Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
BY
MAMAN ISLAM
Page 35
.......................innalillahi wainna ilaihi raji un, shine abinda d'aid'aikun mutanen da sukaga faruwan abin suke maimaitawa,
Da gudu suka nufi motan da basuyi tsammanin zasu sami wani abu mai rai acikiba, da k'yar suka iya d'ago motar da ta kife suka juyata.
Innalillahi,wainna ilaihi raji un shine abinda masu k'arfin zuciyar cikinsu ke fad'a masu k'aramin zuciya kuwa tuni suka fara zubda hawayen tausayi da ganin irin mummunan abinda yafaru da wad'annan bayin Allahn.
Babu jima jami'an da wasu suka kira suka k'araso suka kwashesu akayi asbiti bajoga da su domin sunfi kusa da nan.
Ba k'aramin tada hankalin ahalinsu wannan had'arin yayiba sosai suka firgita dajin abinda yasamu yarannasu babu kamar Abbi wanda yakasa samun nutsuwa tareda tsoron abinda zai iya faruwa dasu.
Acan gidan Gwaggo Hafsatu kuwa sosai rigima ya b'alle tsakanin malam mijinta da wani bawan Allah wanda ban gane fuskarsa ba sakamakon yadda fusarsa yayi gaja gaja da ruwan hawaye.
Daga ganinsa kaga wanda yake cikin tsantsar damuwa da tashin hankali kamar ma wanda yake a firgice.
Tun kafin akaisu asbitin Yusra tace ga garinku nan abin kuma da ya matuk'ar gigita jama'ar yanka rago suka gani a wuyanta wanda basusan dalilin faruwarsa ba.
Absulmajid wanda da farko bai wani jigataba bayaga 'yar kurkurjewa dayayi amma ganin abinda yafaru da Yusra take numgashinsa ya d'auke ya sume awajen.
Koda aka samu Yusra ta farfad'o ta farfad'one a wani irin firgice dan da ife ife sakamakon firgicewar da tayi domin ita kad'aice taga faruwan komai kafin afkuwar had'arin.
Ummi wacce taci kuka har taji babu dad'i ganin yanayin da 'yarta ta farko ba k'aramin damuwa ya k'ara mataba domin tasan cewa dole akwai abinda ya faru.
"Umma dan Allah ki daina kukannan haka kar wani abun kuma yazo yasameki bafa su mutuba ance buguwane kuma sun farko" Husna ta fad'a tana share hawayen mahaifiyar ta cikin danne nata damuwar.
Cikin kuka tace"Husna ke yarinya ce bakisan halinda nake ciki bane baki san masifar dana wulla kaina aciki bane saboda masifar son abin duniya irin nawa wallahi Husna, na tsani kaina da duk wani ma mugun hali irin nawa, na sani cewa son zuciya babu abinda yake janyowa sai b'acin zuciya, nayi nadama, sannan dan Allah ina rok'onki kar ki tambayeni komai nida kaina,zan fad'a miki in lokacin yayi
[10/7, 5:05 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 36
....................koda su Ammar da Anty Rukaiyya suka shigo d'akin asume suka samu Husna ga kuma gawar haj. Asma'u da akayima yankan rago yashe akasa
Take jikin,anty Rukaiyya ya d'auki wani irin rawa tasaki wani razanannen ihu saiga ta ak'a sumammiya, sosai hankalin Ammar ya kuma tashi ya rasa yadda zaiyi dasu sai kawai yafashe da wani irin kuka mai masifar cin rai.
Lokacin da labarin rasuwar Yusra da kuma irin abinda ya sameta yafaru ba k'aramin tashin hankali iyayennata suka shigaba hatta alh. Sambo kasa daurewa yayi ya rika kukan rashin tilon 'yar tasa sosai.
Haj. Kulu kuwa kusan zaucewa tayi ta rik'a wasu irin surutai marasa ma'ana sosai tadawo abin tausayin da duk wanda ya dubeta sai yaji kamar ya zubar mata da hawaye.
Anan gidan su Abdulmaji aka had'a gawar Yusra da ta haj. Asma'u akayi jana'ezarsu akaikaisu makwancinsu na gaskiya, shikenan rayuwar dama duk wanda yayi da kyau to mai kyau zai gani insha Allahu.
