Chapter 13 Reading ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM HN Novels

ZATO NE Lokacin da Gaskiya Ta Bayyana by MAMAN ISLAM

Author :  MAMAN ISLAM Category :  KDP NOVELS

Chapter   13 / 20

36K to 39K   out of 58.1K words

BY
MAMAN ISLAM

Page 31


................,,kallonta yake da mamakin abinda ya d'ago nata hankali haka, sam bata kula da shiba domin idanta yariga da yagama rufewa.



A hankali yataso yak'araso yackamota jikinsa tuni ya manta da abinda yafaru ganin halinda take ciki.


K'ok'arin k'wacewa takeyi yayi saurin rungumeta tsamtsam a jikinsa amma hakan bai hanata fad'in abinda takeson fad'an ba.





"Abdulmajid dan Allah dan Allah ka temakeni dan Allah tak'arasa cikin sakin matsanancin kuka mai k'arfin gaske,





A rud'e yace "me kikeso Fatima me yake damunki meya tsorataki haka Fatima?"
Ya tambaya yana jijjigata dan ganin kamar bata hayyacinta.




Cikin wani irin matsanancin tashin hankali tace "kaine Abdukmajid kaine bana sonka bana son aurenka domin babu komai acikinsa sai tsoro da fargaba da tashin hankali




"Ke" ya buga mata tsawan da saida ta girgiza cikin wani irin bak'in ciki da takaicin maganganunta yaca "bana ciki da iskanci da rainin hankali, har nine Fatima kike kallon tsabar idona kike fad'ama duk maganar da kikaga dama to Fatima duk abinda kike tunanin zakiyi saidai kiyi amma kisa ranki kamar yadda nafad'a miki nidake mutu karaba aurena dake auren zobene ba saki bayaji" daga haka ya tureta da mugun k'arfi yayi band'aki cikin tsautsayi tafad'a kan hannunta har saida yayi k'ara, tasaki k'aran azaba amma ko kallonta baiyiba bare tasa ran zai kula yaga abinda yayi mata.





Kuka tafashs dashi tana kallon hannun dayake mata wani mugun zafi ta fashe da kukan tausayin kanta wani irin k'unci takeji har wani d'aci d'aci takeji mak'ogoronta.





Ta jima awajen tana kuka har yai wanka ya fice yabarta anan cikin wani irin fushin dabata tab'a sanin yana dashiba sai ranar.




Sai datai kwana uku bata sanyashi a idanuntaba zuwa lokacin kuwa hannun yayi mugun kumburi har wani k'yalli yake ga wani irin azababben ciwo da yake mata babu yadda Yusra batayiba akan suje a duba hannun tayi mursisi tak'i yarda aduba hannun wanda tasan cewa babu tantama karyewa tayi.





Hatta Yusran ma ta daina kulata tun safe take murk'ususu a gadonta ciwo ya isheta kuka kuwa bata san iya yawan wanda tayiba daga safen zuwa yanzu yunwane ya tasheta wanda duk abinda ta zuba acikin frij d'inta ya k'are dan haka ta sauko dan samawa kanta abinda zata zubawa cikinta.




Ta gama saukowa idanunta sukafad'a kansa yana zaune saman kujera me zaman mutum d'aya da computer sa saman cinyarsa yana faman aiki,




Motsinta ne yasa ya d'an d'ago kansa domin yayi tunanin Yusra ce datace bari taje tayi wanka bak'aramin fad'uwq gabansa yayiba ganin k'yallin da hannunta yakeyi wanda ta tallafoshi da d'aya hannun mai lafiyan,



A hankali ya mik'e ya isa kusa da ita yakai hannu da nufin kamo nata sai tayi saurin janyewa taeda watsa masa wani mugun kallo tareda dosan hanyar kicin tana share hawayen daya gangaro mata.





Ji yai kamar ya barta amma kuma ganin irin kumburin da hannun yayi sai hankalinta yakasa kwanciya, ficewa yayi batareda ya kuma bi ta kantaba.




