Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 45

48K to 51K   out of 134.5K words

ta fashe da kuka shima dai daskarewa yayi na wani lokaci domin rabon da susami kusanci irin wannan tun tana 12 barsu dai sukan rike Hannu once in aw while saboda Sabo dasukayi dayin hakan.

Kasa hanata yayi illa ma Daga baya ya zuro hannunsa ya rugumeta tsam.

Daidai lokacin su yazeed suka shigo ciki suma tunda bawani zaman makoki za'ayi Ba Dan basason bidi'a Dan haka babu mata a gidan sai waje ne ma mutane basu gama watsewa Ba.

Parking motarsu sukayi awaje kamin suka shigo suka ja suka tsaye baki a bude sallamar tasu ta makale domin abinda idanunsu sukayi artabo dashi ya Abubakar ne rungume da laila tan kuka yana shafa kansa da Hannu daya.

Kallon juna sukayi kamin suka sakewa juna murmushi.

Gira daya yazeed ya dagawa lukman yayinda lukman din ya masa thumbs up

Sidam sadam suka Shiga suka zauna a akujera yayinda ya Abubakar yace shh Dan Allah ki dena kuka sai lokacin laila ta bude baki cikin sarkewar murya tace ya abibi (yadda take kiransa) nikam na Shiga uku rayuwa tai min zafi.

Shafa bayanta ya farayi yace karki damu Komai zai wuce Allah ne gatan bawansa kuma ina tare dake ki daina kuka kinji tace to聽 Ummi. Yace yes Ummi tana inane muje kiraksni inyi mata ta'aziya.

Kuka ta kara fashewa dashi tace Ummi ta fadi ankaita asubiti.

Kallon juna su yazeed sukayi alamun what ? Gaskiya rayuwar yarinyar yana garari.

Ya Abubakar kuwa Cewa yayi Kiyi shiru kinji zata zamu lafiya Insha Allah Kiyi hakuri ki daina kuka. Ko kinaso nima in miki kukane ya fadi hakan a muryar wasa. Girgiza kai tayi tana turo baki yasa hannunsa yadan ja kumatunta yace good girl murmushi tayi kadan yayinda yake goge mata hawaye.

Yazeed ne yayi gyaran murya yana Dan shafe sajensa, Adan tsorace suka saki juna laila tayi saurin cewa bari in dauko hijabi na mu tafi asibiti sannan ta gudu yayinda Abubakar ke Sosa kai yana Dan dariya yace a'ah su angwayene dakansu? Ai banjo shigowanku ba.

Gyada kai yazeed yake yana smirking irin ai dole yayinda lukman kuma ya fadi abinda ke zuciyar yazeed din.

Yace mutumina ai dole bazakaji shigowarmu ba irin wannan dumi da kake sha.

Chanja zancen ya Abubakar yayi ta hangar Cewa kun Shirya my tafi asibitinne? Sukace mukam a Shirye muke shiri ai saikai. Mikewa yayi yace ai nima na Shirya sannan ya nufi kofa yazeed yayi saurin rikosa tareda Cewa聽 in-law dawo Duba rigarka dakyau. Lukman yace wani ai sai ya dauka dambe kayi.

Akunyace yadan Jade rigarsa squeezing din ya ragu. Lukman my man maganar nanfa bata Kare ba gara ma kaji.

Daidai lokacin laila ta fito. Gidan biki suka fara biyawa domin su dauki minal aje dubiyan da ita.

Fitowa sukayi a motan akabar Abubakar da laila daidai lokacin minal ta fito yazeed na kallonta ya saki murmushi.

Dan dunguransa lukman yayi yace my man kaima na....

ya Abubakar na kallon duk abinda ke faruwa Dan haka shima murmushi yake amma ba bakin tsokana.

Cikin gida ko zaliha ido ta rufe tace wallahi sai ta bisu. Aka buga aka raya tace Sam haka aka hakura akayi yarjejeniya da ita Cewa in aka barta toh Idan ta dawo zataci abinci.

Laila ko tana hango minal Yan hanjin cikinta suka kada domin ko bazata manta sanda suka tana haduwa sau daya ba sanda ta biyo ya Abubakar itada Sulaiman, minal ta dawo Daga islamiya ta mata duka Wai Dan tasha ruwa da kofinta. Shekaru 6 dasuka wuce.

