Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
nata ya d'auke gaba d'aya take alh. Munzali yakira wasu k'artin banza suka janye masa ita suka aje wacce yasa aka sakawa irin fuskar hajiya munira sak awajen tareda dunk'uleta waje guda hannunta saman cikinta alamun tana murk'ususu ta rasu.
Wata irin mahaukaciyar dariya ya kece da ita sannan yasakarwa kansa kirari sannan kuma naga ya had'e rai tareda fashewa da kuka.
Haka iyayen haj. Munira sukayi jana izarta cikin tsananin bakin cikin rashin kamilar d'iyar tasu da sukayi yayin da alh. Munzali yake kuka kamar ransa zai fita.
Suko su Abdulmajid koda suka kawo asbiti abinda yai mutuk'ar gigitasu ya d'aga musu hankali shine ganin yadda gaba d'aya jinin da yab'ata musu jiki da wanda ya yake bin jikin Yusra ya bace b'at, babu ko alamunsu k'asan motarsa yakai dubansa inda ya b'aci da jinin, Abdulmajid yakai dubansa take yaga wajen tas babu alamun wani jini take gabansa yai wani irin mummunan fad'uwa.
Ita ko Fatima dubanta takai kan Yusra dataga kamar tana motsi atake Fatimar ta sandare awajen sakamaon idanun Yusra da Fatima tagani yana wata irin ci da wuta ga kuma wasu irin halittu a ciki suna k'yalk'yala mata dariya, take Fatima ta sume ajikin Abdulmajid tsabar gigita da rud'anin data shiga.
Jin fad'owarta jikinshi yace "Fatima yanzun ba lokacin kuka bane wannan abun addu'a yake buk'ata tashi kiga mu fara kaita a duba mana lafiyarta tunda nayi imani har ga Allah wannan cikin mun rasashi kuma nasan tabbas aikin matsafan nanne wallahi Fatima nagaji da wannan masifar yazama dole nayi fito na fito da wannan azzaluman"
Jin duk maganganun da yake shiru babu amsa yasa hannu yad'agota "innalillahi wainna ilaihi raji un" yafad'a da k'arfin gaske wanda har saida ya yajawo hankalin wasu mutanen tareda ma aikatan wajen da gudu suka kawo masa temakon gaggawa aka kwaahe su akayi emmagency dasu, yayin da Abdulmajid ya kifa kansa saman sitiyarin motar wata irin zazzafan kwalla ya kece masa.
"Kana sane sarai da matsalar da kaja mana ko abisa wannan hukuncin daka yanke akan matarka Munira?
To ka shirya wa kanka abinda zaka kare kanka dashi awajen shugaba"
Take hankalin alh. Munzali yayi mugun tashi idanunsa sukayi wani irin ja yace "to yazanyi Asma'u bani da wani zab'in da yafi wannan domin tariga da tasan komai ammafa ba kasheta nayiba kawai dai anbuga mata sandar tsafi atsakiyar kaine kin sani sarai zata farfad'o nanda shekara guda cikin bacewar hankali.
Suna cikin tattaunawar ta bayyana agansu cikin shigar daya d'agawa kowa hankali domin muddun tayi wannan shigar to babu lafiya,
Take gaban munzali da Asma'u ya yanke ya fad'a suka kalli juna cikin fad'uwar gaba amma basu iya cewa komaiba.
Sanye take cikin bak'ak'en kaya yayin da k'wayar idanunta ma yasance bak'i k'irin idanun suna fitar da wani irin hayak'i.
Ga mamakinsu kawai sukaga tafashe da kuka yayin da hawayennata yakasance bak'i kamar ruwan kwalta tasoma magana cikin tsan tsar bak'in ciki da damuwa.
"Munzali ina mai tabbatar maka ka tafka kuskure mafi muni arayuwarka, wayace ka tab'a wannan tak'adiriyar matar taka, koda tace maka tasan sirrinka kana tunanin zan bari asirinmu ya tonune? to ina so kasan cewa duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kanka amma badaniba" daga haka tayi wata irin bacewa wadda guguwar da ta taso saida ta watsosu waje.
Wani irin kuka mai k'arfin gaske alh. Munzali ya fashe dashi take haj. Asma'u ta dubeshi tace"kayi hak'uri kayi shiru kaga a mutane karsu gane abinda yafaru.
Da yake duk abinda yafaru acikin gidansa ne.