.da kyar tasamu ta iya dafa indomie taci anan kicin d'in ta cinye bata iya wanke kayanba saboda d'ayan hannun babu lafiya.





Muje zuwa


Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*




💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 32


................ta fito daga kicin d'in kenan shi kuma zai shiga, sukayi karo, da sauri ta janye duk da cewa sai da ya d'an dunguri hannun kuma taji zafi amma sai ta dake tana k'ok'arin wuce shi yai bala'in d'aure fuska ya rik'ota.




Take hawayen data ke ta danne wa ya kama zubo mata bai saurari kukantaba yajata har falon inda mai gyaran daya kira yake har gabansa ya kaita ya zaunar sannan ya tsaya akanta kamar wani dogari.





A hankali taji yana cewa "gatanan bugewa ne tayi yau kwana uku bansan abun yakai hakaba"




Mai gyaran yakai hannu da nufin kamo hannun nata ta yi saurin jan yewa tana kallon sa da idanun ta da suke cike tab da hawaye tace "dan Allah malam kayi hak'uri wallahi zafi yake min sosai kuma dama baya bari nayi bacci dan Allah kar ka fama min.




Cikin tausaya mata mai gyaran yace "kiyi hak'uri kibari a duba miki dole sai kin daure kinga ya riga da yayi tsami"



Batare da tace komai ba tafara k'ok'arin tashi Abdulmajid yai saurin tsugunawa yasa ta ajikinsa yana kallon cikin idonta sai dai bai ce mata komai ba domin har lokacin yana jin haushin abinda tayi masan.




Da ido yayi ma mai gyaran alama, bata yi aune ba taji ya damk'i hannun da mugun k'arfi take tayi wata irin zabura sai kuma ta shid'e, sao data d'an d'ebi kusan 3 munute kafin ta zunduma wani gigitaccen ihu wanda yai sanadin fitowar Yusra a d'aki da mugun gudu.




Ganin abindaa yake faruwa sai data taya Fatima zubda hawaye dama tasan za'ayi haka domin hannun ya riga yayi tsami,




Duk wani k'ok'arin ta na son k'wacewa a hannunsa abin ya gagara domin sai da aka gama gyaran tsab kafin yasake ta ta kwanta awajen tana maida numfashin wahala.




"Tsagewar k'ashine tayi gashi kuma wajen yayi tsami shi yasa ya d'an bata wahala" yana shafa mata magani a wajen sannan yasa bandge ya d'aure hannun tamau
Tare suka fita da mai gyaran ya sallame shi.




Sannan ya dawo tana inda ya barta sai juya kan wahala take tana mai da numfashi, sosai yake tausaya mata, amma bai bari hakan ya nuna a fuskarsa ba yasa hannu ya cicib'eta yayi d'akinta da ita.




Allah sarki Fatima sarkin tsabta amma d'akinta ko sharan kirki babu, saman sofa ya kwantar da ita ya d'an karka d'e mata gadon sannan ya shiga ban d'aki ya had'a ruwa mai d'umi, ya dawo ya sunkuce ta sai da ya wanketa tas ya dawo da ita ya sauya mata kaya yabata magani tasha ganin jikinya ya d'auki zafin zazzab'i sannan yaja mata bargo ya rufeta ya d'an k'ara k'arfin acn yai waje abinsa.





Tunda ta kwanta bini bini ya lek'ota amma sai yatarar tana bacci tajima sosai tana baccin domin kwana biyunan bata samun bacci saboda hannun.





Tunda ya shige d'akin tana jiyo irin buge bugen dayake da iface ifacen sa mamaki ne sosai ya kamata na abinda ya sami mijin nata yake abu haka kamar tab'ab'b'e,





Tun tana sa ran zai fito daga d'akin har tagaji taje ta kwanta sai dai takasa samun nutsuwa domin bata tab'a ganin mijin nata a irin wannan yanayin ba.






Sosai yanayin haj. Asma'u yabawa 'ya'yan ta mamaki domin duk iya binciken likita cewa suke lafiyan ta k'alau babu wani abu da yake damunta.



