Chapter 5 Reading ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM HN Novels

ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM

Author :  MAMAN ISLAM Category :  KDP NOVELS

Chapter   5 / 20

12K to 15K   out of 58.1K words

a idaninta tayi naga ta kalli mutumin wanda duk ranar datayi hakan mutum ya b'ata mata rai kuma wannan kallon shima azaba ne dan mutum zaiji ajikinsa.



Jinai tana magana yau kuma da muryan jarirai tace "wayace kabita kanason lalatama aiki bakasan cewa idan ubanta yasan kana bin ta sai ya kawo k'arshenkaba? dan mudai munriga da munfi k'arfin duk wani mai shiri akanmu"


"Kar ka sake binta lokacin baiyiba idan lokacin yayi dakaina zan d'auko ta domin muna buk'atarta dan gudanar da wani gagarun shiri amma,ba yanzuba da sauran lokaci



Daga haka ta rufe idanun tana hawayen jini,alamun tagama,bayaninta.





Gani nayi wata irin iska tayi watsi dashi bai fad'i a ko inaba sai bakin falon gidansa, wannan shine hukuncin duk wanda ya sab'a umarninta


A sume yake tun bayan sa adda wannan aba ta watso shi bashi ya farkoba sai bayan da iskar asbah ya hurashi.




Da sauri ya tashi yashige d'akinsa duk jikinsa babu inda baya masa ciwo bin matarsa yai da kallo wadda bata san mai yake faruwa toilet ya shige yayi wanka da ruwa mai mugun zafi wai ko zaiji dad'in jikin sannan ya d'auro alwala yazo yatashi matarsa sannan shi kuma ya wuce masallaci.



Abinda zai baka mamaki shi wannan mutumin mutumne mai mutuk'ar sadaka da kyauta sannan ga taimako gashi babu wani lokacin salla dayake wuceshi




Tun ranar da Fatima tabawa umminta labarin halin data tsinci kanta aciki ta gargad'eta kan cewa ta fita a hanyar Abdul majid babu ita babu shi idan ba haka ba itama zatabi sahun matattun 'yan matansa.


Ita Fatima sam ta manta da wannan abin saida ummin ta fad'a sannan ta tuna da yake babu abinda Abdul majid ya b'oye mata na abinda yake faruwa .


Duk da cewa taji tsoro sosai amma ranta bataji kamar cewa zata iya rabuwa dashiba domin shid'in d'an uwanta ne kuma jininta



Dan haka rabata dashi cikin sauk'i ba abune mai yiyuwaba, abinda ta nunawa umminnata kenan kuma hakan baima ummin dad'iba saidai bata k'ara ce mata komaiba gudun kar Fatima tayi tunanin ko batason alak'arta da d'an uwantane kamar yadda Fatiman tayimata ba haguwar fahimta.





Wata ranar juma'a Fatima da meema suka shirya zasuje kasuwa siyayyan kayan kwalliya da wata babbar super market da akeji da ita a fad'in gombe da kewayenta.


Har sun fito saiga Abdul wanda shi tun bayanda ya dawo daga masallaci bai shigo gidanba yana tareda abokinsa Yasin kallo yabisu dashi kafin yace "ina zakuje haka?"


Fatima tace "kayan kwalliyarmu sun k'are kasan next week zamu fara zamu fara zuwa school"


D'an had'e rai yayi yace "kwalliya zakuje kenan ba karatuba harda wani cewa kayan kwalliyarku ne ya k'are"


Ya kwaikwayi yadda Fatima tayi magana "to ku koma babu inda zakuje" yafad'a cikin rashin son wasa fuskarnan a had'e babu shiri suka juya ganin yadda ya had'e gira Fatima harda kwallan takaici dan tun bayan zuwnsu yaune zatayi fita na biyu dayake gidanma ba wani yawan fita suke ba inba da kwakwaran daliliba.


Da dare suna falon Amma duka yaran gidan gaba d'aya hayaniyarsu ya hana Amma sakat maganar duniya idan tayi idan sukayi kamar sunyi shiru sai su kuma kaurewa dan dole tasa musu ido tana kallonsu wani abin idan sunyi su bata dariya wani kuma tayi tsaki.




Ammar ne k'aninta ya shigo da d'an gudunsa yace anty Fatima yaya Abdul yana kiranki yana b'angarensa.



Yana gama fad'a mata ya juya da gudu ya fita, itako Fatima cigaba tayi da uzurinta domin har lokacin takaicin hanasu fitan dayayi bai k'yaletaba.