Gaishesu tayi kamin su masa Shiga zaliha Kamar an jefota da takalmi a hannu.

Minal ne聽 ta zaro ido Adan tsorace tace zaliha me kikeyi awake?

Lukman ne yakalleta sannan ya kalli yazeed domin a tabbatar masa.

Kai yazeed ya gyada masa alamun itace matar tasa take yaji zuciyarsa yayi masa nauyi domin kuwa bayada interest a bakar Mace shiyasa ma yakeson ayush abinda bai sani ba shine ayush bleaching tayi.

Kara analysing dinta yake yazeed shima ya dunguresa Kamar yadda yamai dazu sannan kasa kasa yace inyi magana ko inyi shiru? Still idon lukman na kan zaliha yace yanzu fito kayi?

Ya Abubakar yace Inlaw barshi ba yanzu zamuyi magana ba sai nan gaba.

Zaliha ko binsu kawai take da ido,yazeed yace kai dallah kamo matarka kasata a mota mu wuce. Ya danyi hesitating kamin ya taka izuwa wajenta ya kamo hannunta. Wani yar yaji amma ya basar zaliha kam da hankalinta baya wajen batamasan an riketa ba ta janye hannunsa taje ta shige motar kamin tace Wai me kuke jirane? Yadda tayi magana Zaka rantse uwar su ce babu Wanda ya mata magana illa shigewar da sukayi.

Lukman ke tuka motar yayinda yazeed ke gefensa sai a abaya kuma minal tana owner's corner sai zaliha a gefenta sai laila a tsakiya sai ya Abubakar a karshe.

What do u think of laila? Kuna sonta?



Next chapter is a boom馃挜.

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty馃挄

23 November, 2019.

[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

馃尮by @mzz_untichlobanty@nt馃尮

*CHAPTER 44*

Yazeed ne yasa Hannu ya gyara mirror yadda zai iya hango minal abinda bai sani Ba kuwa shine lukman ke Satan kallon zaliha ta mirror din Dan haka shima ya hararesa bayan Yan sakanni yasa Hannu shima ya

Juya dauke kai yazeed yayi kamin shima yasa Hannu ya kara juyawa.

Duk abinda ke faruwa ya Abubakar bai lura domin duk hankalinsa ya ta'allaka a yadda yaje zaune kusada laila Dan haka ya kafeta da ido yayinda take wasa da Yan yatsunta ganin yadda ya kafeta da ido bazata iya kallonsa ba.

Minal kuwa window kawai take kallo tana tunanin rayuwa yayinda zally tayi zugum da alamu ta tafi birnin China.

Yazeed da lukman a tare suka kai hannunsa zasu juya madubin kallon juna sukayi yazeed ya harareshi shikuma ya sakar masa murmushi.

Lukman ne ya kalli cikin mirror din Anan ya hango abinda ke wakana a duniyar su Abubakar.

Nuni yayiwa yazeed daidai lokacin suka iso leka mudubin yazeed yayi suka fashe da dariya.

Zabura yayi yace har Muna ido ne ? Lukman yace bamu ido Ba Muna hanya tukunnan suka kuma fashewa da dariya su minal Kam da basu gane meke faruwa ba suka tsaya kallonsu.

Fice wa sukayi suka Shiga asibitin. Wata nurse suka tambaya Inda aka ajiye Ummi din ta nuna musu tare da cewa su Shiga bibbiyu saboda ba'ason hayaniya nan dai suka fara Shiga.

A take laila ta fashe da kuka dakyar dai aka lallabata kamin min sukayi hanyar gida.

Mayar da zaliha gida sukayi,laila kuma aka kaita gidan Kanwar mamanta.

Ya Abubakar Kamar zai mayar da ita ciki. Sai bayan isha'i suka Koma gida, yazeed yayi sallama da lukman tare da Cewa akwai abinda zasu tattauna goben lukman yace ai baki daya kakeson yin magana Ba nima akwai maganar da zanyi dakai.

Shigowa ciki sukayi kamin yacewa minal tayi wanka ta Shirya ta sauko taci abinci Toh tace sannan ta sauko.

Gyada kai tayi sai ta tuna bayason gestures sai tace Toh sannan ta haura sama.

