Chapter 19 Reading ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM HN Novels

ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM

Author :  MAMAN ISLAM Category :  KDP NOVELS

Chapter   19 / 20

54K to 57K   out of 58.1K words

zata saka ya fisge tawul d'in babu shiri ta rungume,shi tana,masa kukan,shagwab'a tace






"Haba dan Allah yaya meye haka, gaskiya idan zaka shigo ka ding".......bata samu daman k'arasa abinda zata fad'aba tayi tsi sakamakon manna bakinsa da yayi ak'irjinta yana mata wani irin abu, jitai kamar zata fadi dan haka ta rik'eshi k'am, shikam tunima ya manta da abinda ya kawoshi d'akin saboda wata duniya da yafara tafiya hannunsa yasa a hankali,fara shafata yana,mata wasu irin abubuwa masu wuyar fassarawa tuni,jikinta ya hau rawa takasa tsaiwa dole ta zame a wajen yabita yana dad'a gigitata da salonsa ranan Fatima da kanta tasan cewa ba k'aramin missing juna,aukayi ba dan saida ta rik'a rok'on ya k'yaketa haka har saida yaga ta fara masa kuka kafin ya sarara mata.





Saida suka shafe sati biyi da dawowa kafin Daddy ya had'a meeting ya gayyaci kowa da kowa nan b'angaren Amma.





Kusan sai da kowa ya rigasu zuwa dan saida suka gama shiriri tansu kafin suka shirya suka zo kawu Tanimu ne kawai babu awajen wanda da ace yazo kusan duk sanda zasuyi meeting shine jagoran taron, bayan gaishe gaishe da kuma d'an tab'a hiransu na zumunci sai kuma kai tsaye daddy ya tashi ya fara jawabi kamar haka.





"Assalamu alaikum ya 'yan uwana barka da wannan lokacin da fatan duk kuna lafiya" du ala amsa masa da lafiya yace "to Alhamdulillahi kamar yadda kuka sani abubuwa dayawa sun sha faruwa ga Abdulmajid wanda ya kasance duk matar da zai aura sai dai awayi gari aga babu ita ta mutu ko yankanta ko an murd'e mata wuya da sauransu kuma mutuwa orin na fija an babu ciwo babu komai, kamar yadda kuka sani nima na sani wasu dayawa daga al'ummar unguwar nan suna zargin nike kasge duk wani wandacya rab'i d'ana suna zargi da ZATON tarin dukiyar da Allahu subahanahu wata ala yabani na jinin mutane ne yayin da acikin gidannan kuma wai 'yan uwana suke ZATON Abdulmajid da kashe duk wacce ya nuna da nufin son aurenta wanda wannan abun duk ya kasance ZATO NE to amma akace wak'a abakin mai ita yafi dad'i yanzu dai ga Fatima ga kuma Abdulmajid dan haka sai su dubi girman Allah su fad'a mana ainihin wanda ua sace su da kuma dalilinsa nayin haka dan haka gareku"





Daddy ya karasa jawabinsa tare da neman waje ya zauna ya lyin da wajen yayi tsit na d'an lokaci wanda suka rik'awa Abdulmajid wani kallo na daban jikinsu yai sanyi shi kam kawu Ridwan kasa had'a ido yayi da Abdulmajid domim yafi kowa tada hankalinsa lokacin da Amma,taso a had'a auren Ihsan da shi tsalle,yai ya dire yace wallahi bazai bawa d'an shan jini 'yarsa ya shanyi mata jiniba yayin da daga gefe marigayiya Asma'u ta dinga zugashi saboda tsoron hukuci da alk'awarin da aka d'auka akan duk wani wanda ya rab'i Abdulmajid wanda mutane da dama suke,tunanin domin,dukiyane.






Abdulmajid sai da ya d'ebi kusan second goma kafin ya ce "innalillahi wa inna ilaihi raji un" da d'an k'arfinsa sannan yace "makashin mu yana tareda damu shine yake aikata komai yake lalata komai shike aikata duk wani kashe kashe kuma yake zab'ar duk wanda yaso yasaka shi a k'ungiyar su ta asiri daddy menene had'inka dashi mai kayi masa mai ya tab'a had'aku? domin yace fansarsa akanka take kuma nine garkuwanka shiyasa yake tab'ani yake sakani cikin duk wannan halin domin ya girgizaka yasakaka adamuwa ya d'orama kama ciwo wanda zaiyi tacinka dukiyar dakake tak'ama dashi ya k'are a wajen neman magani kayi mutuwan wulakanci wai me kamasa ne wacece Hauwa????????













