Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 38
...............lokacin daya shiga har Abbi ya gama shirinsa na tafiya office, ganin d'an uwan nasa kamar baida nutsuwa yasa ya fasa fitar yaja shi falonsa suka zauna yana dubansa da kulawa yace.
"Dan uwana lafiya naga kamar kana cikin damuwa?"
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Abubakar niko na tambayeka mana?"
"Ina jinka Umar Allah dai yasa lafiya dan naga yanayin ka kamar da wani abun da yake damunka?"
"Akwai"cewar Umar "akwai yaya amma kafinan ina son insan irin marakin daka d'auka akan lamarin Abdulmajid da kuma abinda yake faruwa?"
Wani irin murmushi Abbi yayi mai ciwo tunowa da yayi da Yusra da abinda yafaru da ita aransa yace lallai Allah Allah ne idan yai duba da inda yamai da hankalinsa yake neman hujja akan abin sai kuma abin ya fito ta wani yankin da ban.
Ya d'an dubi d'an uwan nasa yace "Umar abinda ya faru shine ni ina zaton wuta a mak'era sai kuma na ganta a masak'a abinda nake nufi anan shine wanda nake zargi akan wannan matsala da ban wanda kuma suke bayyana da ban kaga ikon Allah da kuma k'arfin da addu'a yake dashi ko?
Na sani Rukayya ta fad'a maka abinda haj. Asma'u ta aikata da kuma dalilin mutuwar ta nasan taga komai, abinda nake so da kai Umar ka kwantar da hankalin ka wannan ba komai bane a cikin iko da kuma k'udura na ubangiji kaga sai tona aairinsu yake dan haka d'an uwana kayi hak'uri kaga sarautar buwayi gagara misali.
Acan gidan boka duna kuwa bayan ya d'auke kan haj. Kulu dan yaga nema take ta jik'a masa aiki shi yasa yaga gwara ya gama mata aikin kafin shi ta tozar ta shi.
"Yaya danAllah ka temaka ka kaini gida kaga bikin Meema sai matsowa yake gashi har yau ban samu mun tattauna akan komai ba" ta fad'a tana zama ajikin sa d'an janta ya kumayi ya had'e bakinsu saida ya d'an jima yana kissin d'inta kafin ya dubeta cikin d'an damuwa yace.
"Wai dan Allah Fatima mai yasa bakison zaman lafiya ne?
Na fad'a miki na kuma gaya miki zuwanki gida akwai matsala Abbi yace duk randa na,kaiki daga ranan kinyi ban kwana da duniya domin yanzu shirin da akayi akanki ta hanyar zuwa gidankune kawai zaiyi tasiri akanki dan haka nake so dan Allah kiyi hakuri ki rufamin asiri domin duk ranan da akace babu ke to ki tabbata nima zan biyoki domin kece mahad'ina.
Muje zuwa
Maman islam
[10/6, 8:13 AM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 39
........................cikin sanyi jiki Umar yace "wannan wane irin abune? Abubakar wane irin jagwalgwalo ne haka me Asma'u tanema ta rasa menene yaya baya mana da har zata dinga jifansa da sharri kala kala?"
"Nima ban saniba Umar amman dai abinda na fi zargi shine son zuciya ne da kuma son abin duniya wanda ya ke kai mutum ya baro, yanzu duniyar nan ta lalace Umar domin kowa idanun sa ya rufe so yake ko ta halin yaya sai yayi kud'i kaga wannan burin shi yake haukatamu"
"To wai su waye sauran da suka had'u da ita Asma'un har suke neman kassara rayuwar d'an uwanmu?"
"Kar ka tsawaita bincike Umar domin hakan bazai haifar da d'a mai idoba sannan kuma ina so in sanar da kai cewa kabi a hankali kuma kasani da kad'an kad'an yafi maka sanin ko waye domin sanin hakan lokaci d'aya zai iya zama ajalinka zaka iya tafiya wajen aikinka kuma bance kaje kayi ta tunani ba"
Cikin damuwa da tashin hankali Umar ya koma b'angaren sa har lokacin Rukaiyya tana inda ya barta, k'arasawa yayi ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta ya rik'a gam kafin yace "Ummu Ihan ko zaki iya fad'a min sauran mutanen dake tare da haj. Asma'u?"
