Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   34 / 45

99K to 102K   out of 134.5K words

in karar da littafinnan da wuri ko kuma acid gaba da gashi?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty ?



14th February, 2020

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss_untichlobanty ?

*?CHAPTER 75?*

Sauri minal keta yi tana tsallake steps da bibbiyu saboda lattin da sukayi domin yau jirginsu zai daga zuwa Abuja inda zasuje baban jeedmar group kuma anan ne za'ayi meeting din tallafawa yazeed kamin government ta wankesa.

Bude Mata kofa kurtu yayi ta shige luku ya finciki mota. Ba bata lokaci jirginsu ya daga sai federal capital territory of Nigeria.

Koda suka isa yazeed bai tsaya isa gida ba direct jeedmar group ya nufa. Sunayin parking ya fito cikin kwarjini da haiba yana? takunsa mai daukan hankali gwanin ban sha'awa. Dukda cewa a cikin damuwa yake hakan bai hana kyawunsa fitowa ba.

Ezekiel da lukman kawai aka bar masa a matsayi escorts dinsa sai masu gadin gidansa shima an rage wasu daga cikin su. Haka masu yin hidima duk an rage masa kuma duk munafurcin Alhaji tukur gadon kaya ne.

Tun daga bakin kofa ake gaishe sa tare da bada buda hanya yana zuwa bakin kofan shiga kofan yace "new individual detected please wait ......" scanning iris dinsa yayi kamin yace "welcome president it was nice you visit kindly put your thumb"

Saka thumb din nasa yayi take kofar ta bude masa gaba daya directors sun jeru Dan haka yana shigowa suka bi bayansa.?

Files suka fara miko masa ya daga musu hannu. Suna shiga gaba daya uncles din nasa suka Mike Yana zama suma suka zazzauna. Yace good day to you all ! As we already know we are here to discuss........ nan ya musu bayani ya sanar dasu duk abinda yake wakana sannan yace zasuyi signing contract before abubuwa su wartsake masa zasu dinga bashi 10% percent na eibar da suka samu idan companies dinsa suka dawo zai biya su.

Abinda ya basa mamaki shine yanda sukayi caaa! Sukace Sam Sam basusan wannan labarin ba. Daga karshe ma watsewa sukayi ba'a gama meeting din ba hakan yasa ran yazeed ya baci kuma ya tabbatar da cewa hatta dan uwanka zai iya cutarka sannan sai ka shiga matsala zaka gane masu sonka.? Fita yayi suka tafi ainihin family house dinsu dake central area, hmm ba'a cewa komai domin yafi na Kaduna kyau masha Allah tabarakallah.

A parlour ya samu minal ga abinci an kawo Mata amma ta kasa ci tayi jungum jungum. Umma hanifa dattijuwa ce kuma me aikin su yazeed ne tun suna Abuja ganin batada kowa na dangi sai Allah yasa koda zasu bar Abuja basu sallame ta ba, sai suka barta yaci gaba da zama a gidan tana gyarashi kuma ana biyanta kudinta har yau sannan ba ita kadai bane akwai maids guda goma.

Gaishesa sukayi kamin suka watse, gaisawa sukayi da umma hani kamin ta basu waje saboda ta fahimci yana bukatar hakan.

Riko hannun minal yayi zuwa daki duk ta kagu taji yadda aka kaya suna shiga tace da fatan komai lafiya? Ajiyan zuciya kawai yayi, hakan yasa ta fahimci me yake nufi baki ta basa kamin ta dauki musu abinci yace AI bazai ci yasani ko akwai poison ta masa pancake kawai aiko haka akayi.

Kwanciya yayi bayan yayi sallar azahar ta ja masa bargo kamin ta koma kan couch ta fara nazarin yadda lamarin zai bille. Zaro ido yayi tare da murmushi alamar idea tazo Mata hakan yasa ta nufi jakar yazeed ta dauko paper da pen ta fara rubuta list. Sallan la'asar aka Kira hakan yasa ta tasheshi tana mai cigaba da rubutu. Daukewa yayi tare dayin bismillah yaga tanata rubutu baibi ta kanta ba yayi alwala ya fito still tana rubutu.