Wanka shima ya Shiga yayi sannan ya saka kayan baccinsa ya sauko yana Cewa yunwa nakeji amma hanji na ya daure maybe I should take some cappuccino.

Sofa ya samu ya zauna kamin ya janyo wayansa ya fara scrolling messages.

Minal ce ta sauko cikin wani farin rigan bacci na satin amma Ba shara shara bane saide yana like mata a jiki once in a while.

Kallonta yake tayi har ta ido gabanshi bai ankare ba tace gaji still kallonta yake.

Hannunta tasa ta tafa a gaban fuskansa tace nace maka gani.

Hannunta ya kamo ya janyota ta fado jikinsa kokarin tashi ta fara yi ya kankameta sannan ya Daga mata gira daya yace sannu da zuwa.

Kiciniya ta farayi tana Cewa ni Dan Allah ka sakeni Wai na maka kama da yar iska ne? Murmushi yayi yace Kayan jikinki ya amsa mini wannan,sannan tunda gaki kwance ajikina ai kinzama yar iskan ko turo baki tayi ta fashe da kuka ni wallahi ba yar iska bace yace time will tell. Itadai bata kulasa ba banda ci gaba da magana da tayi tace to ai kaika janyoni kuma ka wani rikeni sai kace zaka mayar ni ciki yace to wa ya sani ko cikin zan mayar dake.

Ganin babu sarki sai Allah yasa yasa ta kwanta luf ajikinsa babu abinda ke tashi a parlourn sai sautin numfashinsu kasa kasa minal taji yace "sai Anyi magana mutum yace shi ba Dan iska bane.

Tace me kace yace tunani nake. Harararsa tayi sannan ta kuma kwanciya can sai yace Wai meyasa bakison kirana da suna nane ? Saide kawai ki fadi magana,Ko kuma kicemin oga sir. Ko bakisan sunana bane ?

Girgiza kanta tayi a kirjinsa tace na sani mana ba kaima baka kirana da sunana ba saide ka dinga cemin insaram yace to mene sunan nawa?Dago da kanta tayi tana washe ha'kwara ita a dole kunya tace kawo kunnanka kaji.

Matso da kunnansa yayi a hankali kuma a kunyace tace oga ya..zeed.

Sanda tsikar jikinsa suka tashi domi. Tunda yake bai tabaji sunansa yayi masa dadi Kamar yadda yayi a bakinta ba.

Dan haka yace me ki kace ?ma'ke kafada tayi alamun bazata fada ba.

Puppy face yayi Yace please my insaram! Turo baki tayi tace ba gashinan ba kana sake cemin insaram yace to na daina Idan kika fadamin sunana to zan chanja miki suna.

Hannu tasa ta rufe fuskanta sannan tace oga yazeed

Yace to ki cire ogan tace yallabai zansa ?yace a ah tace to yaya kakeso Insa maka yace ah ah kawai ki kirani da suna na.

Tace a ah ba tarbiyya bace in kiraka da sunanka ko ba Komai ka girmeni.

Murmushi yayi yace beauty is secretly trying to be romantic da muryar tsokana. Turo baki tayi cikin shagwaba da wasa tace wallahi ya yazeed da gangan kake min turanci Dan kasan ban iya ba yace sorry Toh na daina karki damu kema zan koya mini turanci. kinaso ki Koma makaranta gyada kai tayi yace good zannayi miki lesson a gida inyaso sai Kiyi jamb da WAEC ko ? Tace eh yace beauty tace Waye beauty kuma yace Kece mana Sabon sunanki kenan. Ya miki? Ta gyada kai tare da Cewa eh yace kinsman ma'anarsa tace yana nufin kyau ba? Smiling yazeed yayi sannan shima ya gyada mata kai yadda take mai sannan yana kumatunta yace Ashe de beautyn tawa ba laifi.

Shiru wajen ya sake dauka kamin yazeed ya sake Cewa beauty ta dago ta kalleshi yace inason ki saki jikinki in Muna tare kinji? Ta gara kai yace kinaso ki zama kawata ? Ta sake gyada kai turo baki yayi yadda take mai inya mata abinda bataso yace bazakimin magana ba? Tace inaso in zama kawar taka. Tasar da ita yayi ta daina shima ya gyada zamansa Daga kishingida sannan ya miko mata Hannu yace friends? Shaking hannunsa tayi yace bakice friends dinba tace friends sai suka kyalkyale da dariya.