Takuce maman islam
[11/30, 6:11 AM] Hayat: 💦💧 ZATO NE💧💦


NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM

☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIN☀️


Page 54
.......................duk da irin sab'anin da ya rik'a had'a su ba k'aramin duka mutuwar tayi mataba sosai jikinta yayi sanyi musamman da yau abun da yake ta b'oyewa tsawon lokaci ya fasu sannan ga kuma mutuwar mijin nata wanda babu tantama tasan cewa Tanimu ne ya kashe shi innalillahi wa inna ilaihi raji un rabon da gwaggo Hafsatu ta shiga tashin hankali irin wannan tun mutuwar tilon 'yarta wanda alokacin har ga Allah yayan nata ta zarga kamar yadda sauran mutane suke fad'a cewa wannan dukiyar nashi Na jini ne, take wanda itama data rasa mafita kawai tabi bayan magautan d'an uwanta ma hassada masu bak'in ciki da arzik'in da Allah ya masa.




Wani irin kuka ta kuma kecewa dashi tareda rarrafawa ta shige jikin Amma tana mai cigaba da sakin shashshek'a yayin da tausayin ta ya hana Amma cewa komai sai shafar kanta da ta hauyi itama nata hawayen basa tsaiyuwa.



Da farko Kawu Tanimu a iya rugar Tanimu ya rik'a bulayin neman Badamasi sanin kansane bazai tab'a b'uya a d'aya daga cikin gidajansaba hakan yasa koda wasa baiyi tunanin nemansa a gidansa ba.



Shima kuma Badamasi tunda yasan cewa dole Tanimu zai gane cewa shine ya temaki su Abdulmajid kuma yasani Indai har sukayi ido biyu dashi tashi ta k'are rayuwar shi tazo k:arshe kuma yasan bazai tab'a bawa ransa cewa zai tsaya a rugar Tanimu ba hakan yasa ya koma gida ya kulle Kansa yana ta addu a tareda rokon Allah ya kawo k'arshen wannan azzalumin bawan .




Gaza kuwa duk inda ta shin hankali yake to nata ya ninka nan domin aikinnata ma baya tafiya duk da kasan cewarta jinnu kuma shahararriyar b'arauniyar sirrikan tsafin duk wani matsafi data sani a wannan karon abin yak'i aiki, tana cikin wannan rud'anin Tanimu yazo mata da bak'in labarin cewa wai ba aga Badamasi ba take ranta ya b'aci idanunta ya koma wani irin kore shar kallon datayi masa yasa yafita da sauri batareda yaji daga garetaba, yana fita ta fashe da wani matsiyacin kuka yana magana da wani irin yare mara dad'in ji take wasu 'yan k'ananun jemagu suka bayyana tayi musu rad'a a kunne suka b'ace.




Su Abbi kuwa basu fara zuwa neman kawu Tanimu ba saida sukaje gidan da Abdulmajid ya kwantata musu sun jima suna buga gidan yak'i bud'e musu suka kira Abdulmajid suka fad'a masa hatta kiran wayarsu yak'i dagawa kuma yana shiga, Abdulmajid yana masa kira d'aya ya d'aga bayan sun gaisa ya sanar masa cewa Abbi me da Daddynsa zasu taimaka masa ne akan mugun nufin da Kawu Tanimu yake nemansa da shi, bai yarda ya bud'e musu sai da duhu yayi yana ganin su yaji sanyi aransa ko ba komai zasu taimaka masa da yak'ar wad'an azzaluman shed'anun mutanen.



Bayan ya shigar dasu ya kawo musu ruwa da abinci mai kyau dake daman can ya iya girkinsa sannan kuma dake yana da komai na buk'ata hakan yasa tunda yarufe kansa agidan babu wanda yasan yana ciki dan ko k'wakwk'waran motsi baya yarda yayi.




Bayan sun gama cin abinci sunyi sallah ne kuma Badamasi ya k'ara shigowa suka gaisa sannan suka k'ara gaisawa tareda yiwa Badamasi tambaya akan rugar Tanimu kasancewar sa wanda yafi kowa sanin sirrin rugar ciki da wajen ta.





