Chapter 18 Reading ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM HN Novels

ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM

Author :  MAMAN ISLAM Category :  KDP NOVELS

Chapter   18 / 20

51K to 54K   out of 58.1K words

kicin am redy"






Had'e rai tayi tace "nidai gaskiya yunwa nakeji kuma yau kwakwan manja nake shi'awa" ido ya zaro yace "baby a ina kuma zamu samu kwakwar manja yanzun dan Allah ki,canja wani abun amma wannan ai kin had'ani da aiki"





Kuka tasa masa tace "ni wallahi shi nakeso kuma shi zanci kuma tare zamu tafi siya" ganin tana kuka yasa duk ya gigice yace "naji naji yanzun bari na d'an dafa miki ko indomie ne ki faraci sai muje ko?"




Tubure masa tayi tace ina sam ita bazataci komai ba sai wannan kwakwan, haka suka ya biye mata suka faki idon iyayen nasu suka fice dake an hanasu fita harda jami an tsaro aka saka musu masu kula dasu dan haka duk motocinsu sai da aka nuna musu akace idan d'aya daga cikin motocin zai fita su lek'a suga wanda yake ciki, hakan da sukayi yasa Abdulmajid yayi ordern sabon mota batare da sanin kowa ba tanan suke fitansu insun so kuma,har office bai fasa zuwaba.






Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: 💦💧ZATO NE 💧💦
Na
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WIRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
_________________________
☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀️
_________________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM


Page 51
............dakallo dukan su suka bi Daddy suna jiran amsar da zai bawa Abdulmajid yayin da shi kuma Daddyn ya kafe Abdumajid d'in da wani fitinannen kallo zuciyansa na wani irin bugu, shi tunani yake ma wace Hauwa a ina take meye had'insa da ita shi kam iya saninsa da mai irin wannan sunan tun shud'ewar wani zamani ne wanda babu alamun wanzuwar su Abdulmajid a wannan duniyar dan haka ma babu wata,hauwa ayanzun dan ko uwar Abdulmajid bata san da zaman wata Hauwa ba har rana irin tayau kuwa

Dan haka yake tantama ba waccen Hauwan ce Abdulmajid yake magana akaiba amma duk da haka sai ya daure yace masa



"Kai wacece haka dakame min magana akanta ban gane inda tambayar ka ya dosaba ni banda sani akan mai irin,wannan sunan inbaya ga Jidda d'iyar k'anwata Hafsatu"




Sosai Abdulmajid ya kafe daddyn nasa da ido yana kallonsa tareda auna maganarsa a mizani kafin yace "Daddy wanda yasace mu yace d'aukar fansan ran Hauwa yake yace yana maka haka ne,dan ya rama abinda kayiwa masoyiyarsa Hauwa wanda hakan yazamo silan barinta duniya yace duk duniya babu wanda yakaisa san Hauwa amma ya hak'ura yabar maka saboda sonda take maka amma ka k'ita ka wulak'anta ta har sai da hakan yai sanadin data kamu da ciwon zuciya k'arshe kuma tazo ta rasa ranta duk a dalilinka kuma yace yana da alak'a ta jini da Hauwa, dan haka kawai daddy ka fad'amin wacece Hauwa ni kuma na baka labarin abinda zai baka mamaki da kuma asalin wanda yake haifar mana da tashin hankali acikin zuriyarmu"





Wani masifaffen kallo daddy yake,bin Abdulmajid dashi l, zuciyarsa yana wani irin bugu fat fat fat, sosai yake mamakin abun dan shi dai a iya sanin sa bashi da wata Hawwa bayaga wacce yatab'a soyayya da ita shekaru kusan talatin da bakwai baya, wanda suka rabu sanadin had'uwar sa da maman Abdulmajid d'in daga nan bai kuma sanin komai akantaba sai labarin rasuwar ta wanda yayan sane Tanimu da kansa ya bashi labarin rasuwar, to wai waye wannan mai d'aukar fansar tunda bai san wasu dangi nataba dake dama wajen kakar ta take zaune a wancen lokacin.





