Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
gabansa ya fad'i sannan cikin wata irin murya tace
"Kai dumb'uru karfa ka d'auka tsoronka nakeji nake binka sannan inaso ka rik'a tuna cewa kaifa mutumne ni kuma aljana ina da sigan da zan iya yin komai na bikane saboda wani buk'ata nawa kuma na biya dan haka abinda nakeso dakai ka zubamin ido nima burina kamar yanda naka ya cika ko kashiga bala'i"
A mutuk'ar tsorace Dumb'ur yake kallon Gaza tareda mamakin abinda takeson aikatawa matar da ya k'watota daga hannun azaluman 'yan uwanta ya maida ita wani abun yau itace take neman wulak'anta shi ta muzanta shi, shi kam duk randa Gaza ta gujeshi nashi ya k'are.
Gwaggo Hafsa ce zaune ta rafka uban tagumi tana tunanin wannan karon mai gidannata yayi nisan zango dan bai tab'a dad'ewa hakan ba sai wannan karon.
Zaune duka yaran nata suke cikin tsantsar damuwa sun kafeta da idanu hankalinsu har baya tareda su ganin halin da mahaifiyarsu take ciki har yau bata samu farfad'owaba, lokaci lokaci Husna takan share hawayenta.
Sosai Yusra ta canja musu kullum cikin damuwa take sai wata irin rama take wanda sai daya mutuk'ar d'aga hankalin abokan zamantan, kuma tambayan duniya tace musu lafiyanta k'alau.
Yauma a tsorace tashiga d'akinnata cikin fargaba wanda ya kasance mata kamar jiki ayanzun sai data gama duk wani abu datake gabatarwa sannan ta haye gadon tayi kwanta da zummar intaji baccin tayi addu'an amma ina yauma kamar ko yaushe kafin tayi wani yunk'uri baccin ya kwasheta batareda tayi addu'an ba.
Cikin baccin nata ne taga wannan matar wadda tayi sanadin zubewar gudun jininta, tana murmushi ta matsota tareda shafar cikinta tana cigaba da wani shu'umin murmushi tace "Yusra kin burgeni sosai yadda kika kuma cika min burina na kuma samamin muradina yau kuma zanyi dinner da d'an tayin babyn da kika kuma k'unsa" daga haka ta kuma sa hannu ta bugi cikin Yusran da d'an k'arfi wanda yayi sanadin da Yusra ta saki wani irin gigitaccen k'ara wanda duk wani mahaluk'i dayake gidan saida k'aran ya mugun firgitashi domin da iya k'arfinta tayi k'aran.
Rige rigen shiga inda take harda ma'aikatan gidan sosai hankalin Abdulmajid yatashi ganin yanayin da Yusra take ciki da gudu ya k'arasa yana jijjigata amma ina tariga da ta sume.
A d'imauce ya sungumeta da mugun gudu suka fito yana salati da sauri driver ya bud'e mota mai gadi ya bud'e get suka tafi da mugun gudu sukayi asbiti.
Sosai hankalin Fatima yatashi ganin irin uban jinin da Yusran take ambaliya harda wani irin guda guda bakin kirin yayin da likitoci suka rufu akanta dan ceto ranta.
Kuka take kaman zata ranta zai fita hankalinta amugun tashe takasa samun nutsuwa ko kad'an wani irin tsorone yake bin ko wane huda na jikinta.
Ganin halin datake cikine yasa dole shi ya danne nasa damuwan yajata jikinshi yana rarrashinta da k'yar uasamu baccin tsoro yayi awon gaba da ita wanda batayi hakan ba saida ta rungumeshi k'am k'am.
Yusra kuwa sai goshin asbah suka samu suka sha kan matsalan suka yi mata alluran bacci hankalin hajiyanta kuwa idan yayi dubu to atasheyake.
Muje zuwa maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💧💦ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 28
................cikin baccin ne tayi mummunan mafarkin dayasa ta farkawa a mugun firgice take jikinta ya kama wani irin rawa takama wata irin jijjiga.
Da gudu Abdulmajid da Fatima wanda dama tuntuni suna wajen cikin jimamin abinda ya faru suka yi rige rigen zuwa har suna bangazar juna batare da sun kula hakan ba.