Sosai ya rik'a tona musu asirin kawu Tanimu tare da kwatanta musu hanyar da zasubi tareda b'oyayyun abubuwan da kosu makusan tansa bays amincewa dasu akai da wani kafurin d'aki wanda koda mantuwa ne bai tab'a gigin barinsa a bud'eba sannan bai tab'a bari wani ya shige shiba koda wasa wannan d'aki daga shi sai Allah ne kawai suka san abinda yake cikin sa, bayan ya gama musu dukkan bayanai ne Abbi ya dubeshi yace.



"Dole dakai zamuje Badamasi domin kafimu sanin hanya" arazane Badamasi ya subi Abbi sannan ya hau girgiza kai tareda fad'in



"Kayi hak'uri alhaji na tabbata idan nakai kaina wajen Tanimu sai dai wani baniba kaga kenan burina na d'aukar fansar ran iyayena ya lalace, dan Allah alhaji karma tilastani zuwa inda Tanimu yake domin nasan shi nasan waye shi yana da duk wani salo da dabarar mugunta kala kala sannan cikin ruwan sanyi yake sulwantar da duk wanda ya shiga hannunsa"




Kafad'ar Badamasi Abbi yadafa yana kallon yarda jikinsa yake tsuma har lokacin yace "sanyi mana abokina kar ka d'aga hankalinka dayawa mana kar wani ciwon ya kamaka abinda nake so dakai shine kasalokacin cewa duk abinda yasameka daga Allah ne babu maiyi ko hanawa sai Allah idan kaga har Tanimu yayi nasaran kasheka to dama can lokacin ka ne yayi dan haka ka k'addara mutuwar ka a hannun Allah yake ba hannun kowaba sai dai ace wani yayi sila amma rai da rayuwa duk suna hannun mak'agin kowa da komai ne wato Allahus samawati wall arad dan haka ka daina tsoron komai tafiya zamuyita da kai babu abinda zai faru sai ikon Allah".




Abbi yajima yana rarrashin Badamasi kafin ya amince ya bisu suka tafi har masaukin bak'in Kawu Tanimu wanda yake tsakiyar daji wanda yake ma mutane rufa ido suke d'auka a k'ofar gidansa shago yake.







A can gombe kuwa bayan andawo daga kai mashinaulaiman 'yan uwansa suka d'an shishshigo sukayiwa gwaggo Hafsatu gaisuwa suka d'an zauna na wani lokaci kafin sukayi sallama wa ita da 'yan uwan ta dan acan garinsu zasuyi nasu zaman karb'ar gaisuwar.





" Baby gaskiya nidai nagaji kawai tunda Abbi sun tafi kamo wannan mugun mutumin mu koma gidanmu mana dan Allah nidai gaskiya nan gidan an takuramu da yawa wai harda wasu masu tsaro dan kar mu fita" kallon baki da wayo Abdulmajid yayi mata kafin yace "zokiji"





D'an matsawa tayi kusa dashi tana turo baki gaba wai ita a dole an takura su, tana k'arasawa ya cafke bakin yana aika mata da wani irin hot kuses masu zafin gaske.




Sosai ya shiga rud'ata da salonsa dama yayi missing kwana biyu bai samu ya d'an keb'e da itaba, ita ko hankalinta ne yayi mugun tashi ganin cewa afalon Amma suke da k'yar tasamu tajashi b'angaren su na nan dan tasan tunda idanunsa suka rufe indai bai samu muradinsaba babu zaman lafiya, shikam babu kunya dan a tsananin buk'ace yake da ita yaja hannunta suka fice daga wajen sukayi shashin su.







Duk wani Abu da zatayi dan ganin ta dai daita komai abin yaci tura ta gano indai tana so komai ya tafi dai dai dole sai taje da kanta wannan karin ta d'auko abinda ke cikin Fatima dole shine warwarewar dukkan matsalo linta, gama wannan tunanin ke da wuya ta b'ace dan tasha alwaahin ko me zai faru wannan karon sai ta shiga gidan ta biya buk'atar ta.