Duk tsit akayi ana kallon daddy wanda ya lula wata duniyar mai nisa yayin da Abdulmajid yake fatan ace duk shiri ne na azzalumi Tanimu yayin da shi kuma,daddyn ya matsantawa kansa da son gano waye wannan wanda yake azabtar da ruhi da gangar jikinsu ta hanyar hanasu nutsuwa da samun kwanciyar hankali, yayin da yaya Ridwan ya jafe d'an uwan nasa da idi shima ya tuno Hauwa da yadda suka rik'a tura masa ita lokacin har ya amince zai aureta sai kuma mahaigiyar Abdulmajid ta bayyana wanda ya rufe idinsa yace nan duniya bashi da matar da ta wuce ta shidama bawai yana son Hauwa bane zai aureta ne saboda nacinta da kuma na 'yan uwansa.




Abbi yace "duk bama wannan ba yanzun dai abu mafi muhimmanci shine,mu nemi hanyar dazamu ceto Badamasi dan na tabbatar wannan la anannen mutumin da wannan shegiya kafurar aljanar bazasu tab'a k'yale shiba domin ba k'aramin lalata musu gagarumin shirinsu yayiba da har ya raboku da can, sannan kuma yaya babu wani b'oyayya ba kowa bane yake wannan aikin face yaya Tanimu kuma,ina mai tabbatar maka ba akan wata Hauwa yake aikata hakan ba kawai dai yana nuna mana 'yan ubanci ne kasancewar mu kowa mamarsa daban"



Ba daddy ba hatta Amma saida tayi suman zaune dajin abinda Abbi yace saidai kuma tasan halin d'anta sarai duk abinda zaiyi yanayinsa ne da lissafi tasan tunda yace haka to hakanne kuwa in ko hakane Tanimu baiwa kansa adalciba kuma kansa ya cuta basuba azahiri kuma cikin sanyi tace,



"In ko hakane Tanimu bai kyautaba yanzun fisabilillahi yarasa wanda zai cutar sai d'an uwansa jininsa amma kuwa baiyi wayoba wallahi Allah ya ganar dashi idan zai gane" ta fad'a cikin k'unar rai somin abin ya mata ciwo sosai ana haka saiga mijin gwaggo Hafsatu yafad'o d'akin a burkice cikin tsantsar tashin hankali yana fad'in na shiga uku na shiga uku na shiga ukuuuuuuuuuuuuu








Kumin afuwa wllh zazzabine yamin kamun kazar kuku


Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*






💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 47


.......shiko Badamasi kuwa yana ganin anbar k'ofa a bud'e ga kuma kawu Tanimu yakama baccin asara yasa ya lallab'a sad'ab sad'ab ya shiga suna zaune kamar ko yaushi yadai jikin na Fatima da d'an dama dama suna ganinsa farin ciki ya kamasu yayin dayai saurin d'ora hannunsa saman lifs d'insa dan kar suyi magana, yayi musu alamar su taho da sand'a, hakan kuwa akayi ya kama hannun Fatima suka fice cikin sauri.






Cikin tsabar mamaki suke kallon badamasi bayan sun fito wajen domin jejin Allah suka tsunci kansu babu gida gaba babu gida baya, to yaushe hakan yafaru dan a iya saninsu a cikin gidan kawu Tanimu aka kullesu ad'akinsa na saukar bak'i to ina gidan ya shiga, gane hakanne yasa Badamasi yace





"Kunga ku wuce mutafi yanzun ba lokacin damuwa bane kuma,dama aikin malam,rufa idone yanzun zaku ganku a muhalli mai kyau da zaran shiri ya rushe sai kuga ashe kango ne kuzo muje kafin Gaza ta gane da zaran munfita anan akwai shirin dana mata bazata ganmuba" daga haka ya rumtuma da gudu, ganin haka yasa Abdulmajid yayi saurin tsugunawa Fatima ta haye bayansa suka kwasa da mugun gudu.






Tun suna gudun a dad'in rai har suka soma sarewa domin saida suka shafe cikakken awa biyu kafin su d'an sasara suka kama tafiya da sauri ba k'aramin gajiya Abdulmajid yayiba amma sam hakan bai dameshiba ya gwammace shi ya wahala akan ace Fatima ta wahala.