Girgiza masa kai tayi sannan tace"a a ni babu wanda na tab'a gani tareda ita, abinda na sani kawai shine duk sanda taso magana da abokan aikin ta to zata d'auko wani k'warya ak'ark'ashin gadon ta mai d'auke da jan k'yalle da kuma bak'i da wasu tarkace wanda bana gane ko menene, sannan daga ta bayan madubin ta akwai wani abu wanda da shine take ganin duk wanda take so kuma taje duk,inda takeso asanda taso batareda ta fice anga fitar nata ba, sai dai Baffan Ihan ina so kasan cewa da akwai wani shak'ik'in d'an gidan nan da suke k'ulle k'ullensu tare"
Daga haka ta tashi tabar masa wajen batareda ta jira cewar saba, yana nan zaune kamar wanda aka dsa kusan mintuna sha biyar wayansa yayi k'ara batareda ya duba yad'aga "Ihsan ta shirya zasuje rugan yaya Tanimu" daga haka ya datse kiran batareda ya jira cewar saba,
Ruk'ayya ya k'walawa kira tana fitowa ya fad'a mata sak'on ta d'anyi jim cikin shakka yace "nima daga sama naji dan haka kawai kibisu da addu a"
Tace "wallahi Baffa ina matuk'ar tsoron fita dasu Abdulmajid domin wannan azzaluman kamar wanda ake sanar dasu duk sanda zasu fita sai sun sa an tafka babban asara"
"Karki damu ki barma Allah komai sai kiga ya duba mana"ajiyan zuciya ta sauke tace "to ai shike nan bari naje na fad'a mata" yace "yauwa Allah yai muku albarka ya kare minku daga dukkan sharri"
Amin tace tana ficewa daga d'akin.
"Baby yau zamuje rugan kawu Tanimu maza jeki shirya m" Abdulmajid ya fad'awa Fatima yana shigewa toilet, da gudu Fatima tayi d'akin ta cikin k'ank'anin lokaci tayi wanka ta shirya cikin riga da zani na atamfa tayi kyau sosai, sanda ta fito har shima ya gama shirinsa yana zaune cikin kujera yana faman danne dannen wayarsa.
K'arasowa tayi ta shige jikinsa tareda kwantar da kanta ak'irjinsa tace "baby na shirya" d'an shafa kanta yayi yace "to zafa mukai sati acan kije ki had'a kayanmu kuma har da Ihsan zamuje"
Cikin wani irin farin ciki tayi saman da gudu domin tana matuk'ar son rugar kawu Tanimu yana mata dad'in zama sosai tana shi'awar kiwo sosai ad'an zuwan da suketi kafin su dawo duka duk zuwa sai Abbi ya kawosu har umminta,
Binta yayi da kallo har sai data gama shigewa sannan ya d'auke idonsa tare da sakin murmushi, Allah yasani yana matuk'ar son Fatima da komanta mai ban shi'awa.
Bata jima da shigaba Ihsan ta iso gidan itama cikin shirinta dan haka Fatima tana saukowa suka fito parking space, har ta mik'a hannu da nufin amsar mukullin sai kuma tayi saurin janyewa tareda komawa gefan Abdulmajid wanda ya bita da kallon mamakin abinda ya hanata amsar car key d'in,
Ihsan ya mik'awa mukullin tareda fad'in "to ke amshi kijamu" cikin alamun tsoro tace "nifa yaya hannu na bai gama fad'awa ba" d'an murmushi ya saki kafin ya kira Idi draiver suka kama,hanya.
"Abu Fatima dan Allah ka maida ni k'asarmu ni wallahi garin nan ya isheni duk a tsorace nake gashi yanzun kullum na kwanta wasu irin mafarkai nake marasa dad'i"
Kallon ta yayi cikin murmushi kafin yace "ummu Fatima kenan duk kinbi kin sawa kanki damuwa akan wannan abun babufa abinda zai faru sai ikon Allah"
Cikin damuwa tace "dan Allah Abu Fatima ka maidani garinmu nagaji da nigeria babu dad'"
Sai da ya d'an dara domin maganarta ya bashi dariya kafin yace "to shikenan Ummu Fatima yanzun ki hak'ura har su Fatima su dawo sai na fara muku shiri har su Naseer ko"
Rungume shi tayi tareda sakar masa kiss sannan tace "na gode mijina.