Sansadowa yayi ya warce papers tare da cewa me ki keyine? baby. Turo baki tayi tare da kokarin kwance paper dinta canja hannu ya fara yi sanda ya bata wahala kamin ya bata. Yace list din menene wannan tace list din kayan abinci ne. Dafatan akwai space a group building yace eh tace masha Allah daga gobe zamu fara saida snacks and desserts sannan zamu dinga yin contract na? abinci. Murmushi kawai yayi sannan ya tashi ya fice da sauri domin idonsa ya ciko da kwalla kar minal ta gani. Ita ko jikinta yayi sanyi ta dauka idea dinta ne bayaso hakan yasa ta yaga papern sannan ta fada gado ta fara kuka. Ace mijinta yana matsanancin hali kuma bazata iya taimaka wa ba?

Yazeed kam kukan farin ciki ne ya kama sa da nadaman yadda ya dinga treating dinta, Allah yasha dashi da ace ya sake ta da yayi baban asara. Komawa yayi yaga tana kuka yasa yayi saurin karasawa bakin gadon tare da fadin baby na lafiya kuma juyawa yayi ya kalli kujeran da suka zauna yaga ta yaga papern. Da sauri ya kwaso su kamin ya dawo gefenta ya zauna tare da fadin ya haka ? Me yasa kika yaga mana plan din? Cikin shessheka ta tashi tare da cewa na dauka bai maka bane ace kana da kudi kana da group ince maka ka fara saida abinci dukda cewa quantity da quality me kyau ne kuma naga cewa ba'a daukan shawaran Mata.

Murmushi yayi ya goge Mata hawaye tare da cewa wa yace miki na Rena shawaranki ? AI sana'a bata kadan albarka kawai ake nema. Batun shawara kuwa kin fini karfin tunani ma amatsayinki na mace. Murmushi tayi tace Allah? Yace kwarai kuwa mata ta sannan ya rungume ta.

Pieces din paper din ya bata kamin ya fita ya karbo glue ya like musu takardan sannan ya janyota suka baza shopping din kayan abincin su Dan da zafi zafi ake dukan karfe.

Gidan radio da talabijin aka sanar AI kan kace me wannan sun Sami order yafi dari saboda ana matukar son yazeed. Minal sanda ta tsorata ta fara? darewa tana ganin bazata iya ba yazeed yace karka damu zasu dinga Tahowa da masu aikin gidan su sai su dinga tayata, kuma ai shima yananan.

Haka suka dawo gida sunyi likis ranan da wuri suka kwanta 9pm a gado ta musu.

Kirrrrrr!kirrrrr!kirrrrrr!

Tsaki minal taja tare da sake shigewa jikin yazeed. Bacci sukayi bayan sunyi sallan subh sai suka saita Alarm din 6:30am suka saita dan shirya tafiya aikin su akan? lokaci, badan ranta yaso ba ta tashi suka shirya sai jeedmar group sai dadi takeji.

Direct area dinsu suka tafi banida girma office 3 ne a ciki ba manya sosai ba sai kitchen da reception. Aiki suka fara minal da yazeed na girki saura na packaging da branding. Sallah da cin abinci kawai suke tsayawa yi. Masu delivery nata yi. Ga orders 3 na biki yazeed in yayi aiki sai ya dawo ya goge wa minal gumi sai yaci gaba. Haka suka yi ta yi har yamma tukunna suka tafi gida gaba daya sunyi likis wanka da ruwan zafi sukayi, tare da sallah da cin abin ci. Sai gado a kwana a tashi cikin sati daya aiki ya fi karfin Dan mutum ga riba sun tara sosai kawai sai suka siya engine. Sosai sukayi dedicating time dinsu suna aikin su.

Mutane kuwa ganin abin da akayi wa yazeed ba'ayi masa adalci ba gashi an kasa proving komai, an duba account summary dinshi da kuma information na company transactions dinshi duk kudinshi data company dinshi ne albashinsa ne kawai from government.

Dan haka mutane suka fara zanga zanga cewa dole a sake masa dukiya tunda yana taimakon talakawa.

Zaune take akan kujera tana juya wa tare da busa shisha. Wani number ta Kira tace maza kiyi aikin ku da fatan mutanen sunzo? Akace yes ma tace don't make a mistake......

Order phone din su yazeed aka Kira ya dauka nan akayi placing order na birthday party abincin 25 people.

Aka hada aka kai bayan 2 hours sai ga police wai abin cin da aka kai is poisonous kawai suka rufe shagon take yazeed ya Kira yan NAFDAC yace ya sun duba abincinsu ba'a basu number ba police yanzu sunzo sun rufe musu aiki.

