Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
maimatawa da gudu minal ta rugo tanaso ta fada jikinshi ta rungumeshi amma ba hali saboda jikinshi baki daya ciwone. Dakyar mom ta Mike idanunta sai anbaliyar hawaye suke tace my son? Me zan gani haka? Kaine kuwa ? Ji yadda ka koma. Hawayene ya gangarowa yazeed minal tasa hannu ta goge zakiyya ko tama kasa yin komai kawai kallo take yayinda zaliha ta karasa kusa da mijinta jiki ba kwari riko hannunshi tayi tace ahhh! Ta hararesa kasa kasa tace kaide anyi rago ka duba yazeed jarumi. Turbune fuska yayi yace a haka kika aurenin dai kinga ko bakida bakin magana.
Da badan yanayin da ake ciki ba da babu abinda zai hanasu yin fada. Ciki suka dunguma baki daya batareda sunbi ta kan gawan ba Wanda ya kasance na Joshua.
Tarairaya da kula kam yazeed yashashi a wajen ahalinsa? cikin Kan kanin lokaci duk an since bandage din jikinsa na wuya da hannu ne sukayi saura. Kwance yake kan gado yana anfani da wayana da dayan hannunshi sai ga minal ta shigo niki niki da kayan abinci zakiyya na biye da ita zakiyya ce ta taimaka masa ya zauna minal tace ya yazeed(bata kiransa da yazzy baby a gaban zakiyya) kasan me? Murmushi yayi yace a ah. Tace nayi maka pancake. Murmushinsa ne ya kara fadada yace a lallai yau zanci abinci dayawa.
Zakiyya tace ni kuma zobo na maka yace masha Allah nikam Dan gata ne. Murmushi suka mai kamin suka zuba abincin da zobo zakiyya ce ta zauna a gefensa tana bashi yayinda minal ke masa tausa Kamar yadda dr ya uemura saboda har yanzu baya tafiya dan haka zama waje daya zai iya ja mai matsala.
Dadi yakeji sosai a ranshi sanda yaci ya koshi yayi nat kamin yace na koshi.
Zakiyya tace AI ni mamaki ne ma ya isheni wai yaushe ka fara cin abinci dayawa minal ya nuno yace aunty minal ne ta koyamin ya fadi hakan kamar yaro. Dariya suka mai kamin taja hancin minal kallon juna suka tsayayi. Zakiyya ta lura da hakan aranta tace ya Allah karka raba masoyannan ya Allah ni kuma ka bani Wanda zai nuna min soyayya fiye da wannan. Ganin abin ba karau ba yasa ta tattare kwanukan ta fice dasu tare da rufe musu kofarsu.
Can mutaneku suka farga dubawan da zasuyi sukaga har ta kwashe kwanikan ta fice. Hannun minal yazeed ya riko ya daurata a cinya yace my minal kenan kinsan nayi missing din lips dinki ko ? Murmushi tayi tana Dan sauke kai tace nima domin ta dan rage jin kunyarsa. Pecking lips dinta yayi yace minali na, tace na'am yazzy baby yace akwai wata magana da nake so muyi. Tace ina jinka yace inasonki kuma kema kin sani saide kaddara ta Riga fata domin bazan danne miki hakki ba. Ki saurareni da hankalin fahimta inaso ki sani wannan Abu daya sameni daga Allah ne, hankalinta ne ya fara tashi ganin yana shirin kuka. Shafa kanshi tayi alamun yaci gaba yace ba... zan iya biyawa mace bukatarta balle ta kai ga a Sami rabo. In hankalin minal yayi dubu toh ya tashi amma sai ta dake tace innalillah wa inna ilaihi raji'un!kayi hakuri insha Allah komai zai daidata. Riko hannunta yayi yace inaso ki amince na rabu dake ki samu wani miji kiyi aure domin ko a musulunci zamanmu akwai matsala. Rungumeshi tayi kam tana kuka tace wallahi idan ka kara tunanin rabuwa dani saina falls maka Mari ko da haihuwa ko babu ni zan zauna dakai har abada. Kuka take sosai domin ta tausayawa yazeed saboda yasan yadda yake burin samun haihuwa. Kuka tasha sosai kamin yazeed yace taje ta kiramai zakiyya.