Su Fatima kuwa ana kiran magrib suna tsayawa ak'ofar gidan kawu Tanimu wanda yake cike da mutane maza da mata domin kuwa shi d'in babban malamin da duk al 'ummar yankin suke matuk'ar ji dashi.
Aiwala Abdul yayi yabi su kawu masallaci yayin da su Fatima suma suna shiga alwalan sukayi suyi nasu sallar tare da sauran jama'ar dake cikin gidan.
Abdulmajid kuwa basu shigo gidanba sai da sukayi sallar isha sannan suka shigo da kawu Tanimu zuwa lokacin kuwa duk mutanen sun watse wanda sanadin zuwan sune yasa kawun nasu ya sallame su, banda hakabwasu har kwana suke a gidan .
Bayan sun ci abinci sun huta ne suka shiga har turakar kawu Tanimu domin gaida shi.
Yana zaune saman buzunsa yana lazumi Ihsan wacce bata tab'a zuwaba d'akin take k'arewa kallo tare da mamakin ganinshi k'al k'al wanda hakan yake nuni da cewa mamallakin d'akin yana da matukar tsafta.
Gefen sa wata katuwar kanta ce cike da litattafan addini kala kala sannan gefan kantar kuma turaruka ne irin na wuridi d'innan suma gasunan burjik sai da Ihsan tayi mamakin yawansu.
K'arasawa sukayi har gabansa suka durk'usa, idanunsa akansu ya aje carbin dayake ja agefen sa sannan ya dubesu cikin murmushi da farin cikin ganinsu musamman Ihsan wanda yau ne zuwanta na farko.
Cikin girmamawa suka gaidashi ya amsa cikin sakin fuska tareda tambayar su iyayen,su sukace duk suna lafiya suna gaida shi, sun d'an tab'a hira ka d'an kafin su nemi makwanci domin duk a gajiye suke
Maman islam
[10/7, 7:57 AM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 40
....................washe gari tunda suka idar da sallar asuba suka koma suka kwanta domin har lokacin gajiyar bata gama sakinsuba.
Sai dai kuma hayaniyar da tafara tashi sama sama bai barsu sun kwanta ba domin gidan haka yake indai akace anyi sallah zakuga mata da maza suna ta tururuwan kama layi.
To yauma hakan ne yakasan ce kafin kace me gidan ya kacame da hayaniyan jama'a hakan kuma ne yayi sanadin hana su Fatima komawa baccin kamar yanda suka so, sai faman juye juye sukeyi.
K'a'idar kawu Tanimu baya fara ganin mutane sai k'arfe tara na safe wanda inya fara baya rufewa sai d'ayan dare sannan kuma idan ya sallami mutane a daidai wannan lokacin yake nasa uzurin.
Yau kam bai wuce kai tsayeba sai da ya gaisa da 'ya'yan nasa kafin ya wuce d'akin saikar bak'insa yana fad'in "kai Abdulmajid idan kun gama karin kumallo saika zo tareda su da to ya amsa sannan ya juya ya fita Ihsan ma ficewa sukayi tare da Hanifa d'iyar kawu Tanimu ce wacce bata fi sakuwar Ihsan d'in ba,
Suna fita Abdul ya d'an matso kusa da Fatima yajata jikinsa tare da sakin ajiyar zuciya yace "gaskiya baby jiya kasa bacci nayi"
Zuba masa ido tayi kafin tayi sannan ta tambayeshi da idonta "me yasa?"
Nuna ta yayi yace "kece mana Fatima ada ina iya hak'urin rashinki na kwanaki biyun da kuke keda marigayiya amma yanzun nasani bazan taba iya rasakiba dan haka gaskiya nidai kisan yadda zakiyi dani domin bazan iya jurewaba"
Ya fad'a cikin sigar shagwab'a, dariya ta kwashe daahi sannan ta kwanta a jikinsa tana fad'in "to yanzun ya kakeso ayi?