Tunda tasamu ta farko take risgar wani irin kuka mai masifar tab'a zuciya takasa magana bata iya cewa komai banda kukan, sosai hankalin ummin ya tashi tayi rarrashin har tagaji ta zuba mata ido itama hawayen take na fargaba da tsoron abinda zai je ya dawo domin taji duk irin sambatin da Fatiman take anan tasan duk abinda yai sanadin faruwar hatsarin da sukayi.
Tsoro take na abinda zai iya faruwa da 'yar tata ta sani tabbas tunda yanzun babu Yusra to dolene tasayi yadin tashin hankali ta d'inka tasa ajikinta dan tasan babu makawa kan Fatima wad'annan shed'anin azzaluman zasu dawo.
Rushewa ta kuma yi da wani irin kuka jikinta na karkarwar tsoro bata tab'a dana sani da nadaman biyo mijin nata nigeria irin yauba bata tab'a sanin cewa 'yarta zata had'u da munanan k'addarori irin wannan ba, E mana mummunan k'addara irin wacce bata tab'a hangoma d'iyar tata ba wannan auren ya zamemata alak'ak'ai mazamo bara zana agareta da kuma 'yarta.
D'i Fatima ta tsaya da kukanta tare da kafe mahaifiyar tatada idanunta da suka k'ara wani irin girma saboda kukan da tasha ta k'oshi take itama jikinta ya d'auki rawan tayi saurin rungume mahaifiyar tata tareda fashewa da wani sabon kukan sannan cikin wani irin murya mai matuk'ar ban tausayi tace
"Ummi ki yafemin nasani nima mutuwa zanyi Ummi wallahi ba accedent d'in da mukayine yai sanadin ba yankata sukayi wannan matsafanne bakiga wuyantaba wallahi sune Ummi dama sanda zamu tafi saida Yusra tace min tayi mafarkin wani zaki yabita da wuk'a zai yankata wallahi Ummi kuma shine ya yankatan dan Allah ummi karku mai dani wannan gidan nima,kasheni zasuyi ta k'arashe da fashewa da wani irin kuka mai cin rai.
"Yazama dole ki koma" atsorace dukansu suka d'ago kai sunavkallon Abbi wanda ya shigo yanzun fuskar nan tashi babu alamun walwala ko kad'an atareda dashi.
Ya dubi Ummi cikin damuwa yace "ban tab'a tunanin baki da hankaliba Ummusalma sai yau, banyi tunanin cewa kema tunanin ki irin nabane, haba Ummu Fatima ke da zaki kwantar mata da hankali amma kece me biye mata kuna wannan shirman banzan?
To kisani tun wuri duk abinda zakiyi wallahi sai dai kiyi amma ki k'addara wannan auren babu mai rabashi,sai dai mutuwa"
Sai kuma ya maida kansa ga Fatima yace "ke kuma Fatima wallahi baki isa ki maidani tsohon banzaba nasani sarai ina sane da abinda nakeyi dan haka kar nasake jin kina wannan shashancin akan d'an uwanki, haba Fatima idan kika guji Abdulmajid amatsayin sa na d'an uwanki jininki wa kike tunanin zai rab'e shi haba Fatima karki manta shifa nakine kuma dakike tunanin bana sonki ne shiyasa na had'a wannan abun sam ba haka bane ni nasan dalilin dayasa nayi hakan kuma ki k'addara kowa da sanadinsa dan haka karki k'ara sawa ranki cewa akwai wanda ya isa ya cutar dake batareda amincewar Allahu ba"
Sosai ya dinga mata nasiha har saida ya fahimci jikinta yayi sanyi tana fahimtar abinda yake fad'a mata kuma tayi masa alk'awarin insha Allahu bazata k'ara d'aga hankalinta akan wannan ba kuma zata zage wajen taya d'an uwanta mijinta yak'ar duk wani mak'iyi nasu.
Sosai yaji dad'in yadda ta fahim ceshi, ya dafa kanta tareda sanya mata albarka sannan yaja hannun ummi wace itama jikinta yagama yin sanyi da bayanin mijinnata suka tafi duba Abdulmajid, wanda shima bai dad'e da farfad'awa ba.
