Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
domin haushinta sukeji Wai ta fisu kyau,domin ko Kamar inna ta dauko amma hasken baba dukda Cewa innan ma Ba baka bace amma batada haske sosai amma akwai gashi masha Allah Wanda amina har tafita hakama kyau
Suna zuwa zasu wuce daya daga cikinsu mai Suna bilkisu(bakace er lukuta mai katon timbi ga katon lebe da boobs yadda kasan kwarya saide batada hips Wanda hakan yasa ta zama Kamar an ajiye buhun hatsi gata gajeruwa anci red lipstick,brows dinnan ba'a magana) ta bangaji Amina da kafada
Dan cika amina ta cika amma sai ta basar saboda tunda tayi mafarkin laser fever ya kasheta ta rage jagwal
Ganin bata kulasu Ba yasa sameera (doguwace siriiiiriya gashi batada shape,Ba gaba Ba baya atakaice de yadda Kasan sandar snooker ko ince 1 irinsu akewa kirarin singul amama no front no back gashi taci uwar bleaching had tafara zama danyen nama),
Tace ke Amina wannan wani irin iskanci ne zaki mangari billy ko hakuri bazaki bata ba
Amina batace Komai Ba ta ci gaba da tafiya
hannatu ce(wannan ita ba'a magana)tazo ta bankade Amina.
Ai ji kake tas! tas!! tas!!!
To readers wa aka wanka wa mari haka Indai Amina aka Mara to Ba zaman lapiya
Nide bara in labe daga bayan bishiya in debo muku rahoto
Give me some bossa !
By
Voting
Sharing
Commenting
And
Liking
Your er uwa mai nishadan tarwa da fadakarwa
Examination mode on
Mzz untichlobanty馃挄
12th may 2019
[1/11, 1:28 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒:
馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
By miss untichlobanty
*馃崁CHAPTER 7馃崁*
Wani wawan mari amina ta sakewa hannatu har sanda taga tauraro
Sameera ce ta hayaiyako zata daki amina,wani lafiyaiyan mari
Amina ta aika mata atake ta dauke wuta ta suma zaliha ce tace ni amina zo mutafi kamin kisa da naushi Kiyi kisa taja hannunta suka tafi ayayinda akabar bilkisu sakoko a tsaye batada tudun dafawa gashi yau zasu wanki wani alhaji yace su ukun za'a hada lokaci daya (Allah shi kyauta)
Atake taji wani bakin ciki ya rufeta taji ta kara tsanan amina.....
Amina kuwa dasuka je islamiyya sunyi latti gashi malam isa ke taran latti ya iya bulala Kamar Allah ne ya aiko shi
Shikadai ne yake iya dealing da amina kuma tana tsoransa sosai amma tsabar bakin ciki da haushin daya rufe mata ido bata lura dashi Ba
Sai saukar bulala da taji batasan sanda ta karbi bulalan ta karya Ba hade da banka masa harara ayayinda ta murkuda cute pinky lips dinta tace Allah ya isa ta wuce
Malam isa sai da yasha jinin jikinsa domin yasan yadda take tsoranshi(saboda ya iya bulala itakuma duk abinda zai taba lafiyar jikinta bataso)
amma yau harda karya bulala wadda take tsoro Kamar maciji gashi fiskanta yayi jaaa(red)alamun Bacin rai kuma dama shima dai yana shakkunta karfin hali ne kawai irin nasa amma ya girgiza yau Dan haka satinnan dole ya Dan tsagaitawa amina idan Ba hakaba shima zai karbi rabonsa ko ta kullo masa jagwal.
Haka suka Shiga aji Amina tasha mur,zaliha nata aikin ban hakuri hakadai har aka tashi suka dawo gida tana kumbure kumbure.