"Kawai ki tashi mu d'an lalubi wani wajen na d'an rage zafi" ya fad'a yana kallon cikin idanunta, wanda ta zarosu gaba d'aya tana kallonsa da mamakin sa sannan tace
"Gaskiya badani za'ayi wannan fitsaran ba kai yanzu dan Allah idan nace na amince sai ka aikata wani abun anan?"
Yace "dan Allah d'an gwada koda wasa ki gani me zai hana yarinya kuma ma da zaki wani ce fitsara naga ai ba abin kunya nayiba halalina ma amsa" murmushi ta saki sannan tace "bada ni za ai wannan d'anyen aikinba"
Shima murmushin yayi tareda janta jikinsa yace "amma ai a bari na d'an rage zafi ko dan wallahi a mugun matse nake"
Kafin ma tayi wani yunk'uri ya had'e bakinsu yana sakar mata wani irin kiss wanda dole yasa ta mik'a kai batare data shiryawa hakan ba.
Lafiyayyen break first aka kawo musu harda soyayyen naman zabbi kamar ba ruga ba haka suka zage sukaci suka k'oshi sannan suka he amsa kiran da malam d'in yasa ayi musu.
Wannan karon ba a d'akinsa ya sauke suba a d'akin saukar bak'insa ne shi kansa Abdulmajid bai taba shiga d'akin ba dan haka sukayi matuk'ar mamakin had'uwar d'akin, wanda falon yaji wasy irin had'ad'd'un kuheru masu d'an karen kyau da burgewa zagaye suke da wani had'adden glass teble mai sufar kwai sannan ga wasu k'ofofi wanda a k'alla zasu kai guda uku sai wata k'arama wacce da alama k'ofar toilet ce atak'aice dai zasu iya wajen da d'an madaidaicin gidan da akayiwa kofar shago daga ta waje da cikin gidan malam d'in.
Cikin nutsuwa suka k'arasa gaban malam d'in sabuwar gaisuwa suka sake masa sannan ya nunawa Ihsan kwanukan daya gama kari yace taje dasu ciki, a hankali ta taahi ta tattare kayan tayi cikin da su sannan shi kuma ya maida hankalin shi kansu yace.
"Yauwa Abdulmajid duk da kasan cewar Abubakar yamin bayanin,abinda yake,faruwa daku zanso k'arin bayani dan kunsan masu karin magana sunce wak'a abakin mai ita yafi dad'i" batare da wani b'ata lokaci ba Abdulmajid yafad'a masa iya abinda ya sani sannan Fatima ma ta bashi labarin duk irin abinda take gani tareda mugayen mafarkan da idan tayisu suke zama gaske.
Sosai ya fahimci bayaninsu sannan yaja k'asa take gaban Abdulmajid ya b'aci dan bai tab'a sanin kawu Tanimu yana duba ba kuma ya sani duba ba abune mai kyau ba, amma sai baice komai ba.
Shikuwa kawu Tanima zane yafara yi akan k'asar yana gogewa sai da ya shafe kusan mintuna sha hud'u kafin ya nuna ma fatima wani glass fari kar mai masifar santsi yace ta mik'o masa yana karb'a ya d'orashi saman k'asar rufe ido yayi yana magana a zuciyarsa wanda su basa jin abinda yake cewa sannan ya bud'e idon ya d'an bugu glass d'in kad'an sai ga shi kuwa ya samu abinda yake nema,yace su dawo kusa dashi su gani, babu musu kuwa suka lek'a.
Take gaban Fatima yayi wata irin masifaffen tsoro ne ya kama Fatima da sauri ta fad'a jikin Abdulmajid cikin wata irin kid'ima cikin rawar baki tace "sh...shin wallahi shineee......
Muje zuwa
Maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*
FCWA
*Home of qualities and trusted writers of the nation*
https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17
_________________________
💧💦ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Daga marubuciyar
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 7
......................kusan abinda yafaru a hanyar zuwan su shine yasake faruwa da k'yar Abdul majid yakawo kansa gida.
Cikin kwana d'ayannan da sukayi har Fatima tayi wata irin rama tayi wujiga wujiga da ita, abin tausayi duk ta wani firgice.
Lokacin da suka isa gida ana kiran sallahr azhar Ummi tana kicin ta had'a abincin rana taga giftawar Fatima da sauri.
