Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
yanzunma abincin yake dad'a narkewa, sai ya maida hankalinsa ga mutumin yana neman k'arin bayani da ido.
"Guba ce"yafad' yana kuma bashi hannu su gaisa, wannan karon baikiba shima ya bashi sukayi musabaha yayin da mutumin yaci gaba da cewa
"Yau anshirya kashe wannan ne yafad'a yana nuna Fatima da har lokacin take kwance saman cinyarsa tana baccin bashin dataci watavirin mummunar fad'uwar gabane ta ruftowa Abdulmajid aransa yake nanata kisa Fatimar tasa za akashe masa? lallai kuwa da anyi d'an k'aramin yak'i agidan Tanimu ya aiyana hakan aransa yayin da wancen gabada cewa "dan a tsari yau aka shiyar kasheta yayin da kai kuma za a gusar maka da tunanin ka amaida ka gida da gawar ta kamar dai yadda aka b'atar da hankalin abokiyar tafiyar ku ta manta duk abinda tagani ta kuma fad'i abinda ya d'orata akai
Ina baran addu arku masoyana kan wani buk'ata mai girma da ya sakoni gaba na gode taku
Maman islam
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 46
.......sosai yake kallon mutumin sannan wani irin tsoron kaidin kawu Tanimu yana shigarsa koda yake mutumin da ya kashe iyayensa meye ma bazai aikata ba, ai ya tabba imani yajima da yin k'aura wa zuciyar kawuvTanimu tunda har ya mai da shan jinin mutane ba abakin komai ba yamai da kisan kai tamkar yankan dabbobi.
Shi kuwa mutumin cigaba yayi da fad'in "kwanannan za ai bikin bawa Gaza jinin al'umma wanda in irin hakan ya tashi mafi k'aran ta a yanka mata kusan mutum d'ari yara da manya da kuma tsofi da saffa saffa, to a irin hakane ake kan mai uwa da wabi duk wanda ajalinsa yayi sai kaga an had'a dashi domin biyan bak'ar buk'tar su, ina mai tabbatar maka matuk'ar akayi bikin kuna nan to jinin wannan matar taka ya hallata su bawa Gaza dan haka abinda nakeso dakai ga wannan" yaja ledar take away wanda harda naman kaza acik ya tura musu yace "kuci ku k'oshi sannan nayi alk'awatin muddin ni aka turo zan fita na siyo muku abinci koda wasa kar ku sake kuci duk wani abu dazasu kawo muki domin tunda ya fara da haka zai ida nufi"
Sosai jikin Abdulmajid yayi sanyi yazama dolevya k'ara kan addu ar da yakeyi dan ya fahimci kawun nasa ba k'aramin majununi bane ahi kuwa mutumin d'auar kedar ya jawo ya tura gabansa sannan yace
"Ga wannan ma dan Allah kayi hak'uri nasan matsayin ka ya wuce nan sai dai bani da zabin da yafi wannan, garin kwakine da shuga da gyad'a duk ranan da bani aka aiko kawo muku abinci ba to wannan shine abinda nake so kuci dan gudub afkuwar wani abu a gareku idan oga yaga baku cin abincin hakan zai fusata shi ya fito daku yace zai d'auki matakin gamawa da ita dan yanzu duk wani fata da buri nasa yana akanta ne, to ni kuma duk ranan da ya fita daku to a wannan ranan zan temaka muku ku gudu,dan haka ku kasance cikin shiri kuma ku riga ci kuna koshi don musamu damar ai watar da shirinmu cikin kuzari wannan ruwan saboda ibadunku na kawo muku
Sosai Abdulmajid ya gode masa domin ba k'aramin dad'in temakon da yace zai masa yajiba
Yayin da badamasi kamar yadda yace sunansa yacigaba da cewa yana tura musu d'aya kedar mai take away.
"Ga wannan kuci yanzun"abinci ne mai rai da lafiya sannan ya kuma jan d'aya ledar yace
"Wannan kuma duk lokacin da bani na kawo muku abinci ba kar kuci dan Allah ku daure kuci wannan na sani kunfi k'arfin wannan amma cin wani abu daga hannun oga kai tsaye akwai gagarumin matsala.