Wani irin mugun gumine ya rik'a tsatstsafowa ako wane kafan gashi na jikinta, atare suka ruk'ota suna mata addu'o i kafin tasami nutsuwa ta fashe da wani irin gigitaccen kuka.
Abdul ya rik'o hannayenta duka biyun yana kallon cikin idanunta saidai yakasa ce mata komai saboda tsaban tausayinta ya saki hannun ya juya da sauri ya fita kiran doctor.
Fatima ta matso ta kamo hannunta tana wani irin kuka takasa cewa komai, rungumota Yusra tayi jikinta tana son tsaida nata kukan amma abin ya faskara haka suka had'u sunayi gwanin ban tausayi.
Tare suka dawo da likitan ya dubata tareda yi mata tambayo bata da wata matsala azahiri dan haka yabasu sallama tareda shawarwarin yadda zata na kulawa da kanta.
Tunda suka dawo gidan yake ta aikin rarrashi sun kasa daina kukan tambayar duniya abinda yake sata kukan amma ta kasa dan haka ya gabza tagumi yana ta kallonsu yayin da zuciyansa yake wani irin zafi
"Yusra" ya kirata cikin wani irin yanayi mai wuyan fassaruwa ta d'ago idanuwanta wanda sukayi wani irin rinewa saboda tsaban kuka ta watsasu akansa batareda ta iya cewa komaiba.
"Kinga k'anwarki itama tun d'azu take ta kuka nayi rarraahin duniya tak'i ta daina, kuma kukanki ne yasata kuka dan Allah ku taimakeni kar zuciyana ya buga kudaina wannan kukan plss nd plss kar na had'oye zuciya saboda damuwa, na rok'eki Yusra ki taimaka ki fad'a mana damuwanki sannan ki daina wannan kukan da bazai amfaneki da komaiba sai k'arin wani damuwan dmdan Allah"
Ya k'arasa cikin wani irin muryan dayasa Yusra taji wani irin sabon damuwa ya k'ara ya lullub'eta, abinda yake damunta ba mai k'arewa bane kuma ba mai fad'uwa bane kamar yanda mijinta da abokiyar zaman ta suke buk'atan ji ta fashe da wani sabon kukan tareda fad'awa jikinsa tana wani irin shasshek'a, abinda wannan la a nanniyar ta fad'a yana matuk'ar razanata.
"Kai jaririya kina da k'ok'ari kina da himma naji dad'i yanda kika k'ara harbomin sabon baby zan shana sannan zan ta d'aga miki k'afa kafin amfaninki ya k'are sannan ingigita tunanin ubanki Munzali mara tsoron Allah sannan abu nagaba ki k'addara idanunki biyu kikejin wannan sharhin kuma duk wanda kika bawa labari daga ranan bazaki k'ara kwanan duniya ba,zakiyi mutuwa mafi muni inkuma kina tantama ki gwada ki gani" bayan gama wannan dogon bayaninne ta bugi cikinta wanda yasa ta kuma missing babynta akaro na biyu.
Wani sabon kukan ta kuma rushewa dashi tareda kamo hannunsa dana Fatima tana fad'in "dan Allah kuyi hak'uri bazan iya fad'a muku abinda yake damunaba yafi k'arfin na fad'a amma dan Allah kutayani da addu'a domin ni yanzu addu anma kasashi nakeyi dana soma sai naji kamar an murd'emin baki nakasa cigaba idan kuma naso yi a zuciyana sai wani abu mai nauyi ya tokaremin kirjina, abinda nasani kawai shine dole kafin na mutu kusan abinda yake firgitani abinda yake damuwa na kuwa duk kunsanshi dan haka babu buk'atar ce muku komai akan hakan.
Sosai Fatima ta fashe da kuka tareda k'ank'ame Yusra a jikinta tana kuma kallon Abdulmajid tace "wai shin yaya wannan mutanen idan sunfi k'arfinmu sunfi k'arfin Allahne?
Haba yaya so kake acigaba da kashe duk wanda kake tareda shi nidai wallahi bazan yarda inaji ina gani akasheni akan abinda bansan tushe da makansaba nidai kawai gida zan tafi babu mamaki ma kasan komai inbanda haka duk abinda akeyinnan ka kasa tab'uka komai mu kenan kullum cikin tashin hankali da damuwa.