Koda zakiyya taga idanun minal tun daganan tasan akwai matsala cikin tashin hankali tace minal me ya faru? Fada kukayi?girgiza kai kawai tayi kamin tace yana kiranki sannan ta wuce dakinta.
Sallama zakiyya tayi ta shigo amma me? Yazeed ma dai a wargaje take tunani ta fara to kodai sakan minal yayi?
Jiki babu kwari ta karasa ta zauna. Bayani ya Mata yadda yayiwa minal amma batace komai ba can ta sauke ajiyan zuciya tayi salati kamin tace faduwa ce tazo daidai da zama domin kuwa nima ba Dade inaso inzo muyi magana dakai. Bazan boyeta ba tunda nake dakai ban taba gane cewa banasonka ba saida na shiryu,shi yasa ko jini banson hadawa dakai,ashe duk zamannan da muke kudinka da family name nakeso. Da badan kuskurena ba da yanzu kaga jininka domin ni ke Shan magungunan hana haihuwa a baya koda aka Sami kuskure ciki ya shigeni zubarwa nayi. Ina rokonka sa ka yafemin kusa kurai ba bazan kara ba. Tana kaiwa gabannan ta fashe da kuka hawaye ne ya silalo wa yazeed. Indai hakane toh fa zakiyya ta cuceshi amma ya zaiyi ? Dole ya yafe Mata tunda tayi nadama. Paper da Niro ta miko masa tare da cewa na gode da irin soyayyar daka nunamin. Tabbas baka tauyemin hakki ba kuma kikayi tunanin zan rabu dakai Dan abinda ya sameka ne ah ah zan rabu dakai ne saboda na cutar dakai kuma Allah ya kawo me kula dakai kiyimin izini in rubuta takaddar tunda kai hannunka da matsala. Gyada Mata kai yayi yace sau daya ya sake gyada kai. Abin abin tausayi rungumeshi tayi sukayiwa juna dogon sumbata kamar karsu rabu amma dole ta rabu dashi saboda ta kuntata mai dayawa yanzu itama gara tayita dakon sonshi a boye tunda ta nuna batasonshi kuma karya take dukda ko tanason dukiyarshi a baya suna shima tana sonshi. Kawai de ta biyawa son zuciya ne tare da hudubar Sheridan.
Haka ta fito wujiga wujiga ta shiga nata dakin itama sai kuka. Ashe haka zafin zawarci yake? Yanzu shikenan batada aure? Anya batayi kuskure ba kuwa? Ranan ko abinci bataci ba.
Koda yan uwa sukaji lamarin abun Baiyi dadi ba. Barin ma su inna yanda suka nuna kulawa domin da ace wasu iyayen ne rufe ido zasuyi wuce sai an sako musu yarsu, amma su cewa sukayi tayi Wanda yayi Mata idan tanaso ta zauna indai bazata cutu ba.
Wata rana zakiyya tana kokarin fita aiki domin yazeed ya bata manager of art and designing na company din kaya. Sanye take cikin Arabian gown tayi rolling? domin yanzu shine dressing dinta. Tana sauri bata Ankare ba sukayi gware da Jamal? Wanda keta sauri shima Dan yanzu shi da lukman ke managing companies din yazeed hakan yayi sandiyyan zubewan files dake hannunshi. Tasa hannu zata kwashe shi ma yasa hakan yasa ya riko hannunta a take suka hada ido. Wani yanayi ya fara shiga domin tun kamin yazeed ya auri zakiyya yake sonta domin shi yanason Mata masu kwalisa da wayewa (ba wayewar data sabawa addini ba) tuni boyayyar soyayyar ta yunkuro. Zakiyya kam wani bugo zuciyata yayi Wanda abin ya bata mamaki domin bata taba jin irin haka game da Jamal ba.
Kallon hannun nasu dake hade Dana juna tayi shima ya kalla da sauri ya saka tara da Sosa kai ya bata hakuri. Hakurin itama ta bashi kamin ta fice domin duk wani second da takeyi a wajen bugun zuciyarta karuwa yakeyi.
