Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 45

69K to 72K   out of 134.5K words

sannu da zuwa sannan ta dauki office bag dinshi zata juya tana fadin zo muje kasha ruwa ka Shirya ko bak.....? bata karasa Ba yazeed ya finciko ta ta fado jikinsa turo baki tayi tareda fadin kaga ka batamin kwalliyata ko?dariya yadanyi tareda Cewa ina kwalliyar Anan ji yadda kika lafta man baki.

Tace kana nufin banyi kyau Ba?yace wa ni na isa?irin wannan kyau dakikayi ai ko Amarya kawai dai kin tunamin da ranan dana fara ganinki. Turo baki tayi tace shine kukayita min dariya ko? Shafa bayanta yazeed ya fara tareda fadin Kiyi hakuri baby na lokacin ai bansanki Ba.

Kuka ta fara bilhakki da Gaskiya harda shessheka tace shine kuma....kuma ranan da na Shiga motarka...ka..kaci zalina a gidannan har ciwo kaji min. Serious face yasa tare da gyara zama mai kyau sannan itama ya gyarata sosai akan cinyarsa murya kasa kasa abin tausayi Kamar wani maraya yace Kiyi hakuri MINAL dina kinsan kuskure ne da Bacin rai sannan kuma da rashin sani amma Nayi miki alkawari Indai ina cikin haiyaci bazan kara cin zarafinki Ba tace kuma har lebena ka dalle Mun馃槶 yace na tuba please tareda hada hannaye. Hannun Nasa ta riko tare da turo baki da alamu zata fara shagwaba ne tace to na yafe maka amma da sharadi.

Zaro ido yayi yace yafiyan ma sai an kara min sharadi?yace toh ko bakaso a yafe ne? Yace a ah Ba haka nake nufi Ba inajin wannan sharadin.

Janyo kunnansa tayi tace tashimuje daki ka Shirya sai.......

Yace ehm sai me?gyaggyara tayi ta kwala masa ihun SAI MUJE KACI SINASIR! Sannan ta diba a guje Yazeed har wani zuuut yaji a kunnansa tashi yayi hannunsa daya kan kunnansa yana fadin yau kin Shiga uku a hannuna.

Dakin ya bita ya samu tana hada masa ruwan wanka.

Ban dakin ya Shiga bayan ya ajiye jakankasa aiko tana ganinsa ta bude baki zata kwalla ihu ya hade bakinsu.

Mukut! Ta hadiye ihunta tare dayin lamoo a jikinsa. Murmushi yayi aiko ya fara mata cakulkuli. Dariya take kyalkyalawa tana bashi hakuri shima sai dariya yake mata yana fadin zaki kara min ihu a kunne?tana dariya harda hawaye take fadin ban karawa waiyo Allah cikina,kayi hakuri bazan kara Ba.

Garin shure shure ta bige makunnin shower nan ruwa ya musu sharkaf.

Dakyar yazeed ya lalumo ya kashe saboda karfin ruwan guduwa zatayi ya janyota jikinsa tareda fadin ai baki isa ki shigar min daki a haka Ba. Tace to kaima a jike kake ai yace dama ni wanka zanyi kinga sai mutu tare ko馃槈?

Girgiza kai tayi tace a ah fa ni iskanci na baikai nan Ba. Yazeed yace hmmm to ai sai ki jira inyi wankan in dauko miki kaya ta Daga kai alamun Toh.

Hannu yasa a ruwan tunda bata tana hada masa Ba yasanyi.

Kallonta yayi yace irin wannan sanyin ruwa haka. Tace to ai ni banga famfon ruwan zafin bane kuma famfo kawai na iya budewa ban iya aiki da sauran abubuwannan ba. Yace zo kigani Toh. Matsowa tayi nan ya gwada mata suka controls din jacuzzi din tare da aiyukansu sannan yace ga Inda zaki dinga ganin temperature din ruwan kuma ni ina wanka a 40掳C. Gyara kai tayi yace good yanzu kunna Inda zai dumama ruwanda kika zuba Daga famfo.

