Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 45

117K to 120K   out of 134.5K words

Allah stay tune.

DON'T FORGET TO COMMENT.

ONE LOVE FROM

Miss untichlobanty ?

10 April, 2020.

?? *KURUCIYAR MINAL* ??

? _by miss Untichlobanty_ ?

? *CHAPTER 82* ?

*RECAP*

Jijjigata suka fara yi suna kuka suna kiran sunanta wani ya haskosu da tocila tare da cewa kai! Su waye a wajen ne? Matsowa kusa yayi ganin kamar yara ne. Haska Fuskar minal yayi cikin rawar baki yace YAR UWA?.... KECE?

*CONTINUATION*

Gumi ne ya fara tsatstsafo masa cikin tashin hankali ya sake furta yar uwa? Ashe rai kanga rai? Daukarta yayi tare da cewa yaran su biyosa. Zayyana tace ka San mu ne? Ina zaka kai mana ummin mu? Bai kulata ba har suka iso gidansu dakin mahaifiyar sa ya kaita.

Ummu sabir tana cin goronta taga ya fado da mace da yara tace kai dannan, me zan gani haka? Yace ummu nasan bazakiso ba amma ki daure ki danne zuciya kinga matata ma tabar gidannan ne sandiyyar ki. Kwata kwata bana iya zama da mace saboda ke ki daure kibar wannan baiwar Allah ta zauna ko na lokaci kadan ne tsaki taja tace kar ka fice da wadannan Ababa a daki kaima sai in tsine ma. Hawaye ne suka cika masa idanu jiki a sanyaye ya juya ya fita tareda kaisu dakin matarsa. Kwantar da minal yayi sannan ya yaiyafa Mata ruwa. A hankali tace ruwa, ruwa.

Ruwa ya dauko ya ba ma zayyana yace ta bata sannan ya fita ko zai samo abinci. Garzayawa yayi ya koma gidan da yake gadi ya sanar dasu abinda ya faru, nan suka bashi abinci da wasu surutu sukace yakai ma minal din.

Koda ya dawo minal har ta Dan ware nan ya basu tare da ficewa sallar asuba.

Bayan ya dawo minal tayi masa godiya harda hawaye kamin yace niko kamar na sanka. Murmushi yayi yace Dan uwa ne fa. Shiru tayi ta gama nazari bata gano wani Dan uwa ba. Nan sabir ya labarta Mata yadda akayi? aiko ta dinga yi masa godiya.

Dakin mahaifiyar sa ya leka ya sanar da ita zai koma bakin aikinsa. Dauke kai tayi tare da fadin da fatan tare zaku tafi? Yace haba baba kiyi hakuri mana zasu bar gidannan amma yanzu ki daga musu kafa. Naji kawai tace hakan yasa shi sauke ajiyan zuciya harda godiya sannan ya fice.

A hanyarsa ko tunanin halin mahaifiyar sa yake ita indai harka ba ta kudi bane to baza'ayi da ita ba. Tunda ya rasa aikinsa ya kasa gane kanta. Haka ya isa gurin aiki hankalinsa ba a kwance ba.

Samu yayi gidan anata shirye shirye ya tambayi me bayin flower me ke faruwa ne ? Me bayin flower yace bakasan cewa yau diyar Alhaji na biyu zata dawo ba? Sabir yace ikon Allah gaskiya naji dadi. Mai bayin flower yace cab lallai an barka a baya kace kaji dadi? Wannan yarinyar bata ganin kowa da gashi a tsakiyar ka. Sabir yace kaga malam, ni banason gulma. Sannan ya koma bakin aikinsa.

A gida kuwa sabir yana fita mamar sa ta fito ta samu sahla da zayyana a bakin rijiya runa dibar ruwa. Warce gugar tayi tace Dan...... wa ya Baku izinin shan ruwa a gidannan? Zayyana tace ishi mukeji. Tace kinci ..... sahla cikin muryarta na abin tausayi tace kiyi hakuri. Idonta sun ciko da hawaye .