NAFDAC suka ce gasunan zuwa after 30min sai ga su. Yazeed yace ga yan sandan can suna jira they should talk to them, shugaban tawagar tafiyar NAFDAC din yace it's true abincin is poisonous. Yazeed yace toh me yasa suka yi musu register a baya ? Sukace ai Sam basuyi musu register ba sannan sukace ma yan sandan a tafi dashi cell dukda cewa military officer ne ai yayi laifi sannan bulldozer zata zo ta rushe part din ko kuma ya bar wa government yace ai ba nasa bane mallakin matarsa ne Dan haka basuda right akai. Sojoji ya Kira har Wanda gwamnati ta kwace masa sanda suka zo sai ga jama'a ma sun iso, domin live komai ke faduwa ga yan jarida rututu.

Sojoji da mutane suka kewaye yazeed mutane sukace ba'a isa a rushe wajen ba yayinda sojoji sukace ko yabar maganan ok su bude wa yan sandan da nafdac wuta. Atake aka fara yarda jita jita wai yazeed shi ke supporting din terrorism wasu kuma nacewa ya hada kai da yan boko haram ne.

Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .

Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.

Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ?a?arin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji karan harbi.

CABDI ANA CAKWAKIYA, YA KUKE GANIN LAMARIN ZAI KAYA?

MASHA ALLAH! DONT FORGET TO FOLLOW ME, VOTE AND COMMENT AND INA BUKATAR ADDU'AR KU MUN KUSA FARA EXAMS SO ZAKU JINI SHIRU GASKIYA.

THANK YOU! TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss Untichlobanty ?

23rd February, 2020.

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss_untichlobanty ?

_RECAP_

Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .

Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.

Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ?a?arin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji.

*?CHAPTER 76?*

Shiru wajen yayi tsit kowa yana register din abinda ya faru.

Faduwa minal tayi akan guiwanta tare da rike hannunta da aka harba. AI nan kakejin dau!dau! An sakewa Dan sandan nan bullet biyu a hannu.

Nan fa shugaban nafdac ya fara hadiya yawu tare da kokarin zamewa ya gudu, wabi cacuma sojoji suka masa sukace ko ya fadi gaskiya ko yaji ba kyau. Tsilli tsilli yayi da ido Dan yaga mutuwa a gabansa. Nan fa ya fara in ina,wani soja me zafin rai me suna musa ya gwabje sa da bindiga atake ya soma bayani cewa kudi aka biyasa ya fadi hakan.

Akace wa ya biyasa yace Alhaji tukur gadon kaya ne. Nan take ya basu registration number tare da bada hakuri yazeed yace ai dole a tsigeshi nan fa ido ya Rena fata m, haka ya dinga bada hakuri yana nuna nadamar da yayi sanda yazeed ya tabbata ya wahala yace yaji ya tafi zaiyi tunani amma fa hakan batayi wa Musa dadi ba Dan haka yasa shi lungu ya dan jijjibgesa ya sauya masa halitta kamin ya barsa.

Asibiti aka kai minal da Dan sandan nan jina jina nanfa magana ta lafa, chef of police din yace a masa afuwa ba laifinsa bane na yan NAFDAC ne da sukayi musu karya kuma munafiki harda shi a ciki.

Haka dai magana ta watse aka sasanta toh anan ne mutane suka sake tada mayar baya akan a sakewa yazeed dukiyarsa.

Shugaban yan sanda yana zaune a office gadon kaya ya kirashi yace asan yadda za'ayi da mutanen nan dake zanga zanga. Nan ya Kira yan sanda 3 yace a saki teargas a wajen zanga zanga. Daya daga cikin su mai suna lieutenant sabir murya kasa kasa cikin girmamawa yace :sir! This is totally dishonest and unfair, some police are the cause of the negative views people have on us. If not for dishonesty? these people did nothing wrong, they did not temper with government property neither did they go against the law. They are just practicing a peaceful riot. To tell the truth me and my people will not participate in this (yallabai wannan fa rashin gaskiya da rashin adalci ne, wasu yan sandan su ke jawa wasu bacin suna,idan ba rashin gaskiya ba mutanen nan basu taba kayan gwamnati ba basu yi wani Abu da ya Saba doka ba, peaceful riot sukeyi Dan haka shi bazai sa yaranshi suyi ba.)

Mari chef of police din ya wankawa lieutenant sabir kuma yace yaje shi bayan kwana 3 ya dawo ya karbo dismiss letter. Yace shidai da ayi aikin rashin gaskiya dashi gara ya rasa aikinsa.