Saida sukaje wata ruga wacce k'ananun gari biyune tsakaninsu da rugan Tanimu kafin Badamasi ya k'arasa jikin wani k'aramin gida da alama gidansa ne yasa mukulli ya bud'e suka shiga sosai suka sha,mamakin ganin komai,fes da alama,yana amfani dasu akai akai.






Ya shigar dasu wani d'aki k'aton gaske wanda yame mamaye da carpet gefansa kuma,katuwar katiface suka zube saman katifar suna maida numfashin wahala yayin da sukaga Badamasi ko ajikinsa da alama ya saba da irin wannan azababben guje gujen.





"Ga abinci kuci sannan ga toilet nan kuje kuyi wanka ku huta zuwa gobe zanje na duba na gani inda dama zamu wuce a goben inbabu dama,kuma dole,sai kun k'ara hakuri domin sai komai ya lafa dan badan na samu nayi wa Gaza gagarumin ta adin da ayanzun bincikenta zai koma kan wanda ya mata b'arnane kuma,idan na sake,na zauna anan zatayi saurin ganoni dan haka zan koma,can wajen su akwai komai kicin na buk'ata akwai gas kudafa duk abinda kuke so, sannan akwai sababbin dogon riga da jallabiyu acikin d'ayan d'akin kushiga duk inda kukeso na yarje muku"




Sosai suka sha godiya sannan ya juya ya fita ya datsesu da mukulli kamar yadda gidan yake tun kafin shigarsu.







Cikin sauri Abbi ya fito ya samu Ummi dake zaune saman duguwar kujera duk ta wani fige ta lalace tsabar damuwar datasakawa ranta.





Zama yai kusa da ita ya dafe kanta yana kallonta cikin damuwar yanayin datake neman jefa kanta aciki yace "yanzun ke dan Allah ummu Fatima bazaki cire damuwar arankiba gashi ductor yace kina neman kamuwa da hawan jini?"





Wani irin murmushi tasaki mai ciwo tace "dolene na damu Abu Fatima kana ganifa har yau babu wani labari"






"Hmm waya fad'a miki ai ki kwantar da hankalinki idan wannan ne ki kwantar da hankalinki Fatimanki tana nan a hanya ta kusa dawowa dan Allah ki kwantar min da hankalinki"




Batare data iya tace komai ba ta tashi tabar masa wajen, shima ta wajensa ya fad'a mata hakane dan ya kwantar mata da hankali amma babu wani labari duk wata hanya da yake tunanin ganin haske ta kulle.






Bayan fitar Badamasi daga gidan direct mota ya shiga ya koma can gidan domin tafiyar da sukayi ba d'an kad'an bane yana zuwa ya sami kwalba ya karkarce jikinsa sannan ya fad'i a wajen kamar wanda wani mumminan abu yafaru da shi







Yana fita daga gidan Fatima fashe da kuka tace "nagaji wallahi yau kusan wata biyu muna gark'ame sai kace masu laifi ko laifi mukayi iyaka horon da zamu samu kenan"





Ta k'arasa cikin fashewa da wani sabon kukan shi tsabar yana cikin tsantsar damuwa bai iya yace mata komaiba kawai yajata jikinsa ya rungume tsantsan yana sakin wani zazzafan ajiyar zuciya.






Hayaniyar mutane ne ya tada kawu Tanimu wajen k'arfe takwas na safe wanda ko sallar asuba bai samu yayi ba wanda dama inta wuce shikenan baya bin takanta.




Abinda ya gani ba k'aramin d'aga masa hankali yayiba domin tashin farko da ya fito k'ofar da yagani a hangame ya antaya ciki,






Take cikinsa yayi wata ir8n juyawa sakamakon ganin babu kowa ad'akin d'akin shikenan asirinsa ya tonu kwanansa kuma yana gab da k'arewa





Zafi kan zafi ga bala in da zai fuskanta a wajen gaza ga kuma mummunan tonon asirin da da wad'annan la'anannun yaran zasuyi masa wannan wane irin bala i ne






Muje zuwa


Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*_______________________________________*



💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM



Page 52
..................duk suka bishi da kallon mamaki da tsoro domin jikinsa a wani irin kwaile yake kamar wanda aka kwarawa ruwan zafi jikinsa haka yayi.