Daidai lokacin cikinsa yayi masa karar yunwa abinda bai tana faruwa dashiba ko a mission kuwa.

Pouting yayi yace beauty yunwa nakeji tace muje kaci abincinka to yace nope cappuccino zansha tace cup...po聽 mene? Yace cappuccino kin gaba sha ? Girgiza kai ya harareta tace a ah.

Yace okay muje kitchen in nuna miki yadda akeyi kai kawai ta gyada suka nufi kitchen dauko duka ingredients yayi sannan ya nuna mata yadda akeyi tace kai Ashe da sauke itama ta hada wani cup karba yayi ya murna yaji yayi dadi sosai zai iya rantsewa bai tabashan cappuccino me dadinshi ba.

Kurba itama tayi kamin ya riko Hannunta suka hau kan kitchen island suka zauna.

Yazeed nasha ahankali yayinda a kurba uku ta tada nata har tana kwarewa yazeed yace sannu bari in dauko miki ruwa tace barshi kawai bari in hada lamurje (lemonade) Insha saboda wannan cappuccino din maka na Daga min zuciya okay kawai yace

Lemon tsami ta dauko yace Kiyi ahankali kada ki yanke tace Toh. Lemonade ta hada tana kokarin saka sugar taji cikinta ya wani murda Dan dafe cikin tayi amma Ba tayi magana ba yazeed ya lura domin tunda ta fara hade hadenta yake binta da ido.

Ajiye cappuccino dinshi yayi yazo ya rikota yace lafiya tace babu kawai sai ta saki kara kadan yace ki fadamun menene?

Girgiza kai kawai tayi sannan ta dauko lemonade din tace sha kaji yayi dadi? Kurba yayi yace yayi sosai ma kuwa kin tabbata you are okay tace eh sha Rabi sai kaban in shanye inna na cemin duk sanda mutum taci abinci to Tasha ruwan lemon tsami saboda yana taimakawa wajen narkar da abincin.

Kara kurba yayi sai yaga minal tana hade fuskatana cije lebe.

Ajiye cup din yayi ya dafa kafadarta da hannu biyu amma kamin yayi magana minal ta saki kara Innalillahi ya yazeed cikina! kamin kace me kumfa ya fara fitowa Daga bakinta.

*Na Shiga uku ni yar mutum 2 jikar mutum 4 me kuma ya sami minal?*

Lemme kuku run for my life before you kill me!

Miss untichlobanty馃挄

24 November, 2019.

[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳

馃尮by @miss_untichlobanty馃尮

*CHAPTER 45*

Sulalewa tayi Take yazeed ya bita Ya tsuguna fuskanta cikin tafukan hannunsa yace ke rosy cheeks! Rosy cheeks ! Menene? Kunfan dake kara bulbulowa a bakinta ke kata Daga masa hankali.

Cikin shakewa da kafewar murya minal tace ma..d..dara. Ganin kamar bakinta yayi motsi yasa yazeed ya saurara da tamboyin da yake mata Dan ya rikice.

Ahankali ta sake Cewa mad...darrr..aaa kamin wani kunfa ya kuma fito wa Daga bakinta.

YAZEED yace madara? Ta rufe idonta ta bude a hankali alamun eh. Da Sauri ya kwatar da ita ya mike ya dauko madara ya bude ko kallon Inda kofi suke beyi Ba ya kafa mata.

Tana fara sha ya sauke ajiyan zuciya Wanda yayi dadai da murdawan da cikinsa shima yayi.

Basarwa yayi amma murdin da cikin ta kara yi yasa yayi sauri zau ajiye gorar madaran daya kawowa minal.

Minal kam ta lura da yanayin yadda yake yatsine fuska Dan haka a take tayi saurin sa hannunta ta hade gorar da hannunsa takai bakinsa daya fara zubda kumfa.

Sanda ta tabbata ya shanye kamin ta kwantar dashi a wajen jiki babu kwari ta nufi fridge ta dauko ruwa da wani madaran sai kitchen towel.

