRPs36

?? *KURUCIYAR MINAL*??

? _By miss Untichlobanty_ ?

? *CHAPTER 96*?

RECAP

A gidan sabir da bushra ba laifi ana Dan zaman lafiya,yana Dan aikinsa saide me ya lura tunda sukayi auren bushra tayi sanyi dayawa bawai tuban bane kadai akwai matsala hakan yasa yauwa kamar kullum ya tisata a gaba yake tambayar ta matsalar ta. Da Kumar ya samu ta budi Baki zatayi magana ta "ance ana bukatar bone marrow transplant cikin gaggawa da a lissafi na yanzu kwana 20 yayi min saura."

CONTINUATION

Salati sabir yayi yace bushra shine kika boye mini baki sanar dani ba ko wani daga gida tace nima a kurarren lokaci na sani shiyasa ma na nemi tuban kowa Dan na fahimci rayuwa ba'a Mata garage sai ta aiko ma Abu alokacin da baka tsammace sa ba.

Riko hannunta yayi tare da zura Mata hijabi sai family house Dina Alhaji mansur domin a fara gwadasu ko za'a samu Wanda yahau daidai a dangi kamin a fita waje wato MRD (matched related donor)

Babu bata lokaci suka nufi asibiti yayinda mom tayi kokarin kiran yazeed amma is not rechargeable Dan haka tabar masa message.

A gidan kuwa su zaiya ne suka iso nan akayi introducing Mata su waye su zaliha. Kabir yaron su luku ne yace la kamar su daya kuma sai ya saka kuka tare da rungume sahla. Cikin damuwa tace menene? Yayinda hankalin kowa yayo kanshi.

Jan hanci yayi yana goge kwalla cikin kuka da shessheka yace meyasa ba'a cemin na shirya ba? Luku yace big boy ka shirya me? Yace ganin kyau mana ashe hassanan rafi kyau kuka barni nayi garajen zabar Mata. Kama haba yazeed yayi Dan ya rasa abin cewa yadda yake zato zance yayinda minal tace iko sai rabbu zayya kuwa waks ta yanko inda ake cewa "ni bazance komai ba Dan zafi ban shafa ko mai ba"

Shiko kabir cewa yayi AI da nasan akwai Wanda yafi aunty sahla kyau da nace yarta nakeso. Riko hannun zayya yayi Mata fuskar abin tausayi yana Mata wani munafukin Dariya yace aunty zayya ta zaki bani yarki? Sai inyi Mata biyu da yarki Dana aunty sahla Dan bakyau daukar alkwari sannan ba'a cika ba da sai ince na fasa nata. Minal ne ta daki zaliha na wasa tunda a gaban yara suke tace zally ke yanzu duk iyayin naki sanda kika juyewa danki kai kuma kana gani ka barta uncle luku? Kabir ne ya kyalkyale da dariya yace daddy dama sunanka luku? Yace daga yau daddy luku zauna ce maka. Zuwa yayi ya shafa cikin sahla dukda ba'a ganin komai yace uwar gida ta ina miko gaisuwa.

Zayya ne ta kama kwankwaso tace "ummi..." wato minal "ni fa ban gane ba wai wannan yaron me yake nufi ne yake ta zancen wani uwar gidansa?" Tsayawa yayi a gabanta ya gyara Riga tare da ninke hannu yace ni nan da kike ganina babban saurayi, ko cikin turawan nan mr. handsome ake cemin Dan haka.......

Wucewa zayya tayi Dan bata da lokacin sa ta zauna a gefen minal tare da cewa ummi ke nake saurare... zana zahir ma yayi yayinda sahla tayi sauri sauri ta zauna a gefen zayya tace sister albishirinki ai kin kusa zama aunty..... zayya tace tun Bance goro ba? Sannan ta washe baki tace kice Allah? Minal tace wai ku bakuda kunya ne? Zayya bata ma bi ta Jan zancen minal ba ta rage murya kasa kasa tace sis bani sirrin... sahla tace yafi karfinki saide kije kice wa mijinki ya fada miki. Zayya tace an gama Dan itafa tunaninta wani abin za'a sha shiyasa ko ajikinta a inda take zaune ta kalli sahir tace bro wai kasan sirrin ? Toshe Mata baki sahla tayi tare da wucewa daki da ita Dan taga alamun kan da matsala.