Kwarai maganan Fatima ya mugun dukan zuciyarsa wani irin mamakinta ya kamashi yakafeta da manyan idanunsa wanda suka k'ank'ance tsabar fitina da tashin hankalin furucin Fatima gareshi kasa cewa komai yayi ya mik'e a mugun fusace yabar wajen jikinsa har wani rawa rawa yake tsabar tashin hankalin da ya kuna rufto masa yanzun.
Da kallo duk suka bishi yayin da Fatima tasaki tsaki Yusra kuwa fuskan Fatiman tana mata wani irin kallo kafin tace.
"Haba Fatima haba dan Allah meye hakan? Au ashe ko kowa yakasa masa uzuri ke bazakiyi masaba kintab'a ganin mutumin dayake cutar da har abinda yake mafi soyuwa arayuwarsa? Fatima tun muna mu biyu dake kije ki bashi hak'uri domin kuwa kin tabka kuskure kinyi laifi sam bakiyi daidai ba"
Wani irin banzan kallo Fatima ta watsa mata tareda sakin wani dogon tsaki ta kwace fuskanta tabata waje, sam ita bataga kuskuren magananta ba akan me zai aurosu yabar su kullum cikin damuwa da fargaba suke nan kullum basu da wani cikakken nutsuwa kullum garin Allah ya waye da tunanin abinda ranan zata zo musu dashi suke, ina sam bazai sab'uba tagaji kam.
"Ruk'aiyya wannan shine karo na k'arshe da zan k'ara ganinki cikin damuwa na kuma tambayeki ki raina min hankali wallahi Ruk'aiya duk randa kika k'ureni zan miki abinda baki yi tunani ba"
Tad'ago idanunta da gaba d'aya suka sauya kala gaba d'ayansu tayo waje dasu sai kuma ta had'e hannayenta waje guda tace
"Na rok'eka dan Allah ka daina yimin wani tambaya akan duk wani hali da zaka ganni aciki Abbanau, kowane abu akwai muhallinsa kuma komai da lokacinsa, saboda haka ina so kasan cewa lokacin kasaninne baiyiba idan lokacin yayi zaka sani"
Cikin tsabar takaici yake dubanta yana mamakin halinta yana lura da itada irin halin damuwan datake ciki amma kullum ya tambaye ta sai tace tana neman hujja wane irin hujja ne wannan?
Tun ranan da Fatima tayi wannan abun ita dakanta ta fita a harkansu gaba d'aya dan ita a ganinta da kuma halin k'uruciya irin nata tana ganin ta fad'i abinda yake ranta ne wanda kuma shine daidai awajenta.
Har ga Allah tagaji datashin hankalin datake fuskanta acikin gidan dabata fi wata biyar acikinsa ba bazata k'arar da wani jin dad'i na cikakken wata guda acikin wannan gidaba.
Sosai Abdulmajid ya d'auki fushi dasu harda Yusra baiwar Allah datake ta fama da kanta ganin haka itama ta tattara komai ta aje agefe.
Muje zuwa
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 29
...........tun ranan datayi abinda take ganin shine dai dai awajenta bata k'ara yarda ko d'aya daga cikin mutanen gidan sun had'uba domin hatta Yusran ma haushinta takeji dan haka ta tattarasu ta zubasu akwandon shara.
Rabonta da ganin iyayenta tun zuwan da sukayi duba Daddy farkon aurensu kusan wata hud'u kenan dan haka yau tasha alwashin ko yardansa ko babu zataje taga iyayenta dan haka take takira Abbi tace ya fad'awa Ummi yau zata zo musu wuni.
Tana kashe kiran yana kiran Abdulmajid, wanda yake zaune a office d'insa bayan yagama sallamar fatner d'insa hannunsa dafe saman goshinsa har yau bai daina mamakin halin Fatima na rashin wayo da gab'untaba sosai yake jin b'acin ran abinda ta masa.
Anya Fatima tasan yadda take a rayuwarsa tasan kuwa irin yadda ta kama zuciya da ruhi da duk wani kafa najikinsa yana matuk'ar jinta a kowane fitar numfashinsa, kai dolene ma abinda tayin ya tab'a masa zuciya.