Sai da Amma ta kuamayi mata magana sannan ta mik'e tana zumb'urar baki, yayinda su meema suka kwashe da dariya gamida tafawa.


Irindai shak'iyancin nan na 'yan mata, falonsa ta sameshi dagashi sai 'yar farar singlet da tree queter da robar ruwa hannunshi yanasha.


Tana shiga ya mik'o mata ruwan hannunshi ta karb'a ta nufi frij zata ajiye, a hankali tajiyo muryarshi tana kallonshi da mamaki, a ranta tace ji mutum saikace nace masa ina jink'ishi da zai wani bani ruwa.



Kamar yasan abinda yake ranta yace "inbazki shaba bani abina"


Ta kuwa mik'a masa, ganin haka ya had'e rai yace "sha kona b'ata miki rai" kallonsa take da tsabar mamaki, amma ganin babu alamun wasa atareda shi yasa ta sha ruwan.


Sannan yace tashiga d'akinsa akwai ledoji ta d'ebomasa tashiga, ledodin wajen da sukayi niyar zuwane ya hanasu manya har guda uku,


Ta kawo gabansa ta ajiye yaja yafara bud'awa sannan ya d'aga kai ya subeta tana tsaye akansa kamar wata 'yar sanda "zaune mana karki fad'omin aka"





Zama tayi tana wani ciccin magani shi wallahi ma dariya tabashi yadda take wani muzurai kamar zata saka masa duka.


Kallonta yayi yace "matso kiga kayan da nasiyo ko sunyi muku"



Cikin d'auke kai tace "nifa dama nafasa siyayyar nan kawai kaba meema ko ita tana buk'ata"


Kallonta yayi cikin had'e rai yace "wato kema zaki koyi raini ko ta d'auka i dan kin fita sai ki zubar.




Nifa nac..........wata tsawa ya buga mata wacce take jikinta yafara rawa da gudu ta d'auki kayan zata fita batareda ya nuna mata kayan yadda sukeba.



Cikin daka tsawar yace "na fitar miki dana kowane 'yar rainin hankali da gudu ta dawo kawai tayi tuntub'e da roban ruwan data ajiya saigata ta fad'a masa duk ya rikitata da madifarsa kawai sai tafashe da kuka




Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________






💦💧ZATO NE💧💦
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM

Masoyana masoya labarin ZATO NE inajin dadin comment dinku ina alfahari daku love u All love u much




Page 8

......................Zuba mata ido kawai yayi yana kallonta yadda take zubda hawaye babu k'akkautawa.


Yace "sai ki d'agani karki ballani ko?" da sauri tacsauka ajikinsa tana tura baki


Kansa ya d'an shafo ya zuba mata ido yana sakin wani kyakyawan murmushi, duk wannan zumbure zumburen baki saiyaga tak'ara masa wani sihirtaccen kyau.



Kayan ya jawo batare da ya kuma bi takantaba, yayin da ita kuma take ta hararansa ta gefen ido, sarai yaganta sai dai ba bata damar ganewaba yaci gaba da rabaya kayan yabata na kowa amma nata yafi yawa.



Ta kwashe kayan tayi hanyar waje har takai bakin kofa yace "hi!!

Cak tatsaya batareda ta juyoba yace"daman agarinku haka akeyi idan anbawa mutum abu babu godiya?"


Kallonsa tayi ta bud'e kofar ta kalli hanya sannan tace "ai ba rok'onka nayiba ga kayanka nan"



Ta ajiye masa ta falla da gudu, ganin yadda tazage iya k'arfinta tana falla gudu abin saida ya bashi dariya, aransa yace yarinyar nan tafara koyan rashin kunya wajen su Hauwa'u zanyi maganinkine, kayan ya kwashe ya mayar bedroom d'inshi kafin ya shige bath room.




Da yamma suka shirya Amma ta aike su gidan wata aminiyar ta inna shatu, Fatima tace "Amma kibamu aron mukullin motarki muje da kanmu dan Allah"


Amma tace "jimin 'ya da k'arfin Hali ke da kike bak'uwa agarin kuma ki tambaya kiji ko Meema da tasan gari bana bari tafita ita kad'ai"




Nacin da takafane yasa Amma ta bata mukullin tareda gargad'arta akan ta kula tayi tuk'i cikin nutsuwa.





Ai da gudu Fatima,tayi bangaren Mammy tana kwala kiran meema meema wace ta gama shirinta itama tafito tana taku d'ai d'ai dakagansu kaga 'yan mata masu aji gaji da gayu sannan sam kud'in iyayensu baisaka su girman kai ba.