A hankali suka tura k'ofar yana zaune saman gadon ya zuba tagumi da duka hannayensa k'aran bud'e k'ofar ne yasa yayi saurin d'ago kansa ya kafe Abbi da idanunsa wanda suka sauya kala.
Abbi ya k'araso kusa dashi tareda dafa kafad'arsa, ganin yanayinda yake sai baice komai ba sanin cewa idan yana cikin damuwa bai fiye maganba.
Kwantar da kansa yayi a damtsen hannun abu take wasu irin hawaye suka zubo masa wanda tunda wannan abun yake faruwa dashi hakan bai tab'a faruwa ba sai yau.
Kuka yayi mai yawan gaske kuka ne nabak'in ciki da takaicin abinda yake faruwa dashi kukane na tsantsar tashin hankalin rashin sanin wanda yake binsu da wannan masifar.
Sosai ya koka kafin Abbi yasoma rarrashinsa shima,nasiha yayi masa sosai tareda kwantar masa da hankali sannan ya fad'a masa cewa duk masi nemansa da sharri alfarmar annabi (S A W) sai asirinsu ya tonu,
Ranan sadakar uku aka sallamosu dukansu daga asbiti bak'aramin ramewa duka su biyun sukayiba darect gidansu Abbi yace draiver ya wuce dasu dan haka kai tsaye can d'in aka wuce dasu.
Suna komawa wanka Fatima tayi ta sanya wata doguwar riga mara nauyi sannan ta d'an had'a tea tasha saboda yunwar datake damunta, kai tsaye d'adakin Abdulmajid ta shiga d'ago kai yai ya zuba mata ido har ta k'araso kusa da shi ta d'an shafi fuskarshi, wani irin murmishi yasakar mata mai ciwo, tayi saurin fad'awa jikinsa tareda sakin kukan tausayin kansu sosai take kukan, shi kuwa kasa rarrashin ta yayi sai bayanta dayake d'an bubbugawa a hankali.
Sai da tayi kuka mai yawa kafin cikin wata irin murya mai mugun sanyi yace "kiyi hak'uri Fatima ki daina kukan haka bamu da yadda zamuyi kawai mu zuba ido muga sarautar Allah naso na sauwak'e miki sai dai Abbi da Daddy sun haneni da hakan sun tabbatar min da cewa matuk'ar na rabu da ke raina zai mummunan b'aci, Fatima INA SONKI ina miki son da bantab'a yiwa wata 'ya mace irinsaba Fatima tun kina 'yar ficiciyarki Allah ya jarabceni da tsantsar k'aunarki Fatima a yanzun ina rayuwane cikin firgici da tsoron kada na rasaki zan iya jurar kowane irin abu amma banda na rasaki Fatima shiyasa naso na sakeki har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana k'arshen wannan fitinar sai dai kash su Abbi sun takamin burki akan k'udirina, ya zanyi ya zanyi Fatima na sani dole wata rana tsoro da fargaban abinda zai iya faruwa dake ya iya zama sanadin rayuwata"
Ya k'arasa maganar tareda zubowar wasu irin zafafan hawaye, da sauri ta fad'a jikinsa tareda fashewa da wani sabon kukan kuka take har tana shid'ewa taso ta nuna masa b'acin ranta akan furucinsa na wai zai rabu da ita akan wani banzan dalili mara tushe da makama taso ta nuna masa cewa duk runtsi duk wuya ruwa da iska tana tareda dashi sai dai ina kukan daya yariga yaci k'arfinta bazai bari ta iya furta masa komaiba
Maman islam ce
[10/7, 5:05 PM] Maman Islam: .+بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 37
.....................sun jima,gaba d'ayansu cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa kafin yasamu ya daure ya soma rarrashinta, sai dai takasa yin shiru sosai take tare da far gaba da wani irin tsoro na abinda zai iya samun su, sannan ta wani gefen ba k'aramin b'ata mata rai magan ganunsa sukayi ba wai zasu rabu abinfa ya bugeta da kyau.
Acan gidan su Yusra kuwa yau akeyinta domin alh. Munzali ne yaiwa gidan dirar mikiya cikin rashin nutsuwa da fitar hayyaci babu ko neman iso tunda ga bakin get yake kwala wa haj. Kulu kira.