Koda ta fita motanta kin tashi yayi gashi tayi latti sauran motocin kuma duk sanyi kura saboda hunturun sanyin nan da muke fama dashi, wabi sonja tasa ya wanke Mata tana tsaye sai duba lokaci take Jamal yace kinyi latti ko? Zo muje tare in yaso sai a kawo miki motan kinga dai this is your first week at work. Badan ranta yaso ba haka ta shiga suka fice.
Shiru Motan ya dauka Jamal nason ya Mata magana amma ya rasa mai zakice can yace madam zakiyya yau kinyi kyau. Murmushin take tayi tace na gode dukda ko deep down taji dadi amma ba wannan bane a gabanta. Can yace dan Allah in tambayeke mana tace ina jinka yace wai shin yaushe zaki kara aure idonta ne ya ciko da kwalla Wanda Jamal ya lura dashi hakan yasa yace kiyi hakuri bansan tambayan zai bata miki rai ba. Girgiza kai tayi tace AI babu laifinka daganan kowa yaja bakinshi yayi shiru har suka isa kowa ya wuce office dinsa.
Akwana a tashi yazeed ya daina aiki da keke ya fara using sanda sannan ko ina na jikinsa ya warke sai abinda ba'a rasa ba. Zaune yake kan gado yana nazarinsa minal ta fito daga wanka daga ita sai towel yace my beautiful wife wish....? tare da kashe Mata ido daya sarai ta gane me yake nufi amma tace you wish what. Janyota yayi yace DA SO SAMUNE mu raya sunnah nida ke a daren yau. Murmushin karfafa guiwa tamai tace komai yanada lokaci AI . Shafa kanta ya fara yace yau nayi magana da mashkur kuma yace akwai wani dr daya sani may be he can help, a Germany yake so get ready jibi zamu tafi. Tace okay Toh mikewa tayi ta fara cire masa kaya domin shima yayi wanka. Tsokanarta yake yana fadin iye matar yazeed kefa kiba ma kikayi abinki kamar kazar gona ok? Turo baki tayi tace wallahi karka kara cewa inada kiba idan ba haka ba tam. Yace idan na kara menene hukunci na? Ashararan wasa tamai tace kara ka gani.
Lokacin daga shi sai boxers yayinda take tsaye a tsakanin kafafunsa hannayenta zagaye da wuyansa tunda ta gama cire masa kayan. Gyara zama yayi yace minal yar lukuta. Pecking lips dinsa tayi tace wannan hukun ci da dadi yake kice in yita fada. Ya a
Sake cewa minal mama lutiya wannan Karan kumatunsa tayi pecking, maimatawa yayi Aiko ta fara masa cakulkuli tana cewa wannan shine ainihin hukuncin garin sai ya Rama ya tube Mata towel aiko tayi saurin gyara tare da cewa waiyo. Dariya yayi yace kwantar da hankalin ki ko duka matan duniya zasuyi tsirara babu abinda zan iyayi a halin yanzu. Murmushi kawai tayi kamin ta taimaka mai ya shiga toilet din jacuzzi ya shige abinsa da wandon shi yace ta tsaya a waje ya cire sai ta karba tunda ita uwar kunya ce.
Koda ta karba ta jiya zata fice ya janyota ta fantsama cikin ruwan sannan ya cire towel dinta dayasha ruwa yayi firo dashi. Kokarin tashi takeyi yace bara in zuba ido dakyau kina mikewa inga bulus kinga yanzu rose dinnan da muka zuba akai ya rufa miki asiri. Kuka ta fara mai.........
KSI JAMA'A WALLAHI NA GAJI.
MASU KUKAN MUTUWAN YAZEED SAI A DENA KO ?
ME ZAKU IYA CEWA GAME DA ABINDA YA SAMU YAZEED?
SHIN KUNA GANIN ZAKIYYA DA JAMAL ZASU DACE?
DAGA KARSHE WANNAN PAGE SADAUKARWA CE GA @?+234 703 556 2830? @??ɑl??× ?arhanah ?? @?+234 902 212 9952? @?+234 701 059 1165? @?+234 803 932 5035? @?+234 703 555 1832? @?+234 806 563 6189? @?+234 906 569 4954? @?+234 814 123 0581? @?+234 906 132 2838? nagode da comments dinku? sauran ma naku yananan tafe.