Kunnawa tayi tana monitoring temperature din ruwan yana zuwa 40掳c ta kashe yace give me five suka tafa yace my baby minal Ashe kanki yanaja. Tace ka dauka ni din wasa ce? Yace ko kadan kayanshi ya fara cirewa minal ta juya fuskannan yayi ja saboda kunya. Murmushi kawai yayi ya Shiga Ba tareda ya rufe glass dinba.

Dan karkarwa kadan yaga tanayi yace baby minal?tace na'am yace bude drawer din can ki dauko min turaren wanka na. Toh tace taje Inda ya fada mata ta fara dauko abubuwa tana shinshina har ta sami mai kamshin turare ta dauko ta dawo Inda take dazu sannan ta miko masa.

Yace kinmin nisa ai yana smirking Dan shi yasan me ya Shirya mata. Matsowa ta sakeyi tare da mikowa aiko ya cafkota ya janyota findummm! sai acikin ruwan.

Bata fuska tayi tana hararan yazeed yaja hancinta aiko ta fara dukansa.

Hakuri ya fara bata yana dariya. Batasan me yabi ta manya Ba sai tsintar kanta tayi tana mai core kayanta itama yazama Daga ita sai bra pant.

Ruwa ta fara watsawa yazeed tana fadin tunda so kake Nayi wanka dakai bari in haka ruwa.

Funcikota yayi shi zai bata ruwan tace waiyo Allah kayi hakuri aradu ban iya linkaya Ba. Yace me kuma linkaya?

Tace iya ruwa mana yace kina nufin swimming? Tace nima bansan sunanshi ta turanci Ba yace swimming ne. Oya say swimming tace smimming Jan kumatunta yayi yace swimming Ba smimming ba. Tace swim..ming? Yace hmm swimming. Tace swimming yace clap for your self. Tafawa tayi YAZEED yace kinason ki koyi swimming ta Daga kai yace to zan koya miki kinji ta sake Daga kai.

Nan yazeed ya fara koya mata sunayen abubuwan da yake toilet din. Sanda aka zo kan jacuzzi, kasa fada tayi Daga karshe aka barta akan jazuki.

Koda sukayi wankan yazeed ya dauko musu bathrobe guda biyu ita ya mata burgujeje saboda Ba size dinta bane dariya yazeed ya dinga mata yace muje daki inyi mana ordern couples bathrobe ko?tace menene couple kuma yace mata da miji.

Fitowa sukayi minal ta nufi dakinta ta bude wardrobe dinta tana nazarin wani kaya ya dace tasa sai ga yazeed ya shigo zuwa yayi ya fara hura mata iska a gefen wuyanta ta Dan zabura tare da fadin har kaban tsoro yace maganin mai Baron kofa a bude.

Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita sannan ya dibi wasu kaya Daga cikin nata. Wani Riga ya miki mata me hotan lulu Katy yace tasa yana zuwa sannan ya nufi dakinshi kayanta ya jera a gefen nashi na hanging yayi hanging dinsu sannan ya dawo ya Dino Nashan iska da bacci ya zamu harta Shirya tana shirin fesa turare.

Zuwa yayi ya karba shinshina sannan ya ajiye ta kalleshi alamun lafiya girgiza kai yayi tare da fadin karki shaka wannan kisa Wanda kike sawa kullum.

Dan zaro ido tayi tace ya akayi kasan kamshin turarena ? Matsowa yayi yaja hancinta tare da fadin shinshinar ki nakeyi duk sanda kikazo kusa dani馃槈 gwaliyo tamai tace ai nima Nasan kamshinka yace hmm you are not as innocent聽as you act tace meh? yace babu.

Shafa turarenda da take shafawa tayi dama innace ta bata. Dakin yazeed suka nufa yace da fatan kin Shirya?tace na me fa? Yace muje zaki gani.