Bayan sallan magriba inna ta gama abinci ta kwalawa Amina kira bata amsa Ba ta kara kwala mata kira still shiru abinda bata tabayi Ba kenan akirata taki amsawa shiga dakin inna tayi thinking that something is wrong with her daughter to her surprise Amina was sitting down on her mattress
Ke er lele dama kina jina kikai shiru to abincin ki zaki dauka she didn't reply inna rather all she did was sip water from her tiny blue cup
Inna tace er nan Ba lafiya Dan a yadda nasanki ko bata maki rai akayi baki wasa da tuwo amma yau ko motsi bakiyi
Ta fadi hakanne ayayinda take taba goshin Amina Dan inna ji take Amina batada Lpy domin ita bata wasa da tuwo
Jin ko magana batayiba yasa inna ta fita ta samu baba ta labarta masa abinda ta gani baba ne yace rabu da ita zamu hadu atakaice de ranan Amina bataci abinci ba.
Washe gari koda Amina ta tashi tayi shara da wanke wanke ta gama koko,
Sai wajen karfe goma ta tuna da Cewa zata raka zahra anguwa tashi tayi tasa hijabi taje dakin inna tace inna ni zan tafi gidansu zahra tace zan rakata anguwa
wani kallo inna ta watsa mata kamin tace shine gaisuwan ki ?
Amina tace mantawa Nayi ina kwana
Inna tace rike abinki
Sannan a haka zaki rakata anguwan kai Innalillahi aminatu yaushe zaki canza yau kwana uku kenan bakiyi wanka kuma a haka kike tunanin zaki samu miji ki Duba kullum in zahra zatazo gidannan kwas da ita amma ke a birkice
Since bakin zaninta tayi ta miko mata Dari biyu ki siyo sabulu da tirare dan d'uri da sabulun gashi kinji
Bubbuga kafa Amina ta fara haba inna zan bata mata lokaci fa
inna tace to wallahi inbakiyi abinda na fada Ba babu Inda zaki mutum sai shegen kazanta Allah ma daya taimaka bakida karnin kashi ai da mun mutu
Turo baki tayi tana guna guni har ta siyo ta dawo
Inna tace maza Shiga wanka ki wanke kanki sai kizo in miki kitso saura kiyimin gardama ma babu inda zaki
Subul subul tayi Kamar yadda inna ta umarceta ta shiga ban dakin shiru shiru babu ita babu labarinta inna tace wai me kike yine har yanzu kinsan dai jiranki nakeyi ko?
Fitowa tayi gefen kanta duk kunfa inna tace ke haka ake wankar duk dadewannan nanki baki daurayu Ba? Bata ko kula innar Ba ta shigewarta daki ta goge kan sosai ya zama saura damshi sannan ta zauna aka mata kitson ta dauko kayanta mai Dan haske ta saka sannan ta Dan shafa man baki sai tayi dass da ita.
Tana fitowa inna tace ko kefa amma ace mutum bayason wanka minal tace inna kwana biyu ne fa inna tace kaji banziya ko kunya bakiji har kina daga murya gararin makota suji
Tace to Nide na tafi tana fitowa Zaure ta hadu da baba tace baba ina kwana yace Lpy a'a aminatu ce haka ko bake bafa amma ace mutum kullum...............
Tace to baba ya isa mana tunda Nayi wankan yace yauwa er gari kinga in kina Dan kwalliyan nanne zaki samu miji ko Ba haka ba
murmushi tayi ya miko mata naira Dari yace na sanki da awara watakilla shi zakije siyowa ko innan ki ce ta aike ki
tace a'a gidan su zaliha zani zan rakata anguwa Dan auntyn ta ya karye kuma zamu tayata gyaran gida dashi ke basu Dade da kaura wannan gidan Ba
Baba yace Toh sai kin dawo amma karkiyi dare tace Toh kamin ta fita tanayi masa godiyan kudin daya bata
Tana fita tace Kamar baba yasan banda kudi wlh
Abangaren YAZEED kuwa yau ana shiri da mitimiyar domin bataje office Ba,
Ya Shirya musu evening outing zaliha anci ado makeup kamar ya zubo daga fiskanta attachment dinnan ba'a magana sai harhada rai take wai ita adole batason raini(nace uhm shi baice zaki rainashiba sai ke?)
Taku daidai take har ta iso gaban wani Mercedes Benz sai yauki take alokacin YAZEED ya Dade yana jiranta domin yace shi da kanshi zai tuka su kuma bayason escort na soldiers ko daya.