Wani irin wahalallen nishi yake tareda sakin wani irin kuka mai ban tausayi yana fad'in "na cuci kaina na lalata gobena ni tawa ta k'are shikenan tawa ta k'are bani bane banyi da nufiba banyi da niyyaba ki yafemin matata kiyafe min Hafsatu na cutar dake na gurb'ata yardan da kikayimin wayyo Allah na shiga uku ba kowa yajamin ba face tsinanne la'ananne Tanimu"




Yadire tareda fashe da wani irin masifaffen kuka wanda kana gani zaka gane Halinda yake ciki na azaba sosai yake kukan kamar zai had'iyi zuciyansa.




"Tanimu?""
Dukan su suka had'a baki wajen fad'i tareda al'ajabin shed'anci irin na Tanimun basu k'ara shiga mamaki ba saida Fatima tace "muma shine ya sacemu ya dinga gana mana azaba k'arshema,guba ya zubo mana wai muci mu mutu yabawa gunkinsu jininmu sannan ya aikowa da iyayenmu k'ashinmu"




Fashewa daddy yai da kuka saboda takaicin bak'in abubuwan dayake ji yayin da Abbi yace "babu ko abu guda dayaban mamaki game da halin yaya Tanimu domin najima da sanin cewa shi mugun makwad'aici ne akan abun duniya babu abinda bazaiyiba shine sila kuma sanadin faruwar komai amma ku saurari malam Sule shinzaisan komai" Abbi ya fad'a yana nuna mijin gwaggo Hafsatu.




Agalabaice yasoma cewa "kamar yadda na fad'a tunda farko cewa Tanimu gawurtaccen matsafine kuma mugu azzalumi bayada aiki sai cutar al'umma duk wanda yasan zai samu wani cigaba a tattare dashi koda masifa koda bala i sai yajashi cikin qungiyarsu wanda wata bak'a kuma shed'aniya kuma k'ungurmar kafurar aljana take jagoranta wanda itama da hadimace ga wani mugun matsafi washi DUMB'URU daga baya bayan tagama sace duk wani surrukan tsafinsa sai tayi masa tawaye take son had'a qungiya nata na k'ashin kanta, kamar yadda na fad'a tundaga farko cewa Tanimu ya lalata rayuwan mutane da dama kuma ya gurb'ata hallayansu ni d'innan ina d'aya daga cikinsu kuma muna da yawa 'yan cikin wannan familyn atareda shi sannan kuma duk wanda ya mutu shine sila yana aikata munanan aiyukansa ne dan son zuciyarsa sannan ya tabbatar mana da cewa alh. Yuseef shine shugaban qungiyar amma baya so asan yana harkar tsafi saboda kar hakan ya tab'a martaba da darajarsa, daga farko mun yarda da abinda ya fad'a mana musamman idan mukayi duba da irin tarin dukiyar da ubangiji ya yassare maka, sai daga baya nagane cewa duk abunda yake fad'a k'aryane kuma yayi hakane dan yad'a manufarsa akanmu da yadda yake amfani damu wajen cimma manufarsa sai daya maidani qasurgumin bokan da duk yakin sukeji dashi wanda haka ya mantar dani duk wani hakki da nauyi na ubangijina dake kaina"



Nufasawa yayi yana maida numfashi suna kallo jikinsa ya cigaba da kwaikewa kamar wanda akewa d'aya irin na k'unan nan ihu yake iya k'arfinsa yana neman taimakonsu amma dukansu babu wanda zai iya nasa wani abu saboda kwatata babu wajen kamawa ajikinsa duk ya sale, Abbi ne yayi k'arfin halin fara tofa masa addu'o'i kafin ya daina wannan barbarwar,