Minal ce ta fito tana kokarin bada hakuri kawai ummu sabir ta adungure kan sahla kan kace tak ta fada rijiyar. Wani irin kara ta saki ta fara ihun neman taimako mutane ne suka shigo aka cirota kamar gawa kokarin ceto ta samarin sukeyi amma minal gani take kamar kasheta zasuyi hakan yasa ta karbi yarta ta wuce suka fice a gidan Allah wadai mutane sukayi da irin halin ummu sabir sannan suka fice.

Tana tafe batasan inda take wulla kafarta ba Dan ji take kamar tana dauke da gawar yarta ne duba da yanayin sahlan. Zayyana ne taja hannunta ta zaunar da a bakin wani gini tace ummi ku zauna anan bara in kawo mana ruwa.

Tafiya ta fara bata masan inda zata Sami famfo ko rijiya Dan sun fara shiga cikin Abuja, pure water kuwa sai ka siya.

??

Yazeed ne zaune a office yana shan tea sai ya tuno cewa yanada meeting kuma personal assistant dinshi bai tunatar dashi ba cikin bacin rai ya Mike tare da danna kararrawar neman sa Wanda yayi sanadiyyar faduwar wayansbi ya fashe. Shiru yaji har minti biyu suka wuce hakan yasa ya Dan sassauto tare da tunanin ko baya kusa ne. CCTV footage na office dinsa ya duba amma me? Bacci take harda yawun bacci. Wani tafasa ya farayi baisan sanda ya jefi gini da wayarsa ba. Babu wasting time? personal assistant yasan inda dare yayi masa. Yayinda yazeed ya fice domin Nemo wani waya dukda ko zai iya sawa a kawo masa amma duniyar yanzu sai ayi connecting wayan yanda za'a iya samun muhimman abubuwa.

Zayyana na tafe hannunta rike da naira 10 da aka taimaka Mata dashi har ta iso wajen traffic. Wata mota ta gani booth dinshi a abude kawai taje da gulma wai zata rufe kudin ta ne ya fada ciki Dan haka ta shiga zata dauka. Tafiya motar ta fara yi sanadiyyar hannu da aka basu. Nan ido ya Rena fata tayi ihu har ta gaji amma me motar ya kure sauti Dan haka bayaji dadin abun ma booth din a bude Dan haka tana shan numfashi. Cikin gari suka shiga nan fa ta saki baki tana kallon ikon Allah.

Abinda yasa mutane kuwa basu ganin ta saboda a kwance taje kuma booth din bai wangale sosai ba da mai motar zai gani ta mirror ya rufe. Jin an tsaya yasata buya a cikin rigar mota.

Aikuwa baifi second uku ba securities suka duba booth din inda suke ce masa malam you are careless fa, kana bari booth ba'a rufe ba ko? Dariya hausar securityn ya bawa zayyana. Kunshewa tayi yayinda suka rufe masa booth din amma bai rufu ba nan suka gane cewa hook din ya baci ne sannan suka barshi bayan sunmai warning.

Ciki ya shiga ya yayi parking sannan ya fice bayan kamar minti biyar sai ta fito. Kokarin karanta abinda aka rubuta a sama tayi. Shoo....s..ho? Kai sho...pi..re.. a ah ri ne. Sho...pi..ri..te....

Dariya ta kyalkyale dashi tace kai ni banza ce wallahi ashe shoprise ne toh ko me yasa suka rubuta shoprite oho.

Wasu family masu yawa ne zasu shiga ta shige cikinsu suka shiga tare nan fa ta fara ciyar da idonta abinci. Officials idan sun ganta sai su tambayeta ta harshen turanci itako dayake kwakwalwar kamar na uwar ne sai kawai tanuna wani waje tace can sai ta hudu. Su kuwa basu gane ba duba da kayan jikinta sabi ne masu kyau Wanda aka bawa sabir ya basu kuma tanada harke dukda cewa batakai mamanta ba sai suke Mata ganin ajebo.

Tana cikin tafiya ta iso wajen na'urori(gadgets) sakan ido da baki tayi tana kallo cikin karamar muryata ta yara tace kai jama'a kaga wayoyi masu kyau ba irin na ummi ba. Bara in dauko Mata wancan.