Yusra ce ta fad'o masa arai wani irin tausayinta ya kamashi haka kawai batajiba bata ganiba ya had'eta da mai laifi yana hukuntawa ko halin datake ciki bai dubaba take yaja wayansa da niyyyan,kiranta sai kuma kiran Abbi ya katse.
Cikin girmamawa yamasa sallama, tareda gaida shi bayan sun gaisane Abbi yace masa"Abdulmajid me nace maka banace duk runtsi kar ka sake kabar Fatima tazo yanzun ba har sai na nemi hakan da kaina bayan nagama duk shirin danakeyi ba meyasa zaka biye matane kasan masifar dayake binku kuwa acikin lamarinfa hummn to maza kaje ka dakatar da ita kaji na fad'a maka"
Cikin sanyi yace "kayi hak'uri Abbi zanje yanzun na dakatar da ita" suna sallama da Abbin ya dinga kiranta amma tak'i d'agawa ransa ya kuma b'ata masa rai ya zari mukullin motarsa ya fice batareda ya rufe office d'inba.
Tun tana wanka take jiyo k'aran wayanta, saidai koda ta fito batabi takan wayan ba saida tagama shinta tsab ta d'auki makullin motanta da hand bag sannan tazo ta d'auki wayanta dayake saman gadonta anannema taga me kirannata ta d'an tab'e baki gami da turoshi gaba kamar yana ganinta.
Ta fito kenan shi kuma zai shiga suka gwabza karo da sauri tajanye tana kallonsa cikin wani irin tsoro ganin yanayinsa da babu annuri ko kad'an.
Hannunta ya damk'a da mugun k'arfi har sai da tasaki k'ara saboda mugun ruk'on da yamata, ya jata cikin d'akin ya watsata saman gado ya kafeta da wani irin masifaffen kallo.
Kasa had'a ido tayi dashi duk kuma wani fitina datake ji dashi nemansa tayi tarasa domin yanayin data ganshi aciki bak'aramin d'amata hankali yayi ba.
Cikin b'acin rai yace "Fatima ki maida hankalinki fa niba wawa bane dazaki mai dani sa'an wasanki yaushe na fara wasa dake da irin wannan mugun rainin yake neman shiga tsakanina,dake to wallahi muddun kika sake kika fita zakiga abinda zan miki"
Har yakai bakin k'ofa ya jiyo tana fad'in "wallahi banga wanda ya isa yahani fita yau agidannan ba tunda ba haifana mutum yayiba"
Azafafe ya koma cikin d'akin da wani irin taku mai mugun k'arfi ganin yanayinsa yasa ta wuntsula ta shige toilet ta rufo k'ofan kafin ya k'arasa tasaka key.
Wata irin k'wafa yayi sannan yace " tunda babu wanda ya isa me yasa kika gudu mara kunyan k'aryabki tsaya mana kiga k'arshen mara kunya.
Maman islam be
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE 💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ. YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 30
...................tana daga toilet d'in tace "ank'i a bud'e d'in kuma zuwa gidanmu babu fashi dan banga wanda ya isa ya hanani zuwa wajen iyayenaba ehe"
Bai k'ara bi takantaba ya fita a mutuk'ar fusace a bakin falon sukayi karo da Yusra wacce ta fita ta aiki draiver gidansu yanzun, ya d'aga rinannun idanunsa ya zuba akan fusakar ta.
Sai dagabansa ya fad'i ganin irin fitinanniyar ramar da tayi ya d'an jata ya had'e ta da jikinsa yana kallonta cikin tausayawa "ya jikin" yafad'a yana shafar gashin kanta dake kwance a kirjinsa.
Sai data had'iye wani abu mai d'aci kafin tace "naji sauk'i" ganin yanayin datake ciki bai barshi ya koma iffice ba nan yazauna tareda ita yana d'an janta da magana har zuwa k'arfe uku dai dai nan kuma yunwa yasa Fatima saukowa sam bata kula dasuba ta wuce kicin da sauri sam bata kula dasuba saboda hankalinta baya kansu.