Yaune suka gama yanke hukuncin zasu koma gida ayi na garga jiya sai dai kuma yau d'inne suka ga ta tashi dan gwar gwar ta zauna asaman gadon tana k'arewa d'akin data gama tabbatar da na asbiti ne kallo.





Sosai gaban ta ya fad'i fatan ta Allah yasa baayi abinda zai tona asirinta ba.




Husna wacce ta d'ago kai tana kallon mahaifiyar tata cikin tsantsar farin ciki da kuma tsabar mamaki tace "umma?"





Sai kuma ta rungumeta gami da fashewa da kukan farin ciki tace "Allaj na gode maka Allah ka k'ara mana sutura da rufin asiri daman ubangiji baka d'arawa bawa abinda bazai iya ba sai in har shi ya d'orawa kansa.







Tare suke jinyar ta shida Yusra sai dai koda wasa baya sakar mata fuska bare takawo masa wani shirmen itama ko kallon inuwar data d'eboshi batayi sai dai aranta tashabalwashin tana warkewa zasuyita ta k'are dan dole yayi mata abinda take so ko aji kansu.







Bayan kwana uku mai gyarn ya kuma zuwa ya duba hannun aikin yayi kyau sosai, sati guda hannun yayi aka kwance d'aurin akaci gaba da shafa mata magani.




"Abubakar wai me yake faruwa ne tun kwanakifa ka soma cemin ka gano masu cin dunduniyar mu ammavharvyanzun banji kace komai akan maganar ba" wani murmushi Abbi yasaki kafin yace "ka k'ara hak'uri yaya insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe da idonka zaka ga abinda zai matuk'ar baka mamaki dan inbamu yi da gaskeba bama za'a'iya samun matsala"





"To Allah ya kyauta Allah yashiga tsakaninmu da makiyanmu" daga haka sukayi sallama.





Sosai takevsamun sauk'i dan har ta fara gwada d'aukar abu da hannun ta dawo kamar da tana shiga kicin tayi duk abinda take so, sai dai matakin farko data fara d'auka ta daina girki da su dukansu kuma tayi mugun janyewa Yusra domin sai ta kwana ta wuni babu wanda yaganta acikin su shi kuma ganin ta warke yasa ya watsar da al'a muranta ko inda take baya kalla






Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*




💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 33

.....................yau tunda garin ya waye bata fito ad'akin ba haka nan ta tashi da wani irin k'unci tunda ta idar da sallan asuba take ta faman juye juye asaman gadonta abin karima ta kasa fitowa ta dafama kanta.





Sau biyu Yusra tana lek'owa tana tambayar ko lafiya sai tace mata lafiyanta k'alau, dan haka data ga kamar bata son atakura mata sai itama ta shareta.





Sai washe gari ya fito a d'akin wujiga wujiga dashi daganin sa gaba d'ayansa afirgice yake sai dai ita intama mutum tambaya taga bai fad'a ba bata kuma bin takansa acewar ta idan najin ne tana zaune zai fad'a.





Bayan yayi wanka ya fito ta kawo masa k'osai da kunu, atake ya d'aga tangamemen cup d'in kunun ya zuk'eshi tas ya dire cup d'in, da mugun mamaki take binsa da kallo amma bata iya ce masa komaiba.





Bai ce mataba batace masa ba domin ta lura bayason fad'a mata abinda yake damunsa itama bata ce me yakevdamunsa bababu huda d'aya data lura shine yakan shiga d'akinsa na saukar masu neman temako amatsayinsa na malami yajima aciki bai fitoba.






"Duna burinka ya cika nawa ya cika dan haka ka kwantar da hankalinka ni dakaina zan kashe 'yar duna wanda yai sanadin mutuwar tilon 'yarka tak a duniya dan haka duk wani bincike da kake ka daina shi itama Asma'u na kyaleta abisa ganowa danayi tana da sauran aikin dabata kammalawa Dumb'uruba wanda ni nasaka yasakata dan haka inaso kasan cewa data gama zamu gama da ita sai mu gudanar da babban aikin nida kai akan zuriyar Ahmad".