Daganin yanayinta babu nutsuwa atattare da ita,da sauri Ummi tak'arasa abinda take tabi 'yar tata, saidai sanda tashiga d'akinnata har ta tayar da sallah, dan haka itama ta juya dan gabatar da tata sallar.
Ab'angaren Abdul ma yana shiga b'angarensa wanka yafarayi agaggauce sannan yayi alwala ya wuce masallaci.
Yana dawowa daga masallaci direct wajen mammy ya wuce , suna dirning area ita da autarta suna cin abinci.
Mammy tabi d'annata da kallo tana amsa sallamar dayayi memma tayi masa sannu da zuwa tanafad'in "nidama nasan Fatima bazata iya sati guda abajoga yadai fad'ane kawai.
Kallonta Abdul yayi yana tambayar ta da ido, wai yaushe akayi hakan?
Memma tace sanda kuke shirin tafiya tace min ita tanason ku d'an kwana biyu acan bayan tafiyar ku kuma naga message d'inta wai zata lallab'aka har kuyi sati"
Murmushi yasaki har saida kyawawan hak'oransa suka bayyana memma tasaki baki tana kallon yayan nata wani mashahurin kyau yake yi aduk lokacin da zaiyi dariya.
Gaida mammy yayi yana dungure kan meema yace"duk kin d'aukemin hankali da d'an banzan surutunki ko uwata ban gaisarba.
Dariya memma tayi kafin tace "wai ina Fatimanne yaua naganka kai kad'ai koda gaske ka barota acan d'in?"
Itama mammy kallonsa take tajiran jin amsar da zaibata, "ban saniba suda kinga k'yaleni yunwa nakeji mammy zubomin abincin dan Allah"
Mammy tace "bangane baka saniba inakabaromin yarinya?"
Ta masa tambayar tana tura masa flat d'in abincin data zubo masa, saida yayi bismillah yafara cin abincin dan yunwa yakeji sosai Fatima bata bari sunyi karin kumalloba ta uzzura masa suka taho.
Duban mammy yayi yace "tana fat d'insu dan ko kari bata bari munyiba tace ita gida zata tafi"
Nan kuma ya kwashe duk abinda yafaru a hanya ya fad'awa mammy, bak'aramin girgiza tayi dajin wannan abinba tabbas duk ma wanda yake bin baya d'annata baizai denaba ya zama dole ta fad'ima Abbu dan tasan tabbas zai iya bada taimakon daya kamata.
Abangaren Fatima,kuwa saida tayi sallah sannan tayi wanka,dake sanda ta shigo gidan anriga da antada sallah.
Bayan ta shirya cikin wasu riga da sket 'ya kanti kalar blue mai duhu sunyiwa jjar fatarta kyau sosai.
A falo tasami Umminta tana cin Abinci kusa da ummin ta zauna tagaida ita sannan taja abincin yayinda ummin take tambayarta yanda ta barosu.
Tace "duk suna lafiya ummi tace agaidaku, ummi ta d'an k'ara kallon 'yar tata da kyau ganin yadda ta zuk'e lokaci d'aya tace
"Ciwo kikayi ne adaren jiya naga kin zuk'e?"
Ajiyar zuciya Fatima tayi kafin ta dubi ummin da idanunta da har sun,ciko da kwalla take abinda yafaru yafara dawo mata kamar yanzune abin yake faruwa babu 'yar b'oye b'oye tsakainta da umminta take ta kwashe duk abinda faru ta fad'awa ummin, wanda itama ummin bak'aramin girgizata abin yayiba karfa kuma wani abu yasami tilon 'yar tata dan tanada kusanci da Abdul majid?
Ai kusancin su ba aure bane kuma ko Abdul majid yace yanasin Fatima,bazata tab'a amincewa ba dan,abinda ta lura dashi duk wanda zai mu 'amalance shi koda da soyayyane sunan shi gawa.
Wannan kenan
Ab'angaren mutuminnan kuwa tsaye yake gaban gunkiyar nan yau idanunta har ya wuce rannan haka duk wani k'ofa najikinsa babu inda baya kwarar dajini.
D'ago wutar dakeci