How is the novel?is it good?any suggestions?
Ramadan Mubarak and happy sallah in advance
2nd June 2019
Show some love
Mzz untichlobanty馃挄
[1/11, 1:30 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒:
馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
*CHAPTER 8*
Tana shigowa ya kunna mota domin yaji haushin bata masa time da tayi domin he values time so much. Tafiya suke a hankali babu Wanda ya kula kowa
馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮
Abangaren minal kuwa ta isa gidan su zally ta sameta tana kwalliya an rike mirror da bakin eye pencil sai zana girannan ake baki wuluk abin abin dariya
'Daka mata duka tayi a cinya
Kinga abinda kika jawomin ko? kullum in zakije anguwa saboda iyayi sai kinyi kwalliya kinsa inna ta Mani kitson dole ta sani kwalliya.
Sai alokacin zally ta kalle ta tace kawai kice kinyi kwalliya kinaso ki nuna mini聽 shine zaki fake da guzuma ki harbi karsana!
To wallahi bashi dukannan.
Minal tace wannan ke ta shafa sannan ta zauna tace kinsan yau Dana hadu da baba a Zaure na dauka duka na zaiyi saboda tabarar danayi musu a gidan
Ga mamaki na bemin maganar Ba kuma harda bani kudi
zally tace iye lallai kwalliya ta biya kudin sabulu,wato haduwar taki har akan baba tayi tasiri, yo ina batun su babba?hararanta minal tayi taci gaba da cewa amma matsalata dake ko kwalliyan baki iya Ba kinsan mu yan boko kuma wayayyu anaso adinga yin make up mai kyau amma kin wani shafa powder da man baki
Minal tace iye sannu wayaiya yar boko.
Zaliha tace ke nifa zan cigaba da karatu domin suleiman yanason inyi karatu har kudin WAEC ya biya min a wata makarantar private kuma yace zai Nayi mini lesson in munyi aure.
Minal tace lallai ma yarinyarnan wato haka zamuyi dake? tafiya makarantar gaba zakiyi ki barni?
Zaliha tace a ah zama zanyi in jiraki harsai kin zama farfesiya
kallon zaliha minal takeyi yayinda zalihar taci gaba da kwalliyarta.
Can zaliha tace ni yanzu banida burin daya wuce in Tara kudin Indan siya man kara haske Dan ba'kina yayi yawa wallahi.
Minal tace man me?! Sauri zaliha tayi ta rufe mata baki tace toh sannu sarkin karadi so kike iya taji ko?
Tureta minal tayi tace to in tajin ma ai haka akeso ni ban taba Sanin bakida hankali bama sai yau,ke bakisan Cewa butulci wa Allah bane ace yayi ki baka kice Wai bakinki yayi yawa ? Kin FISA sanin daidai ne? Kuma ai koba Komai mayukan blitin dinnan yana 'bata fata bara kij,i kuma iyada lahani sosai saima kinji ciwo in yaki warkewa zakiyi bayani.
Karkiga ke baka ce wallahi wani zai iya mutuwa akan bakar mace kuma wallahi sai kiga fara ko a kafa aka daura masa sai ya kunceta.
Kima godewa Allah kinada kyau farare nawa ne munana?mtswww!
Ajiyan zuciya zaliha ta sauke kamin tace kuma fa maganar ki Gaskiya ne waje daya kika kwafsa Ba man blitin akace Ba bleaching ake Cewa. minal tace Koma menene Nide tashi mu tafi.
Zaliha tace Gaskiya kizo na Dan miki kwalliya minal tace Wanda Nayi ma ya isa.
Tace shiyasa bazaki taba samun saurayi Ba ki Duba ki gani kafin a tsaida lokacin aurena samarina dayawa
Amma ke wa ya taba miki kallon birgewa ma
Shiru minal tayi kamin tace kuma fa hakane wato shine sirrin baki taba fadamin Bako,Allah ya isa
Zaliha tace ai shiyasa kullum inna ke miki fada akan wanka baki gane Ba
Minal tace to me mike jira zana mini ado Yan mata
zama tayi zaliha ta shafa mata Jan powder aka zana girannan akayi mata Layin baki da green
Yadda Kasan er tashe
Fitowa sukayi zasu tafi sukayiwa iya sallama tanata kodasu Wai en matanta zasu haska titi
Koda suka fita zaliha ta ballawa Amina harara tace er uwa matsalata dake baza'a taba iya gyaraki Ba kaf duniya Ba Wanda zai iya in aka gyara nan sai asamo wani matsalan
wannan wani irin tafiyane?