Zaunar da ita yayi a bakin gadonsa sannan yaje gaban madubi ya janyota drawer dozen din 60leaves da kwalin bairo ya dauko ya mikawa minal yana murmushi yace dazu na siyo miki wannan dashi zamu dinga yin karatu.

Karba tayi tana Washe baki tare da jin dadi ta rungume yazeed tana fadin waiyo yazzy baby na na gode yanzu nima zan iya karatu. Sakeshi tayi tare da fara tsalle a tsakiyar gadon tana fadin yay! Nima zanyi ilimi zaliha sai kin iso!zaliha sai kin iso !

Yazeed ne ya rikota tareda da fadin ke madam zaki kara Mani gado bakisan kin girma bane yar lukuta dake. Hararansa ta farayi yayinda dariyar nan ta dauke. Kicin kicin tayi da ido tareda fadin nice yar lukutar? A tsorace yazeed ya girgiza kai Kamar da haske tareda fadin Ba haka nake nufi Ba.

Tunkaroshi ta farayi Kamar zakanya yayinda yake baya yana Daga hannu alamun yayi surrender.

Ganin ta hayaiyako ta iyo kansa yasa ya arce a guje. Nan fa suka fara nuna fasaha da kwarewa wajen iya gudu. Sanda suka wargaza dakin kaf kamin minal can ta tsaya tana haki tareda fadin na hakura ka tsaya.

Zuwa wajenta yazeed yayi shima yana haki. Ruwa ya dauko musu a fridge din dakinshi sannan yace ai sai mu gyara dakin ko?minal tace Toh tana kokarin saita numfashinta.

Bayan sun gyara minal ta dauko takarda daya da bairo daya sannan ta ajiye sauran. Zama yazeed yayi tareda Cewa mu fara ko?murmushi take sake masa yace hajiya lafiya dai ko?ko bakyason karatunne?

Pillown da take boyewa a bayan ta ta fara dukan yazeed dashi tana fadin ancema na hakura ne? zaka kama ka kirani yar lukuta?dauko pillow shima yayi nan suka cigaba da jifan Muna da pillow kamin ta fara yiwa yazeed cakulkuli tana Cewa ya kaji abun? Dariya yazeed yake yana Cewa Kiyi hakuri,na tuba,bazan kara Ba,waiyo cikina,cikina fitsari nakeji.

Dariya ta fashe dashi shima yazeed din dariya yaci gaba dayi. Sanda dariyan ya lafa yazeed yace maza ki matso muyi karatu. Tace fitsarin fa? Tana dariya kasa kasa yace ai na fada ne Dan Nayi escape.

Matsowa tayi tace amma fa yunwa nakeji yace muje muci Toh Dan nima yunwan nakeji.

Abincin sukaje sukaci yazeed sai Santi yakeyi Anan yake ce mata ai bai taba cin abincin dayake mai dadi Kamar nata Ba. Sannan Gobe tayi abinci dayawa Dan su mom da Dr Mashkur zasuzo. Dadi ta dinga ji har yazeed yana mamakin yaushe suka saba har haka.

(Dan wasu matan da ance surukarsu zatazo Kamar ance mutuwanta zaizo. Wasu ma ko auren mutum basayi Idan uwarshi tana Raye sai kaji Suna "da fatan dai bashida hawan jini" Wai sirikarce hawan jini! Allah dai ya kyauta ya ganar damu amma lamarinku akwai gyara.)

Jinshi kawai takeyi Dan tasan yana cikin sinasir ne kawai. Wai bai tabacin abinci mai dadin shi Ba.

Tace yazzy baby, yace umm? Dan bakinshi ya cika da abinci. Tace wani abinci kafiso ne yace eh Toh ada dai pancake ne amma a yanzu tuwo ne.

Dariya tayi tace aiko kaci sa'a na iya pancake Dan aunty fauziyya tana sonshi sosai.