Juyawa tayi taga wani ya fito mutane biyu na binshi a baya. Sai taji ana sanarwa da turanci tabe baki tayi tace ko me suke cewa oho.

Wallet din mutumin taga ya fado da alamu bai lura ba Dan haka ta dauka budewa tayi taga kudi har ta juya da gudu tanajin dadi sai ta tuna abinda minal ta fada Musu "misalin abinda ba naki ba kamar wuta ne, shin zaki dauki wuta balle kici?" Juyowa tayi da gudu ta fara binshi tana uncle! Uncle! Uncle!

Yana tafe yanajin anata uncle amma bai dauka dashi akeyi ba.? Jin ana uncle me kaman larabawa yashashi tsayawa tare da ganin wake damun mutane da ihu haka. Wata yarinya ce ta tsaya a gabansa tana haki. Cikin ?ufula yace ehm? Lafiya? Cikin yatsine fuska irin na ka renamin wayo zayyana ta kama kunkumi tare da cewa kaji min mutuminnan fa. Kama rasa abinda zaka ce min sai uhm lafiya? Karka kaga shekarana 8 karfi gareni. Nausa hannu da kafa tayi yayinda tayi murmushin gefen baki yace calm down little girl me kikeso. Tace ni ba little bace fa ehe yace okay big lady (babbar mace) inajinki, uncle yana sauri. Kauda kai tayi tare da miko masa wallet dinsa shafa aljihunsa yayi yaji babu. Murmushi ya danyi ya karba tare da shafa kanta yace godiya nake boss lady 5k ya miko Mata ta karba ta jujjuya yadau ta Rena ne sai yaga ta dauki daya ta dawo masa da sauran tace daga gani manyan kudi ne Dan haka kwalli daya ma ya isheni a madadin wadannan ka mayar dani wajen ummi na. Murmushi yayi yace angama boss lady muje ko sannan ki rike wadannan din ma na baki.

Washe baki tayi tace ba gode sannan ta riko hannunshi suka fito. Mota suka shiga nan ta fada masa abubuwa Sheda data rike a kanta na inda tabar minal yace boss lady wannan wani irin kwatance ne babu sunan anguwa sai sunan wani gini ta ina zan gane. Driver dinsa yace na gane wajen sir yazeed yace muje toh. Suna cikin tafiya tace kai gaskiya uncle motar ka nada kyau. Yace Allah ko boss lady? Nikam ya sunan boss lady. Cikin jin dadin zancen ta gyara zama tace sunana zayyana zaka iya cemin zayya, kaifa uncle yaya sunanka? Yace sunana uncle yazeed. Tace naji dadin ganinka uncle yazeed. Hirarsu suka cigaba dayi har suka iso tace yauwa tsaya anan gasucan bude kofa tayi ta sauko tare da cewa uncle na gode sai wata rana yace haba boss lady bakyaso inga mommyn mu ne? Tace nk no no mummy na kyakkyawa ce sai da kudi ake ganinta. Rugawa tayi a guje zai bita secretary dinshi yace sir mutanen nan sun iso suna meeting hall kuma kai suke jira and masu neman aikin personal assistant dinka sun hadu for interview hakan yasa ya hakura tare da sa ran zai dawo domin meeting din is important yaso ace ya kalli Fuskar maman amma ta bashi baya da alamu mutanen dake cikin motar gefenta ke mata magana.

Zayya tana isa taga wasu yan Mata suna fadin baiwar Allah ya haka zaki zauna da yarinya me bacci a titi kina kuka dauke kai tayi ganin sun takura yasata cewa ta mutu.... zayya tace me?! Ummu me kike cewa sahla ta mutu? Har idonta ya ciko da kwalla ya fara zuba faduwa tayi a guiwanta ta matso kusa da ita tace kanwata karki barni Dan Allah.? Daya daga cikin yan matan ne tace karkice ta mutu muje gida a kawo likita ya duba ta dai tana da rai.

Mikewa minal tayi cikin fitar hayyaci tace kin tabbata tana raye baiwar Allah karki sakamin rai fa.