Minal tace me matsalar tafiyannawa ?
zally tace kinga yanda ake tafiya yanga ta soma Kamar talotalo (lol karfa kuce ina kushe characters dina zasu Waye, just for entertainment ne 馃槀馃槀)
Minal ma ta fara kwaikwayanta abin har gwara na Zally domin minal ita nata Kamar agwagwa馃槀.
Ana cikin haka aka fara ruwa Kamar da bakin kwarya
Yan matanka suka nemi wurin buya domin kada ruwa ya musu duka,
amma sanda aka sami matsala domin ya ca'be musu ado
Abangaren yazeed kuwa parking yayi domin ruwan ya tsagaita ganin zakky baby ta 'bata masa lokaci gashi ko kulashi batayi Ba balle yasa ran zata bashi hakuri abin sai ya bata masa rai
Yace
Zakky what's all of this ?
Tace
Meaning?
Yace
first you wasted my time,also came out walking like a snail and you can't even apologize?
Tace
What wrong have I done that I will apologise? Is it wrong to walk majestically?
Look that's fashion
She said that Prolonging the fashion
Yace
Fashion my foot,the hell with it
Alokacin ruwan ya tsaya kunna motan yayi
Ayayinda zakky ke Cewa
Look idan ka fito dani just to disgrace me ne am not in the mood please hurry up ma ni am starving gushhh
Wani wawan acceleration ya kwasa ya kure speed din motan shi dama ba mutane akan titin
Alokacin dadai su zaliha sun fito daga Inda suka labe domin su tsallaka titi takalmin minal ya Tsinke tsallakawa zaliha tayi koda ta juya ta hango minal bata tsallako Ba tace Ki tsallako kamin abawa motocin Hannu .
Minal tace ke aradu sai na gyara takalmi na.
Zaliha tace wallahi ko ki tsallako ko in tafi in tafiyata minal tace da nace ki jiranine?
Tsugunawa tayi ta cire takalmin ta fara kokarin gyarawa yayinda zaliha tayi tafiyatta tana mai jin haushin minal din.
Neman kara minal ta farayi bata zamu Ba aiko tana Daga kanta taga wani a tsakiyar titi Dan haka Ba tare da nazari Ba ta hay kan titin domin burinta kawai ta gara takalmin ta.
Alokacin kuwa aka bada Hannu kuma daidai lokacin fada ya kaure tsakanin zakiyya da yazeed CeCe kuce suke tayi yana hankalinsa kenan daga titi yana Cewa zakky don't try me this evening
Minal kuwa ta dauko karanta tana kokarin gyara takalmin tare da tafiya a hankali akan titin domin itama ta tsallaka taga mota a guje yana iyowa kanta
Duk kayan cikinta sanda suka kada.
Daidai lokacin yazeed ya lura da ita kokarin kaucewa yayi ya fada cikin wani Dan rami Wanda ruwa ya taru kuma ya daki motan wani
Tun daga sama har kasa yawatsawa minal ruwa ta sule ta fadi kasa yayinda mai dayan motan ya fito......................
Hahhhh finally
This is my sallah gift to u guys hope you like this chapter
NOTE:
All pictures of characters shown here are not related to the story.
Kindly share, and comment thank you
Much love
4th June 2019
Mzz untichlobanty馃挄
[1/11, 1:33 AM] Mzz_Untichlobanty馃挒: 馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳
By miss untichlobanty
*馃崁馃尮CHAPTER 9馃尮馃崁*
Juyowa yazeed yayi ya kalli zakiyya yace oh gush,look at the mess you cause!