Hira sukasha sosai kamin yazeed yace ina wayata mu dauki hoton tarihi. Kabir dake game ya kalla yace big boy je ka Kira mana aunties dinka. Sannan yace wa minal ta dauko wayarsa a daki tace aiko kaga mun manta bamu Kira safina ba. Bata rai yazeed yayi Dan shi already ya sake ta tun sanda ya dawo hankalinsa Dan haka yave kirata dama akwai abinda zan fada Mata sai muyi hotan karshe.

Dauko wayan minal tayi ta kawo masa sannan ta tafi kiran safina aiko tana bude bandaki ta kwalawa yazeed Kira haurowa sama sukayi suna tambayan lafiya hannunta na rawa ta nuna musu bandaki salati suka saka. A bayansu sukaji ance kin kasheta KIN KASHE KIN YAR UWA TA.

A asibiti kuwa an gwada su duka family din wato donors su maman ta da nafisa da auntyn su ana tsammanin result sukaga su yazeed sun shigo da gawar safina wajen su sukaje suna tambayar lafiya wata fiririyar fitsararriya ne tace me kuwa ya faru an kashe mini yar uwa toh wallahi za'ayita. Ran yazeed ne ya baci yadda ta hakikance cewa minal ne ta kashe safina. Mari ya falla Mata yace ke bakida hankali ne kinsan cewa wannan magana ba karama bace? Zance ne ya miki dadi har kike Barbada cewa ita tayi kisa bayan kinsan hukuncin kisa ne ga Wanda ya kashe?

Likita ne ya fito ya tabbatar Musu da cewa tabbas safina ta mutu. Daidai lokacin ma likitan bushra ya fito shima yace babu Wanda yayi matching.

Iyayen safina ne suka fito suma suka iso da yan sanda. Yace wacece ta kashe mini ya fitsararriya nan me suna Billy ta nuna minal kamata yan sanda zasuyi yazeed yayi dariyar manya yace da alamu ku din sabbin jini ne bakisanni ba ko? Toh Wanda be sani ba ya sani Wanda ya sani ya kara sani nine nan retired major gen. yazeed ABDULMAJEED umar.

Kuma duk Wanda ya sake ya taba mini Mata toh lallai ya shirya zaman gidan yari. Anyi bincike ne da za'aje ita ta kashe ta ahalin lamarinnan me sauki ne dakinta akwai CCTV kawai dubawa za'ayi.....

Haka dai yazeed yayi musu wankin bargo kamin aka duba footage din aka ga abinda ya faru nan suka basu hakuri akayi Jana'izanta yayinda aka tambayi su yazeed ko they are willing a duba bone marrow su ko zaiyi matching da na bushra. Koda suka koma gida jikin kowa yayi sanyi na mutuwar safina dukda ko ba wani dasawa sukeyi ba.

Anyi jungum jungum a parlour kowa na kallon kowa, zayya de magana daya ke ci Mata tuwo a kwarya,? ganin kamar basu damu ba yasa ta gyara zama. Parlourn yayi tsit Dan haka tayi gyaran murya tare da turo baki tace gaskiya ina magana. Wai ya naga kowa yaki ya fadamin sirrin ne? Abinda ya fito na gaba a bakinta ne yasa kowa yasha jinin jikinsa.

YA SAHIR GASKIYA FA DOLE NIMA KAYI MIN CIKINNAN EHE!

AYI MIN AFUWA KWANA BIYU KUN JINI SHIRU BANYI UPDATE BA BA LAIFINA BANE LAIFIN MAI DAMBU DA TAYI LITTAFI ME DADI.