Abakin falon suka gabza karo dukansu saida suka kai k'asa meema ta dallamata harara tace "ji dalla zata fasamin kai ke komai bazakiyishi da nutsuwa" ta fad'a tana shafa inda sukayi gwaran.



Itama hararanta tayi tace "ai garin murnan infad'a miki Amma tabada mukullinne mukayi gwaren"





Meema zaro ido tace "haba da gaske?"



D'ago mata mukullan tayi batareda tace mata komiba, wani tsalle meema tayi ta dira gaban Fatima suka tafa, suna murnan samun damar fita sukad'ai batare da driver ko wani daga cikin yayyennasuba.


Da sauri meena taja hannun Fatima,tace "kinga zo mutafi kafin mammy taganmu tunda dama Amma ta fad'a mata zata aikemu, dan muddun taga key d'innan wallahi k'wacewa zatayi tasa driver ya kaimu.



Ai da gudu suka fita suka shige rantsatsiyar motar Amma ta miliyoyin kud'ad'e Fatima ta figa da gudu, dan da meema tave tabata tuk'in cewa tayi tabari adawowa sai ta kawosu gidan.




Sanda mai gadi ya bud'e musu get suka fita suna shan kwana motar Abdul majid yana danno tasa hancin motar dake glass d'in mai duhune babu damar ganin na ciki saida naciki yaga nawaje.


Shima baisan su waye acikiba a tunaninsa Amma ce zataje unguwa shiyasa ya wuce ciki abinsa.




Yayin da meema da Fatima suka kalli juna suka tafa suka kwashe da dariya Fatima tace " hummmm yaya kenan ai inkasan wata baka san wataba.




Hankali kwance sukaje gidan inna shatu bayan sun gaisa suka fad'a mata sak'on Amma tasa mai aikinta takawo musu ruwa da lemo suka d'an tab'a hira.




Sannan sukayi mata sallama, tace "kubari driver ya maidaku sukace ai da akwai mota a hannunsu nan ta basu turare da hijabai irin na saudiyyannan.



Bayan sun bar gidan inna Shatu kai tsaye gidan watak'awar meema sukaje Maryam Aminu.


Sanda suka shiga maman Maryam,suka,samu afalon ita da yayan Maryam d'in mai suna,Muktar.


Maman ce ta amsa sallamar da sukayi suka sami waje suka zaune mama tanayiwa Meema tsiyar wai batason zumunci.


Meema tace "wallahi ba haka bane mama tunda yaya Abdul ya dawo kowa yashiga taitayinsa agidan ya kasa ya tsare ya hana kowa sakat"




Yaya muktar yayan Maryam wanda sai yanzu yayi magana tun zuwansu yace "ai gwara haka kawai asaki yara sakaka babu kwab'a babu harara ni ya burgeni wallahi"





Yak'are maganarsa idanunsa na kan Fatima wace tun shihowarsu yakafeta da idanu kamar wani maye suk inda ta juya saitaji idanunsa na yawo ajikinta shiyasa taji duk zaman ya gundireta.




Meema tace "wai' ina mutuniyarne mama banji duriyaryaba?"



Mama tace "nan mak'otanmufa na turata takaima mara lafiya abinci kinga taje tayi zamanta"



Mama tana rufe baki Maryam ta shigo falon da sallamarta, gaba d'aya suka amsa, tabisu da kallo dukansu idanunta yafara sauka kan meema ta daka wani uban,tsalle cikin ihun murna ta ruk'unk'umeta tana fad'in



"K'awata dama kina,suniyar gaba d'aya kin b'uya abinki dama gashi ba wani damunki zumunci yayiba mune,sarkin naci muka gaji muka daina"




Murmushi meema tayi tace "ai kema kin sani basai namiki k'arin bayaniba"



Maryam tace "wai kina nufin yaya Abdul majid bai fara aiki da gemanyn ba?"




Tace "Daddy ne ya hanashi wai bai yarda yayi nisa dashiba, aikinma dan ya nuna yanasone Amma daddy yafison ya zauna tareda shi a companynsa"



Maryam tace" Allah ya taimaka tashi muje d'akina in nuna miki wani abu, da sauri Fayima ta rigasu mik'ewa dan dama gaba d'aya atakure take saboda mayataccen kallon da Muktar yake binta daahi.




Abdul majid kuwa yana shiga gidan da motarsa ya hango sa'idu drivern Amma aransa yace yau kenan Amma an tuna baya da kanta taja,motar kenan.