Minal ko lokacin da ta d'aga idonta taga Wanda ya watsa mata ruwa ya juya yana magana da wata(saboda motar Ba ita yake using ba babu tinted)abin ya mugu bata haushi
Minal ta fara magana a hankali lallai ma mutuminnan ya watsa mini ruwa sannan ya tsaya magana da budurwarsa?
Mikewa tayi zata zazzaga masa rashin mutunci daidai lokacin me motan nan ya fito yazeed dake shirin fitowa shima yace bawan Allah kayi hakuri....
Mutumin ne yayi saurin katseshi ta hanyar Cewa聽 wa make gaji Kamar captain yazeed murmushi yazeed yayi yace nine Dan Allah a Duba ma asarar da Nayi sai inbiya ga card dina ya fadi hakan yana kokarin bawa katinsa mutumin yace ka barshi kawai yallabai ai paint nema ya Dan kurje Gaskiya Muna alfari dakai a ka sannan Allah ya kara yi maka jagora yazeed yace ameen amma dan Allah ko wannan ne ka karba mutumin yace waneni ranka shi Dade kuda kuka bamu rayuwarku Dan kukaremu shine har sai na karbi kudinka Dan ka gurjemin mota?ai kake wallahi Ba Komai sai alolacin ya lura da zakiyya cikin fara'a yace ina wuni madam ? Ya tsine tayi kamin kasa kasa tace lafiya tana mai kauda kai.
Dariya mutuminne ya dauke yace ranka shi Dade zamu iya yin selfie? Murmushi yazeed yayi yace Ba matsala. Quick selfie mutumin ya musu sannan ya Shiga motarsa yana mamakin abinda zakiyya tamai dukda ko bai Santa Ba amma da alamu tanada alaja da yazeed din.
Yazeed ko da ya mance da ya watsawa minal ruwa dukda ko laifinta ne tana tafiya ahankali akan titi amma shima harda laifinsa daya biyewa zakiyya ya kunna motarsa zai wuce minal tayi saurin riko hannun kofar
sauke glass yace baiwar Allah dan Allah Kiyi hakuri ban lura bane wallahi hankalina ne ya sauke Daga titin amma kema hada laifinki kina tsallaka titi bakya kallo ki kula Dan Allah
ya fadi haka yayinda ya zabgawa zakiyya harara yana kokarin Ciro kudin a aljihunsa.
ganin zakiyya ta fashe da dariya, abin ya kara bawa minal haushi
Su watsa mata ruwa amma ko su kallo Inda take yarda wani tsayawa Suna surutu da photo da wani mutumi sai kace Yan film bayan sun gama Iskancin nasu zasu ta fita rikosu shine ya wani kwame a mota yana bata hakuri
Sannan budurwarsa tana mata dariya
kwafa minal tayi kamin ta kama kwankwaso ta fara jijjiga tayi kicin kicin da ido
Tace wallahi Allah ya isa na ya za'ayi Ku watsan ruwa kuma kunai mini dariya
Babu abinda yazeed ya tsana Kamar ayi masa Allah ya isa
Hakan yasa shi mugun mamaki amma ganin fiskanta kwalliyar ta cabe bakinnan sai yalki yake Kamar tasha man gyada
Abin ya basa dariya amma ya shanye,50k ya miko mata yace gashi ki siya sabulu聽 kije a Duba ki kiji kanwata ?
Minal tace me kuddin zai min kuma babu wani batun Kanwarka ni karkayi min zakin baki Dan bazaiyi aiki Anan Ba. Ta fadi hakan sannan ta murkutsa baki
The girl is now getting on his nerves
He just pressed his car accelerator trying to leave
Not yet Mr.yazeed abdulmajeed
Wani tsalle minal ta daka ta sake rike hannun kofarsa
Zakiyya babu abinda take sai dariya Dan ita ganin clown takeyiwa minal,fadan nasu yana kayatar da ita hakan yasa ta dauko wayarta ta fara video.
Malam ya zaka watsamin ruwa ka kusa bigeni har na fadi kasa amma ka hakimce a mota kana miko mini kudi me zanyi da kudinka?ai fitowa zakayi ka Duba Lpy ta.
Fitowa yayi a harzuke
Kusa da ita yazo ta