Haj. Kulu wacce suke tareda mai gidannata suna dad'a jimanta rashin tilon 'yar tasune tajiyo muryan alh. Munzali yana mata wani irin kiran mafa rauta take zuciyar ta ya tsinke gabanta yayi wani irin fad'uwa innalillihi,wa,inna,ilaihi raji un shi takama maimaita wa domin dajin wannan kiran bana lafiya bane.
Shiko alh. Munzali sam bai kula da d'an uwannasa dake zaune yana kallonsa ba domin ko kad'an baya tareda nutsuwar sa kansa tsaye kan haj. Kulu yayi gadan gadan yana cewa.
"Wallahi Kulu bazan yardaba sai kin biyani 'yata dama saida na fad'a miki ki fita harkar duna ki fita harkar duna tunda yasha alwashi akan yarinyar nanan nasan sai ya cika burinsa, amma kika k'i ji to ga irinta nan ba rasa 'yata mafi soyuwa agareni ya fad'a" cikin fashewa da wani itin kuka sannan yaciga ba da cewa.
"Wallahi Kulu daza'a bani zab'i tsakanin Yusra da Faisal wanne zasu d'auke na gwamma ce su kashe Faisal su barni da Yusara ta haba Kulu me yasa zaki had'a hanya da boka Duna?"
Ya k'areshe maganar da tambaya cikin wani irin shashek'a, shi kam alh. Sambo dake nutse cikin kujera sam bai fahimci ina magan ganun k'anin masa suka dosaba bai fahimci wacce 'ya Munzali yake magana akai ba, hasalima,duk cikin yaransa babu 'ya mace duk mazane.
Cikin rufewar ido da b'acewar tunani haj. Kulu tace "tab' lallai Munzali ban tab'a sanin kai tabba taccen d'an iska bane sai yau inbanda abinka meye abin tada hankali akan 'yar shegenka ta mutu, bandama toshewar nasira irin naka ai wannan rufin asirinmu ne ni da kai"
"Wallahi Kulu akan Yusra zan iya fuskantar ko wane irin k'alu bale dan haka ni bana dana sanin kasancewar ta 'yata sannan bana shakkar yadda na sameta dan haka haj. Kulu kisa aranki kamar yadda kikasa na rasa 'yata kema,sai na sakaki a masifar da bakiyi tunanin shigantaba" cewar alh. Munzali.
Wani irin had'e rai haj. Kulu tayi kafin ta saki wata shu'umar dariya tace "Munzali kenan baka da hankali wallahi kuma baka da tunani sannan duk inda akace yaro tofa yaronne, maganar gaskiya Munzali ina son kasan cewa Yusra ba 'yarka bace kamar yadda takasance ba 'yar alh. Sambo bace"
Ara zane dukansu biyu suka kafeta da wani irin kallo ma8 cike da tsantsar mamaki da tsoro, wanda ita sam bata kula da hakan ba taci gabada cewa.
"Munzali nayi amfani da kaine kawai saboda wani muradina sannan na b'atar da tunaninka ne har insamu wannan nuri nawa saboda haka yanzu ina sonbkasan cewa daga kai har d'an uwanka babu mai 'ya acikin ku"
Cikin tsabar tashin hankali da gigita suka had'a baki wajen fad'in "to 'yar waye" sanadin wannan tambayr yasa haj. Kulu ta tuna tarefa suke da mai gidan nata kafin shigowar Munzali, take cikinta yayi wata irin masifaffen kartawa sabida tsantsar tashin,hankalin data shiga na b'aram b'aramar datayi agaban mai gidann nata shikenan dubu ta cika yai asirinta ya tonu, amma dake cikakiyar 'yar duniya ce sai tayi wani irin dakewa tace
" 'YAR GIDAN BOKA DUNA CE shine mahaifinta kuma boka duna ba kowa bane face abokinka alh. Sambo kuma mijin 'yar"....... bata kai ga fad'an abinda takeson cewar ba sukaga ta fad'i tana shure shure.
Da gudu sukayo kanta suna jijjiga ta sai dai ina dan atake tafara wani irin bak'in amai mai mugun kauri kamar kumfa suna kallo idanunta ya kafe ya juye take tace ga garinku nan.
Wani irin kuka alh. Sambo ya fashe dashi cikin tsantsar tashin hankali ya dubi alh. Munzali yace.