NAMECY @?Ma'ani??? na sadaukar da Rabin littafinnan kacokan agareki ina godiya da support da kika nuna min Allah ya barmu tare nagode baki dayanku.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU
Miss Untichlobanty ?
31st January,2020.
*ANOTHER BANGER*
*??KURUCIYAR MINAL ??*
?By miss_untichlobanty ?
*?CHAPTER 72?*
Kuka ta soma mai tace kai yazzy na wannan fa ba adalci bane,fuskar yara ya Mata yace sorry my love kawai inaso muyi wanka tare ne. Turo baki tayi tace ni yanzu gaka fa sanyi nakeji. Lips dinta na kasan ya kamo ya tsotsa,murmushi tayi tare da rufe fuskarta a kirjinsa. Shima murmusawa yayi tare mai sauti. Dagowa tayi ya dangwali hancinta yace wa yaga minal Dina a kasar waje. Dariya tayi tace kyau kenan.
Haka sukayi wanka suka fito suka shirya tace yazzy baby yace na'am tace? in the next 2weeks birthday Dina ne fa yace haba? Tace eh yace wow ok.
Zaliha zaune a parlour tana kallon zee world taga an mayar Mata tashan ball. Kicin tayi da ido tare da juyawa aiko kamar yadda take tsammani luku ne a tsaye a bayan kujeran da take. Murmushi yake sakar Mata da ka gani kasan na neman magana ne.
Tsaki taja tare da cewa menene haka ni ka miyar min bakaga ina kallo bane ? Shafa gemunshi yayi kamin ya jewayo ya zauna a gefenta tare da riko hannunta. Fincikewa tayi tana aika masa harara janyota yayi zai rungume ta Mike a take tana mai kallon sama da kasa tace wai me kake nufi ne? Kallonta kawai yakeyi kamin shima ya Mike matsowa ya farayi a take gabanta ya fara lugude saboda wani Abu da ta gani a idonsa. Ko wani takunsa daya tare da zuciyarta yake bugawa jin ta hadu da bango gashi kirjinta na gogan na luku yasa gumi karyo Ma ta. Hannu tasa a kirjinsa jiki babu kwari zata hankadeshi amma ta kasa. Hannunsa daya yasa ya kamo nata duka biyu tareda likawa da bango a take ta hadiyi wani yawu kutt. Gaba daya ta tsure ta rude ta kidime sai zazzare ido take numfashinsa ke sauka a fiskanta har ya hade goshinsu. Dayan hannunsa yasa ya riko fuskarta tareda fara shinshinar wuyanta. Ido ta rufe ta ruf yayinda take juya kai gefe domin bashi dama. Jin ya tsaya yasata bude ido. Kallonta yake yana kunshe dariya aiko suna hada ido ya fashe da dariya baya ya fara yi yana dariya harda kama ciki tareda nunata. Cikin dariya yace dubata kin dauka wani abin zan miki sai anyi magana ki bude bakin cakwaikwaiwa kice bakyaso na. Harara ta zabga mai kamar idonta zai fita tare da tsaki ta wuce bangan bangan ta fada daki tareda buga kofa. Kan gado ta fada ta fara chatting ko ta huce haushi ji take kamar ta kamoshi tayi masa dukan tsiya.
Bayan ya gama kallon ball dinshi ya shiga dining area babu abinci kitchen ya shiga shima yaga empty.
Knocking yayi har sau uku amma ba'a amsa ba hakan yasa ya Shiga kai tsaye kwance ya sameta tayi bacci a ruf da cikin tana chatting messages sai shigowa yake kwanciya yayi luf Akan bayanta tare da zura hannunsa ya rungume kunkuminta. Cikin bacci taji Abu me nauyi ya danneta hakan yasa ta bude ido badon taso ba Dan mafarkin sulaiman dinta take wai har sun haifi yara.
Kamshin turaren lukman da taji shi ya tabbatar Mata da cewa shine ba kowa ba. Kokari juyawa tayi amma ina linzami yafi karfin bakin kaza.