Yazeed yace Toh kimin gobe. Ma'ke kafada tayi yace please tace nope yace pleeaase! Ta sake Cewa nooo turo baki yayi Kamar zaiyi kuka tace fine zanyi. Murmushi yayi yace iye my baby kin lura da Cewa kin fara sirka English word acikin Hausa kuwa?dadi ta fara ji ya miki mata hannun hagu suka gaisa yana fadin congratulations baby! Murmushi tayi tace thank you, yace you are welcome. Shiru tayi yace my pleasure zakice ta gyada kai.

Abincinsu suka cinye cikin jin dadi sannan suka Koma daki.....

Kinga sister murmushin ya isa haka kar bakinki yayi ciwo馃槣

Yau no dogon surutu kawai I love you wujiga wujiga. Duk wacce batayi commenting ba kuma ta karanta itace ma'kiyiyar su yazeed dinnan. Thank goodness its not my handwriting馃樁

One more thing; NEXT UPDATE BA CHAPTER BANE QUESTIONS AND ANSWERS NE. ZAKU TAMBAYI CHARACTERS DIN TAMBAYOYI A COMMENT SECTION SAI IN ANSWER MUKU A NEXT UPDATE HOPE KUN GANE ABINDA NAKE NUFI? SANNAN ZAKU IYA TAMBAYANSU KOME KUKESO.

CHARACTERS DA ZAKU TAMBAYA SUNE KAMAR HAKA:

1. Yazeed

2. Minal

3.zakiyya

4.zaliha

5.lukman

6.mom

7.inna da baba

8.dijeh

9.ya abubakar

10.Laila

11. Jamal

12.Mashkur

13. Unknown makiyiya

Da fatan zaku tambayesu ?

Takuce karamarsu babbarsu,karamar tsuntsu me babban gida.

Miss untichlobanty馃挄

18 December, 2019

IDAN AN SAMI TAMBAYOYI DAYAWA TO ZASU ANSWER YAU IDAN BA HAKA BA SAI GOBE

[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty馃挒: *馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL 馃弳馃弳*

馃尮by miss untichlobanty馃尮

*CHAPTER 59 IS LOADING..........*

A Gaskiya bazan boye muku ba inajin dadin comments聽 da goyon bayan da kuke bani alla h ya barmu tare.

Saide wani hanzari ba gudu ba na lura da Cewa bakuyin sharing kuma a Gaskiya Allah ya gaji ban fara rubutu Dan Nayi Suna ko wani Abu ba. Na fara rubutu ne domin na fadakar kuma na nishadantar kinga Idan har wasu bazasu karanta su karu dashi na Toh ba anfani ai.

Anyway enjoy!

馃尮馃崁TO YAZEED馃尮馃崁

Q1. yazeed shin kana ganin minal zata soka?

A. Kaji wata tambaya to dama Dan wa akeyin littafin badan Inda ita bane? So na wajibun.

Q2. Yaushe ka fara son minal ?

A .nima ban saniba Gaskiya.

Q3. zaka saki zaliha a nan gaba

(Yazeed yana harara) so kike untichlobanty ta shafeni a labarin saboda na bada Satan answer?

Q4. Waye kake ganin yake muku Muna furci a gida ?

A. Da nasani zan bata lokacin wajen kawo likita Dan yayi wa Jenifer magani ta warke ta fada min ne?

Me tambaya:Allah ya baka hakuri.

Q5. Idan ka kama me hada maka zafi a gidan ka me zaka mata? Ooooo kun fiya tambaya wallahi. Ke untichlobanty ki kwashe wa dannan fans din namu Kuyi gaba.

Untichlobanty: (kasa kasa) kaifa Ba ubana bane balle ka bani umarni ko ka tsare ni.

Yazeed: me kikace?