Direct b'angaren Amma ya nufa dan yasan bazai rasa wani d'an abin tab'awa ba tunda bata rabo da kayan motsa baki.


Ga mamakin sa Amma na zaune saman doguwar kujera da kwqnon shan fura tana shan kayanta, da baki asake ya k'arasa shiga cikin falon ywna kwllon Amma yace.



"Amma waye naga yafita a motarki yanzu shigowana Amma ta d'an dubeshi tace tace "ban saniba uba na ka wani shigomin babu sallama zakayi min tambayar rainin hankali"




"Yi hak'uri Amma nayi tunanin nayine, ya fad'a tareda komawa yayi sallamar ya shigo Amma ta amsa tareda mik'a masa kwanon furar datake sha, ya amsa yana kallonta, tunma kafin yakuma yi mata wata tambayar tace "Fatima ne da meema na aikesu gidan Shatu"




Wani irin kallo Abdul maji ya dingabin Amma dashi wacce tunda tayi masa bayanin ta d'auke kansa daga gareshi, yace "yanzu Amma fisabilillahi wannan mahaukatan yaran kikabawa mota suka fita dashi?"






Wani banzan kallo Amma ta watsa masa kafin tace "ina katin shaidar da ka amso musu ?"



Ta fad'a tana mik'a masa hannu alamun yabata, ransa ne yab'a ya mik'e yana fad'in "gaskiya ni ba a kyautamin ba da za aba yara tuk'i yqran da kansu yake rawa suje suja mana wata fitinar"



Amma tace "aniyarka ta bika mai bak'in baki babu abinda zai faru sai alkhairi kuma babu abinda zai samu jikokina kuma babu ruwanka da harkansu ehe"




Shidai kam a zuciye ya juya ya fita falon Amma tayi tsaki tace "aikin banza mutum ka d'auki zafin rai da rana tsaka ya d'orawa kansa" ta maida hankalinta kan akwatin tv tana ta mita.



Shiko Abdul majid kai tsaye gidan inna Shatu yaje, nan gwaggo shatu ta tabbatar masa da ai sun tafi, kenan yawonsu suka tafi, lallaima yarannan zan koya musu hankali haka yai ta zagaye har yagaji ya koma gida.



Yana zaune wajen mai gadi yana jiran yaga ita inda zai b'ullo har aka kira sallar magrib babu alamarsu sukaje masallaci suka dawo.


Suko su Fatima basu tashi sanin lokaci yajaba saida sukaji kiran sallar magrib, take kuma ido ya raina fata suka mik'e a gigice suna salati da salallami.


Da k'yar Maryam tasamu sukayi sallah sannan suka kamo hanyar gida.


Abakin get suka tadda Abdul majid yana waya bak'aramin faduwa gabansu yai da ganinsaba adake Fatima ta danna hon mai gadi ya bud'e yanai musu sannu da zuwa suka shige cikin sauri Fatima ta tsaida motar ta fito a guje tayi b'angaren Amma tunma kafin ya shigo dan rasan dole ransa zai b'aci tunda ya kafa musu dokar fita da mota su kad'ai.


Amma na saman abin sallah da carbi,a hannunta tana ja.

Dakai ta amsa sannun da suke mata sunsan intana lazumi bazata yi musu maganaba dan haka suka,ajiye mata sak'on. Harda wanda innan tabasu da kayan kwalliyar da maman maryam ta basu duk nan suka bar mata, sukayi bangarensu jin ana,kiran sallar isha.



Tana murd'a kofar falon suka four eyes dashi take dabara ta fad'o mata kawai sai ta d'an durk'ushe abakin k'ofar tayi sak.


Shi kuma ganin haka ya buga mata wata uwar tsawa yace "bazaki k'arasoba 'yan banzan yara marasa kunya ku kun raina mutane ko?"

.


Itako duk da cewa ba k'aramin girgizata tsawar da yamata tayiba amma hakan baisa tayi ko gezauba ammafa zuciyarta wani irin bugu take na tsoro haka kawai mutum ya koyi masifa k'arfi da yaji.




Shi kuwa ganin haka ya mik'e a fusace yayi kanta tunkafin ya k'araso jikinta ya kama wani irin rawa da ta tuna inya damk'eta bazai mata da sauk'iba yasa yana zuwa wajen ta ta fad'i tana wata irin jijjiga.