Saida yasamu sassau kafin yaci gaba da cewa "wanda yai nasarar fara jefawa acikin mummunar hark'allar tasa shine MUNZALI k'anin Sambo abokin alh. Yuseef a sanadin haka suka had'e kai sukayi ta zaluntar sa har suka haifo masa YUSRA wanda shi Munzali yasan d'iyarsa ce kuma yasan cewa matuk'ar Abdulmajid ya aureta to Tanimu bazai barta da raiba shine ya ari bakin uban rik'onsa yazo yayi yanda yaga dama dan afasa auren yayin da kuma yakasance ita haj. Kulu bata da bokan dayake mata gagarumin aikin datake samun nasara sama dani shine fa nayi yanda nayi har akayi auren ashirina na d'aukar fansar abinda Munzali yayi min na rabani da tilon 'yata wadda ita kad'ai Allah ya bani a duniya akan idona Munzali yayi mata yankan rago bisa umarnin Tanimu duk dayasan cewa ina d'a daga hadimansa amma wai danya cigaba da saka rud'ani azuk'atanku yasa akayiwa 'yata haka shine ni kuma na nace ayi auren Yusra da Abdul majid na rik'a zuga iyayenta har akayi hakan sannan fa kuma sai abin yabar hannuna sakamakon GAZA tana son jinin Yusra wanda zatayi wani abu na mussaman dashi shine itama,tayi mata yankan rago akan idona,kuma akan idon ubanta wanda savoda son zuciya irin nasa yake neman,fansa akaina shinefa GAZA tasako shi cikin aikinta akan zata taimakeshi akaina yanzun dai intakaice muku fad'an na kai da kaine sukeyi atsakaninsu domin mallakar wani kambu na DUMB'URU shugaban mu duka wanda yak'i bata damar hakan yanzu zancen danake muku suna can suna,fafata yak'i tsakaninsu akan wannan kambun sannan kuma ta gefe guda ga wata rigimar ta b'ullo wanda Badamasi ya haifar na tabbata GAZA bazata barshiba"


Kafin yakai k'arahen labarin matan wajen kuka suke sosai babu kamar gwaggo Hafsatu da har take jin kamar zuciyarta zai fashe dan tsabar takaici da k'yar Abbi yace "kace kuna da yawa kamar ku da su waye Tanimu ya saye imanin na ku?






Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*




💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 50



..............yauma har suka fice babu wanda yasani saida yaje yafara nema mata kwakwar manjan sannan suka biya gidab cin abinci yaci ya k'oshi tana zaune tana kallonshi ita yanzun bata iyacin abinci sai kuma abinda suka fara horuwa da cinsa alokacin da suke gidan yarin kawu Tanimu wanda badamasi ya kai musu wato garin kwaki a lokacin kafin Abdulmajid yasan cikine da ita har mamakin yadda take zagewa taci ta k'oshi yake bayan zai iya cewa bata tab'a ganinsa ba sai ranar.






Suna cikin tafiya ta hango mai agwaluma tace ya tsaya ya saya mata nan ma saida suka siya babban leda aka cika musu, sun d'an yi gaba kad'an taga mai awara tace shi zataci, intak'aitavmuku kafin sukai gida siyayyar da sukayi ya wuce misali.




Suna zuwa gida ta baje kayanta tayi zaman dirshan takan awaran tafara sannan tace yadafa tama kwakwar yasa attaruhu da albasa yasaka manja da maggi sannan karyasaka mata kori yasa tafarnuwa kad'an, murmushi yayi baice komai ba yashiga kicin d'in yafara wanke kwakwar sannan ya had'a attaruhu da albasan ya jajjaga ya had'a kayan duk datace ya kunna gas ya d'ora ya koma gefe dan yasan ko ya koma falon cewa zatyi yabar mata abu zai k'one.





Ita ko duk tarkacen da suka siyo babu wanda bataci da yawa ba dan rabonta da abinci,irin haka tun kafin su tafi gidan yarin Kawu tanimu tana zaune ta jiyo k'amshin kwakwa tace ya kawo mata haka sannan ya dafa mata indomien yazun taji tana son ci haka dai ranan ya wuni ma bautan Fatima ko kad'an bata barshi ya hutaba shi kuma bai nuna mata gajiyansa ba






Misalin tara da rabi na dare yashigo d'akinta fitowarta kenan,a wanka tana d'aure da tawul wanda ta saukeshi a k'uginta batayi tunanin zai shigoba shiyasa bata damu data rufe jikintaba ihu tasaka lokacin data ga shigowarsa da sauri ta nemi hijab

18 / 20