Untichlobanty:(ina tutturo baki) banyi magana Ba. Sisters kuzo mu tafi wajen minal

馃尮馃崁TO MINAL馃尮馃崁

Q1. Ya kike jin zamanki da yazeed?

A. Gaskiya Ba laifi Dan ban taba tunanin rayuwa zata yi mana dadi Ba.

Q2. Wa kike ganin itace makiyiyar Ku?

A. Aunty zakiyya kowa zai fara zarga Toh amma ai harda ita a ciki kuma nata yafi yawa.

Q3. Waike bakya kishin zakiyya ne?

A. Inayi mana amma ya na iya dole na danni zuciya inyi hakuri wata rana sai labari.

Q4. Ya kikaji sanda yazeed ya fara sunbatarki ?

A. (Cikin jin kunya)Wani Abu naji yana mini yawo ajikina sannan ya ratsa ko wani lungu da sako.

Untichlobanty:(cikeda karadi) muma dai Allah ya kaimu lokacin mu馃檶

Kowa ya kuramin ido...

Untichlobanty: ina..ina nufin Allah ya nuna mana lokacin bikin su....su ya Abubakar (Sosa Keta tareda kallon gefe)

Q5. Ya kike ganin zata kasance tsakanin zaliha da lukman?

A.(gutsiran Awara, tattaunawa)

Untichlobanty: minal bakiji sister tana tambayanki bane?

Minal:(sake gutsiran awara tareda kurba zobo) tunda gasu a gabanku sai Ku tambayesu ai.

Untichlobanty: Dan sammin awaran Toh

Minal:(harara Kamar zata kasheni)

Untichlobanty: sisters muyi gaba ko?

馃尮馃崁TO ZAKIYYA馃尮馃崁

Q1. Sannu zakiyya ya jikin?

A. Tambayata kukazoyi ko ya jiki?

Mai tambaya: Allah ya baki hakuri.

Q2.Wa kike ganin ya kona miki shagonki?

A. (Cikin Daga murya)Masoyin mutum zai rabashi da arzikinshi ne? Kunsan dole makiyinane mana. Mtsw waya sani ma ko dangin shegiyar nan ne?

Minal:wallahi ni Ba shegiya bace

Zakiyya: ke zan faffasa miki baki.

Yazeed: order please!

Zakiyya and minal: (hararan juna)

Q3. Bakyajin kishin minal ne?

A. Mtsw ji wani tambayan banza! A woman with class like me ne zanji wani Abu Wai kishin minal? You are not serious. Next question please.

Q4. Yaushe zaki Koma gidanki?

A. Gobe kuma da ayush zan tafi kunada matsala da hakan ne?

Mai tambaya: wane ni?

Q5. To ya baki Fadawa yazeed zaki dawo Ba?

A. Duran bazata zanyi inga wainar da ake tuyamin a gidana.

Q6. Yaushe zaki haihu ne?

A. Ke banson shashanci da wulakanci fa nine zan haihun? Dallah malamai Ku tashi Ku matsamin

Untichlobanty:(na cika Nayi FAM.)ke zakiyya karkiga ina ganin girmanki ki nemi ki batan rai. Ya zaki dinga cin mutuncin fans dina?in ki kayi wasa yanzu sai in shafeki a littafinnan.

Zakiyya: tafi nono fari.

馃尮馃崁TO LUKMAN馃尮馃崁

Q1. Ya kake ganin matar da da yazeed yasa ka aura?

A.ban gane ya nake ganiba.

Mai tambaya:tayi maka?

Lukman: Idan ma bata yi Ba yana iya?yarinyar bata wani birgeniba kawai de in tana magana inajin dadin kallon labbanta.

Untichlobanty: Nide banji wannan Ba.

Zaliha: (ta saki baki tana karewa lukman kallo)

Q2. Toh ya kake gani zata kasance Idan ka fara aiki a companyn yazeed?

A. Company din yazeed ai bawa ne kuma zan rike masa amana Abu daya Dana sani shine I will be stressed dan haka zan matsala masa lamba ya jonani.