Take kuwa mutane suka fara bashi baki cikin tausayawa domin sunyi tunanin yakasa jure rashin da akayi masane.
Acan asbiti kuwa tuni Fatima ta farfad'o tana ta kuka, amma Yusra ko yatsar ta bai motsaba fad'an irin tashin hankalin da Abdulmajid yake ciki ma b'ata bakine,
Cikin yini guda kacal yayi wata irin masifaffiyar rama ga kukan Fatima dayake masifar hargitsa masa tunani, gajiya yayi da koke koken yajata cikin mota ya rungumeta tsam tsam tareda had'e bakinsu waje guda shikenan ya sami sauk'in kukan.
Muje zuwa
Daga maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 18
..............................sosai yayi kewar Fatiman ya dinga bi da ita cikin salonsa mai sanyi da saka nutsuwa.
Bak'aramin tashi hankalinsa yayiba, dole anan cikin motar ya kauda k'ishirwan dayake damunsa.
Take baccin data dingacin bashinsa ya kwasheta anan, ya dinga kallonta cikin tsantsar so da k'auna gami kuma da ta sauyawa halin da suke ciki su duka.
"Munxali kanemawa kanka mafita tun kafin dare yayi maka"
Cikin tsantsar tashin hankali yake duban Asma'un kafin yace "to ya kikeso nayi Asma u kina kallofa ni ina can ina haukata ashe tsirara Munira take kallona, tagama sanin duk wani sirri nawa bansan wanne abu zan aikata dayafi wannanba"
Cikin matuk'ar damuwa Asma u tace "hakane Munzali koni nasami kaina a irin matsayin daka tsinci kanka irin hukuncin da zan yanke kenan, sai dai kuma yayinda muka shiga halin k'ak'a nikayi sai muke mantawa da umarnin shugaba GAZA datace duk wanda zai yi wani abu yafara shawartata dan haka nema kuka sami wannan matsalar, abinda zai faru kawai yanzu kaje kasamo mata yara 'yan shekara uku hud'u kaga tana sonsu sosai, kaga idan kai hakan dakanta zata samar maka da mafita"
Cikin share hawayen dayake tayi tun d'azun yace "kina ganin ganin idan nayi hakan ba wani damuwa?"
Cikin k'arfafa masa gwaiwa ta tabbatar masa, sun d'an jima tana kwantar masa da hankali kafin tatafi shi kuma ya koma wajen zaman makokin.
Cikin fad'a shugaba dumb'uru yacewa gaza d"aanme zatayi haka akan me zata bari su rasa d'aya daga cikin manuan hadiman da suke biya musu kowace irin buk'ata kuma duk tsananinsa.
Itama gaza cikin tsan tsar bacin rai tace "akan me zai saka Munira cikin doguwar suma yasan amfanin da numfashinta yake dashi kuwa a cikin tafiyar?
Taci gaba dacewa rayuwarta tamkar nasaran mune haka kuma mutuwarta kamar tona asirinmune, sanka maza atasheta daga haka ta b'ace.
Cikin tashin hankali dumb'uru yake bin inda gaza ta tsaya da kallo kamar wanda yake neman wani abu wajen gaba d'aya jikinsa babu inda baya rawa ya shiga had'a sihirin da zai tada Haj. Munira daga dogon suma amma ba cikin hayyacintaba.
Ta jima tana bacci kafin ta bud'e idanunta fes tasaukesu asaman fuskarshi wanda ya tallafe da duka hannayensa cikin sanyi ta dinga kallonsa aranta tana tunanin abinda ya hanashi awaitar da komai yadda ya kamata akanta koda take yarinya mai k'aramin shekaru amma tana da ilimin da zata gane cewa ba iya haka ake auratayyaba kuma bak'ramin haushi tajiba ganin Yusra da ciki dole tasan wani abu yafaru amma sai bata nunaba, kuma sautari idan wani abu yataso masa na shi'awa natuk'ar ad'akinta yake yasan ta yadda zaimawar kansa nutsuwa.
Hura mata iskar bakinsa yayi, tayi saurin dawowa daga duniyar tunanin da tatafi ta watsa masa dara dara idanunta, ya d'age mata gira tareda fad'in "yane?"
Turo baki tayi tareda kawar da kanta gefe batare data iya cemasa komaiba.