Yace my wife ina abinci na tsaki taja tace ban dafa ko kaga alamun nayi girki ne? Nifa la takuramini ehe maida bakinka kace kowa yayi rayuwarsa yanzu kuma zaka wani zo kana likemin. Wata bazawarar Dariya yayi yace hmm bakida dama nide yanzu ba fada naso nema ba so nake ki dafa mana abinci. Dariya ta sheke dashi dashi tace idan naki fa sai ayi kaka?
Yace ki ki yi din kiga ikon Allah tace toh baza'ayi ba. Zip din Riga ya fara bude Mata tace me hakan bai kulata ba ya fara? balle Ma ta bra yace ince bazakiyi ba tace waiyo kayi hakuri dan Allah zanyi wallahi zanyi yace good for you. Rufe Mata yayi ya rufe zip din kamin ya ciccibeta tana wantsal wantsal bai direta ko ina ba sai kitchen a gaban gas cooker yace fara harararsa tayi tace toh ba sai na hada kayan ba lo kanka zan dafa? Hade rai yayi yace baki daddara ba ko? Janyota yayi da karfi ta fadi jikinsa take ya fara kissing dinta a zafafe tun tanajin sugar har taga ba haza ta fara kuka. Shikam yama mance Dan kokarin bude Mata zip ya fara karan kuka data kara shi yasa ya dawo sense dinsa saketa yayi tare da goge bakinsa sannan yace na baki 10mins ki dafo min abinci ki kawomin. Da sauri ta girgiza kai yace good kamin ya fice yana murmushi itako gaba daya ta tsure da sauri ta daura indomie. Tana cikin zubawa a tukunya yace saura minti 2. Ta sake rikicewa hade hannu biyu tayi a gaban gas cooker tayi kneel down tare da cewa kayiwa Allah ka dafo na shiga uku waiyo. Lukman dake labe yana Mata video sai dariya. Itako hawaye take tana yarfa hannu tace noodles ka taimaka ka dahu kar ya dawo waiyo na shiga uku.
Koda ta kawo yace kinyi lattin minti biyu 2 rau rau tayi da ido tace kayi hakuri abincin ne bai dahu ba. Yace hmm zanyi tunani juyawa tayi zata tafi ya make mazaunanta ta jiyo tana kallonta da mamaki yace ko zaki Rama ne da sauri ta girgiza kai tana shigewa daki tace Allah ya isa na kamin ta rufe dakin da sauri Dan mugun tsoron lukman ta farayi.
Minal kuwa karatu ta koyawa yaranta kamar kullum yanzu har sun haddad izu biyar sannan sunyi Rabin hakkul Mubin su usulus Salasa ma duk sunyi nisa azkar ma haka.
Wajen zakiyya taje suka sha hira abinsu domin yanzu sun zama aminan juna. Minal tace nikam ina Jamal fa ya kuka kaya? Murmushi zakiyya tayi tace hmm ai in fada miki...........
Zakiyya zaune a office taji anyi knocking amsawa tayi tare da bada izinin shigowa ba tare da ta dauke idonta daga kan screen din system dinta ba. Zama yayi a daya daga cikin kujerun dake gabanta,kamshin turarenshi shi ya sanar da ita cewa Jamal ne ba kowa ba hakan yasa ta dago suna hada ido ta masa murmushi. Gaisawa sukayi yace ya aikin ? Tace Alhamdulillah gashinan muna fama. Mikewa tayi domin hado masa tea sai binta yake da kallo har ta gama, ahanyarta na kawowa tayi Tuntube da rug din dake shinfide a office din cup din ya fadi ya fashe ita kuma ta fada jikinshi kallon kallo suka tsaya yi kamin tayi saurin mikewa tana fadin astagfirullah am sorry. Gaba daya tama rikice rashin sanin abin yi yasa ta sa hannu ta fara dauke kwalaben amma kamin jamal ya hanata har ta yanki kanta.
Yace subhanallah tare da rike yatsan yana fadin wa yasaki ? Da kin Kira anzo an miki AI dubi kinjiwa kanji ciwo itakam bata masan yanayi