Sai a lokacin suka kalli fuskarta take suka ja da baya baya sunan fadin wayo Allah mun shigesu. Nafeesa tace aunty me nake gani haka?

GENG GENG GENG ME YASA KUKE GANIN SUKA TSORATA? SANNAN YAYA RAYUWA ZATA KASANCE? DONT FORGET TO VOTE, COMMENT AND FOLLOW ME.

DEDICATED TO @?+234 703 556 2830?,@?+234 814 123 0581? and #kuruciyarminalfans

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

miss Untichlobanty ?

12 April, 2020.

?? *KURUCIYAR MINAL*??

? _By miss Untichlobanty_ ?

? *CHAPTER 83*?

*RECAP*

Zayya tana isa taga wasu yan Mata suna fadin baiwar Allah ya haka zaki zauna da yarinya me bacci a titi kina kuka dauke kai tayi ganin sun takura yasata cewa ta mutu.... zayya tace me?! Ummu me kike cewa sahla ta mutu? Har idonta ya ciko da kwalla ya fara zuba faduwa tayi a guiwanta ta matso kusa da ita tace kanwata karki barni Dan Allah.? Daya daga cikin yan matan ne tace karkice ta mutu muje gida a kawo likita ya duba ta dai tana da rai.

Mikewa minal tayi cikin fitar hayyaci tace kin tabbata tana raye baiwar Allah karki sakamin rai fa.

Sai a lokacin suka kalli fuskarta take suka ja da baya baya sunan fadin wayo Allah mun shigesu. Nafeesa tace aunty me nake gani haka?

CONTINUATION

Nafeesa wacce bazata wuce shekaru 18 ba tace aunty me nake gani haka? Me aunty bushra keyi anan ba yanzu muka barota a gida ba? Dakata, y

anzu na gane abinda sabir ke fada dazu Allah sarki ashe da gaskiyarsa

Mintuna kadan da suka wuce

Sabir na komawa gida ya iske wannan labari haka yadan bi sawu amma bai gansuba cikin tashin hankali ya nufo gidan da yake gadi domin su taimaka a sanar a gidan rediyo, talabijin da sauran su.

Acan kuwa......

"Oyoyo aunty Bushra sannu da dawowa" nafeesa wato feena ke fadin haka yayinda ta rugo a guje saura kiris ta fadi a beni sanadiyyar karar motan da taji. Wata budurwace ta fito daga ciki tana yarfe gashinta dake kan farin fuskarta tare da gyara tabarau din dake manne a idonta murmushi ta saki lokacin da ta sanya kanwarta nafisa a idanunta. Rungume juna sukayi feena na turo baki cikin shagwaba tahau magana...

Amma wani hanzari ba gudu ba na kasa saurara balle har na rubuta abinda take fadi domin nifa ba kowa nake gani a tsaye ba sai minal cikin kananun? kaya saide wannan tafi minal kiba da kirji sannan minal ta fita gashi? da tsayi.

Sauran yan gidan ne suka fito suna Mata marhaban. Ana cikin haka sabir ya shigo duk ya hada gumi yana fadin hajiya wannan baiwar Allahn ta gudu daga gida sabod........

Maganarce ta makale masa a makokoro cikin rawar yatsa yake nuna bushra yace yar uwa me kukeyi anan sannan ina yaran. Wani kallon ka renamin wayo ta mai tace (Dan Iska me ka kirani yanzunnan?) what the fuck did you just called me? Baki ya bude zai bada amsa amma bai samu dama ba sanadin Marin data yanka masa. Mahaifiyarsu ce ta riko ta tare da cewa ke bushra bakida hankali ne zaki daki namiji? Kuma ya girmeki? Banason rashin tarbiyya, au abinda kika koyo a turan kenan? Toh bari mahaifinki ya dawo zakiga ikon Allah.