Sosai Duna ya d'anji hankalinsa ya kwanta domin ba k'aramin bashi tsoro had'in kan Munzali da Dumb'uru ya bashiba, domin shi wani irin shed'anin mutum ne da baisan wani abu waishi imaniba, zai iya komai akan biyan buk'atar sa.





Yace "angama mai girma Gaza indai wannan abun zai tabbata ni kuma zan temaka miki ki cimma burinki nazama shugabar matsafan wannan yankin, wanda ta hakane zaki rama abinda wanda muka kwatoki hannunsu suka miki".






Wani matsiyacin murmushi ta saki tace "shike nan zaka samu yadda kake so dan haka jeka ci gabada sha'anin gabanka.





Tunda take saukowa daga saman yake kallonta afakaice batare da yabari tagane yana kallontaba ita sam bata ma kula dashiba saida tazo dab dasu sannan ta kula da su suna had'a ido da Yusra ta d'an sakar mata murmushi, ta wuce batareda tace komaiba.




Baisan sanda ya buga wani uban tsalle yasha gabanta ba yana kallon cikin idonta wanda fir ita tak'i yarda ta kalleshi tayi masifar had'e rai ba kuma tace masa komai ba, shima bai ceba sai hannunta da ya kama ya maida ita d'akinta kafin yace.



"Yanzun ke dan tsabar baki da hankali a haka zaki fita dubafa kiga kayan dayake jikin ki wato ga d'an iska kina aure bari kiyi shigar da duk ranki yake so ki fita masu aiki suna kallonki ko?"







Jikin nata tabi da kallo, sanye take da fara kar d'in 'yar shet me hannun shimi sai wandan da yakai mata har kwairinta ita sam bataga aibun shigarta ba domin kayan bawai irin sun kamata d'innan bane sai dai sun mata cif cif kamar dama an gwada tane.




Kallon sa tayi ranta a matuk'ar had'e kafin tace "wai ina ruwan ka da harka nane ni banshiga nakaba inba shishi giba ni banga dalilinka nason sai ka shiga nawaba dan Allah ni kasamamin lafiya haba jabi ka addabeni ka addabi rayuwana ka barni mana nima na shak'i iskar 'yanci"




Ta k'arasa tareda fashewa da kukan dataji ma tana tarashi, shi kam tagumi ya zuba yana kallonta da mamakin kalamanta sam baiga wani abu daya mata natakura ba saidai bazai lamunci tafitar masa a hakaba wasu banzaye suyi ta kalle masa ita a haka ina sam bazai sab'uba bindiga a ruwa.






Batare data hankareba ya fisgota jikinsa ya had'e bakinsu yana mata wani irin salon dayasa dole tayi lub a jikinsa.





Sosai yayi missing d'inta dan haka bai mata da sanyiba saida ya fanshe duk wani bashi daya san ya ci, domin Fatima ba irin matan da ake iya dogon fushi dasu bane.










Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*_____________
_______________________*






💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKSAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 34

...................bayan yagama samun dukkan nutsuwar da yake buk'ata atareda ita ne yajata jikinsa ya k'amk'ameta, wannan halayyasa ne matuk'ar zai sauke wani nauyi sai yayi kamar zai ballaki tsabar ruk'on da zai miki.





Fahimtar da yayi Fatima tafara bmfushi dashi ne badan ta dainaba yasaka shi ajiye nasa girman kan agefe ya zage yake baje duk wata fasaha tasa akanta a duk lokacin da yake d'akinta.






Tunda aka
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*_____________
_______________________*






💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKSAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 34

...................bayan yagama samun dukkan nutsuwar da yake buk'ata atareda ita ne yajata jikinsa ya k'amk'ameta, wannan halayyasa ne matuk'ar zai sauke wani nauyi sai yayi kamar zai ballaki tsabar ruk'on da zai miki.





Fahimtar da yayi Fatima tafara bmfushi dashi ne badan ta dainaba yasaka shi ajiye nasa girman kan agefe ya zage yake baje duk wata fasaha tasa akanta a duk lokacin da yake d'akinta.