KARDE KU MATA KU ANTAYO MIN COMMENT TARE DA VOTING SANNAN INA ME BAKIN CIKIN SANAR DAKU CEWA KURUCIYAR MINAL.DINMU YA KUAA YA KARE DOMIN KUWA CAKWAKIYAR ZAYYA DA SAMUN CIKI ZA'AYI SHIKENAN AMMA FA BA SHIKENAN BA DOMIN KUWA SHIMA ZAI BADA KALA SOSAI.

INSHA ALLAH ZAN MUKU UPDATE DA WURI! LOVE YOU ALL?

miss untichlobanty ?

2nd June, 2020

?? *KURUCIYAR MINAL*??

? _By miss Untichlobanty_ ?

? *CHAPTER 97*?

RECAP

Anyi jungum jungum a parlour kowa na kallon kowa, zayya de magana daya ke ci Mata tuwo a kwarya,? ganin kamar basu damu ba yasa ta gyara zama. Parlourn yayi tsit Dan haka tayi gyaran murya tare da turo baki tace gaskiya ina magana. Wai ya naga kowa yaki ya fadamin sirrin ne? Abinda ya fito na gaba a bakinta ne yasa kowa yasha jinin jikinsa.

YA SAHIR GASKIYA FA DOLE NIMA KAYI MIN CIKINNAN EHE!

CONTINUATION

Bata rai yazeed yayi dukda bece komai ba yayin da minal ta dage goshi domin shirme zayya ya fara fita Mata akai. Zaliha ne ta e ke tashi ki bawa mutane waje bamason rashin kunya. Kallon sahir tayi ya kawo agaji amma baice Mata komai ba sai harara daya falla Mata yabar dakin. Tashi tayi a kufule tana bubbuga kafa da yarfa hannu ta tafi dakinta ta fada kan gado kuma ta sake tana fadin to ni me nayi ? Daga cewa inason na haihu shine ya zama rashin kunya? Kowa bayason ya taimaka mini? Toh AI in kunsan wata bakusan wata ba.

Wayarta ta janyo ta rambatsa ma halsey Kira dukda ko tana jin haushin katin ta da zai kare Dan international call kati yake sha kamar me.... ringing wayar ya fara yayinda take gunagunin gara ta Kira halsey Dan yeonsil sai tayi ta tsokanarta kuma bata wani bata shawara arziki ba. Dauka halsey tayi tare da fasa ihu tace besty har nayi missing dinki, nina kings yanzu na iso kasarmu wai shin kinyi magana da yeonsil kuwa? Me yas......

Zayya ne ta datseta ta hanyar cewa ni duk ba wannan yasa na kiraki ba taimako ko ince shawara nake nema. Gyara tsayuwa halsey tayi Dan a airport ma take tace toooo ina jinki.

Muryan abin tausayi zayya rasa tace kinga ni ina dawowa gida kawai sai na tarar yan biyu na tana da ciki.... halsey tace toooo? Kukam hausawa haihuwar wuri gareki daga aure? AI aurennan ma yayi wuri mukam kinga........

Zayya tace zaki saurara ko surutu zaki min? Halsey tace toh ina jin ki.... zayya tace toh nima fa so nake na haihu... halsey tace mene? Kee zayya yar yarinya dake kice zaki haihu shekararki sha shida ne fa idan kika fara Yoon fitsari fa? Zayya tace wai ke bakisan zamanin da suma daidai irin shekarunnan suke haihuwa ba? Wasu ma basu kai ba sun mutu ne? Kuma da mutum be kai ya haihu ba ai bazai dau cikin ba nide yanzu shawara nakeson ki bani a garin ya ake samun ciki? Ajiyan zuciya halsey ta sauke tace toh mude a garin mu abinda na sani shine idan mutum yana neman haihuwa bai samu toh sai yaje wajen baita yayi sadaka sannan ya sanar a tayasa addu'a.

Zayya tace toh toh toh na gane... halsey tace ko kuma... zayya tace a ah ya haka ? Kina fatan kar wannan hanyan ta bulle ne da Zaki bani wata? Ki bari na gwada wannan mana. Kashe wayar na tayi tsabar kaguwa bata jira taji sauran zancen ba.

44 / 45