Hakuri suka bawa sabir Wanda ya kasa yin komai yayinda tayi tsaki tayi wucewar ta. Fadawa tayi a kujera, tayi ciro da takalman kafunta tare da cewa (ji wani mafari mara kyau)what a bad start! Aunty jalila kanwar wacce takeda shekaru 32 maman su tace gaskiya bushra kin bani mamaki menene haka? Ya zaki Mari sabir? Mutumin kirki ga gaskiya kuma.... datseta bushran tayi ta hanyar cewa aunty kuyi min uziri ku siyomin icecream keda feena, kaina ciwo yake zamuyi magana anjima. And please ku zaku siyo kar a bada sako ma driver ko wani kazamin.

Tabe baki aunty jalila tayi kamin ta shiga daki tana fadin aiki ya sameki sannan ta shirya suka fice tare da cewa yarta shameela wacce take sa'ar su zayya ta zauna ta sakawa bushra ido idan tayi wani Abu ta sanar Mata. Ita kuwa abin nema ya samu saboda rawar kai gareta.

Hakuri suka sake bawa sabir sanda ya bude musu gate yace ba komai sannan suka fita suna cikin tattauna halin da ta dawo musu dashi feena tace la aunty kinga wata baiwar Allah zaune da yarinya a hannu ga za'ayi ruwa kuma dai nan ba wajen bara bane. Haka kawai aunty jalila taji tanason ta tsaya dukda yadda zamaninnan ya baci.

Magana sula fara Mata amma taki ta dage kanta balle ta kulasu sai kuka take ana cikin hakane zayya ta dawo......

CIGABAN LABARI

Ajiyan zuciya minal ta sauke tana mamaki da akace akwai me kama da ita. Feena tace aunty zo kiji, cikin kunne ta fada Mata wani Abu sukayi yar shawara.

Tsugunawa tayi a gaban minal tace kinga yanzu ruwa za'ayi kuma da alamu bakida wajen zuwa me zai hana ki biyo mu. Girgiza kai tayi tare da cewa ni yanzu bazan yarda da kowa ba ku barmu ni da yara na kawai mu mutu.

Aunty jalila tace wannan wacce irin... kasa karashe wa tayi sanadiyyar ruwan daya tsinke zayya ne fara rokanta akan su bisu kawai kar ruwa ya halaka yar uwata. Badon ran minal yaso ba tabisu.

Yazeed kuwa suna cikin tafiya ruwa ya balle Abu na farko da ya fado a ransa shine boss ladynsa. Ganin hankalinsa bai kwanta yasa yace su juya koda ya koma yaga wayam haka yanaji yana gani ya hakura.

...........

Suna shigowa gida suka sassauko a motar da sauri suka shiga ciki saboda ruwa yayinda akabar? feena da zayya suna dauko ledan icecream. Shameela na ganinsu tace mummy wallahi kina fita aunty bushra ta sa ya sabir aiki wai ya goge Mata takalma..... aunty jalila tace yanzu tana ina? Tace tana dakin mama.

A waje kuwa daidai zayya ta juya ta hango wani kamar ta sanshi amma ta share batayi magana ba taci gaba da yiwa feena hira suna dariya suka shiga ciki.

Surutun da shameela keyi na ya tsaya lokacin da ta lura da minal dake bayan jalila. Kallon saman beni tayi ta kuma kallo minal sai ta bazama a guje tayi sama cikin haki ta bude dakin mama taga bushra a cikin dakin sai ta kallo minal, ta sake kallo Bushra ta kalli minal kawai sai ta fashe da kuka.

Waiyo umma(abinda take kiran mama dashi) na shiga uku na haukace. A tsorace mama da bushra sukayo kanta suna fadin lafiya ? Nuno minal tayi da yatsa aiko minal da bushra suka hada ido.

Kallo kurilla sukewa juna yayinda mama ke fadin ke jalila me nake gani haka? Murmushi tayi kamin ta fara fadawa mama yadda akayi. Mama tace no wonder sabir ya Kira bushra da yar uwa ya dauka itace ashe.... wani tunani ne ya fado Mata bata karasa zancen ba tace ke dakata hakan na nufin itace Wanda ta gudu yake neman ta. Ke shameela je ki Kira mana sabir, da gudu ta fita a bakin kofa sukayi karo ita da zayya. Tsaki taja kamin ta fice zayya ta bita da kallo. A lalle za'ayi cakwakiya

40 / 45