Tunda aka sallamo ta daga asbiti suka kasa gane kanta ta zama wata irin shiru shiru duk fad'a irin nata yanzun duk abimda yaran zasuyi sai dai tabisu da kallo, sosai abin ya damu yaran nata domin sunsan cewa uwar tasu bata da hak'uri ko kad'an.





A bangaren Fatima kuwa tunda ta fahimci cewa ta haka Abdulmajid yake son hukuntata sai tayada makaman yak'inta sai dai tasha alwashin tanaji tana gani bazata bari akansa a wani salwantar mata da rayuwaba hakane ma yasa ta dage sosai da addu'a dan sosai take jin tsoron abimda zai iya faruwa nan gaba tunda dai bawai an k'yalesu bane.






"Tunda muka had'e kai da kai nasan dole Gaza zata nemi Duna kuma kasani 7sarai bala in Duna ya wuce tunanin mu mu duka tunda shi masanin qur'ani ne sannan mahaddaci kaga yasan komai dan haka nake so ka nemeshi kafin ita kaga ni mun d'an samu matsala kwanakin baya"




Cikin,damuwa Munzali ya fesar da wani zazzafar iska ya d'an dafe kansa yana kallon Dumb'uru kafin yace.



"Akwai matsala oga nasan kasan abinda yafaru akan 'yarsa dana bawa qungiya jininta yanzun haka idanunsa suna kan 'yata Hauwa dan Allah ka san hanyar dazaka b'ullo masa inajin yarinyar sosai"



Ya k'arasa maganar da matsanancin damuwa afusakarsa, sosai Dumb'uru yayi shiru cikin dogon nazari shi kansa akwai binciken da yayi akan yarinyar kuma jininta yayi daidai da cikar burinsa, sannan baiyi zaton inya nemi abinda yake so game da yarinyar za'a sami masalaba ganin cewa bata hanyar aure yasamu yarinyarba, amma a zahiri sai ya nuna masa zai temaka masa wanda ba hakanne aransaba shima.






"Ku shirya dukanku zamu je bajoga duba gwaggo Hafsatu bata da lafiya" cewar Abdulmajid da yafito cikin sauri ya shige d'akinsa.



Da murna,suka tashi kowacce tashiga d'akinta dan shirin, ita Fatima tana murnan yau zata wataya yayin da Yusra wannan ne karonta na farko dazata je bajogan.





Sanda suka fito tun ya gama shirinsa ya d'an dubesu yace "kowaccen ku ta koma d'akinta ta d'auko kaya kala d'aya kunsan bazai yiyuwa muje yau mu dawo ayau d'inba"





Sosai suka d'auki hanya tun suna hira har Fatima wacce tasa rigimar ita zata jasu tagaji yace Yusra ta karb'a itama ta d'ana.





Tunda Yusran ta,karb'i tuk'in Fatima ta koma bayan ta kwant, ta bungire ta kama bacci yayin da su kuma sukaci gaba da hiran gabansu.





Sosai baccin yayi mata dad'i tana tsaka da baccin taji ana goga mata abu kamar gashin mage (kyanwa/ mussa) ta d'an bud'e idanunta cikin yanayin bacci me zata gani wata jibgagiyar magece kwance ajikinta yayin da idanunta suka kasance wani irin fari k'al gwani tsoro Sosai jikinta yakama rawa, takai dubanta kan Yusra da Abdulmajid da suke ta hiransu suna shek'ar dariya abinsu saida abinda ya kuma mugun kad'ata zakinnan ne wanda ta tab'a gani awannan hanyar ta bajoga kuma adaidai wannan wajen dayabisu har gidan gwaggo Hafsatu yauma shine amma cikin motar su yasaita wuyan Yusra da wata sharb'eb'iyar wuk'a




Suna had'a ido sai taga kamar ma yana mata dariya haba wani irin razanannen ihu Fatima ta saki wanda yasanadin da motar ta kwace a hannun Yusra tatafi ta daki wani k'aton dutse take motar takife da su innlillahi wainna ilaihi raji un.





Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*





💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN

13 / 20