Gas ta kunna ta d'ara 'yar ma daidaiciyar tukunya ta soya mai tasa soyayyar miya da naman kaza tad'an had'a kayan hadi sai data tabbatar ya d'an tsirata ta tsai da ruwa yana tafasa ta zuba kayan had'i tareda couscus ta koma gefe tana jiran ya gama ta juye domin ba k'aramin yunwa take jiba.
Tana gama ta juyo karab idanunsu ya had'u wani irin mugun fad'uwa gabanta yayi sam batayi tunanin yana gidanba ta yi zaton tun tuni ya koma office shiyasa ta fito kanta tsaye, cikin tsoro tayi baya bisa tsautsayi ta take tab'aryan data take wajen wanda taga fad'uwanta tana shirin d'aukewa ta manta, taga taga tayi zata fad'i yayi saurin tarota ita da flat d'in abincin, wanda dama shi yazo nema dan shima yunwar yakeji sosai.
Sai da ya gama daidaita mata tsaiwar ta sannan ya d'auke flat din abincin batareda yace mata k'alaba yai waje abinsa batareda ya ko k'ara kallon inda takeba.
Bayansa tabi da harara cikin tsaban takaici batareda yasan tanayiba Allah yasota ta rage wani a tukunyar wai ko Yusra zata gani taci dama takanyi hakan idan tayi girki kuma Yusran inta gani tana d'iba taci, anan kicin d'in ta tsaya taci sannan ta wanke kayan da ta b'ata ta gyara wajen tsab sannan ta dice.
Shi kad'aine yanzun Yusra ta shiga ciki yana zaune saman kafet d'invtsakiyar falon yana cin abincinsa bai yarda ya kalli inda takeba bare tasa ran yasan da zuwanta.
Itama da gudunta ta haye saman dayanayinsa ba k'aramin tsoro yake bataba duk yabi ya koma mata wani kalan tsoro.
Yauma kamar kullum zaune take kamar kullum tana faman tunanin,yadda zata sami wayansa wanda ya d'inma,ta kira iya adadin da bazai k'irguba amma ko tafiya layin bayayi.
Kwatsam taga mutum ya shigo kamar wanda aka wurgo, zumbur ta mik'e tana kallonsa cikin mamakin ganinsa haka wujiga wujiga kamar wanda yake cikin matsananciyar wahala, baima kulada itaba ya shige d'akin dayake karb'ar bakinsa idan yana gari, da sauri ta zabura zata bishi sai dai kafin ta k'arasa ya banko k'ofar da mugun karfi nan ta tsaya tana taradaddin abunda ya sameshi.
"Abbi nifa gaskiya na takura fisabilallahi awani d'aureni niba akuyaba har ga Allah nagaji aurennan ya isheni dama kai kamin dole yanzun kuwa Allah ji nake kamar na gudu nabar gidan" Fatima kenan take korowa mahaifinta wannan bayanin cikin damuwa bayan kiran wayansa datayi
Wani irin murmushi Abbi yasaki mai ciwo, aransa yace Fatima da ace haka kawai nabarki da tuni bakya raye aduniyar ke da abokiyar zamanki na riga da nagama kawo badan komai ba ason zuriyar Alh. Yuseef ta yaduba sai dan dukiyarsa dan haka zanwa tufar hanci.
Amma azahiri sai,cewa yayi "Fatima kiyi hak'uri insha Allahu komai zai wuce kuma nine na hana Abdulmajid ya kawoki saboda wani abu dana hango zai faru a zuwan naki amma idan kina son ki mutu zaki iya zuwa"
Sosai Fatima ta tsorata da abinda mahaifinta yace hankalinta yayi mummanan tashi tafashe da kuka mai sauti tareda aje wayar ta fita da gudu daga d'akin cikin tsan tsar tashin hankali Abbi dayake jinta ya aje wayar cik8n tausayin halin da suke ciki.
Dake yau,lahadi ne yana zaune ad'akinsa saman gado daga shi sai gajern wanda babu riga da comouter sa agaba yaba shigar da wasu sakonni, ta bugo kofar da mugun k'arfi wanda ita kanta batasan tayi hakan ba tsabar rud'anin datake ciki.
Da sauri ya d'ago kansa yana kallon yanayinda tashigo dashi cikin mamakin abinda ymd'aga mata hankali irin haka.
Muje zuwa maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN