Author : MAMAN ISLAM Category : KDP NOVELS
barkatai tayi ta kirama amma amsar d'ayace a kashe take.
Sosai hankalin ta yai mummunan tashi yau kusan sati guda kenan ta daina samun mai gidannata a waya tun bayan daya tabbatar mata yana hanyarsa na dawowa washe gari tundaga ranan bata k'ara samunsaba.
Da sauri ta d'auko wani jan k'yalle ta d'aga kasan gadonta ta d'auko wani kaskon wuta na k'arfe ta shinfid'a kyallennan akan kaskon ta kawo garin magani ta zuba saiga hayak'i mai masifar k'auri yana tashi sosai hayak'in ya turnuk'e d'akin sannan kuma,ya soma washewa, wata irin guguwace mai k'arfin gaske ta hau tashi daga daga saman kaskon saiga fuskar Gaza tana wata irin dariya wanda take dariyan ta d'agawa Asma'u hankali, domin har idan kaga dariyan Gaza ta shirya wani mugun abunne, ilai kuwa tayi mata nuni da bango saiga mahaifin Asma'u a hannun Gaza tayi masa wata irin shak'a sai kakarin mutuwa yake kafin tace "idan ya wuce kwanaki uku baki bani jinin mijinki ba to da d'aid'aya saina k'arar da duka danginki kafin injuyo kanki inyi miki kisan wulak'anci kisan da zaki tozarta a idon duniya wannan shine k'arshen me kwad'ayi dama masu karin magana sukace son zuciya b'acin zuciya"
Daga haka ta b'ace b'at
Take Asma'u ta fashe da wani mugun kuka da sauri ta toshe bakinta dan kar ta taso yaranta da suke bacci kuka take mai k'arfin gaske kafin ta mik'e tana kaiwa tana kawowa.
Munzali ban mutuba kuma nice ajalinka badai kun tsafaceniba kuna tunanin kuke da duniyar to Allah shine me duniyar kuma shiyaga dama ya ara muku lokaci kuke yanda kuka ga dama ina tausaya maka randa dubunku ya ciki sannan ina mai farin cikin sanar dakai cewa har yanzu abunda kuka mayar Allah naku baiyi nasarar kashe hajiya zakiyya da babban d'ankaba kuma sune ajalinka suna ajalinka sune ajalinkaaaaaa,
A mutuk'ar gigice yatashi daga baccin da ya kwashe shi yafara dube duben d'akin yayin da jikinsa yake wata irin rawa da sauri ya maida hankalinsa inda yaga kamar inuwar mutum saidai baiga komaiba.
Fashewa yayi da kuka yana fad'in na shiga ukuna ni munzali wane irin fitina wannan tsinanniyar Muniran take,son jazamin? sani na dake bai amfanamin komaiba Munira sai wahala tarrayata dake nema yake ya haukatani ko ya tonamin asiri kifita hanyata Munira ko na wulak'anta fatalwarki, baccin da bai komaba kenan ya kwana sumbatu.
Fatima kuwa tun ranan da suka raba raini da Abdulmajid koda wasa bata sake ta k'ara yarda sun keb'e daga ita sai shiba domin kuwa taji 'yan maza.
Yayin da shi kuma abin yana damunsa ya fahimci indai tasan ranan girkintane take rufe k'ofa amma ranan girkin Yusra saitaga dama zata rufe wannan abun yana damunsa dan haka shida kansa ya shirya mata dabara ta hanyar hargitsa mata lissafi nan kuwa lissafin ya kwace mata da haka ya samu ya shiga d'akin nata ranan ma ba karamar wuya tasha a hannunsaba
Muje zuwa
Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 24
.........................washe gari da safe da ta tashi ko kallon inda yake batayiba bare yasaka ran zata gaidashi, dan acewarta wannan baso bane mugunta ne ana fad'in ina sonki kuma ana gana mata masifar azaba?
Kasan cewar wannan karon bata sha azabar datasha irin ranan farkoba tama rigashi ficewa daga d'akin ta wuce kicin ta had'a abin kari sai dataci ta k'oshi sannan ta koma d'akinnata da nufin gyrawa.
Turus tayi tareda turo baki ganinsa kwance d'ai d'ai asaman gadon ko alamun tashi bashi dashi baccinsa yake kashirban.
Cikin sand'a ta nufi gadon ta d'an lek'a fuskarsa ta d'an zaro ido tayo baya da nufin komawa yai saurin rik'ota yana mata dariya.
Kukan shagwab'a ta fashe masa dashi, shi kuwa fisgota jinkinsa ya k'amk'ameta yana shak'ar k'amshinta.
Cikin alamun tsoro tace "ni kasakeni gyara d'akina nazo nayi"
"Ainima gyaran auren zamuyi irin najiya" yafad'a da irin muryarta, kafinma tayi wani yunk'uri ya had'e bakinsu yafara mata salonsa mai saurin rikitata, yauma saida ta jijjiga a hannunsa kuka kuwa sai da tayishi ta godewa Allah domin kuwa ba da sauk'i Abdulmajid yake zuwar mataba.
Tundaga lokacin Abdul ya manne mata ya wani zamar mata kamar wani mayen k'arfe duk ranan kwananta kuwa kusan kullum sai ya makara aeajen aiki.
Sosai fitinarsa ya damu Fatima datayi k'orafi kuma yace cikin data nema yake son bata, tayi nadamar wannan furucinnata yafi sau ak'irga.
Koda suka je gida Ummi taga 'yarta duk ta zuk'e ta k'are tasata ad'aka tana tuhumarta dafarko taso b'oye mata amma data matsa kuma taga bata da k'awa ko aminiyar dazasu tattauna matsalanta daya wuce Ummin sai tafad'a mata sosai kuwa Ummin taba shawarwarin dazata k'aru tareda bata magunguna masu matuk'ar kyau da amfani.
Bayan kwanaki biyu da maganarsu da Gaza aka aiko mata mahaifinta babu lafiya sosai hankalinta ya tashi irin wanda ko 'ya'yanta basu tab'a ganin ta shiga damuwa irin hakaba.
Koda taje asbiti babu yanda yake kuka kuwa saida tayishi har taji babu dad'i nadaman shiganta wannan k'ungiyar kuwa tayishi yafi a k'irga.
Gaza kidakatar da wannan shirin da kikeyi domin wannan hargitsa mana mutanen da kikeyi nasan akwai abinda kike son cimma Gaza sanin kankine abinda Asma'u da Munzali sukewa qungiya zai wahalan gaske mu sami zakwak'uran da zasu iyashi na fad'a miki da babban murya karki kashe mahaifin Asma'u wanda kikeson yin hakan abisa son zuciyarki.
Kuka Gaza ta fashe dashi kafin tace "duk da cewa aikina ya riga da yayi nisa banso ka ganoni da wuri hakaba shugaba DUMB'URU saidai ina mai sanar dakai cewa na rigada nayi nisan da bazanji kiraba saura k'iris na zama sama da kowa a wannan k'ungiya tamu kuma na gagari kowa dan haka ni yanzu shugabar kainace babu wani wanda ya isa yasani ko ya hanani daga haka ta b'ace b'at tabar wajen.
Tunda tabar wajen yake tsaye cikin tsantsar damuwa baitab'a tunanin aljana gaza zata juya musu bayaba duk da irin temako da kulawar da suke bata sannan suna mata duk abinda take buk'ata duk dan tsoron zuwan irin wannan ranan.
Shima b'acewa yayi ya nufi wajen boka Duna nan yasameshi shima cikin tashin hankali Gaza ta ziyarce shi sannan shi kuma tasanyashi wani aikin wanda tace matuk'ar baiyiba bazata tab'a taimaka mishi yacimma burinshi akan Munzali ba tofa k'ak'a tsara k'ak'a?
Tundaga bakin get yake jiyo hayani yansu ba kamar muryan Fatima data na kowa tashi da sauri ya k'arasa ya d'auka wani abunne yafaru yanda yaji tana ihu tana fad'in ita wallahi bazata yardaba dole itama abata tata.
Turus yayi ganin Meema zaune tana faman kallon Fatima datake fad'in "wallahi bari nima honey ya dawo yasin yakaini gidan dan anga bananan sai adinga abu babuni,an maidani barema kenan"
Meeman ce tafara ganinsa tsaye ya rik'e qugu yana kallon Fatima dake ta zuba mita batasan ma da zuwansaba, saida Meema tayi masa sannu da zuwa sannan ita ta juyo kafin kuma ta kwasa da gudu ta shige jikinsa
" tace yauwa honey na sannu da zuwa"
Amsata yayi tareda manne mata kiss agoshi yana fad'in "ina 'yar uwar takine?"
Tace "tana d'aki tana wanka, sannan taci gabada da cewa mijina dan Allah ka kaini gida wajen Daddy nima sai ya siyamin irin motar da yasiyawa Meema, kagafa irin motar danake mafarkin samune ni bansoma Meema ta rigani mallakan taba wallahi"
Ta k'arasa maganan tareda d'an turo d'an bakinta gaba, saida ya tsotsi bakin kafin yace "to kin tab'acemin kina sone?
Hararan wasa tayi masa kafin tace "lallaima honey kai yanzu dan Allah sai nace maka ina son abu kai ko irin bari naga d'an abu mai kyau na gayu bari na kaiwa matana baka tab'a yi manaba ai masu iya magana sunce ko kana da kyau ka k'ara da wanka"
"Zokiji" abinda yace mata kenan yajata sukayi samansa suka bar Meema anan falon, wanda itama datagaji da zaman jiran tayi tafiyarta.
Aidai yau nayi kokari banifa dalafiya wallahi amma nayi har sau biyu
Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 25
..........................basu suka saukoba sai bayan sallar magriba lokacin tuni Meema ta manta da komawa gida.
Saida ta d'an dubi inda sukabar Meema kafin ta zaro ido tace "na shigesu ni jikar shatu"
Kallonta yayi ya tambayeta da ido lafiya?
Tace "kagafa Meema tayi tafiyarta shikenan zataje ta yad'ani adangi kamar tsumma, tace tazo gidana na shareta"
Ta k'arasa maganar da d'an damuwa akan fuskarta,
Kamota yayi ya d'an sakata ajikinsa kafin yace "idan tayi zuciya itama ta hak'ura dakaratun yayi auren kinga itama sai ji abinda mukeji ko?"
Ya k'arasa maganar yana kallon cikin idanunta, turo d'an bakinta tayi gaba tareda d'an bubbuga k'afa kafin tace.
"Gidan fa nakeso kakaini wajen Daddy yanzu nakarb'i motana nima"
Kallon ta yake da mamakin ta wani lokacin mamaki take bashi idan ta dage tana wani abun
Yace "yanzun ke Fatima ni bazan iya siya miki motaba sai kince Daddy ya siya miki salon suga gazawata ko?"
Turo bakin ta kuma kafin tace "yo ni bangani ba da watana nawa agidan wata nafa hud'u agidannan amma ko d'an gift d'innan na amarci baka saiminba" takarasa maganar tareda manne fuskanta a k'irjinta alamun jin kunyar abinda ta fad'a
Sosai yake kallonta da mamakinta domin abin na Fatima azimunne wani shu'umin murmushi yasaki tareda shafar fuskanta baidai ce mata komaiba ya juya ya fice.
Zaune suke ita Yusran kafin Yusran ta mik'e ta nufi d'aki tana fad'in bari nayi wanka Teema nazo nabaki labarin danace zan fad'a miki wallahi sai cikin ki ya k'ulle dan dariya.
Da gudu Husna tafito daga d'akinsu tana ihun neman temako Anwar tafara karo dashi tace "mun shiga uku yaya zokaga umma zata mutu wallahi mutuwa zatayi aman jini takeyi"
"Jini?" yafad'a arazane tareda tureta yai b'angaren nasu da gudu itama ta rufa masa baya tana matsanancin kuka.
Sanda suka shiga tuni ta sume domin ta riga data gama galabaita da gudu ya sungumota sukayi waje.
Kuka take ta rusawa tana salallami tareda fad'in "o duniya wai ace makashinka yana tareda kai ni Rukayya mamaki zai kasheni wallahi"
"Ya kashekin" Alh. Umar yafad'a amutuk'ar fusace sannan ransa a mutuk'ar b'ace, cigaba yayi da fad'in "wallahi Rukaiyya sabon halinkinnan ya ishenifa 'yan kwanakinnan kullum da kalan abinda zan gani me yake faruwa?" yafad'a cikin daka mata wata irin mummunan tsawa wanda tsabar firgici batasan lokacin datace
"Matsafa"
Plss manage
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 26
.......................a mamakince yake kallon matar tasa data riga gama rud'ewa yace "matsafa kuma?
A ina kuma meye had'inki dasu?"
Dake bata tareda nutsuwanta sam bata gane me yake cewaba kukanta kawai take casa.
A mutuk'ar hasale ya buga mata wani mugun tsawa yace "dallah malama kija baki kirufemin ki fad'amin abinda yake faruwa kin wani zauna sai kukan banza kikewa mutane"
Agigice tace "dan Allah kayi hak'uri nima bansan ta ina zan fara fad'a maka wannan mummunan labarin mai almaraba"
Ganin yadda ta gigice ne yasa ya kama hannunta cikin nutsuwa ya zaunar da ita sannan ya d'ebi ruwa mai sanyi yabata tasha sannan zauna akusa da ita ya rik'o hannunta yana murzawa a hankali ya soma magana kuma cikin nutsuwa.
"Rukaiyya ki nutsu ki fad'amin abinda yake damunki suwaye matsafan a ina kika gansu kuma me had'inki dasu har suke neman haukataki?"
A firgice tad'ago idanunta da suka gama rinewa tsabar kuka ta zuba masa kafin tasaki wani siririn kuka,zuciyarta na wani irin bugu bata san cewa firgicin data shiga har yakai tona abinda batason bayyanu warsa yanzuba batasan cewa duk nuk'u nuk'unta da son k'warara hujja akan abinda takeyi tana neman fasuwaba sai yanzu datake jin wannan tambayoyin awajen mijinnata, wata dabarane tafad'o mata ta d'an gyara zama tareda goge gutun hawayen ta dubeahi cikin tsaban damuwa tace
"Abban Salim ina cikin wani hali bana tareda nutsuwata 'yan kwanakinnan abinda nake gani yana matuk'ar firgitani wallahi Abban Salim matsafane"
"A ina?"
Yayi mata tambayar tace "a mafarkina mana kamar ido biyu haka nake ganinsu wani lokacin"
Wani irin takaicine ya kama Alh. Umar wai duk wannan mummunan d'aga masa hankalin datayi duk mafarkine tayi, dubanta yai cikin takaici yace
"Sakaci kawai da addu a da ace kuna addu a yayin dazaku kwanta ai da hakan bai faruba jiba dan Allah yanda abin yake tasiri akanki to da ace kuma yaranki sunanan kike wannan sakarcin kice musu me?"
Sosai yayi mata fad'a fad'a nasiha nasiha sannan ya jadadda mata ta daina sakacin addu a.
A can asbiti kuwa tunda aka kai haj. Asma'u likitoci suka rufu akanta suke ta aikin ceto ranta amma wanda yai nasara duk wani gwaje gwaje daya kamata suyi sunyi abinda saka makon yake basu lafiyanta k'alau, kwanaki uku suka shafe suna abu d'aya amma amsar duk iri d'ayane
'Ya'yanta kuwa ba k'aramin mummunan tashin hankali suka shigaba dan ganin halin da mahaifiyarsu take ciki.
"Anty Yusra yau ki shirya muje mu dubo umma ance andawo da ita gida"
Tun kafin tace komai Abdumajid da shigowansa kenan yace "babu inda zakije k'afan yawo"
Idanu tazaro tace "saboda me?"
Shima nasa ya zaro mata yace "saboda haka nayi niyya"
D'an b'ata rai tayi tareda matsowa kusa dashi ta rik'o hannunsa tace "haba masoyi haba nawan wai dan Allah me yasa kake min hakane duk sanda nace maka zan fita saika hana ko gidama fa sau biyu kacal na tab'a zuwa amma anty Yusra da kanka kake kaita, koda yake dama ni ai tura makani akayi itako auren so kukayi shiyasa bambancinka mu ma mabayyani ne"
Daga haka ta sakar masa hannu tareda fashewa da kuka tayi hanyar d'akinta da gudu da ido ya bita har ta banko k'ofar da mugun k'arfi ya sauke ajiyan zuciya kafin ya k'arasa kusa da Yusra ya dafa kanta yace "baby kuna lafiya?"
A sanyaye tace "lafiya lau" tana shirin tashi ya rik'ota yace "kema tafiyan zakiyi kibarni in ita yarinya ce aike da hankalinki, in fad'a miki wani abu Yusra?"
D'an dubansa tayi batareda tace masa komaiba yajata jikinsa yace "Yusra duk abinda yake faruwa dani akwai sa hannun wasu daga cikin mutanen gidanmu, shiyasa kikaga bana son Fatima ta cika yawan zuwa gidan yanzu har sai komai ya lafa ita kuma take d'aukan hakan da wani manufa na daban.l"
Da matuk'ar mamaki Yusra take kallon Abdulmajid jikinta yana wata irin rawa ta k'amk'ameshi tareda fashewa da wani irin kuka rik'eta ya kumayi sosai yana rarrashinta ta d'an jima tana kukan kafin yasamu tayi shiru.
Ita ko Fatima tunda ta shiga d'aki take ta tisgar kuka tarasa me yasa yake mata haka agabanta Yusra zata tambayi zuwa gidansu yasata agaban mota yakaita wani lokacin ma har da Fatiman zasu kaita amma ita data tambayi gida sai yace ba hakaba gaskiya wallahi tagaji da wannan kisan mummuk'en da yake mata.
Da yake ranan ba ita ke da girkiba ko d'uriyansa bata jiba n
bare tasa ran zai rarrasheta hakan kuwa ba k'aramin k'ona mata rai yayiba.
Washe gari tana tashi ta gyara d'akinta tayi wanka ta shirya cikin wani mini tree quater da wata 'yar best kayan sunyi mugun amsarta badan tanajin mugun yunwaba da babu abinda zai sa ta sauka k'asan, kasancewar jiya bata samu daman cin abincin dareba yasa ta tashi da matsanancin yunwa.
Suna dirning suna ka break suka jiyo k'aran takun cokalan takalminta duka suka maida hankali kanta, suman zaune Abdulmajid yayi domin ba k'aramin tafiya da tunaninsa Fatima tayiba tunda tazo gidan bata tab'a yi masa irin wannan shigan ba.
Ko kallon inda suke batayiba bare su saka ran zata kulasu ta wuce kicin indomie ta dafa had'e da soya k'wai guda biyu anan kicin d'in ta tsaya ta cinye ta d'auraye flat d'in juyowan da zatayi suka gabza karo dashi wanda tunda tafara cin abincin yake tsaye yake kallonta d'agowa tayi ta zuba masa idanunta na d'an seconds kafin tajanye tareda rab'ashi zata wuce yayi saurin rik'ota.
Iya k'arfinta tasaka da niyan kwacewa sai dai ina k'arfin ba d'ayaba dan haka tsaya kawai tareda fashewa da kuka tace "ni ka cikani ina da abinyi"
Kallon cikin idanunta yakeyi wanda suke cike taf da hawaye kafin yasanya hannu yana share mata hawayen tareda fad'in "ni banga abin kuka ba tunda babu abinda nayi miki"
Itama kallonsa tayi tareda mamakin rainin hankali irin nasa yo rainin hankali mana inbanda rainin hanka duk irin abinda yake mata amma yace baiga abinda yai mataba, lallai ma mutumin nanan.
"Cikani" ta kuma fad'a cikin zafi "ai kina da k'arfi" yafad'a cikin kallon idanunta sannan kuma ya d'an jata jikinsa cikin lallashi yace
"Haba babyna wai duk fushinne tun jiya har yanzun baki huceba?"
Wani banzan kallo ta watsa masa batareda tace masa komaiba, yasaki wani k'asaitaccen murmushi yace "to shirya muje shikenan?"
Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
💦💧ZATO NE💧💦
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 27
..........sosai hakan yayi mata dad'i ta haye saman da d'an gudunta, tayi saurim shiryawa sukabar gidan cikin nishad'i hannunsu sak'ale da juna.
Bai kaita gidanba, yawo sukai tayi gidan abokansa har kusan k'arfe tara lokacin tuni Yusra ta jima da dawowa, tana zaune afalo tacin indomei ta d'an kallesu ta maida kanta yayin da takejin wani abu aranta.
A hankali ya k'arasa kusa da ita ya zauna tareda rik'o hannunta yakai abincin data d'ebo bakinsa tareda lumshe idonunsa akanta yana fuskantar yanayin ta kamar tana cikin damuwa.
"Gaza a daina wahal da Asma'u haka gaza domin ita domin tana da matuk'ar mahimmanci atareda mu"
Idanunta ta bud'e yagansu wani yellow shar dasu saida