Sunyi nisa sosai sun Lila a duniyar masoya domin ita Kanta tasan cewa tana da buk'atar mijin nata shiyasa yasamu had'in kanta d'ari bisa d'ari, tafiya tayi nisa sosai yana gabda kaiwa duniyar masoya tayi ido biyu da wani jib ge gen......


Kuyi min afuwar jina shiru wannan karon mamana ne jikin ya Dan motsa bana zama Sam wllh



Taku maman isi
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*_______________________________________*


💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 53
.....................dukvsuka kafeshi da kaifafan idanunsu yayin da zuciyar ko wannen su ya shiga wani irin bugu suna tsoron kar ya fad'o wani nasu ko makusancin su.



Shi kam lissafi yafara kamar haka.
"Haj. Asma'u matar yaya Rudwan tana da matsayi na musamman acikin qungiyar, sannan ita ba wanda yajata kwad'ayi da son abin duniyane ya kaita sai, sannan kuma duk wani abuda zai faru wanda yadanganci cikin gidannan ita ke jan ragamarsa idan kuna musu kuje bayan wadrop d'inta tanan take gudanar da duk wani abinda takeso kuma tana iya fita batare da wani yaganta ba dan fitanta yafi tsakiyar dare idan gari yayi shiru sai ta fesawa yaranta wata hoda wanda har ta dawo bazasu farkaba kuma idan shi yaya Rudwanun yana gari harshi take had'a, da zarar kuma ta dawo akwai sunadarin dazata k'ara fesawa su farka akan lokaci.




Sai Munzali k'anin alh. Sambo shima,neman duniyarsa ne ya kaishi. yaya Habiba kuma ita,ta rasu ne akan yajata a cuci d'an uwanta ganin cewa tana da rawar kai sai tak'i shine da ta tashi haihuwar fari saida ya bari ta hafi d'an ya d'auke shi ya hura mata iska aciki sannan ya murd'e mata wuya ko shurawa batayi ba, shine likitoci sukace ta rasu bata kai ga haihuwar ba ta rasu,



Bayannan akwai uwar gidan alh. Munzali saudat haihuwar ta goma yaran suna mutuwa in ka,d'auke d'ansa na fari shima,duk Munzalin ke kaisu wajen tsafi sannan kuma haj. Munira tanan sun b'oyeta suna ta gana mata azaba akan ta gano cewa mijinta matsafine shine yayi mata wata allura wacce sai tayi kwanaki bata farkaba ya tabbatarwa da iyayen ta ta rasu sannan suka koma,daga baya suka hak'o ta sannan ya tsaface haj. Kulu matar abokin yaya Yuseef ya maidata kamar matar sa duk sanda ya buk'ace ta jiki na rawa zata amince masa, ta haka ne suka samar da Yusra sannan shine yasace k'wayayan haihuwar d'an uwansa alh. Sambo ya aiwatar da wani tsafi ta yanda bazai tab'a haihuwaba har abada kuma shi a yanda aka tabbatar masa idan yayi hakan asirinsa bazai tab'a tonuwa ba sai dai sun manta da cewa ubangiji yana arawa mutum rana da lokacine duk randa ya tashi tona musu asiri bazasu gane kansuba kuma sun manta rana dubu na b'arawo rana d'aya tak na mai kaya sannan ramin k'arya k'urarrene".