"Haba abokina kada ka damu, cewar Abdulmajid sannan yaci gabada cewa ai dama bawa babu inda baya samun kansa kawai dai mu kasance masu godiya ga Allah a duk halin da muka samu kanmu sai ubangiji ya ni imtamu da abinda bamuyi zato ba dan haka kar ka damu kuma mungode sosa.
Dariyansu kawai kakeji a d'akin da sukan keb'e da karuwansu idan sunso hutu yau sab'anin hakane domin k'walewar su suke sosai sukayi mankas ba kowa bane face su alhaji badamasi, yayinda kawu Tanimu yake tsara abinda zaiyi da su Fatima wanda Gaza tace masa kar yasake ya bar Abdulmajid d'inma domin shi har yafi Fatima had'ari atareda su.
Tagefe guda kuma ga yadda ahegun yaran suke son tsayar masa da aiki domin yau kwanaki uku kenan yadda ake kai musu abincin haka ake komawa akwaso basa tab'awa abinda yafi komai dugunzuma zuciyarsa kenan domin ya fahimci so suke su b'ata masa shiri.
Suna tsaka da holewar su muryanta ya ratso cikin d'akin cikin wani irin mummu nan tsawa tace "ku wane irin shasha shune kuna nan kuna watsewar ku asirinmu yana shirin tonuwa"
Tsi sukayi cikin wani irin fargaba wanda kusan tunda salon abin ya sauya GAZA takeson mamaye komai ya kasan ta kusan zame musu tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairiba, shiru suna sauraron yau kuma da ne tazo yayin da jikin kowa yake d'an rawa rawa.
"Kuna nan kuna lalacewa wancen banzan ya d'auko hanyar lalata komai Tanimu zan kashe shifa wallahi zan gamada rayuwar sa, dan bazai yiyu inaji ina gani wani banza ya rusamin shirin da nashafe shekaru sama da talatin ina shirya shiba dan haka zan gama dashi kuma,ina so yau d'innan ka kawomin tsinannun yaran nan da ransu zan zuk'e jinsu, sannan kai Garzali a fitomin da Munira itama duk taurin kanta yau zan tsotse jininta itama badai tak'amarta tace ban isaba kuma bazan iya da itaba to yau zanga k'arshenta"ta k'arasa tana huci yayin da sauran duk suka fice sukabar su suna cigaba da tattauna yadda taron shan jinin su Fatiman zai kasance.
Can b'angaren su kuwa tun ranan da Badamasi yace kar su k'ara cin duk abinda za'a kawo musu matuk'ar ba shine ya kawo musu ba, basu k'ara sanyashi a idanunsu ba sai yau kimanin kwanaki shida kenan.
Lokacin daya ahigo talatainin darene wanda da ayaune zasu shanye jininsu sai kuma,suka sauya wata shawarar acewar Gaza akwai munafiki a cikin yaran,Tanimu kuma,tanasi tasan ko waye dan dama mutum goma take so masu shegen taurin kai wanda suke nuna,sunfi k'arfin tsafinta dasune zata zama gagarumar da babu kamar ta a duniya dan haka yanzu tasamu mutum uku Abdulmajid Fatima haj.Munira, sai kuma wannan b'oyayyen daya bayyana.
Sai dai kuma duk yadda sukaso ganin wanda yake shirin fidda su Fatiman hakan,bai faruba domin yariga da yagano shirin su ta hanyar shima,nasa shirin dayake dan haka ya had'a musu gadar zare ta hanyar lalata duk wasu abubuwa da Gaza ta tanada domin ranar yaud'in dan haka agigice suka rankanya can fadarta inda take gudanar da duk wasu hark'llolinta abinda ya d'agawa Gaza hankali shine babu Munira babu dalilinta a wajen an fidda ta take ta shige d'akin data ke shirya duk wani shiri nata cikin tsantsar tashin hankali ta manta da batun su Fatima.