Muje gida muyi wanka "muci abinci sai ki samu ki d'an hutako tunda sunce ta dawo hayyacinta harma tasami bacci "
Bata sami damar duban inda take ba ta kawar da kanta gefe har ga Allah haushinsa takeji, a shirme irin nata gani take yamafi son Yusra tunda har yayi nasarar yi mata ciki amma ita baima tab'a kusantartaba bare tasa ran zai mata cikin, take taji wani irin haushi da b'acin ran abun ya kamata.
Wata irin mahaukaciyar dariya tasaki mai k'arfin gaske sannan afili tace "Abubakar kayi ganganci, kuma kayi kuskuren bada tsaronka ga iya Abdulmajid ni kuma da wannan damar zanyi amfani wajen cimma burina zan had'asu gagarumin fad'a zan saka tsanarka a zuciyar Fatima Abdulmajid akan abinda bai taka kara ya karyaba.
Abangaren Munzali kuwa da k'yar ya iya samin yara hud'u saboda yanzun idon mutane na kansu, saboda an riga an farga da yawan sace sacen da ake na mutane andawo da idanu kan yara.
Lokacin da yakaiwa gaza wannan yaran ba k'aramin farin ciki tayiba domin a lokacin tana kan wani aikine wanda ake buk'atar jini sosai, dan haka tace maganar Haj. Munira dole suna buk'atar ta araye saboda cigaban su, dan haka dole za atasheta.
A matuk'ar firgice yake kallon gaza kafin yace"kuma nayiwa danginta k'aryar cewa ta mutufa kar kuma aganta?"
Tace "kar ka damu za'a tsaface ta ta yadda babu wanda zai ganta ko yaji maganarta amma ita zataga kowa kuma zataji maganar kowa dan haka zata cigaba da numfashi na sanar da dumb'uru.
Sosai hankalin Munzali kwanta sai dai kuma yayi maganar boka Duna akan yana son ganin bayansa wata irin mummunan tsawa gaza ta daka masa tace " kul d'inka domin duna yana da mutuk'ar amfani ga kowa cikin domin yana da bud'ad'd'en ido naganin kowace irin matsala ce zata kunno mana kai"
"To maganar 'yatafa yace sai yaga bayantafa kuma son da nake mata ko d'arln dana samu ta hanyar aure banji inayi masa son da nakewa wannan yarinyar ba"
"Tace wannan kuma,tsakaninku sai kuje ku sulhunta kankau"
Sosai ran Munzali ya b'aci da wannan hukuncin na gaza sai dai babu yadda zaiyi tunda ya fahimci suna na hannun damarta ne duk abinda yace anyi angama.
Pls manage na dawo gida zaku dinga ganina akan lokaci
By maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 21
....................cikin tsan tsar bak'in ciki datakaicin abinda tayi masa ya tureta daga jikinsa ya dafe kansa, yayin da idanunsa sukayi wani irin ja saboda tsabar b'acin rai da kuma halin buk'atuwa.
Hannu yasa da zummar janyeta daga kannk'afafinsa sai lokacin ya lura da cewa ta suma da k'arfi ya hau jijjigata amma shiru a mutuk'ar firgice ya mik'e ya nufi wajen frij d'insa ya d'auko ruwa mai mugun sanyi yana zuwa bai tsaya wata wataba ya shek'a matashi a fuska.
Wata irin k'ark'afar ajiyar zuciya tasaki mai k'arfin gaske saboda sanyin ruwan kafin ta soma bud'e idonta a hankali ta saukesu saman fuskar Abdulmajid.
A tsorace ta somabin jikinsa da kallo ga mamakin ta Abdul d'intane ba wannan mummunan gwaggon birinba, cikin tashin hankali ta fashe da wani irin gigitaccen kuka ta fad'a jikinsa, yayin da shima ya k'ank'ameta zuciyarsa tana wani irin bugu saboda tsan tsar b'acin ran dayake taso masa mak'ogoronsa har wani d'aci d'aci yake masa.
Da k'yar yasamu ya rarrasheta sukaje sukayi wanka gami da d'auro alwalla, har suka fito daga toilet d'in Abdulmajid yana mamakin abinda yake son faruwa dasu,
Ya fahimci duk ranan daya buk'aci son keb'ewa da Fatima sai wani abu ya faru kamar yau, zai iya cewa wannan shine kusan karo na uku kenan da irin hakan ta faru dasu yazama dole ya nema musu mafita.