Nan dai ya shiga lissafo musu yawan mutanen da suke cikin wannan harkar kuma duk wanda aka sani sanannu wanda saida mamaki yasa suka rik'a jijjiga kawunan su saboda al'ajabi sannan yace "ni kuma bance ku yarda dani ba zandai fad'a muku gaskiya ne wanda nake so ku gane kafin na mutu kamar yadda nace muku NINE BOKA DUNA haka kuma duk wani abu da zanyi wallahi wallahi wallahi Allah ne shaidana bansan ina,aikatasuba amatsayina na,musulmi makaranci ma haddaci wanda yai imani da k'addara kharan au sharran nakanyi mamakin wani abun idan na aikata kuma idan Hafsatu zata shaidrni zataga ina yawan rufe kaina ad'aki to wallahi bak'in cikin munanan aiyukana ne yake cin zuciyana nayi ta fama domin jinya nakeyi sosai har ga Allah babu yadda yaya Tanimu baiyi daniba na k'i amincewa saboda bana so na lalata gobena lokaci guda na tsunci kaina acikin mummunan yanayin da ban san yau shene a inane taya nake aikatasu ba wallahi duk randa nayi wani abun sai nayi dana sani mara iyaka kuma sai nayi rashin lafiya sosai shine dalilin da duk lokacin danayi wani mugun aikin matata zataga na rufe kaina a d'aki ina jinyar zuciyana da kuma gangar jikina da Tanimu yake azabtarwa acewarsa ta hakane idan bala insa ya isheni zan amince na kasance d'aya daga cikinsu batare da ya sani wani abun ta hanyar tsafiba, sai dai kuma wani ikon Allah lokaci guda naji hankalina,ya dawo jikina ta sanadin aikin da yasani nayiwa 'ya'yan wan matata kisan gilla ta hanyar yankan naman jikimsu gunduwa gunduwa atsakiyar kasuwa wanda yace idan ina aiwatar da wannan mugun aikin to babu fa wanda zai ganni, ananne hankalina ya dawo jikina naji wani abu mara dad'i yana sukana abisa aikin da yasani take nayi masa musun wannan aikin ya d'ebi kwanaki yana bina nak'i amincewa shinefa yayi min alluran guba wai dan kar na tona masa asiri haka nan suma yanzun ta kwab'e musu dan mafita suke nema sosai sannan dan Allah ku taimakawa garzali domin shima yana cikin wani hali saboda neman sa suke ido rufe kuma matuk'ar sukayi ido da ido wannan gubar datake yawo ajikina yana nan yana yawo da ita dominsa kuma indai suja had'u sai dai wani bashi ba wannan shine gaskiyar abinda na sani ni yanzun tawa ta k'are domin wannan gubar bata da magani sai in kwana bai k'areba dan haka nake rok'on dan girman Allah ku yafemin abisa kuskure na badan niba badan na isaba dan zatin Allah na sani cewa babu ni babu wani rabo domin ban aikta abinda zan adarba agaban mahalicina duk aiyukana munanane'.





Yak'are tareda jan wani irin zazzafan numfashi wanda ya wuce da rayuwarsa batareda sun ankare da hakan ba domin jikinsu ya riga da yayi sanyi hankalinsu ya masifar tashi musamman daddy da mamakin kawu Tanimu yake neman illata rayuwarsa, Abbi ne kawai yayi k'arfin halin cewa.





"Kar kace haka malam Sulaiman domin Allah mai yawan gafara ne kuma baya hukunta bawa abisa laifin aka tilastashi yinsa ko kuma ya aikata shi cikin gushewar hankali ko tunani sannan kuma dakake cewa baka da rabo bakasan gaibu ba sai ubangiji dan haka ka dage da istigifari tun kafin ka koma ga Allahu subahanahu wata domin shi mai yawan yafiyane ga bayinsa dan haka mu baka mana komai ba kuma koda kayi mana mun yafe maka duniya da lahira dagani har 'yan uwana na ari bakinsu naci musu albasa"




'Karan fad'uuwar dayayi ne ya ankarar dasu sukayo kanshi da sauri gaba d'ayansu gwaggo Hafsatu ne tafara tab'ashi sai kawai tabkoma gefe tareda fashewa da kuka domin tariga ta tabbatar da cewa rai ya rigada yayi halinsa dama 'yan magana sunce tsakanin mata da miji sai Allah da duk bayanin da yake cikin zafi take tana sak'a irin matakin da zata d'auka kansa amma yanzun ganinsa amace yazama gawa sai wani irin imani da tsoron Allah ya shigeta take ta shiga istigifari tana nema masa gafara wajen Allahus samawati wal ardi.





Sosai mutuwar ta daki 'yan uwanta ga kuma abinda suke shirin yi na binkito inda Tanimu ya b'oye tare da bin diddigin Badamasi dan cetosa daga sharrin Tanimu dan haka dole suka kasu kashi biyu rabi suka tsaya suka sallaci malam sulaiman rabi kuma suka had'u da jama an tsoro suka tafi neman Badamasi da kuma aboki kuma aminin shed'an Tanimu



To masoya labarifa yana ta gangarawa yana tafiya zai k'are zai wuce





Takuce
Maman,isi
[11/30, 6:11 AM] Hayat: 💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


☀️FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATION☀️


Page 55



.............mutsits tsika idanunta ta

19 / 20