Bakinta ta goge sannan ta goge masa nasa bude ruwan tayi zata kafa abaki taji muryansa kasa kasa yace ki dau kofi. Ba musu ta dauka ta zuba tasha sannan ta zauna ta daura kanshi a cinyanta sannan ta bashi ruwa.

madaran ta kara bude musu ta zuba cup din zata sha yayi saurin mikewa Daga cinyarta Dan karfinsa ya fara dawo masa.

Pouting yayi Kamar yadda take masa kullum yace rosy cheeks ni zan fara sha. Dariya ta kyalkyale dashi saboda yadda yayi maganan Kamar wani Yaro.

Bashi tayi yasha sannan itama ta kafa kai tana sha, ji tayi ya fashe da dariya dan haka ta dago da idonta tana masa kallon dariyar me kake yi ?

Yace rosy cheeks literary we just kissed tace uhm? Yace munyi Sumba nida ke saboda daidai Inda na kafa bakina nan kika sa naki. Zaro ido tayi Take madaran ya kwareta sannu yayi mata ya shafa bayanta sannan ya bata ruwa.

Hararansa tayi idonta ya ciko da kwalla muryarta na rawa tace Nide wallahi bamuyi Sumba Ba danni ba..... Sai kuma tayi shiru.

Yazeed sarai yasan me zata ce dan haka yace uhmm? Tace babu sannan ta dauke cups din ta wanke ta nufi dakinta yayinda yazeed ya kira doctor tunda dare beyiba sosai 9:10pm nema.

Koda doctor yazo yazeed yayi masa bayani Dr din yace poison ne.

Yazeed yace ya sani. Dr din yace menene last Abu da sukaci kamin attack din yace cappuccino ne amma kuma abinda ya bani mamaki kullum ina sha ban taba samun attack dinba.

Doctorn yace lets check the expiring date then. Dubawa sukayi amma akwai har shekara 1 da wata 3 before yayi expire. Doctorn zan kaishi lab in bayar domin test dan something is fishy.

OK kawai yazeed yace聽 ya raka Doctorn har bakin main door sannan ya rufe.

Dakinshi ya nufa ya kunna CCTV sannan ya tafi kitchen direct.

Forwarding Inda su tala sukayi su girki yayi making sure indonshi akan Ronan cappuccino powdern.

Chan bayan sun fita yaga Jennifer ta shigo tana sanda da waige aiko bata tsaya ko ina Ba ta dauko cappuccino powdern tayi mixing da powdered poison sannan ta zaro wayanta tayi kira kafawa a kunnenta tayi kamin chan tace angama aikinindai yasha to zai mutu murus...... gyada kai tayi kamin tace yes ma amma ma problem din baza'a budemin gate Ba sai da izininsa.

Shiru ta kuma yi da alamu tana sauraron dayan bangaren kamin tace yes ma karki damu zan labe da motansu ya shigo ni sai infita...........thank you ma.

Take ya dauki wayansa ya ranbadawa lukman text Cewa a nemo masa Jennifer ko a ina take a muce ko a raye.

Aikinsa ya fara a apple laptop dinsa amma hankalinsa Sam baya kan aikin da yakeyi hankalinsa ya ta'allaka ne akan wakeson kasheshi tunda acikin cappuccino akasa guban kuma shi daya ke shan cappuccino a gidan.

Bayan Kamar 30 minute wayanshi ya fara ringing dauka yayi ta dayan bangaren lukman聽 yace sir mun samota a kawo motor park da alamu so take tabi motar asuba. Yazeed yace great! aikinka yayi kyau, Ina alfahari dakai.

Lukman yace thank you yanzu haka ma tana hannuna we tricked her to come with us.

Yazeed yace tayaya kuka yi ne?

Lukman yace my man Ba Kai daya bane charming fah kawai nuna mata Nayi ina bukatarta a gado Ba musu ta biyoni tana shigowa mota taga bani daya bane ta fara zagina tana kuka Wai na cuceta na yaudareta zanjawo a kasheta.

Dariya yazeed ya sheke dashi jin yadda lukman din ke kwatanta yadda tayi maganan yace shegiya ai kadan ta gani.

Minal ko bayan ta Koma dakinta wanka ta sakeyi ta canja rigarta sannan tasa hular baccinta

17 / 45