Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
k'arayi dan tabbatar da abinda idanunta suke gani sai taga ya sakar mata wani irin shu'umin murmushi mai kama dana mugunta, Abdulmajid ta kalla wanda yayi nisa a dunyar nishad'i ga wannan mugun abun yafara tunkarota take jikinta ya d'auki wani irin rawa, dukan sa tafarayi tana "yaya yaya yaya aljana amma ina baisan tanayiba sobad'ad'in surutai kawai yake mata tak'ark'arewa tayi ta galla masa wani azzalumin cizo take kuwa yai wani irin zabura ya watsar da ita gefe yana kallonta da mamakin dalilin dayasa tayi masa hakan, idanunsa ne suka sauka akanta.
Shi ba jemage ya ganiba wata irin halitta ya gani mara kyaun gani, ko ba'a fad'a masa ba yasan cewa su Abbi suntafi su kuma sun kewayo su gama dasu ta bayan fage kenan.
"Yayaaaaaaaaa" Fatima ta kwalla k'ara ganin yadda abin ya tunkaro ta a gigice, da sauri ya tarota ganin tana shirin shidewa, cikin azama ya maida mata duguwan rigarta ya d'agata cak ya goyata abayansa, ya tsaya tunanin ta inda zai fara dan basirar sa ta d'auke bai san me zaiwa wannan muguwar halittar ba, ita ko Fatima saura kad'an ta sume masa ganin yadda take tunkarosu tana zaro harshe kuma idanunta akanta gashi tana nuna cikinta yayin da shegen murmushin bai bar fuskanta ba take taji cikinta yayi wani irin azababben murd'awa take numfashi ya fara rawa haka jikinta ya d'auki sheking ta ko ina da sauri Abdulmajid ya dubeta cikin mummunan tashin hankali take ya fara neman tsari da wannan mak'iyiyar Allah da manzonsa.
Yayin da take tunkaro su tana sakin murmushin k'eta take Abdulmajid ya dage iya k'arfinsa ya fara fad'in BISMILLAHIL LAZI LAYADURU MA'A ISMIHI SHAI AN FIL ARD WALA FI SAMA I WA HUWAS SAMI IL ALIM.
Da iya k'arfinsa yake addu ar yana maimaitawa take Gaza ta tsaya cak tana kallonsu da wani irin yanayi take munafikin murmushin ya bar kan fuskarta sai ma had'de rai datayi tana tunanin ta yadda zata d'auke hankalinsa daga addu ar da yake yi dan addu o i ya hau jefo mata kala kala wanda bata isa ta tunkarosu ba, sai a lokacin Fatima ta farajin sassaucin azaban da ya soma rud'a k'wak'walwan ta ta dubi Gaza cikin k'arfin hali ta saki murmusht tareda d'age mata gira alamun dai munfi k'arfinki, ni ko nace ji Fatima da k'okari kina ruwa yasin.
Su kuwa su Abbi duk inda hankalinsu yake yayi masifar tashi domin abinda suka gani a wannan gidan ya wuce tunanin su harda mutum wanda suka aje namansa ya zagwanye ya zama skeleton gawan jarirai da k'ananan yara kuwa ba a magana duk da kasan cewar su maza wani abun saida yasaka su hawaye yayin da har masu rai irin wanda aka sace ba akai ga kashe suba.
Sun jima suna tafi a wannan k'aton gidan kwallin kwal a dajin wanda ak'alla zai kai gidajan wasu talakawan guda d'ari koma sama da haka tafiyace bata hankali ba kafin su riske k'aton falon da ya k'awata shi kamar ba za a mutuba k'afar Badamasi ya nuna musu wacce ya basu labarinta tunkafin su zo yace
"Yanzu dai duk inda za aje a dawo na tabbata yana cikin nan domin tunda yasan cewa Abdulmajid sun gudu kuma ga bala in da ya sakoshi gaba na Gaza dan nasan bazata tab'a barinsa ya samu kwanciyar hankali ba to tabbas yana nan yana nemarwa Kansa mafita"
Abbi ne yafara nufar wajen bakinsa d'auke da addu a sannan baba Ridwan shima nasa bakin d'auke da tasa addu ar suka buga k'afar da mugun k'arfi saiga shi ta bud'e, abinda suka soma cin karo dashi k'aramin girgizasu yayi ba domin a take daddy ya zube a wajen yana rawan jiki shi kam dama baba Ridwanu bashi da wahalar kuka take ya fashe da kuka ya ruga zai rungumo mahaifinsu daya gani a sak'ale yana reto, da mugun azama Badamasi ya Rik'oshi yace "karkaje Alhaji wallahi tarko ne yaga shigowar mune domin ba anan ya adana gawar mahaifinku ba"
Dukan su suka bishi da kallon rashin fahimta tare da son jin k'arin bayani fahimtar hakanne yasa yace "tabbas Tanima kafiri ne kuma fajiri mak'iyin addinin Allah uwa da ubansa basu sa an haihuwa ba na rantse domin duk lokacin da wani zai mutu to akwai sa hannun Tanimu kuma bayan Jana izar duk wanda ya mutu Tanimu yana komawane ya hak'o gawar dan shi na shi kalar tsafin da gawa yake amfani, kuma gawar mahaifinku wanda shine ya kashe shi da hannunsa da kuma gawar mahafiyarsa wadda ita CE farkon gwajin tsafinsa wacce ta mutu tun yana shekara goma amma lokacin daya zama matsafi saida ya rabota da makwancinta na gaskiya yazo yake neman duniyarsa da gawarta said kuma ita Hauwa wannan dai wacce yaiwa su Abdulmajid k'aryar cewa saboda ita yasace su wallahi k'arya ne hatta lokacin auren da akasa duk da ba haifeni ba ya fad'a min saboda yardan da min yace shine silan komai dan ya amfana da hakan sai Amma ta bayyana ta lalata masa shiri shine ya shek'e Hauwa sannan kuma ya ya d'auki alk'awarin hana Amma sakat ta hanyar kaahe duk d'an dazata haifa yayi nasarar hakan domin yara takwas ya kashewa Amma sai Abdulmajid da Meemah ne kawai suka gagare shi shinefa yake ta kashe duk wacce Abdulmajid yace yana son aura, sannan kuma fa Kansa yake shiga har garin yace Alhaji Yusif matsafi ne wannan shine dalilin da yasa kake ganin kamar mutane na zarginka ba zargi bane tabbatar musu akayi kunga yanzu muyi abinda ya kawomu dan da yasan da zuwan mu da yanzu muna nan muna k'aramin yak'i"
"Abbi yace baza akai ga haka bama domin bazamu bashi damar hakan ba, take Abbi yafara da karatun k'ur ani mai girma ayoyin lalata sihiri yafara karantowa take wajen ya d'auki wani irin kururuwa.
Shi kuwa Abdulmajid saida ya gama gigita Gaza da karatu da addu o i kafin ta ankare ya d'auko wani ruwa a kwalba da Abbi yabashi ya yarfa mata take tahau wani irin ihun daya firgita su duka sannan ta hau hajijiya ta b'ace b'at.
Kawu Tanimu da idanunsa suke rufeyaji yaji wani irin zafi yana ratsa shi kamar ana tsatstsaga masa jikinsa da reza take yai hanzarin bud'de idanun sa take gabansa yai wani irin fad'uwa ganin Gaza cikin wani irin yanayi ga jikinta yana wani irin kwailila abin ya masifar d'aga masa hankali dan yasan ba iya Kanta abin zai tsayaba dole ya shafeshi, ilai kuwa cikin b'acin rai tace
"