Muje zuwa
Ku kara hakuri dai ankusa cimma matsaya
Maman islam
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
By
MAMAN ISLAM
Page 48
..................ko takan Badamasi bai bi ba ya tsallake shi ya wuce cikin tsantsar tashin hankali yayin da mutanen da suka kewaye Badamasi suka d'agashi suka gyara shi.
Shi kuwa Tanimu fada ya nufa cikin fitar hayyaci yana zuwa ya tadda gaza cikin tashin hankalin, da ya ninninka nashi wanda yake ciki take ya k'ame awajen lokacin da take tunkaro shi cikin wani irin mugun yanayi mai ban tsoro, sannan tayi magana cikin watabirin murya mai masifaffen amo
"A kashe su duka bana so sukai zuwa azahar suna numfashi" zubewa tanimu yayi a wajen tareda fashewa da wani shegen kuka wanda ya kuma d'aga hankalin gaza tace
"Lafiya?"
Yace "yaran sun caccakawa Badamasi amintaccen bawana kwalba sun gudu"
Kalalo jajayen idanun ta Gaza tayi cikin wata irin masifaffen fad'uwar gaba tace "ban gane yarenka ba, ban fahimci mekake nufiba sun gudu fa kace, ina sam da sake wallahi bazai sab'uba maza abazama a nemosu tun kafin su fice a garinnan dan nasan duk inda suke basuyi nisaba maza kafin kaima,na dawo kanka jakin banza ka saki baki kana baccin asara har yara k'anana su naka wayo wallahi kayi asara k'aton banza kawai fita kabanivwaje kuma karka dawo min nan sai ka kawo minsu inba haka ba zan musanya dakai da kuma,iyalanka ne"
Cikin asalin damuwa da tashin hankali Tanimu ya fice yana kuka shab'e shab'e da hawayen sa yana ta maimaita ya shiga uku har yaje gidansa sai dai kuma tashin hankalin sa ya nunkune sakamakon labarin daya samu cewa Badamasi ya gudu.
Washe gari da safe Fatima dakanta ta shiga kicin tayi musu girki mai rai da lafiya sukaci suka k'oshi, bayan sunyi wanka babu dad'ewa Badamasi ya shigo gidan kamar an wulloshi babu wata wata yace su taho babu musu kuwa Abdulmajid ya figi hannun Fatima suka nufi tasha cikin matuk'ar sauri shatar mota ya d'auka musu iya su biyu kawai ya biya yace akaisu har gida.
Kai tsaye gida ya dawo bayan ya tabbatar da cewa motarsu ta d'aga tayi nisa draiban kuwa gashi da mugun gudu
Shigarsa gida babu dad'ewa saiga kawu Tanimu da tawagarsa lokacin Badamasi yana dressing ciwon dayaji wa kansa wanda yake masa azabar rad'ad'i.
Akansa kawu Tanimu ya tsaya yana huci yace "kai Badamasi dan ubanka ina ka shiga lokacin da yarannan suka fice suka gudu"
Sosai gaban Badamasi ya fad'i, sam baiji zuwansu ba dan da gaske ciwon yake masa zafi sosai cikin sanyi da tsoron kar Tanimu ya gano shirin dayake yace.
"Mai gida shammatana sukayi bansan yadda akayi har suka bud'e k'ofar ba sai saukar makami naji wanda ban tashi sanin inda kaine yakeba sa hayaniyar mutane ne yatasheni yafad'a" tareda faahewa da kuka dan ogan nasu ya gasgata shi
"Ba kuka zakayi ba Badamasi tashi kawai zakayi mu bazama tasha tasha munemo su danna san yanzu daga nan tasha zasu nufa gaza tace indai bamu nemosuba mune masadinsu"
Kai dai kaine madadinsu ni na gama duk wani shirina na ganin na tarwatsa ju daga kai har azzaluman da kuke wa aikin Badamasi ya fad'a aransa.
Tare suka fita nemansu da tawagar su, saida ya kaisu duk tashoshin dayasan sunfi nisa domin acewarsa idan suka tashi baza su tsaya akusa ba sun san za a nemesu.
Saida suka gama bulayinsu sannan sikaje asalin tashar da su Fatima suka hau mota inda aka tabbatar musu da cewa zuwa lokacin sunjima da tashi ai kuwa Badamasi yasha ruwan zagi da rashin mutunci dan acewar sa duk shine yaja musu badan haka ba da tuni su Abdulmajid sun dawo hannunsu.
Sosai driver ya dinga sharara gudu na fitar hayyaci domin ganin sun isa da wuri yayin da tsakanin Fatima da Abdulmajid akarasa wanda zai masa magana akan ya rage gudu domin dukan su babu mai iya magana banda matsanancin gudu babu abinda zuciyarsu yake yayin da kowannen su yake addu a da fatan kub'uta acikin zuciyarsa.
Sai daya gama k'arewa Badamasi zagi da cin mutunci sannan yace su koma ya bincika yaga inda suke ya datse hanyar, wani ikon Allah duk k'warewa da iya aikinsa ranar kasa gane komai yayi wanda kansa yagama d'aukar zafi dan haka ya tarwatsa kayan aikin yayin dayake kuku wurjan jan.
Wata irin ajiyar zuciya suka sauke lokacin da mai motar yake danna hon a k'ofar gidan suka rungume juna,cikin tsantsar farin cikin tsallake rijiya da bayan da sukayi.
Sai da mai gadin ya lak'a gidan yaga wad'anda suke ciki yasaki wani irin ihun murna yasaki wanda sai dayai sanadin fitowar duka mutanen gidan.
Ummi jiki yana rawa ta k'araso da gudu ta rungume Fatima tareda da fashewa da wani irin kuka yayin da Fatima ta yanke jiki ta fad'i a wajen, duk sukayi kanta a gigice.
Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 49
.............gaba d'aya hankulansu tashi yayi matan saka fashe da kuka suna jijjigata Ummi kuwa surutan bata masan abinda take fad'a ba kawai take Abbi ne yayi k'arfin halin bud'e motarsa ya d'auko roban ruwa ya shafa mata a hankali amma ko gezai dole sai asbiti suka nufa da ita shi kanshi Abdulmajid yana buk'atar ganin likita saboda d'an karen yunwar da ya kwasa.
Har sun juya zasu bar tashan wani ya kira kawu Tanimu gefe yace "ranka ya dad'e ai wancan da kuke taren dashi shine ya d'auma wanda kuke neman shatar mota zuwa cikin gombe" mutumin yafad'a yana nuna Badamasi jin abinda wannan tsinannen bawan yace yasa Badamasi bai tsaya wani jikinri ba take da mugun gudu yayin da kawu Tanimu yaba sauran yaran umarnin su kama masa shi, sai dai kafin kace me tuni sun neme shi sun rasa kamar walk'iya haka ya b'ace musu, 5ashin hankali iya tashin hankali babu irin wanda Tanimu bai shigaba ya dinga kuka wurjanjan da hawayensa tun sha biyun rana suke bulayin neman Badamasi har k'arfe biyar d'in yamma basuga ko mai kama dashi basu ganiba dan dole suka koma gidan Gaza cikin tsantsar tashin hankali da damuwa.
Sai dai wanda suka tadda Gaza aciki yaci uwar nasu ya shanye domin ta koma kamar wata horuwa tayi wani kaca kaca da ita idanun nan sun dad'a komawa fici ficin gaske ga wani uban ja da sukayi kamar an barbad'a musu barkono jikinta kuwa yayi wani irin busu busu kamar wacce ta shiga fulawa cikin wata irin murya da basu tab'a saninta dashi ba tace.
"Kan boka Duna nake so maza akawomin shi da gaggawa, saboda sanin cewa yafika hatsa bibanci na baka daga nan zuwa sati d'aya kuma kada kabari ya sake ya shiga cikin gombe dan in ya shiga komai namu ya lalace.
Acan asbiti kuwa bak'amin wuya Fatima tasha ba kafin ta dawo hayyacinta kuma dad'in da d'awama tana d'auke da cikin watanni uku da 'yan kwanaki wanda su da kansu ma basu san dashiba hakan ya kuma cilla zuk'atan su cikin farin ciki da kuma fargaba domin basu san abinda zai iya faruwa da Fatiman ba kar azo ana irin na Yusra.