Q3. Ya kake ganin feelings din abokinka akan amaryarsa?

A.(Cikin kyalkyalewa da dariya) ya mutu murus a Cikin tekun kaunarta.

Ai lobashi Nayi nace ya saba da ita har ta Haifa masa yara sai ya saketa. Nasan bazai iyaba ko ada balle yanzu.

Yazeed:amma kaide Anyi Dan iska.

Lukman: iskanci na ya jawo ka fara son amaryarka馃槣

Minal:(side Hannu tareda kici kicin da fuska ) dama zuwa kayi kake fada musu Cewa na zama yar iska.

.... Kowa Yana kallon minal daketa huci......

Untichlobanty: minal sake masa kwalar Riga Ku bari Ku sani saki sai kuyi.

Minal:(harara na)

Untichlobanty: me Nayi?

......

馃尮馃崁TO ZALIHA馃尮馃崁

Q1. Malama zaliha ya mukaji da hakuri?

A. Alhmdllh

Q2. Kina ganin zaki iya zama da lukman?

A. Waye kuma lukman?

Mai tambaya: mijinki mana.

Zaliha: au dama sunanshi lukman?

(Kowa ya zaro ido)

Zaliha: kudena kallona Kamar na kashe mutum. Zanje gidan NASA inga gaji da ganina ya sakoni.

Lukman: mtsww

Q3. Yanzu dai atakaice kina so kice mana baki s.......

(Wayan zaliha yana ringing)

Zaliha:ina zuwa Dan Allah(ta fice)

Lukman: ke wa yake kiranki?

Untichlobanty: Ba kunnan zomo gareta Ba please

Lukman: yi mana shiru.

馃尮馃崁TO MOM馃尮馃崁

Q1. Sannu da aiki mom

A. Yauwa...(jera kaya Cikin akwati)

Q2. Mom ya kike ganin yanayin zaman danki da diyarki?

A. (Fara'a sosai) kice yaran arziki aini ban Cewa Komai sai Alhamdulillah.

Q3. Me yasa kakeson ki dawo Nigeria?

A. Saboda inyi rainon Cikin jikana kuma ga zakiyya ma masifa ya fada mata kinga itama tana bukatar lallami.

Q4. Ance miki minal din Nada kuna biyu ne?

A. (Hade rai) Insha Allah akwai Idan babu ma yana kan hanya. Kuma ni ko zakiyya ce ta Haifa ban damu Ba Nide a haifo kawai.

Mai tambaya:Toh sai kin iso kenan

Mom: Insha Allah

Untichlobanty: sai anjima.....

馃尮馃崁TO YA ABUBAKAR馃尮馃崁

Q1. Yaushe ka fara son Laila?

A. Tun randa na fara daura idanuna a kanta wato tun tana yarinya.

Q2. Ya kaji lokacin da ka dauka Anyi raping Laila?

A.ji Nayi Kamar na mutu tsabagen bakin ciki amma dukda hakan ban daina Sonya Ba illa ma nunkuwa da yayi.

Q3. Me zakace game da warware matsalarku da Allah yayi?

A. Alhamdulillah! Nayi farin ciki sosai da akace babu abinda ya sameta sannan duk nauyin dake zuciyata ya sauke tas!

Q4. Yaushe zaka Sauri Laila?

A. Bayan matsaloli sun Dan lafa.

Untichlobanty: Mun gode!

Ya abkr: Ba damuwa.(shafa kan laila)

Untichlobanty: 馃幎wani ya kasa hakuri a daura,yana nema ya tarowa kansa zunubi馃幎

Yazeed: waike baki iyayin shiru ne?

Untichlobanty: Gaskiya na fada ai

Yazeed: (ya jefomin pillow na kace馃槢)

馃尮馃崁TO LAILA馃尮馃崁

Q1. Ya kikaji lokacin da abubuwa suka rikice

24 / 45