"Dama amana ta kukeci kai da ita har kake tunanin 'yar dana gama tabbatar wa tawace ta kace haba Munzali kaifa d'an uwana ne uwa d'aya uba d'aya shine har ka iya kake neman matar aurena?
Wane abokina ne Duna nasan cewa duk abokaina babu wanda baka saniba wanne mai wannan sunan da nansan dashiba cikin kuka Munzali yace.
"Kayi hak'uri yaya wanda baka zata ko tsammani ba shine DUNA kuma ko na sanar da kai babu abinda hakan zai haifar maka sai tsantsar bak'in ciki da tashin hankali wanda hakan zai iya zama sanadin rayuwarka abinda zan iya cewa guda d'aya shine wanda kake zargin bq shi bane wanda zuciyar ka ta hasko maka bai da alak'a da ha hakan wanda dai nace baka zataba d'innan shine duna" daga haka Munzali ya b'ace b'at kamar wani aljani.
Sulalewa yayi a wajen ya zauna tareda fashewa da wani irin kuka yace "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI AKALIFNI KHAIRAN MINHA LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN ALLAHUMA LA SAHLA ILLAH MA JI ALTAHU SAHLAN WA ANTA TAJ ALUL HAZNA IZA SHI ITA SAHLA" haka yai ta kamo addu'o'i yana yi kafin ya d'an samu nutsuwa ya mik'e yai waje.
Tun rasuwar Yusra Fatima bata k'ara yarda ta kwana ad'akinta domin duk lokacin data kad'aice saita ga kamar ana gilmawa musamman ta b'angaren Yusra shiya sa indai akace magrib ya kawo to Fatima bata da kwanciyar hankali har sai taga dawowar Abdulmajid wanda inya dawo bata barinsa ya sake domin duk inda yasanya k'afarsa yana d'aukewa zata maida nata hakan ya haifar musu da wani irin shak'uwa.
Yanzu haka zaune suke a falonsa ya d'an shafa fuskarta cikin yanayi na d'an tsokana yace "baby d'an d'auko min ruwa a falon k'asa na manta na nan ya k'are kuma ban d'auko nasaba"
Wani irin kallo Fatima ta masa tareda shigewa jikinsa tace "dan Allah yaya kayi hak'uri wallahi nidai tsoro nakeji sai dai muje tare na d'auko maka" kallonta ya kumayi tare da d'aure fuska yace "bari ni naje na d'auko sai ki jirani anan" ya fad'a yana mik'ewa dan da gaske k'ishin yakeji kuma babu anan d'in tana ganin ya tashi itama zumbur ta mik'e ta ruk'o hannunsa tace "muje to na rakaka"
Yace" bama sai kin rakaniba ni zan iya d'aukowa da kaina" yafad'a yana sakin wani b'oyayyen murmushi dan duk yagama gano tsantsar tsoron da ya bayyana akan fukanta.
"Dan Allah yaya muje na rakaka in kabar ni anan kasheni zasuyi plsss" ta fad'a tareda fashewa da kuka yad'an dubeta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya durk'usa agabanta yace "to hau na goyaki babu musu kuwa ta d'ane bayansa suka sauka.
Sosai alh. Yusif ya jajantawa aminin nasa wannan gagarumin rashin da akayi masa duka duka tsiran Haj. Kulu da Yusra kwanaki hud'une kacal,
Sosai alh. Sambo ya koma wani iri ko cikakken magana vaya iyawa gashi ya kasa fad'awa kowa abinda ya faru shi kad'ai yake tacin abinsa a zuciyarsa.
Sosai alh. Umar ya tsorata da abinda Rukayyan take fad'a masa hankalinsa yayi mummunan tashi sai yanzu yagano dalilin da yasa Abubakar ya hana yaya Rudwan dawowa ashe da sukaga takasa kawo musu jinin d'an uwansa shine sukayi amfani da jininta "hakan yayi" yafad'a cik8n wani irin b'acin rai sannan ya mik'e ya nufi b'angaren d'an uwan san Abbi kenan
Taku maman islam
[10/8, 9:08 AM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 41
..................jikin tane ya d'auki wani irin rawa tashige jikin Abdulmaji ta rik'e shi k'am tareda fashewa da wani irin rawa tace "yaya wallahi shine ya kashe Yusra