A bangaren su yazeed kuwa bayan an cirewa minal bullet din ta farfado yazeed yana bata shayi sukaji hayaniya a hall din asibiti,saukowa minal ke kokarin yi daga bed dinta yazeed ya kwantar da ita kuka ta fara masa wai tanason ta gani dan haka ya dauketa suka fito Dan sandan nanne suke cakwakiya da sojoji zasu tafi dashi Dan ya harbi matar oga yayinda yake kuka yana fadin bashi ya harbeta ba. Yazeed yace a dakata. Tsit kowa ya yi yazeed ya iso gaban shi yace :kace ba kai ka harbeta ba? Da sauri gyada kai yazeed yace idan na gano kai ka harbeta wani hukunci zan maka yace a tsire ni.

Yazeed yace a kai bullet din da aka harbeta da kuma bullet din bingigarsa a duba su shi kuma kar a tafi dashi a mayar dashi daki aci gaba da kula dashi.

Koda aka Dubo bullet din ba na bindigar sa bane nan yazeed ya fara tunanin yadda zai gano na waye tunda yan sanda ke duba wannan kuma yan sandan ba mutuwa dashi sukeyi ba.

A kwana a tashi minal ta warke yau aka sallamo su kuma basu fadawa kowa abinda ya faru ba especially mom saboda kar hankalin ta ya tashi.

Marhaba umma hani tayi musu tare da sauran masu aikin inda sukayi musu jaje. Su nason minal sosai saboda kirkin ta.

Washe gari zabe? dan haka yazeed yace wannan shekara bazasuyi Zane ba saboda tsaro kar a kuma kawo musu hari. Sabon president yana zuwa ba tare da bata lokaci ba yasa akayi dismissing case din saboda ya gano rashin gaskiya kawai akeyi. Anan ne yazeed yayi resigning.

Mr. President yayi bakin ciki na rashin jami'i mai gaskiya da amana Dan haka ya hada masa taron bankwana a wajen taron ne aka Kira yazeed domin yayi jawabi cikin jawabin Nasa ne yake cewa zai koma ya kula da hard work din mahaifin sa kuma insha Allah? daga ranan har tashin kiyama baya fatan shi ko wani a zuri'arsa su kara involving kansu da government business kawai zasuyi kuma individually zasu dinga taimakon kasarsu ba sai sun tsunduma kansu a cikin ba idan an nemi gudun muwarsu toh zasu bayar. Idan sunga ana Abu da ya Saba doka toh zasu yi magana.

Kuka jama'a keyi wiwi! Anan taron ne akayi presenting award of excellence ma yazeed as the BEST MILITARY PERSONNEL of the year. It was a heart touching moment,box daya na tissue paper na karad saboda kuka anan ne nima aka bani award Dina as THE BEST FICTION WRITER of the year. Muka ci abinci muka sha sannan muka watse ana ma juna fatan ALKHAIRI.

Washe gari da safe suka lulu suka dawo Kaduna domin yazeed yayi shirin fara aiki as JEEMAR GROUP PRESIDENT yayinda minal taga cewa ya kamata su ciyar da almajirai domin godiya ga Allah Dan haka asabar din data kewayo ta Nemo tsofi 20 aka fara girki. Manya manyan tukunya fiye da lamba hamsin guda 20 aka daura kenan ko wacce tsohuwa 1 tukunya 1, yayinda aka biya ko wacce dubu hamsin kuma anyi haka ne Dan a taimaka ma tsofin ma.

inspection minal tazo yi yayinda take testing ana bude tukunya farfesun kaji ta hau kakarin amai. Dannewa tayi ta dandana ai take ta fara amai ba sassauci nan hankalin tsohuwa ya tashi itakam kashinta ya bushe.

Kowa ya rude ya rikice aka samo likita ta dubata tace yuzu dai she can't say amma tana suspecting ciki ne da ita dan haka aka bata pregnancy test tube aikuwa positive. Nan shagali ya karu murnane ba'a cewa komai, run saga ranan minal batada aiki sai cin gurasa da zogale.

BAYAN WATA 7

Minal zaune akan gado ta mimmike kafa bakin nan cike da gurasa da zogale yazeed shigo ya zauna a gefenta,daura kafafun nata yayi a cinyan sa yana Mata tausa saboda sun Dan kumbura yace mummy gurasa na shirya sai tafiya turo baki tayi tace daddy zogale ka tafi dani Dan Allah yace a hakan? AI idan na kaiki can zaki wahala ne gara nan akwai mom kuma ai bakuyi hutu ba karki damu yanzu zakiga weekend din ya kewayo na sake dawowa kinji? Tace Tom shikenan Allah ya tsare ya kuma kare yace ameen.

Saukowa tayi dakyar tare da kanka kwanta me kwabon zogale yazeed

34 / 45