Sai da sukayi sati guda sannan aka sallame su Daddy yace sam bai amince Abdulmajid ya koma can gidansu ba duk da cewa basu san ainihin abinda ya faru dukaba amma yasan cewa akwai babban matsala akad'ai cewansu, to suma basu wani jaba dan sungaji da wannan tashin hankalin aka gyara musu can fat d'in Abdulmajid na da suka koma,ciki, sosai hankal8n Ummi ya kwanta da hakan duk da kasancewar sai tayi kwabaki ma bata sanya Fatima a idanunta ba amma ak'alla suna cikin inuwa gudane.
Wannan k'alla gaggen d'aki duk sanda ya shigeshi bata gane kansa dan a burkice yake fito masa ta rasa uwar menene a acikin d'akin dayasa har ita datake sirrinsa yake sirrinta bayason,ko hanyar d'akin ta kalla,
Tana zaune ta zuba tagumi idanun ta akan k'ofar yau kam tasha alwashin ko menene a wannan d'akin saita ganshi koda kuwa zata b'lle k'ofar ne dan tana da tabbacin bazai bar makullan ba.
Tana nan zaune taga fitowar shi a wani firgice yana sallallami. Agigice ya kama hannunta hijabi kad'ai yasaka mata yajata sukayi waje, tasha yakaita ya saka ta amotar gobe ya biya kud'in sannan yace da kyar cikin muryansa kamar wanda aka shak'e
"Kije gidan yaya Yusif nima ina nan zuwa" kallon mamaki da tuhuma take masa yagani sarai amma sai ya kauda kansa cikin wani irin yanayi, sai kuma yace "Hafsat kisakani acikin addu ar ki nasan nacutar dake da zuriyarku amma hakan ya farune sanadin d'an uwanki idan Allah yasa sun barni da raina zan sanar daku komai da kuma mai had'a muku tuggun wanda yamai da mu karnukan farautar sa muke masa koma yana daga zaune sanye da rigar mutunci yayin da mu muke a cikin gari na mutane kuma kamilallun malamai amma a dokar daji k'ungurmayin bokaye kuma k'asaitattun azzalumai wanda bamusan komaiba sai kashe rayuka da amfani dajinin su ta hanyar neman duniya"
Kafeshi tai da ido lokacin dayake mata wannan bayanin bata ko k'ibtawa cikin tsantsar tashin hankali da damuwar son sanin dalilin da yaja duk wannan abubuwan suke faruwa duk da cewa yabata amsar adunk'ule na cewa NEMAN DUNIYA amma hakan bai gamsar da itaba tana son sanin shin dama duk abinda yake faruwa da d'an d'an uwanta da sanya hannunsu dama su suke haifar da komai ko kuwa suna da wani wanda yake basu umarni daga sama, gabanta ne yayi mummunan fad'uwa lokacin data tuna yace mata duk suna aikine da umarnin 'dan uwanta kenan hasasheb mutane akan yaya Yusif gaskiya ne BA ZATO BANE KAMAR YADDA ITA TA ZATA, kafin sukai gombe tayi wani irin wujiga wujiga da ita saboda tsabar zafin da kanta ya d'auka na son dole wai sai ta gano wanne ne daga cikin yayunta da yake hana rayuwarsu sakat da wannan mummunan aikin, azuwannata ne kuma ta tarar da dawowar su Abdulmajid, abin kuwa yayi mata dad'i har ta d'an saki ranta dake malam kamar yadda take kiran mijin nata yace mata shine ya kama su Abdulmaji yana son kashe su kenan zata iya samun k'arin haske ta wajensu kenan.
"Baby yaufa bani ce da girki ba kuma yunwa nakeji naga kayi zamanka gashi nafara jin yunwa" murmushi yayi yace "to ai baby laifinki ne kefa kikace yau so kike ki wuni saman cinyana haka kikaji kina buk'ta, kuma kinsan buk'atarki biyanshi yafi min komai dan haka yanzun inkince na tashi na shiga