Ganin haka yasashi k'arasowa wajen da gudu tareda kwalla mata kira da k'arfi Fatimaaaaaaaa




K'aransane yasa Ummi dake d'akinta idar da sallar ta kenan ta fito da sauri ganin Fatima ajikin sa asank'ame yayinda shi kuma yake ta maimaita kalmar innalillahi raji un .



Take gaban ummi yayi mummunan fad'uwa musamman da ta tuna mafarkin datayi jiya ga kuma Abdul ga Fatima ita innalillahi wainna ilahi raji un ta firta da k'arfin gaske wanda yasa Abdul d'agowa da k'arfi yana kallon yadda jikin ummin yake wani irin rawa.



Fatima kuwa jin muryan umminta cikin wani hali saura k'iris ta bud'e idonta sanin me hakan zai haifarne yasa tafasa bud'ewar amma take awajen takama wata irin jijjiga.




Muje zuwa wllh daurewa kawai nayi nayi muku wannan saboda girman alk'awari






Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*





💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSNA ABDUL AZIZ YAKASAI

WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA


Page 9

................a rud'e Abdul yake jijjiga Fatima yana tofa mata addi'a, da sauri Ummi ta k'araso tana jijjiga 'yar tata wacce zuwa lokacin ta daina jijjigar tayi lub' ajikin Abdul.


Dubansa Ummi tayi tace "Abdul d'auketa kakai min ita d'akina" tattare hannun rigarsa yayi ya sunkuce ta yai d'akin Ummi da ita,


Saman gadon ya kwantar da ita ta d'an bud'e idonta taga yadda yai wani wujiga wujiga dashi gaba d'ayansa a rud'e yake shi tsoronsa d'aya kar wani abu yasami Fatiman.


Juyawa yayi da niyyan fita Fatima ta bud'e idonta tarwai tana kallonsa tana sakin wani kyakyawan murmushi, aranta tace maganin bak'in ran da ka koyo kenan mutum ya wani koyi wulak'anci.


Alamu yaji ajikinsa ana kallonsa ya juyo da nufin ganin ko itace ta farko, yana juyowa Fatima ta saki wani irin mummuna ihu wanda yai daidai da shigowar Ummi atare suka nufi Fatiman da gudu, ihu take tana fad'in "na shiga uku ummi zasu kasheni rayuwana suke nema ummi karki bari yatab'ani ummi hannunsa na macijine ki taimakamin ummi dan Allah" wani irin gigitaccen ihu tasaki lokacin da Abdul ya k'araso asukwane yakai hannunsa jikinta.


Take ta sandare awajen sai kuma numfashinta yad'auke amugun firgice ummi da Abdul suka kalli juna jikin Ummi na wata irin rawa tace "innalillahi,wainna ilaihi raji un ni Ummusalam na shiga uku karda abinda naganine yake shirin faruwa kallonta Abdul majid yake jikinsa yana tsuma zuciyarsa na wani irin razanannen bugu ya dubi ummi yace "menene yake shirin faruwa, me kika gani, kiyi fad'amin dan Allah ummi"



Ya fad'a jikinsa na rawa kallonsa kawai Ummi take idanunta yana zubda wasu irin zafafan hawaye yayin da itama jikinta yake wata irin rawa bugun zuciyarta kuwa har ya zarta kima.



"Abdul majid matuk'ar kusancinka da Fatima yacigaba da faruwa to babu shakka zasu kashe Fatima sun tabbatar min da haka wanda da farko na d'auka cik8n baccine suke fad'amin hakan amma sai na fahimci ido rufe suke fad'amin hakan, ma'ana koda babaccinake ba matuk'ar zan rufe idanuna to zan dinga jin maganganunsu kuma acikin muryoyin yabbas kamar akwai wadda na sani saidai bansan a inaba kuma yaushe? kuma da wane lokaci? nida ba mazauniyar k'asarba wannan shine abinda ya shigemin duhu Abdul majid me akayi musu suke mana wannan rashin mutuncin da zaluncin?"




Ta k'arasa maganarta tareda fashewa da wani irin matsanancin kuka, Abbi dake tsaye abakin k'ofar yagama sauraran komai ya k'araso cik8n nutsuwarsa da kalama da kwarjini irin na malaman addini, batareda ya kalli kod'aya daga cikinsuba ya k'arasa kusa da Fatima ya d'agota ya dafa goshinta ya tofa mata sannan yasa ummi da har lokacin bata daina kukaba kuma jikinta bai bar rawaba.



Yace "kawomin ruwa a kofi" batareda tace komaiba ta juya takawo masa ruwan ta koma gefe tana kallonsa yana

5 / 20