Kwana sukayi suna sallah dan saida suka gabatar da sallahr asba wanda shi ya wuce masallaci yayin da ita kuma tayi nata anan saman abin sallan bacci yai awon gabada ita.
Sanda ya shigo tana bacci dan haka ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa sosai ruwan ya rik'a ratsashi duk da kasan cewar yanayin sanyi yafara busawa amma hakan bai hanashi sakarwa kansa ruwan mai d'an karen sanyiba.
Saida yashafe kusan 15 munute ruwan yana ratsa shi kafin yayi wankan ya fito.
Cikin wani fari kar d'in lallausan yadi ya shirya ya fito cik8n sauri ya lek'a d'akin yusra itama bacci take hankali kwance a hankali yaja mata k'ofar ya fice.
Kai tsaye gidansu ya nufa direct d'akin Amma ya nufa dan yasan yadda yayi sammako to acenne zai samu iyayennasa wanda yasan duk safiyar duniya anan duka iyayennasu maza da mata suke karin kumallo.
A hankali ya tura k'ofar glass d'in wanda banda ya had'a da sallama da bazasu ji zuwan saba domin duk hankalinsu yana kan mahaifiyar tasu datake ta jero musu addu'a kafin su fara cin abincin wanda hakan zan iya cewa kusan ya zamar musu jiki.
Gaba d'aya su juyo suka zuba masa ido cikin tsantsar mamakin abinda ya kawoshi da sassafe haka wanda shi kuma idanunsa ya hau rarrabawa inda yaga suk iyayen nasu amma banda Mummynsa da Umma.
Cikin nutsuwa ya k'arasa ya durk'usa har k'asa yagaida Amma sannan ya gaida iyayen nasa cikin ladabi sannan ya mik'e ya koma cikin falon ya zauna cikin d'aya daga cikin kujerun falon.
Hannunsa ya zura cikin aljihunsa ya zaro wayarsa ya kama danne danne yayin da Daddynsa ya tsareshi da idanunsa,
Tabbas akwai abinda yake damun d'annasa saidai yasan ko sama da k'asa zasu had'u abune me mutuk'ar wahala,ya iya fad'awa iyayyen nasa damuwarsa.
Amma ce da kanta ta had'o masa abincin ta kawo har gabansa ta jera tareda fad'in "bismillah"
Ba tareda yace komai ba ya sauko k'asa yaja kofin data ciko da had'ad'd'en shayi mai uban kauri yafara kurb'a a hankali yana cigaba da daddanna wayarsa.
Amma tace "to ai sai ka aje wayar ka gama cin abincin ko?"
Kallon ta ya d'an yi sannan yaja flat d'in farfesun kayan cikin wanda Amma tasan yana mutuk'ar so, amma da k'yar ya iya cin yanka uku saboda halin k'uncin dayake ciki ya ture sauran gefe.
Yayin da amma ta tsareshi da ido, shima kallon yake binta dashi had'i da d'age mata gira alamun ya dai?
Sannan yace mata "inajin kin fifi kowa sanin bana iya yin kari da sassafe yanzunma nacine dan karkiji babu dad'i kin had'owa mai gida kari yabarki da kayanki"
Murmushi tayi batareda tace komaiba ta kwashe kayan daidai nan kuma mummynsa ta shigo falon da sallamar ta itama kallon Abdul d'in take da mamakin abinda ya kawoshi gidan da sassafe wanda tunda yai aure bai tab'a musu irin wannan sammakonba.
Shi kuwa Abdulmajid ganin har sungama,sun sallami Amma,suna shirin fita yaca "Abbi wajenka fa nazo"
D'an tsatawa Abbi yayi ya tsareshi da ido kafin yace "to muje falona ko?"
Da haka duk suka fice sauran suka tafi wajen aikinsu shi kuma sukayi fat d'in Abbi.
Kallonsa Abbi yake cikin nazartar yanayin damuwan da yake ci da dai baiso fad'a masa komai ba amma ganin halin da yake ciki naga ya matsa kusa dashi wanda ni kaina banji abinda yafad'a masaba nadai ga Abdulmajid d'in yana wani irin murmushin yak'e kafin yacewa Abbi d'in
"Yanzu Abbi kana nufin duk wannan kashe kashen da akayi tayi duk sune?
Kuma akan abinda bazamu tafi lahira dashiba dole anan zamu barshi"
Abbi yasaki wani murmushi yace "Abdul kenan banda abinka ai yanzu mutane sun fison duniya akan lahirarsu"
Yace "to kawai Abbi mu nuna musu mun ganosu dan su sani"
"Hummm Abdulmajid kenan to kai in banda abinka,ai in suka sani wata hanyar kuma,zasu sauya wacce bamu san da itaba kawai mubisu a hakan da sannu dubunsu zata ciki, kuma shirun zaifi dan ta hakane zamu gano sauran masu basu temako, dan wannan aikin banasu bane sukad'ai"
Ba shi ya koma gidanba sai wajen k'arfe goma da rabi, alokacin suna saman dirning zasuyi karin safe k'arasawa yayi yasa kujeransa a tsakiyarsu, abincin da Fatima take ta juyawa ta kasa kai koda loma d'a bakinta yaja ya ciko hannunsa da soyayyen dankalin batayi auneba kawai taji ya danna mata shi abaki.
Da shigowar sa da zamansa har zuwa janye flat d'in ganta duk batajiba saida ya duma mata abincin sannan tayi wani firgigit tamkar dai wanda ya tashi daga bacci.
Wata dariya ce ta k'wacewa Yusra ganin yadda Fatima tasaki baki da dankali fal baki wanda da gani yayine da tsokana dan yafi k'arfin bakinnata, garin dariyan kuma ta k'ware ta hau tari.
Abdul yazuba mata ruwa yakai bakinta sannan yasa hannu yana d'an bubbuga bayanta yace "kin ganiko garin dariyar k'eta zakije ki jawa kanki wahala.
Yayin da ita kuma Fatima ta turo baki tana hararansu dukan sannan kuma ta fashe da,kuka,ta tashi da sauri ta bar musu wajen.
Ya dubi Yusra yace "kin gani ko kinsata kuka"
Tace "a'a babu ruwana dan tun d'azu take ta faman kukanta babu irin lallashin da banyiba tak'iyin shiru shinema dalilin dayasa kaga bamu ci abinci akan lokaciba"
Duban ta yayi cikin rashin jin dad'i yace "bari inje inji abinda yake damunta ko bata da lafiyane"
Kai kawai ta girgiza masa alamun to dan ta rigada ta ciki bakinta da bread d'in da ta gutsura.
Plssssssssssss manage
Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 19
...................Yana tafe yana zancen zuci aduniya da yarasa 'yarsa mafi soyuwa agaresa akanta zai iya d'aukan ko wane irin mummunan mataki akan duk shegen da ya isa ya rabani da gudan jinina ba.
Haka yatafi yana zancen zuci kamar wani tab'ab'b'e.
Sai da Yusra ta shafe kwanaki bakwai kafin ta dawo hayyacinta zuwa lokacin kuma Fatima tayi wani irin sauyawa sam Abdulmajid baya gane kanta duk abinda zai mata baiyi dai daiba, ganin suna asbiti yasa bai kulataba amma yasha alwashin ana sallamarsu zai binciketa.
Ab'angaren Anty Rukayya kuwa wani irin mummun tsorone ya kamata gamida mamakin abinda sakamakon bincikenta yabata tsabar gigita da mamakin abin saida takai k'asa lokacin data gano wanda yakewa zagon k'asa sosai abin ya d'aga hankalinta, saidai gano cewa akwai mutane dayawa kuma sanannu atafiyar yasa tabarwa ranta har zuwa sanda zata gano sauran abokan tafiyar.
Daddy ne zaune a office d'insa duk abin duniya ya damesa shi kansa ya wani fige ya rame saboda tsabar damuwan daya masa yawa.
Yana nan zaune saiga Abbi ya shigo hankali tashe ya zube gaban Daddyn bak'aramin fad'uwa gaban Daddy yayiba ganin zak'ak'urin d'an uwannasa afirgice.
Cikin tsan tsar damuwa Daddy yace "Abubakar tunda farko saida nace maka wannan abin mubarshi anemi wasu malaman kak'i kayi hak'uri d'an uwana kabar wannan aikin musami wasu suci gaba"
Wani irin murmushi Abbi yayi mai ciwo yana kallon d'an uwan nasa yace "lalle yaya wato kana tsoron kar wani abu yasameni ko?
Cigaba yayi da cewa kar ka manta suma wanda zakasa d'in iyayen